Showing 33001 words to 36000 words out of 50455 words
Chapter 12 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf
kicin fannah ta nunawa yarinyar Mai suna Nana bayan tayi Mata bayanin
aikinda zata riqayi.
Tunda Nana tazo gidan ayyuka sukayi ma fannah sauqi Dan tuni takoma aikinta na office Dana
harkokinta da mazanta.,
Yau Kam kwance take zuciyarta a dagule sbd kukan data kwana tanayi Wanda kusan kullum
saitayisa kafin ta kwanta...
Shiru tayi tana tunanin rashin adalci irin na zuciyarta data kasa cire Deen aranta duk da
yaudararta dayayi tareda cin amanarta ya gudu yabarta cikin mummunan Hali.
Fannah ce tashigo 'dakin cikin shirinta na zuwa office ta kalleta cikin sanyin jiki sbd itama
kwanakin hakanan takejin ranta ba da'di.
Ina kwana anty""""tace murya a sanyaye.
Lpia klau ayshah ya jikinki hope dai bakyajin komai?
Kai ta 'daga tareda tashi zaune ta sauko gadon tana Shirin miqewa tsaye taji takasa yunqurawa
sbd riqewar da bayanta yayi tayi saurin kallon fannah cikeda tsoro tace,
Anty bayana nakasa miqewa..
Wat''''fannah tace da sauri tareda aje handbag da keys 'din hannunta ta matso tana riqota....
Ya salam'' anty bayana da cikina....
A ki'dime fannah tace,
Ayshah bansani ba ko haihuwace Bari muje asibiti kawai idanma ba itabace Sai muji meyene.
Nana ta qwalawa Kira da qarfi saigata ta iso Nan suka kamota suka saka mota Sai asibiti...
Tashin farko nurses na karbarta sukace haihuwace Nan aka Kira doctors suka shige labour
room da ita aka barsu anty fannah cikin fargaba Dan Koda suka iso asibitin ciwon yayi mugun
tsanani.
Abu kamar wasa haihuwa taqi zuwa ga azabar datake ciki tayi yawa Suma doctors 'din dakansu
suna tausaya Mata Amma sunyi iya yinsu haihuwar taqi zuwa Sai naqudar wahala takeyi..
Ganin ana neman rasa uwar da babyn yasa suka yanke shawarar yimata aiki cikin qanqanin
lokaci fannah tasa hannu tabiya komai aka shiga tiyata da ita.
Alhamdulillah cikin ikon Allah ansamu nasarar aikin anciro Mata qaton lafiyayyan balaraben
'danta daya 'dauko komai na ubansa.
Tunda aka miqowa fannah shi takallesa cikin showel na jarirai taji wani mugun so da qaunar
yaron tashigeta ta rungumesa tana Jin hawayen tausayinsa na gangaro Mata.
Ayshah Bata farkaba Sai gab da asuba Kuma tana farkowa babynta tafara tambaya fannah ta
miqo matashi tana kar6arsa taji wani farin cikinda rabonta dashi harta manta,
Cikin tsananin sonsa idanuwanta suka ciko da hawaye cikin farin ciki tace,
My junior Deen,
My love,
My happiness,
My mistake,, you're my everything now my sweet boy...
Murmushi fannah tayi tareda matsowa ta shafo fuskarsa cikin so tace,
Ayshah is now a mother...
Dariya tayi tana kallon face dinsa tace,
Yes I'm a mother now but not only me,, you're his mother too.
Nana daketa faman murna ta matso ta kar6esa cikin tsananin farin ciki tace,
Anty ayshah babyn Nan yanada kyau sosai Amma dai ni Zan ringa goyashi ko?
Eh Nana harsai kin gaji da goyo sbd ayshah makaranta zata koma da zaran yafara wayo.
Cikin tsananin farin ciki ayshah takalli fannah tareda cewa,
Anty da gaske?
Yes ayshah coz already admission letter 'dinki is in hand.
Thank you""""tace tareda kar6ar ruwa da brush 'dinta take miqo Mata.
Kwanansu uku a asibiti aka sallamesu suka koma gida..
Koda suka koma gida ayshah tayi mamakin ganin maqwaftansu na shigowa barka harda friends
'din fannah duk da wasu daga cikinsu ba masu kimtsi bane Amma hakan ya sanyata farin ciki
koba komai sun nuna farin cikinsu sa6anin iyayenta da uban 'dan dasuka gujesu.
