Showing 3001 words to 6000 words out of 50455 words
Chapter 2 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf
rabonta da
school Sai yau dazataje.
Sam yanxu tadaina Jin da'din makarantar Kuma takasa fadawa kowa sbd kada ahanata Dan
tana matuqar qaunar karatun.
Asanyaye take shiri harsaida husna ta lura tace,
Ayshah lafiyarki kuwa?
Kodai jikin ne?
Safarta ta jawo tana sawa cikin muryar karaya tace,
Lafiya qlau kawaidai inajin kasalar zuwane.
Daria husna tayi tana saka hijab 'dinta tace,
Kodai kin gaji da karatun ne so kike ku zarge keda ya Umar''''ta qarasa zancen cikin tsokana.
Murmushi ayshan tayi tareda tuno fuskan ya Umar,,
Tabbas tana qaunar ya Umar halinsa ne bataso na rashin haquri da zafin zuciya Dan da'ace
komai zai rage da tafi sha'awar auren nasu yanxu sbd ta huta da karatun Dan tuni yafara fita
ranta sbd jikinta na Bata ba alkhairi a karatun Nan gaba.
Kwana goma ya share ko cup 'din ruwa baya iya 'dagawa da hannun duk da Dr ya tabbatarda
ba wata karaya 'yar bugewace Amma sun 'dauki ciwon wani irin babba Dan mum har hutu ta
'dauka Dan kula dashi kawai ko dad 'dinsu Saida yazo yadubasa Yakoma Germany and yanda
suka 'dau ciwon wani babba.
Koda ya warke Yafara zuwa makaranta Sam hankalinsa bai wani kwantaba sbd ayyanawa
ransa da yayi Sam ita ba mutum bace aljana ce shiyasa ko mace Mai hijab ya gani koba niqaf
Sai ha'diye yawu
Yanxu ko bakin gate baya iya zuwa Saida Murphy sbd tsoron karya ganta.
Yau suna fitowa lectures din farko ta fito ta nufi ladies toilet 'dinsu sbd period take tanason
canza pad Dan ita Sam Bata iya wuce two hours da pad ajiki Bata canzaba.
Restaurant ta nufa danta siyo ruwan dazatayi amfani dashi.
Ku'di ta miqa aka miqo mata ruwan tajuyo kenan yakawo kowannensu cak ya tsaya cikeda
tsoron 'dan uwansa yanda jikinta ya'dau rawa haka shima nasa Murphy yayi saurin riqesa tafara
takowa ahankali jikinta na tsananta rawa zata bar gun sbd tarigada ta tabbatarda ganinsa ba
alherineba.
Ganin ta nufo gurinsu yayi saurin sakin Murphy cikin tsoro da qarfi yace,,
Ghost,,,,
Ghost, ghost...
Aikuwa bashi kadaiba duka sauran mutanen gurin da gudu aka watse Sai ihu ake wasu harsuna
fa'duwa.
Tsayawa tayi cak tareda duqawa ta fashewa da wani irin siririn kuka jikinta na sakewa.
Murphy dake tsaye shika'dai ne bai guduba Nan take yaji tabasa tausayi ya tako ahankali ya
tsaya akanta cikin tausaya mata yace,
Ki daina kuka Kuma karkiji haushinsu sbd basusan Mai suke taredashiba acikin lullu6inki.
Miqewa tsaye tayi tareda ra6ashi ta wuce kukanta na tsananta.
Mamuhí ½í²‹
_dont forget to vote, follow and comments_
[7/8, 8:41 PM] 0mmer Farouk: *_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU....*_í ¼í½’
_Mi amor-mi vida_....
_viawattpad@mamuhgee_
*3&4*
Toilet tashige da hanzari tareda rufowa tasaki wani sabon kuka ahankali,
Gabaki 'daya rayuwarta a makarantar ta zamar mata masifa Wanda take danganta hakan da
qaddararta.
Rarrashin kanta tayi daqyar kafin ta zare niqaf dinta ahankali takalli fuskarta jikin mudubi taga
baiwa ta kyau da tsarin halitta da Allah yayi mata rashin sani yasa ana mata 'daukar mummunar
halitta.
Share hawayenta tayi tareda maida niqaf dinta tafito tawucewarta gida gabaki 'daya batareda ta
tsaya attending sauran lectures 'dinta ba.
Da daddare bayan sunci abinci itada su husna tareda sauran yaran gidan suka nufi babban
palon baba malam gurin 'daukar karatun dare Wanda qaidar gidance kullum da dare saisun 'dau
karatu.
Awa 'daya da rabi sukayi sunayi kafin aka gama.
Gyara Zama baba malam yayi tareda gyaran murya
Nan kowa ya nutsu sbd sauraron Mai zai fa'da.
Kallon sauran dattijawan qannensa yayi kafin yace,
Mustapha 'dana ne Kuma ya 'dauko zance Mai girma Don kuwa ya take akidar gidan Nan daya
tarar tun kakanni tunma kafin ni mahaifinsa a haifeni..
Ma'ana dai bayan mun tsayarda maganar ha'dashi aure da yar uwarsa jininsa ya tsallake waje
yana neman auren wani yaren ma'ana bahaushiya.
Wani yawu iya lami ta ha'diye Dan kuwa tasan mummunan hukunci 'danta zai fuskanta Dan
anta6a irin haka can baya abun baiyi kyau ba sbd Saida aka rasa rayuka.
Tsit palon yayi babu Wanda ya motsa sbd jinjina girman laifin da mustaphan yayi.
Cigaba baba Mal yayi da fa'din,
Mustapha kaje kashirya gobe bayan sallar juma'a za'a 'daura aurenka saudat a goben zaka
koma gida nijar tareda matarka Kuma bamu yafe katako qafarka Nigeria ba kokuma Kiran 'daya
daga cikinmu Sai bayan shekaru biyar.
