Showing 27001 words to 30000 words out of 50455 words

Chapter 10 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf

08 Jul 2025

2468

can qasan maqoshi yace,

What?

Murya na rawa tace,

Sir one lady is here to see you.

Tsaki yasaki sbd baita6a kawowa arai ayshah zata iya zuwa gidanba yanxu.

Korota yayi ta sauko takalli ayshan tace yace bayason adamesa.


Kallon Deborah ayshah tayi idonta na cikowa da hawaye tace,

Please go and tell him it's ayshah.

Kamar bazata komaba saita koma ai tana ta6a qofar ya daka Mata wata gigitacciyar tsawa a
rikice ta juyo saitaga ayshan bayanta.

Tura qofar 'dakin ayshah tayi tashiga ya Ciro kansa a fusace zai fara zuba masifa idanuwansa
suka sauka cikin nata baisan sanda ya zaburo da qarfi ba yayo gurinta yayi Mata wata
kyakkyawar runguma itama sake shigewa jikinsa tayi tana qara qanqamesa.

Deborah na ganin haka tayi saurin barin gurin zuciyarta na mamakin ayshan.

Sun Jima ahaka kafin ya jata suka zauna bakin gado ya riqo hannuwanta Yana kallon face
'dinta a kasalance yace,

I missed you so badly my love.. please don't ignore me like this again.

Kasa magana tayi ta lafe cikin jikinsa tanajin nutsuwa na da farin ciki na shigarta na ganinsa.

'dagowa yayi ya kalli face 'dinta Yana shafowa yace,

You look so pale my love..

Fuskarsa ta kalla tace,

You don't look good too.

Matsoda fuskarta yayi kusada tasa Yana kallon cikin idonta yace,

What do you expect to see my love,,,,I'm nothing without you ayeeshah.,
I can't imagine my life without you in it...

Sake shigewa jikinsa tayi hawaye na taruwa cikin idanuwanta na tausayin kansu Dan ko ita
tasan Rashi agunta babban qalubalene ga rayuwarta.

'dago fuskarta yayi cikin kulawa yace,

My love is everything ok?... I mean you here..

Gabanta ne ya Fadi da abinda zata fa'da Masa ta zame jikinta tareda miqewa tsaye kanta a
qasa tace,

Deen...Sai kuma tayi shiru.

Miqewa yayi ya Kuma kamota ya zaunar da ita kan cinyarsa tareda zare dogon hijabinta ya aje
ya kalleta da kyau yaga ta qara wani irin fresh fatarta Sai glowing take Sai 'yar ramar datayi..

shafo wuyanta yayi har zuwa qirjinta ta riqe hannunsa ya kalleta da lazy eyes 'dinsa tareda
kallon red lips 'dinta Yana Kai bakinsa kansu.

Kissing dinta yake cikin tsananin buqatarta..
Rigarta ya zame yana Kai hannunsa kan qirjinta yayi saurin zare bakinsa anata yakallesu sbd
cikar dayaji sun qara da laushi.

Rintse idanuwa tayi cikin kunya yasaki murmushi tareda kwantarda ita a gadon yabita.


Saida komai ya lafa ya 'dauketa yakaita toilet sukayo wanka suka fito tana gyara zaman hijab
'dinta tace,

Deen there's a problem..

Saurin aje turaren dayake fesawa yayi ya riqota yace,

What is it my love.

Idonta na kawo ruwa tace,

It's about the wedding they've fixed for me and ya Umar,, the preparation for the wedding has
started.

Jikinsa taga ya'dau rawa idanuwansa na canxa launi ya kalleta cikeda baqin ciki da takaicin
zancen yace,

I'm sorry my love but I can't hide this anymore I will go and talk to them right away.


Riqosa tayi tana hawaye tace,

Deen please don't go let's find a solution first this is not gonna work.

Zama yayi tareda rintse idanuwansa Yana karanto adduar da shaikh ya koya Masa ta idan Rai
ya 6aci.


Saida ya share kusan minti goma ahaka kafin yaji zuciyarsa ta rage quna suka fito Yana riqeda
hannunta suka shiga mota sukabar gidan.