Koda suna yazo ba wani taro dasukayi andai yanka raguna tareda ra'da Masa suna
_Mahmud_,.
Tun bayan haihuwar Mahmud komai na rayuwarta ya canxa ta 'dauki dangana da hakuri tabawa
zuciyarta duk sbd farin cikin 'danta,,
Tsananin son datake yiwa Mahmud yayi yawa Dan ko kukan ciwo ciki ko wani Abu yake itama
zaunawa take ta darza kukanta.
Gata soyayya da tsantsar kulawa yaron kesamu daga ayshah har fannah Dan kullum cikin
yimasa shopping take,,,ko Nana ba laifi tana tsananin qaunar yaron sbd kyansa kamar yanda
tace,.
Ganin irin yanda fannah ke kashe musu ku'di ba sauqi yasa tayi tunanin fara zuwa makarantar
da fannah ta nemar Mata sbd kotayi saurin gamawa ta samu aiki Dan ragewa fannah lalura.
Mahmud nada shekara 'daya da wata biyar ta yayesa tafara zuwa makaranta bayan uwar
siyayyar Kaya da 'dinkuna da fannah tayi mata ciki harda Bata motarta 'daya.
Shigarta makaranta ya qara canza rayuwarta kwata kwata Dan kuwa Sam Babu Wanda zai
ganta yace ayshan gidansu malam babba ce sbd wayewar datayi da wani mugun Jan class
daya shigeta uwa uba ayshah Bata 'daukar reni ko ka'dan yanxu,,
Duk wani kyanta da kyawun fatarta ya da'du Dan bazaka ta6a cewa ta ta6a haihuwaba kullum
ka ganta cikin gayu take danko fannah yanxu Sara Mata take a fannin gayu da qwalisa.
Duk wannan abin da'ake maza tsoron tunkararta suke sbd tsoro da fargabar kwarjininta da cika
idonta dakuma fuska dabasu ganiba.
Qawarta 'daya a school 'din Mai suna Aisha itama Amma shanty ake kiranta,,
Shanty 'yar tsohon ministern ku'di ce kuma ita ka'dai iyayenta suka Haifa Wanda gata da ku'di
suka lalatata ta hanyar shaye shaye da yawon club duk da dai Bata ta6a iskanciba a taqaicema
batada saurayi ko 'daya Dan Bata kulasu shiyasa ayshah ke matuqar qawance da ita batareda
tasan tana shaye shayeba.
Fannah zuwa lokacin girma ya'dan fara zuwar Mata ta aje komai ta rungumi aikinta dasu
ayshah amatsayin iyalinta da nauyinsu ya rataya kanta musamman ma Mahmud da yanxu yafi
Zama da ita sbd rashin zaman ita ayshan.
Yau batada Lectures ko 'daya Dan haka tana gida sunata nisha'di a palon itada anty fannah
suna fira Nana nata wasa da Mahmud Sai tsalle yake Yana dariya.
Kallon fannah tayi tace,
Anty fannah Dan Allah kibawa Yaya Ibrahim dama Mana Kinga Yana tsananin sonki after all
Mahmud fa Yana son yaje agolanci"""""ta qarashe zancen cikin tsokana.
Dariya tayi tana kallon Mahmud 'din tace,
Yaron mummy zonan,,
Da gudu yazo gurinta tareda fadawa jikinta tace,
Anty ce tace Wai zakaje agolanci?
Batareda yasan metake nufiba da agolanci yace,
No I don't want to go..
Kamosa ayshah tayi jikinta tace,
Amma ai kanason dady ko?
Eh"""yace Yana tsalle tareda yiwa Nana gwalo...
Qaran doorbell yasa Nana miqewa taje tabude saiga shanty tashigo taci kwalliya tayi kyau harta
gaji Dan itama ba laifi kyakkyawace farin ayshah ne kawai batayiba.
Da gudu Mahmud yaje yafada jikinta Dan yasaba da it's sosai sbd itama tana tsananin qaunar
yaron ta 'daga qatuwar ledar hannunta sama tace,
Guess wat it s.,,,
Cheese''''yace Yana tsalle.
Girgixa Kai tayi tace,
No.
Ice cream ayshah tace tana kallon ledar.
You failed too'''""shanty tafada Mata tana hararanta.
Mangwaro da yalo"""""Nana tafada tana wage bakinta cikin murna..
