Showing 12001 words to 15000 words out of 50455 words

Chapter 5 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf

08 Jul 2025

2459

sauko ya fice
batareda ya tsaya bawa Davina amsar Murphy datake tambayarsa ba Dan shima nemansa
yake Amma haryanzu wayarsa Bata zuwa.


Duk inda yake sakaran zai ganta ya Duba bai gantaba Nan take yaji jikinsa yafarayin sanyi..

Tunda yafara nemanta tagansa tayi saurin 6oyewa bayan wata mota tana kallonsa zuciyarta a
sanyaye Amma hakanan taji dadin ganinsa yaji sauqi duk da dai tana iya ganin baida wani
kuzari.


Tundaga ranar tafara 6oye Masa duk da baqaramin tirsasa zuciyarta takeba gurin aikata hakan.


Tun mum 'dinsa na 'daukar abin wasa saigata hankalinta yayi mugun tashi sbd wata irin
damuwa da muguwar Rama data sako Nik 'din agaba sbd rashin ganin ayshar gashi yakasa
samun ko wane information akanta.

Sam shida kansa baisan son da yake Mata yakai hakaba Sai yanzu..

Iya bincike da lallashi mum tayi Masa yafa'da Mata damuwarsa Amma yaqi.


Yau tun 6 na safe yatafi makarantar kosu mum basusan da fitarsaba..

Bakin bus stop ya Parker motarsa zuciyarsa sanyaya da damuwar dayake ciki game da ita Dan
yau jiyake kozai kwana ya yini agurin saiya ganta zai iya samun sukunin masifar da zuciyarsa
take ciki.


Ahankali bacci ya 'daukesa sbd rashin baccin dayake fama dashi na kwanakin.

A kunne yabar motar sbd Ac.

Sai 10 ta iso makarantar ana ajesu busstop ta fito ta nufi hanyarta cikin sanyin jiki sbd rashin
kuzarin da itama take fama dashi.


Kamar daga sama ta hangosa kwance Yana bacci cikin motar yayi matuqar ramewa saitaji
zuciyarta na neman karyewa tayi saurin juyawa tabar gurin.


Qarfe biyar na yamma ta gama lectures ta fito a galabaice sbd ranar azumi take..

Cak ta tsaya sakamakon ganin har lokacin Yana gurin saidai wannan time 'din yafito jingine
yake jikin motarsa yayi wani irin fadawa sbd yunwa da wahala Amma yaqi tafiya.


Kamar ance ya juyo Sai kawai idonsa yashiga cikin nata yayi saurin miqewa tsaye daidai Yana
kallonta amarairaice.

Dakewa tayi ta matso tareda ra6asa ta wuce tashige bus tareda sunkuyar da kanta Dan karma
su hada ido.

Binta yayi da lazy eyes 'dinsa suna taruwa da ruwa sbd tunanin qila wani laifi yayi Mata.

Matsowa yayi da sauri zai shiga bus 'din cikin tsautsayi yaron direban motar ya turesa sbd
already motan yacika ya fa'di qasa cikin ruwan saman dake taruwa awurin Nan take kayansa da
jikinsa ya lalace bai tsaya dubawaba ya miqe da sauri zaikuma matsowa aka tada motar
sukabar gurin.

Motarsa yashiga da sauri yabi bayansu saigasu har anguwar su ayshah 'din.

Tana fitowa motar tagansa Yana qoqarin parking ya fito.

Saurin wucewa tayi batareda takuma kallon inda yakeba.

Biyota yayi da gudu batareda ya tsaya kashe motarsa ba..,,

Sauri ta qara gabanta na tsananta fa'duwa daf da zata shiga kwanar layinsu saiga ya Umar...

Wata mummunar fa'duwa gabanta yayi ta saci kallon bayanta taga Sai zubo sauri yake Dan ya
iso wurinta ta rintse ido zuciyarta na tsinkewa da tausayinsa.


Kallonta ya Umar 'din yayi Yana son karanto firgicin daya gani tattare da ita.

Kamar ance ya Duba bayanta saiya hangosa Yana zubo sauri tareda tsalle Yana qoqarin
fa'duwa sbd agwagi dasuka biyosa Sai tsalle yakeye Yana kallota karta 6ace Masa.