Shopping yakaita Amma Sam taqi yarda ta fita motar dole yashiga yayo Mata siyayya yakaita
gidan anty zainab.
daqyar ya iya rabuwa da ita tashiga shikuma ya wuce.





Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_🍒

_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_


*26*


Babban alamarin tashin hankalin ba qaramin Dakar zuciyarsu malam babba yayi ba Dan iya
,'daukar zafi sun 'dauka da ayshah shiyasa malam ya 'dau babban mataki cikin 6acin Rai na
hanata fitowa Koda tsakar gidan bare harta fita.

Tayi kuka har qarfin jikinta ya qare saidai na zuci,
Fuskarta kuwa ta ko'de tayi wani haske kamar Mara jini.

Nuratu ce kawai mai tausayinta tana qoqarin tausauta Dan ganin ta rage damuwa Amma Sam
kullum alamari qara gaba yake Dan ba abinda ke 'daga Mata hankali kamar yanayinda aka
fitardashi batada tabbacin Yana Raye....

Hakan take tunanowa taji kamar zata haukace wani sa'in Sai nuratu ta ririqeta...


Kamar lokuta da dama yauma kwance take ta takure qarshen qatuwar katifarsu zazza6i takeji
sosai Amma batajin ko motsawa zata iya yi sbd raunin dake zuciyarta yayi nasarar karya
dukkanin garkuwar jikinta.

Qarasowa nuratu tayi ta zauna gabanta tareda kallon yanda hawaye suka bushe Mata a fuska
ta dafa qafafuwanta cikin sanyin murya tace,

Anty ki misalta min inda yake zance nadubo mikishi Dan hankalinki ya 'dan kwanta..

Da sauri ta 'dago idanuwanta dasuka koma qanana sbd kuka ta kalli nuratu batasan sanda ta
rungumetaba cikin farin ciki.

Gidan anty zainab tayi qaryar zuwa aka barta tana fita daga gidan saita fara zuwa gidan anty
zainab 'din Sai yamma sosai ta fito ta nufi asibitin da ayshah ta misalta Mata
Bata Sha wata wahalar gano room 'din dayakeba tana shiga Nan ta tarar da wani tashin
hankali.

Zaune yake kan daddumar sallah kansa a qasa kuka yake kashir6an kamar ransa zai fita..

A darare ta qaraso gabansa takira sunansa cikin hawaye Dan baqaramin karyewa zuciyarta
tayiba da ganin shima halinda yake ciki.


'dagowa yayi Yana ganinta yasan nuratu ce qanwar ayshansa datake fa'da Masa ya kalleta cikin
dashashiyar murya yace,

Ayeeshahna tana...

Katsesa tayi cikin hawaye da fa'din,

Ita tasani nazo Naga halinda kake ciki...

Rintse idanu yayi cikin Jin sabuwar soyayyar ayshansa ya bu'dese ya sauke akan nuratu tareda
zubewa gabanta tayi saurin ja da baya jikinta rawa cikin kuka tace,

Me kakeyi haka??

Murya a shaqe yace,

Please take me to her,,,,I want to see her before I die coz I can feel my life is about to end...
I want to see and tell her how much she means to my miserable life because I'm the couse of all
her pains...
Please please ple.....kuka yaso kwace Masa batasan sanda tayi saurin durqusawaba itama tace
zata kaisa.

Ana Kiran magriba suka Isa anguwar..
Dayake duhu ya'dan fara Babu Wanda ya lura dasu suna,
Saidata leqa taga gabaki 'daya mazan gidansu sun shige masallaci matan kuwa duk sunshiga
'dakuna sallah tayi saurin kiransa yashigo takaisa 'dakin da aka maida ayshan aka hanata
fitowa.
Yana shiga tasaki ajiyar zuciya tareda barin gurin.


Duhu ne a 'dakin Amma Yana iya ganinta zaune kan sallaya ta cusa kanta cikin qafafuwanta
tayi Nisa acikin tunani.


Jikinsa ne yayi matuqar saki ya qaraso ahankali ya zauna gabanta tareda Kiran sunanta can
qasan maqoshi.

Kamar a mafarki taji muryarsa tana 'dagowa sukai Ido biyu da qarfi ta fa'da jikinsa tareda
fashewa da kuka tana qanqamesa.