Dariya suka sake dukkansu shanty kuwa cemata tayi,
Comon keep quiet ai bakinki ne magoes 'din.
Chocolates and shortbreads..anty fannah tafada Masa qasa qasa.
This is cheating anty fannah""""shanty tafada tana miqa Masa ledar tareda Zama kusada
ayshah dake miqe a three seater sanyeda black pencil jins da farar armless top 'din shaking
material gashinta a 'daure tsakiyar Kai.
Anty ina wuni?
Lpia qlau Aisha ya gida da mum.
Fine anty please zamuje kar6an 'dinki a wuse market.
Kallon ayshah tayi ayshah tayi saurin cewa,
Allah is not a plan Nima yanxu nakeji abakinta.
No ayshah ba Ina hanaki fita bane you know wat is in your head Ina tayaki Kare wannan
martabar ne sbd gujewa mummunan alamari Nan gaba.
'dan 'daure fuska tayi zuciyarta na zafi sbd koda wasa batason tuno duk wani alamari daya shafi
Deen.
Bedroom suka shiga da shanty ta canxa Kaya zuwa doguwar rigar wata red atampa Mai adon
blue ta zaro blue Vail ta yafa batareda 'dankwaliba ta 'dau wayarta suka fito Mahmud yataso
yace saiya bisu hakanan taji gabanta yayi mummunan fa'duwa tace,
Sweetie kazauna gida gurin mummy Mana idan zamu dawo I promise to buy ice cream for you
my boy.
Maqe kafa'da yayi Yana Shirin yin kuka tajuyo takalli anty fannah sbd baita6a cewa saiya bitaba
idan zata fita yafi yiwa anty fannah haka.
Riqosa anty fannah tayi ya fashe da kuka tareda fa'duwa qasa Yana Shure Shure.
Kamo hannunsa shanty tayi tareda tayardashi ta 'daukesa takalli Nana tace,
Jeki 'dauko hijab dinki muje ki riqesa.
Da gudu Nana ta 'dauko Dan akwaita dason yawa da wasa Dan akwai sauran 'dabi'un qauye
atareda ita.
Tunda suka fito tayi tsit gabanta na fa'duwa hakanan taji hankalinta na tashi
Shanty dake driving ta juyo ta'dan kalleta tace,
Whats wrong eshaah?...sunan datafi kiranta dashi kenan.
I just don't know but I'm having some strange feelings.
Ba komai eshaah just relax okay.
Wata qatuwar shopping complex suka Parker suka fito tareda shiga.
Mahmud dake hannun Nana riqe Yana hango 6angaren kayan wasa yayi can da gudu Yana
cewa Nana,, yeeyyyy catch me if you can.,
Binsa tayida gudu dai lokacinda idanuwan ayshah suka sauka kan qatuwar plasma tv dake
gurin,,,
Fuskar Deen ce bayyane jikin tv 'din cikin taron dubban jama'a fatarsa kawai ta Isa ta nuna
tsananin hutu da kwanciyar hankinda yake ciki tareda farin ciki.,
Bodyguards taga sunata faman kakkaresa masu 'daukar hoto da Yan jarida Sai rige rige suke
yaci wani irin ado cikin dark blue shadda da maiqonta kawai ya bayyana tsananin tsadarta....
Kai Amma wlh yau nataya shaikh nuraddeen auren dayayi Dan kuwa Yana matuqar tausayi da
taimakon addini Dan kuwa shika'dai ne matashin babban shaikh damuke taqama dashi a
qasashen qetare..
Hmmmnn kaidai jabir Bari wlh ni Yana matuqar burgeni daya za6i zamowa babban masani akan
addini maimakon wani aikin Kuma qarin abin burgewa shine dayazo gida Nigeria ya za6i Mata
ya aura.....
'dauke Kai tayi tana qoqarin danne abinda yake taso Mata Amma tuni wani wawan jiri ya 'dibeta
shanty tayi saurin tareta kafin tayi magana saiga Nana a guje hankali tashe kamar zautacciya
tace,
Anty anty wasu sun 'dauke Mahmud sun gudu dashi a mota.
Wat'"shanty tace da qarfi tareda sakin ayshah da itama tuni ta girgije ta kwasa waje da gudu
suka bita tareda sauran ma'aikatan Amma Ina suna fita motar na barin gurin.
Kawai Sai ganin sukayi ayshah ta yanke jiki ta fa'di.