Kallonta Umar 'din yayi cikeda zargi kafin yayi Mata alamar ta wuce da ido.

Sum sum ta wuce Amma saita kasa shigewa konar ta juyo.


Manyan agwagin dasuka fi girma Umar ya 'dauka tareda jefa Masa cikin baqin ciki da takaicin
ganinsa.

Baya yayi da sauri cikin tsoron agwagin cikin rashin sa'a Ashe yakai kwata sai gashi zaune
cikinta.


Batareda 6ata lokaci ba ya yunquro yataso har lokacin idonsa nakan kwanar datake la6e tana
kallonsa.

Qoqarin wucewa yake cikin takaici Umar ya fixgosa tareda wurgar dashi ya nunasa da yatsa
cikin xafi yace,,

Zanbarka yau katafi Amma wlh duk nakuma ganin wannan kafirar fuskar taka cikin anguwar
Nan saina yanka maka ita da kwalba..

Juyawa yayi zai wuce tayi saurin barin gurin tayi gida da sauri zuciyarta na wani irin nauyi.






Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comments_
*_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_🍒

_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_



*17&18*



koda Nik Yakoma gida ya tsaya gaban mirror yakalli kansa saiyaji hawaye sun ciko
idanuwansa..
Tubewa yayi ya jefo kayan qasa ta windown dakinsa ya fa'da toilet yayo wanka Banda zazza6in
wuya Babu abinda yakeji.


A daddafe ya saka kayan bacci black yashige bargo ya kwanta jikinsa na rawar sanyin zazza6i..

Qarfe Tara mum tashigo dakinsa Finn na biyeda ita tana ganin yanda yake shaking cikin bargo
ta qaraso da sauri tana Kiran sunan Jesus..

Tallafosa tayi taji jikinsa da mugun zafi ta kalli Finn cikin tashin hankali tace,

quickly call Dr Finn.

Fiddo wayarsa yayi daga aljihu ya latsa Kiran Dr cikin gaggawa.

Shigewa yayi jikin mum 'dinsa yana fiddo numfashi ahankali cikin azaba yace,

Mum I'm fine,, it's just a fever,,I will get better soon there's no need to call the Dr....

Cikin karyewar murya kamar zatayi kuka tace,

Quite.. you're not fine my love and it's not a normal fever,, you're hiding something from me,,I
can feel it.

Lumshe idanuwa yayi cikin sanyin murya qasa qasa yace,

Mum,,,,mum..i.i..I'm in love....I love someone.

Wat""""tafa'da da qarfi tareda kallon fuskarsa cikin rashin Jin dadi tareda rashin na'am da

zancen cikin damuwa tace,

You can't be in love my boy,, you're too young for that and I ca....

Katseta yayi cikin sanyin murya da cewa,

I love her so very much mum,,,I can't even imagine my life now without her mum...mum..I really
want her for myself,i love her mum..I madly love h....

Rungumesa tayi cikin tausayinsa sbd dukkanin alamu sun nuna Mata baqaramin so yakewa
kowaceceba..

Share Masa hawaye tayi tana adduar Allah yasa ko wacece kada tayi amfani da wannan
zazzafar soyayyar da Nik yake Mata ta cutatar Mata da yaro.



Kwanansa biyu Yana zazza6i Mai zafi ko qasa baya iya saukowa bare ya fita,,
Mum dinsa kuwa hutu ta dauka Dan bawa 'dan lelenta kulawa hakama 'yan uwansa wannan
karon dukkaninsu sun matuqar tausaya Masa sbd yayi matuqar sanyi kamar ba Nik ba danko
irin muguwar sakuwar dayake acikin gidan ta rage kullum Yana kwance.



Duk iya yanda take danne damuwarta saidata bayyana a jikinta sbd ramar datayi su husna
sunyi faman tambayar harsun gaji Amma alamarin bamai kar6uwa bane ko a zuciyarta bare
fa'duwa.

Kwananta biyu kotaje makaranta Bata gane komai sbd dukkanin nutsuwarta ta tarwatse Wanda
Sam takasa samun kuzari ko qarfin tattarota.
Ahaka take lalla6awa har tsawon kwana biyu.