Shima hawayen yake Yana qara shigarda ita jikinsa.

Daqyar suka lallashi kansu sukayi shiru suna sauke ajiyar zuciya...

A sanyaye yace,

Ayeeshah....I'm really sorry ayeeshah..
I'm sorry I was so blinded by love and force you into marrying me and now you're suffering it's
all because of me...
I'm nothing but a pain,,,a sorrow,,,a.....

Toshe Masa baki tayi kuka na qwace Mata tace,

I love you Deen,,,
I love you because I choose to...
I love you because my heart want to...
You change my life,,,,
you bring happiness in it...Deen I can't live without you so please don't leave me here I want to
live with you...

Qanqameta yayi cikin kuka yace,

I love you ayeeshah,,,
I love you and I want you to know that will never change even I'm here or somewhere else....

'dago da fuskarta yayi ya kalla cikin hawaye yace,

Promise me you'll always remember that I nuraddeen Aiden only love you ayeeshah,,,, you
alone my ayeeshah,, promise me you'll never forget that...

'daga kai tayi hawaye na bin fuskarta da gudu...

Ya qara shigarda ita jikinsa shima Yana hawayen.

Mantawa sukayi da yanayin rashin kwanciyar hankali dasuke ciki suka Sha soyayyarsu kamar
ranar suka fara ha'duwa da juna Dan kuwa soyayya Mai sanyi da shiga Rai ya nuna Mata
Wanda tashiga ranta ta tsaya.,,

Kwance take cikin jikinsa lullu6e sbd dukkaninsu ba Kaya ajikinsu ta kwantar da kanta a qirjinsa
tana Jin bugun zuciyarsa ta lumshe idanu tareda 'dago Kai takalli raunikansa dake na'de da
bandage takai hannu ahankali idonta na Tara hawaye ta ta6a yayi saurin rintse ido ta janye
hannu da sauri sbd har cikin ranta tanajin ra'dadin ciwonsa cikin zuciyarta ta kwantarda kanta

tareda qara lafewa cikin jikinsa..

shafo kanta yayi yana rufe idonsa yanajin wani yanayi na shigarsa na qarason kasancewa da
ita.

Qara 'dago kanta yayi ya ha'de bakinsu Yana kallon face 'dinta ba musu taqara bashi hadin Kai
suka Kuma making love hankali kwance.


Washe gari dukkanin familyn gidan suna babban palo gurin karatu adaidai wannan lokacin
yafita yabar gidan batareda kowa ya gansaba...da Shirin gobe zaije yazo da shaikh ayiwasu
baba bayanin aurensu.


Ba laifi a Daren kwanan farin ciki sukayi dukkaninsu musamman mashi daya matsu gari ya
waye yaje yazo da shaikh.


Washe gari gidansu yacika maqil da 'yan uwansu na nesa Dana kusa sbd ranar ne za'a fara
bikinta da ya Umar...

Hidima ake anata kaida kawo da hayaniyar biki itadai tana 'daki kwance wani mugun zazza6i ke
cin jikinta danko hannunta Bata iya 'dagawa sbd kukan datasha...

Nuratu ma nakusa da ita zaune cikin damuwa..


Ummi kuwa tun ranar da alamarin yafaru lafiya tafara yi Mata qaranci Dan baqaramin Dakar
zuciyarta abin yayiba sbd Allah yagani tana tsananin qaunar 'yarta bazataso ace tayi wani abin
tir ba.


Kallon nuratu tayi daqyar ta iya bu'de baki murya a shaqe tace,

Nuratu kije kifa'da Masa an jawo 'daurin auren gobe...

To nuratu tace asanyaye tareda ficewa,,,

Umar dake tsaye bakin qofa yazo magana da ita yanajin abinda tace yayi saurin barin gurin
zuciyarsa na tafasa.

Yana bakin titi yaga shigar nuratu napep yatari mashin yabi bayanta.

Har 'dakin dayake cikin asibiti saidaya bita yagani tana fitowa ya lafe bayan bishiya saidata bar
asibitin ya fito Yana kallon qofar 'dakin cikin wani mugun tunani.

Gaf da magriba Dr yazo ya sallamesa sbd takurawar dayayi a sallamesa 'din...
Sallar magriba yafarayi kafin yafito cikin hanzari zuciyarsa na tsananta bugawa.