Mamuhí ½í²‹
_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU....*_í ¼í½’
_Mi amor-mi vida...._
_Viawattpad@mamuhgee_
*29*
Arikice shanty takamota tana girgixata da qarfi cikin tashin hankali Amma ba alamar ko
numfashi atareda ita bare tasakaran zata motsa.,,
Kallon Nana dake risgar kuka cikin tashin hankali tayi tace,
Kamomin ita maza,
Mota suka sakata cikin mota aguje ta Isa specialist da ita kafin takira anty fannah tafa'da Mata
abinda ke faruwa.
Sumane kawai anty fannah batayiba Jin mummunan zancen cikin qoqarin danne kukanta tace
gatanan qarasowa asibitin,
Tana kashe wayar tasaki kuka ahankali jikinta na matuqar rawa Dan tasan rashin ganin
Mahmud barazanace ga kwanciyar hankali da dadda'dar rayuwarsu musamman ayshah
datasan zaucewama zatayi.
Kodata isa asibitin ayshahn ta farko Banda hauka Babu abinda take musu Sai ririqeta akeyi
tana ganin anty fannah tasaki wani irin kuka Mai qarfi tareda fadawa jikinta tana cewa,
Anty fannah Mahmud 'dina,,,,I can't live without my son,,,,, Mahmud is my life,,,my Mahmud.....
Kukane yaci qarfinta ta rintse idanuwa tana rerosa da qarfi..
Anty fannah da shanty ma duk kukan suke Nana kuwa ita ko magana ba'ayi.
Police sukaje suka bada report tareda zube maqudan ku'di Nan da Nan suka 'dau bayanai suka
fara nemansa cikin gaggawa.
Gida suka koma Amma ayshah ko Zama kasayi tayi ta zari mukullin mota ta Fice da sauri suka
bita Nan suka fara yawo cikin gari lungu da saqo suna nemansa ganin dare yafarayi ba alamar
ganinsa yasa ayshah qara rikicewa Banda kukan tashin hankali Babu abinda takeyi,,
Daqyar suka samu suka tirsasata suka dawo gida cikin dare..
Washe gari ma hakance takuma faruwa tun safe suna yawo Amma ba alamar nasara suna
dawowa gida wani mugun zazza6i ya rufeta sbd kuka da rashin cin abinci danko ruwa su anty
sunyi sunyi Amma Sam ko kallon abinci tason yi Banda kuka ba abinda take iyayi.
Police sunyi iya yinsu har tsawon sati biyu ba wani bayani Sai kawai suka aje case 'din gefe,,,
Duk inda hankalin anty fannah da shanty yake ya matuqar tashi sbd halinda ayshah ke ciki Dan
kuwa sosai ciwo ya kwantar da ita tayi wata irin muguwar Rama ta yamutse ta Fice hayyacinta
sbd komaima sabo yadawo Mata ciwon rabuwa da iyayenta Dana 6atan 'danta da yanda
rayuwarta ta ta6ar6are duk komai ya taru ya zautata.
Anty fannah ma tuni kwanciyar hankali yayi Mata qaura duk ta rame sbd ganin yanda ayshan
takoma kamar Wadda tayi shekaru cikin ciwo,,
Sunyi yawon asibitota harsun gaji Amma Babu wani sauqi..
Wata biyu da 6atan mahmud ciwo ya kwantar da ayshah suka kwanta asibiti jinya..
Zaune take bakin gadon 'dakin datake cikin mummunan yanayi Dan ko gani sosai batayi yanzu
sbd kuka dayafara cinye Mata lafiyar Ido.
Daqyar shanty dake zaune ta lalla6ata takamota suka fito wajen 'dakin kota 'dan sake
maimakon ciki Banda ajiyar zuciyan kuka ba abinda take Dan yanxuma kukan bai zuwa saidai
na zuci dayafi ciwo.
Wata kyakkyawar lady ce ta nufo aminity word 'din cikin shiga ta alfarma ta dogon hijab maroon
har qasa daya matuqar qayata kalar fatarta hannuwanta sunci adon Jan lalle hakama
qafafuwanta wasu matsiyatan heels ne duk da hijab ne ajikinta,
Murmushi fuskarta ke bayyanawa har haqoranta na 'dan bayyana ta qaraso gurin wasu Mata
dake zaune kan qatuwar dadduma suna fira daganinsu kasan gidan masu tsananin arxiki suka
fito.