Yau Bata samu bus da wuri ba shiyasa tayi yammacin dawowa gida,,

Ahankali take tafiya cikin nutsuwa duk da kwanakin nutsuwarta rawa take,,

Daf dazata shiga kwanar layin gidansu taga su ya Umar taredasu Yaya abbakar kusan su shida
kowanne da abun duka jikinsu har rawa yake bama Kamar ya Umar 'din da idanuwansa yafi
nakowa rufewa da 6acin Rai.

Mummunar fa'duwa gabanta yayi tai saurin sunkuyar da Kai cikin tsananin fargaba..

Kallonta ya abbakar yayi cikin 'daga murya yace,

Meyasa kikai yamma sosai yau?

A sanyaye tace,

Bansamu bus bane yau da wuri.

Shikenan maza wuce gida.

Wucewa tayi a hankali gabanta na tsananta fa'duwa,,
kaman daga sama saitaji ya Umar cikin zafi Yana cewa,,

Duk inda yake Yana guraren Nan sbd da idona nagansa Yana tambayar yara Kuma na
tabbatarda akwai abinda yake qullawa.

Cak ta tsaya sbd qafuwanta dasuka 'dau rawa..

Taji ya sani yace,

Wlh Nima yau nayi ido hu'du da shegen kafirin Nan saina karairaya Masa qafafuwa Dan ya koyi
tsaya matsayinsa.


Yawu ta ha'diye da qarfi jikinta na rawa sbd fahimtar datayi kenan Nik nacikin layin,,Kuma ta
tabbatarda ita yake nema....

Juyowa tayi takalli mugayen gororin dake hannunsu taji hankalinta yayi mummunan tashi Dan
tasan duka 'daya za'ayiwa Nik da wannan bazai qara sanin inda kansa yakeba.

'daga kai tayi cikin bugawar zuciya Sai gasa ta hangosa kusada wata qaramar matsatsiyar
kwana Yana tahowa..

Wani mumman yawun tashin hankali ta ha'diye tareda juyowa takalli su ya Umar taga ba
6angaren suke kallo ba Amma gaf sukeda juyowa..

Cikin wani irin zafin naman dabatasan tanadashiba tayi saurin Isa gabansa daidai ya Umar ya
juyo kawai saita janyosa cikin kwanar da qarfi Saida ya fa'do jikinta.

Wani irin kallo yake Mata cikin Jin da'din ganinta qayataccen murmushi na fita a fuskarsa..

Ahankali takallesa qwayar idanuwansu ta ha'du tai qasa dakanta gabanta na fa'duwa cikin sanyi
da laushin muryar tace,

Why are you doing this?

Yana kallon cikin idonta yace,

Because I love you..

Kalmar ta daketa matuqa ta rintse idanuwanta cikin sanyi tace,

It's impossible...so please stop following me...yo don't know wat trouble you're getting your self
into..


Cikeda sonta daya rufe Masa ido yace,

I'm ready to face anything for your love..

Girgixa Masa Kai tayi idonta na gangaro da hawaye tace,

We can never be together can't you get it,,,,we are from a different rel....

Shihhhh yafa'da tareda matsota sosai Yana kallon idanuwanta da lazy eyes 'dinsa murya qasa
yace,

I'm ready to be like you if that's will b the only way for me to get you..,to be with you...
I love you ayeeshah..


Stop please''''''tafada da 'dan qarfi kuka na qwace Mata..

Kaman zaiyi kuka shima murya na rawa yace,

I love you ayeeshah,,, even if I wanted to get it out of my head I can't...

Muryoyinsu ya abbakar taji suna kusanto gurin tayi saurin 'dagowa ta kallesa cikin kuka tace,

Please go from here,, leave please...

Gyara tsayuwa yayi Yana kallon hawayenta dake ta6a zuciyarsa yace,

I'm not leaving until you tell me why you are so worried like this...
and this tears???'''yafada Yana kallon yanda hawayen ke gangarowa..

Karkace Kai yayi cikin son tabbatarda abinda yake zargi murya na rawa yace,

Ayeeshah,,,do you have any feelings for me too???

Rintse ido tayi cikin qaguwa tace,,

No please go...

Jada baya yayi yace,

No I won't go anywhere...

Matsowa tayi cikin magiya da kuka tace,

They will beat you black and blue... please pls leave.