Amenity word yake Daman Kuma akwai qaranci mutane sosai a word 'din...

Tafiya ka'dan yayi daga 'dakin yaji saukar wani mummunan duka a tsakiyar kansa da qaton
qarfen dayafi Kama da guduma...

Baya yayi fuskarsa na rufewa da jini cikin mummunan yanayi ya yanke jiki ya fa'din jini nabin
qasa.


Murmushin mugunta yasaki tareda barin gurin cikin Jin da'din samun nasara.

Cikin tashin hankali nurse datazo tagansa taje ta kirawo Dr Nan hankalinsu yayi mummunan
tashi sbd jinin dake zuba sosai ga ba alamun Rai ajikinsa..

Waya Dr yafitar jikinsa na matuqar rawa yakira mum har kusan so biyar Sai ana shida ta 'dauka
cikin tashin hankali yayi Mata bayanin halinda Nik 'din yake ciki.


Cikin mintuna qalilan ta suka iso hankali tashe
Suna ganin halinda yake ciki mum tace ayi musu Shirin komai subar qasar zuwa gobe.




Duk inda hankalinta yake yayi mummunan tashi sbd har dare bashi ba shaikh...

Koda gari ya waye ko gani batayi sbd kuka gashi da ko Zama Bata iya yi sbd ciwo gashi Sai
shirye shiryen 'daurin aure ake bayan sallar juma'a..

Su anty amina ne suka shigo 'dakin tareda kamota ta tashi suka kaita har cikin toilet daqyar ta
iya 'daga bucket 'din tajuyewa jikinta har cikin Kai tafito suka miqa Mata Kaya ta zura aka fito da
ita sbd Mai qunshi da'aka Kira.


Tana fitowa tsakar gidan wani mummunan jiri ya 'dibeta sbd rashin qarfin jiki da zafin zuciyar
daya yunquro Mata Nan take ta zube gurin asume...

Agigice sukayi kanta suna Kiran sunanta Amma ba alamar numfashi atareda ita.

Da sauri aka zuba Mata ruwa amma ba alamar zata motsa ba Nan hankali ya Kuma tashi su
baba alhaji da ya Umar da mama sakina aka kwasheta Sai asibiti.


Cikin gaggawa aka kar6eta akai cikin emergency da ita.

Zama su mama sakina sukayi jiran tsammani har kusan awa 'daya saiga Dr yafito ya nufi office
'dinsa su baba da ya Umar suka bisa.

Zama yayi Yana warware tie 'dinsa ya kafin ya kalli su baba dake raba idanun jiran bayani.

Alhaji maganar gaskiya yarinyar Nan tana fama da damuwa tareda yunwa Kuma hakan babban
barazanace ga lafiyarta da abinda ke cikinta,,,,ma'ana juna biyun dake cikinta na wata 'daya da
kwanaki....

*_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_


*27*


*_godiya Mai tarin yawa ga masoyan TAURA BIYU aduk inda suke.._*💋



Babbar Riga baba alhaji ya gyara Yana qara gyara Zama sbd shi Sam bai fahimci zancenba ya
kalli Dr yace,

Aa wannan dakake magana ba itace Wadda muka kawoba,,
Wadda muka kawo itama tanan cikin 'dakin sunanta ayshah Kuma budurwace Bata ta6a aure

ba...yauma ne dai za'a 'daura auren nata kaga mijin Nan a tsaye.


Takaici ne ya 'dan Kama Dr Amma fahimtar dayayi da Rashin sanin komai dasukayi akan 'yarsu
saiya gyara Zama Dan sake musu bayani dalla dalla..

Alhaji maganar danake fa'da muku anan bayanine akan 'yarku da kuka kawo..'yarku ayshah
tana 'dauke da ciki na haihuwa 'dan wata 'daya da satittika...


Sharce zufa baba alhaji yayi ya juyo ya kalli baba qarami dashima tuni babbar rigarsa ta Shirin
'daurin aure ta jiqe sbd zufa...

Atare suka juyo suna aikawa Umar da zuciya tagama kashesa Banda mazari ba abinda jikinsa
keyi idanuwansa kuwa ko gani sosai bayayi dasu sbd baqin ciki da tafasar zuciya...