Cikin farin ciki suka tarbeta tareda 'yan rakiyanta guda biyu dake bayanta,
Kujera aka 'dauko Mata da sauri aka aje Mata ta zauna cikin sakewar fuska takalli dattijuwar ciki
tace,
Haj babba Ina wuni,,
Lpia klau *_siyama_* ya gida ya nuraddeen da jama'a.
Murmushi tasaki cikin Jin da'din tambayar mijinta da akayi tace,
Alhamdulillah hajiya ya mama da jiki?
Taji sauqi Dan muna sakaran sallama yau ko gobe insha Allah.
Allah yasa su sallameku yau Dan inason nayi fira da mama kafin gobe mu wuce sbd yanada
wani taron manyan malamai dazasuyi a Madina insha Allah.
Ok Allah ya taimaka ai gskia nuraddeen Yana qoqari Dan wlh samun irinsa acikin sa'anninsa
zaiyi wuya ta yanda yake yiwa addini yaqi da hidima duk da dai ba acikinsa yatasoba mudai
saidai muce Allah yasakawa Wanda yayi jahadin musuluntar dashi,ke Kuma Allah yabaku Zama
lpia da zuria Mai albarka.
Amin""""tace cikin farin ciki da Jin da'din anyabi farin cikinta ma'ana mijinta.
Ayshah datun zuwan matar taji zuciyarta na Mata nauyin ganinta ta rintse ido Amma Jin abinda
suka fa'da yatabbar Mata dako matar wace,.
Jitayi tana qoqarin ha'diye wani Abu daya tsaya maqoshinta Yana neman danne numfashinta ta
miqe da qyar tabar gurin zuciyarta na gaf da bugawa..
Ganin yanayinta yasa shanty saurin Kiran nurses tareda Dr Nan suka fara qoqarin dubata sbd
numfashinta dake sama sama kaman zai fita...
Wani qarfine da mummunan 6acin Rai suka taso Mata ta fusge hannunta da ake qaqarin
zubawa ruwan allura ta cannula.
Riqota shanty tayi cikin tsoron sabon yanayin data ganta ta girgixa Sai kawai ta fashe da wani
irin kuka Mai tafasa zuciya.
Sanyi jikin shanty yayi ta zauna kusada ita tareda dafata cikin sanyin murya tace,
Ayshah Dan Allah kiyi hkr ki rungumi qaddarar Allah har zuwa lokacinda Allah zai iyakance
miki..
Tsananta kukanta tayi ta 'dago cikin kuka tace,
Shanty na rasa komai duk sbd soyayyar Wanda ba Sona yakeba amfani yakeso kawai yayi
Dani,
Shanty rayuwata ta lalace sbd mugun mutumin da yake Kiran kansa da shaikh yanxu,,
Na rasa komai na rasa kowa Banda abinda zan dogara dashi naji qarfin gwiwar qarasa
rayuwata.,
Shanty I'm nothing but a loose...
Inama ace zan manta komai nakoma rayuwata ta da,,,inama ace Zan iya ciresa a Raina kwata
kwata batareda na tunosa Koda na second 'daya bane,,,,,
Shanty I can't bear this pain anymore,,, it is really hurting...I can't bear it.,,,ji nake gwaramin
mutuwa sbd kowa bayasona,,,,
Basa Sona basa buqatana sbd laifi qalilan Kuma naso subani dama na gyara babban kuskuren
Dana tafka...
Gashi mahmud 'dina baya taredani duk nasarasa mutanen danake tsananin so da qauna a
rayuwa so what is the point of living in misery....
Rufe Mata baki shanty tayi cikin tsananin tausayinta cikin hawaye tace,
You're my best my only friend I can't see you suffering like this I promise you won't feel this pain
again,,,you'll be happy again my eshaaa insha Allah..
Bu'de hanbag 'dinta tayi ta 'dauko wasu qwayoyi ta miqawa ayshah tace,
Take this now and I promise you won't feel a thing again...
Kallonta ayshah tayi da jajayen idanuwanta ta kawai da Kai saikuma wata zuciyar ta ingizata ta
kar6a Tasha batareda dogon tunaniba sbd kawai buqatarta ta dainajin ra'dadin da ciwon
datakeji cikin zuciyarta..
Kanta taji yafara 'dan juyawa ta 'dago takalli shanty saitaga biyu biyu take ganinta Nan ta tashi
tana bin 'dakin da kallo Yana juya Mata saitaji abin namata nisha'di Dan kamar a sama take
jinta.....