Kusantota yayi sosai har numfashinsu na ha'duwa Yana kallon cikin idanuwanta da lazy eyes
'dinsa dasuka cikada hawaye yace,

Idan har dukan dazasumin zaisa natabbatarda you love me too then so be it..

Zan jira suzo.

Kuka tasaki ahankali hartana ciccika Nan take jikinsa ya 'dau rawa cikin hawaye yace,

Am sorry my love,,,I know I'm being stubborn but I can't help it because *i love you*......

Kalmar data shiga kunnensu ya Umar kenan daidai lokacinda suka kawo gurin.




Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_



*19&20*



Zafin zuciya da bugawar zuciya ne suka mugun tasowa ya Umar ya rintse idanuwansa Dan
Daman tuni ya fara zargin ayi hakan tun kallonda yaga Nik 'din yayi Mata a station lokacin....


Rufewa idanuwansa sukayi ya qarasa gurin zuciyarsa na tafasa bai tsaya komaiba ya 'daga
qaqqarfan hannunsa ya shararawa Nik wani gigitaccen Mari saiga jini ya 6alle ta hancinsa...


Saukar wani mugun zafi taji a zuciyarta tayi saurin rintse ido ta bu'de hawaye suka gangaro
Mata ta 'dago a cikin karaya ta kallesa saitaga ko motsi yaqi yi ita ya qurawa lazy eyes 'dinsa
dasukai ja sbd azabar Mari ko qyaftawa bayayi...


Fixgota taji anyi da qarfi ta 'dago jajayen you takalli ya Umar 'din ta bu'de baki zatayi magana a
zuciye ya mare bakin da qarfi...
Durqushewa tayi qasa cikin azaba Amma tabbas azabar da zuciyarta ke ciki taci wannan 'dan
Marin..

'dagowa tayi idanuwan Nik suka sauka kan 'dan jinin daya fito gefen bakinta sbd Marin yayi
saurin zubewa gabanta jikinsa na rawa hawaye na taruwa idonsa murya na rawa yace,

You're hurt ayeeshah....
Ya 'daga hannu ya nufi inda jinin yake.....

Cikin zafi ya Umar ya riqe hannun tareda mur'dewa su ya abbakar kuwa Nan suka rufesa da
duka.


Rintse idanuwa tayi hawaye na tsiyaya akaro na farko dataji wata mummunar qiyayyar ya Umar
tana shiga tareda Huda duk wasu jijiyoyin dake aiki acikin jinin ajikinta.

Miqewa tayi batareda tajuyoba takalli irin dukan dasuke Masa ta fara tafiya cikin damuwa tabar
gurin.

'dakinsu ta nufa direct batareda ta leqa ko inaba ta gaida iyayensu kaman yanda tasaba.

Kodata shiga su husna basa 'dakin suna 6angaren mama sakina Dan can sukafi Zama a irin
wannan time 'din..


Zubewa tayi bayan qofa tareda sakin wani irin kuka ahankali tana dafe zuciyarta datakejin
kaman xata tarwatse...


Hayaniyace ta kaure cikin gidan Nan take tani kowa na fitowa sbd hayaniyarsu ya Umar hardai
shi da muryarsa tafi tashi cikin 6acin Rai...

Tanajin an ambaci kafiri ta lumshe idanuwa hawayenta na tsananta zuciyarta na da'da karyewa
sbd batasan mummunan halinda suka sako Nik acikiba...


Da daddare bayan tayi sallah Bata tashi kan sallayarba anan ta qudundune sbd damuwa da
zazza6in datakeji mai tsanani...

Nuratu ce tashigo 'dakin jiki a sanyaye ta zauna kusada ita takalleta murya asanyaye tace,

Anty ayshah su baba malam na Kira..

'dagowa tayi takalli nuratu da jajayen idanuwanta a sanyaye tace,

Sun kashesa ko nuratu?

Girgixa Kai nuratu tayi cikin tausayin 'yar uwarta tace,

Aa,,,,amma dai abun yayi Muni...

Kuka tasaki ahankali zuciyarta naci gabada tsananin zafi..

Anty ayshah da gaske soyayya kuke?

Batareda ta 'dagoba cikin kukan ta girgixa Kai...
Kafin ta miqe cikin sanyin jiki ta fito 'dakin ta nufi babban palon baba malam Dan tasan yanxu

kowa nacan ya halarta..