Juyawa yayi a fusace zai fita baba qarami yayi saurin Shan gabansa tareda sharara Masa
lafiyayyan Mari...

Ji yayi kansa na neman bugawa ya 'dago da jajayen idanuwansa yakalli su baban yaga irin
kallon dasuke Masa ya daki bango da qarfi kamar zautacce yace,

Karma kufara wannan tunanin,, tunda nake a rayuwata ko hannun ayshah banta6a riqewa bare
har ni nayi Mata.....

To idan bakai bane wane?""""" Baba alhaji yafada da qarfi cikin zafin zuciya da 6acin Rai.

Jiki sanyaye baba qarami ya kalli baba alhaji yace,

Muje gida mayi komai acan gaban malam babba.

Fitowa sukayi kowanne daqyar babbar rigarsa ke 'daukarsa sbd kunya da baqin ciki..

Kallonsu mama sakina tayi cikeda damuwa tace,

Lpia kuwa?
Meke damunta likitan yace?

Fuskarsa na kallon wani gurin yace,

Ayshah cikine da ita Dan haka kitashi maza yanzu muje gida ayi komai can gaban kowa.

Yawu ta ha'diye daqyar jikinta itama Yana 'daukar rawa sbd gabaki 'daya ta nemi nutsuwarta ta
rasa dajin wannan mummunan zance daga bakin baba alhaji.

'dakin tashiga ta tararda ayshan ta tashi saurin 'dauke Kai tayi cikin tashin hankalinta daya kasa
6oyuwa tace,

Taso maza gida zamu yanxu..

Ba musu ta sauko gadon ahankali jikinta na tsananta sanyi hakama fa'duwar gabanta na
tsananta..

Koda suka fito su baba harsun samu mota sun shiga suna fitowa Umar yabar gurin yaje yahau
mashin Dan bayajin zai iya shaqar numfashinda jinin Deen dake cikin ayshah yake shaqa.


Tunda suka shiga motar Babu Mai ko qwaqwaran motsi sbd kowada tunanin dayake ransa.

Umar ya rigasu isowa shiyasa koda suka iso ya Tara kowa a palon ana jiran isowarsu Dan ko
magana baya iyayi bare yafa'di abinda yake faruwa..


Suna shigowa palon kowa yabisu da idanuwa sbd fargabar Jin koma menene Dan tun a
yanayin Umar 'din suka tabbatarda koma meyene bamai da'di bane.



Gyara Zama malam babba yayi ya fuskanci baba qarami yace,

Shehu lafiya dai Naga fuskokinku ba da'din kallo..

Gumi na qara yanko Masa yace,

Ba lafiya ba...

Wani 'daci malam babban ya ha'diye tareda maida kallonsa ga baba alhaji dashima har lokacin
zufa yake yace,

Bello yimin bayanin komai yanxu Ina sauraronka.

Yaya muna cikin gagarumin tashin hankali sbd mutunci da sunan wannan gidan ya gama
lalacewa daga yau...
Ayshah gatanan zaune cikine da ita na haihuwa ma'ana dai cikin banxa..

Ba kowa daya ki'dima dajin zancenba ita kanta zabura tayi cikin masifaffen tashin hankali
umminta dake kusada ita ta mayarda ita zaune tareda rufe Ido ta saukar Mata da kyakkyawan
mari tareda fashewa da kuka numfashinta na qoqarin 'daukewa da sauri nuratu da salma
sukayo kanta duk da dukkaninsu jikinsu rawa yake sbd tashin hankalin dasuke ciki.

Malam babba kuwa qoqarin fita hayyacinsa yake sbd hawan jininsa daya Haye gabaki 'daya
Nan take zufa ta jiqasa yafara gani dishi dishi..

Hankali tashe su baba qarami dasu abbakar sukayi kansa ana Masa firfita hankali a matuqar
tashe..

Rarrafowa tayi da sauri gaban malam babba 'din tana kuka sosai zatayi magana babanta da
zuciya tagama kashesa ya rufeta da duka tako ina Nan hankali ya Kuma tashi sbd ganin baban
nata ya zube qasa Yana kuka sosai...


Ba qaramin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login