Kanta a qasa tashiga tareda rakubewa ta zauna qasa..

So 'daya ta 'dago taga yanda kowa ke Mata kallon 6acin rai,qyama da tuhuma..tayi saurin qasa
da kanta Tana danne hawayenta.


Cikin 'daurwar fuska da zafi baba alhaji yace,

Ayshah meye ha'dinki da wannan arnen.

Cikin sanyi da nutsuwa tace,

Babu komai..

A hasale babanta yace,

To meyasa ya biyoki yau harkuka ke6e?

Lumshe ido tayi ta bu'de sbd akaro na farko kenan dazatayi qarya murya a tausashe tace,

Nazo wucewa ne Sai muka ha'du shine yakeson tambayana nace bazan tsayaba.

Sake zaburowa baba alhaji yayi yace,

To su Umar sunce sun gani sonki shi yaron yakeyi.

Girgixa Kai tayi tace,

Ni banta6a sanin wannan ba hasalima yaza'ayima ta yiyu tsakanin ni dashi ba yare 'daya ba,
Ba addini 'daya ba..


Sai lokacin baba malam yayi gyaran murya sbd anxo gurinda yakeso Kuma yayi na'am da
abinda ta fa'dan ya kalleta yace,

Ayshah???

Na'am'''tace a sanyaye batareda ta 'dagoba yace,

Na yarda dake nasan bazaki iya ta6a sa6a Mana ba ko take doka da umarnin mu Dan haka ga

garga'di da umarni Mai qarfi,,,,daga yau ko hanyar dayabi karki Kuma kallo bare har wata
magana ta hadaku harma afara Kuma irin wannan zargin Dan ni ko maganar wani kafiri banaso
acikin zuri'ata bare har irin wannan mummunar zancen ya tabbata..


'dago Kai tayi ta kallesa tareda cewa,

To baba insha allah.


Miqewa tayi ta bar palon ahankali ya Umar yabita da kallon tuhuma danshi yana ganin abubuwa
da dama datake 6oyewa Amma saiyasa ta bayyanasu da kanta agaban kowa na gidan.


Koda wasa dama batai gangancin tunanin bacci zaizo Mata ba hakanan ta kwana cikin tunanin
wane Hali Nik yake ciki.


Koda gari ya waye taje gaida umminta saitaji duk jikinta ya da'da sanyi sbd ganin ga dukkan
alamu ma umminta na cikin tunani da fargabar Kar zancen jiya ya tabbata.

Gaida ummin tayi cikin sanyi tareda kallon nuratu dake Mata kallon tausayi tana gaisheta.

Amsawa tayi tareda kallon ummi tace,

Ummi zan tafi makaranta..

Cikin kulawa da sanyin jiki ummin tace,

Ayshah Dan Allah karki bari zuciya takaiki ga Dana sani da muguwar rayuwa.

Hawaye taji sun taho Mata Dan tasan saidai Kuma wani ceto daga Allah Dan Mai Sha tarigada
Tasha.

Zama tayi tareda kar6ar cup 'din kunun tsamiyar da ummin ke miqo Mata ta kar6a badan zata
iya sha ba saidan kadata kuma bawa ummin damar wata damuwar.

Abbanta ne yashigo tareda sallama ta sunkuyar dakai ta gaidasa cikin sanyin murya..

Amsawa yayi kadaran kadahan kafin ya zauna kan tabarmar kusada ummin Yana cewa,

Ki qara kiyayewa sbd gudun jawo fitina da tashin hankali tareda 6acin suna acikin zuriar gidan
nan Dan yanxu ina amfanin irin hakan tunda shi yaron sun Masa mummunan duka sun barosa

can kangon gidan bayan layi sbd......

Wata mummunar sarqewa tayi tafara tari Mai qarfi sbd gigitar da zancen baban yasata.

Saurin miqa Mata ruwa nuratu tayi tana Mata sannu..,
Baba da ummi kuwa kallo suka bita dashi fa'duwar gabansu na tsanantuwa .


Miqewa tayi ahankali tace,
Na tafi..

Allah tsare ummi tace a gajerance baba kuwa ko amsa Mata baisamu yiba sbd damuwa da
fargaba.


Bakin titi ta tsaya cikin zurfin tunanin rashin sanin abin yi....

Kusan Rabin Rabin awa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login