Sunkuyar da kansa yayi hawayen baqin ciki da damuwa suka ciko idanuwansa sbd hukuncin
da iyayensa suka yanke Masa bazai iya jadasuba Wanda wannan tarbiyace da'aka ba zuriar
gidan kaf tun suna yara.
Saudat kuwa wani irin kukane ya kufce mata ahankali batajiba Bata ganiba laifinsa ya shafeta
bayan auren bazata an datse mata karatu gakuma nesa dazatai da gida bako waya har tsawon
shekara biyar.
Jikin kowane yasaki Banda iyayensu maxa dake da'da nanata yi musu fadan kowa ya kiyaye
aikata irin hakan,
Baba Mal ma fa'da Mai tsanani ya 'dora dashi sbd ran iyayensu ya 6aci matuqa.
Umma sakina kuwa Jan 'yarta tayi cikeda tausayawa suka fice kowama ya fice jiki a sanyaye.
Ayshah kuwa 'dakin ummi tashige ta kwanta jiki asanyaye tana tsiyayar hawayen tausayin
saudat da yaya mustapha.
Kallo 'daya umminta tayi Mata ta 'dauke Kai sbd Bata cika kulata kasancewarta 'yar farin..
Cikin sanyi da karyewar murya tace,
Duk lokacinda Abu yasamu 'dan uwanka Mara kyau to kayi qoqarin nesanta kanka da abun Nan
sbd gujewa mummunan sakamako irin wannan.
Zuciyata takasa nutsuwa da zuwa makarantar ki Dan haka ki guje afkawa cikin irin wannan
mummunan halin.
Tsit tayi tana sauraron nasihar umminta duk datasan Sam ita bazata iya fadawa soyayya da
wani yarenba bayan nata Dan itama gwargwado tana qyamatar wani yaren.
Washe gari ga murna ga baqin ciki Dan kuwa Banda iyayensu maza da sauran manyan
mazajen gidan Babu Mai farin ciki musamman saudat data kwana tana kuka.
Koda zasu tafi bayan 'daurin auren daqyar aka 6an6areta daga jikin umma sakina.
Ayshah kasa tsayawa tayi takoma 'daki ta lafe tana tsiyayar hawayen tausayin saudat Dan
jitake idan itace bazata iya rayuwa ba iyayenta da 'yan uwantaba ko qin ji daga garesu.
Yau Monday kusan kowa nada lectures shiyasa makarantar take cike kowa Sai kaida kawo
yake.
Lecture 'daya tayi 8 to 10 Kuma bazatai wataba Sai 2 shiyasa Kai tsaye ta fito ta nufi masallacin
Mata na cikin school din ko karatun alqur'ani tayi kafin time 'din.
Tun safe mum 'dinsa ke rigima dashi akan yaje makaranta ya dage akan bazashiba sbd tsoron
ninja lady.
Zama tayi bakin lafiyayyan gadonsa dayake dunqule cikin lallausan bargo ta kamo hannunsa
Ya zame hannunsa tareda 6ata fuska yace,
Mum please don't force me,I don't wanna go.
Never Nik,,I will never force you but please Christ sake don't leave your studies for some stupid
crazy mask lady,, you're a man Nik so please act like one..
Kwantowa jikinta cikin sanyin murya yace,
I'm scared mum.
Murmushi Murphy dake tsaye tuni yayi yace,
Nik she's a normal human being just like you....
Hararsa mum tayi tareda 'daure fuska tace,
Not like him,
And I'm giving you 7days if she tries even coming closer to him talk to the pc make sure she
leaves the school for good,
And you Nik get up and get ready I'm giving you 15 minutes to leave.
Tana gama fa'da ta Fice 'dakin Dan itama akwai zafi tana lalla6asa ne sbd tsananin sonda take
Masa Amma Bata wasa da harkar karatun 'yayanta hardaishi Nik 'din daba karatun yakesoba
sbd son jikinsa da rashin son wahala.
Wurgi yayi da pillow kamar wani qaramin yaro yanajin kamar yayi kuka sbd har cikin ransa
tsoranta yake.
Wanka yayi ya shirya yafito tsaf Sai qamshi yake ga wani shining da fatarsa take.
Saukowa yayi Yana 'daura wani tsadadden Rolex watch 'dins na diamond.
Davina ce kawai zaune a dining tana breakfast taci ado cikin wata tsinananniyar gown iya cinya
black saita da'da fiddo hasken fatarta gata dama kyakkyawa kamar Nik din.
Ko kallo dining 'din bai ishesaba ya fice sbd haushin ansashi tafiya makaranta dole
Da hanzari Murphy ya aje tea 'din dayake Sha yabi bayansa.
Tunda suka shiga makarantar yake dube dube gabansa na fa'duwa.
Murmushi Murphy yayi Yana mamakin halayya irinta Nik sbd komai nasa kamar mace yake
yinsa Dan qila ko Davina dake mace Kuma qanwarsa tafisa juriya da qarfin zuciya.
Daqyar yaga sun fito first lecture dinsu suka nufi restaurant sbd yunwa yakeji.
Harsun kusa isa ya dakata Yana tuno abinda yafaru last time dasuka zo.
Kallon Murphy yayi tareda nuna restaurant din da ido yace,
Buy everything and Meet me in the car.
Daria Murphy yasaki kafin ya wuce sbd ganin duk Nik din a firgice yake.
Cikin nutsuwarta take tafiya kamar ko yaushe kanta a qasa gurin lectures zata koma Dan Time
yayi.
Saurin ja da baya tayi sbd karo datayi da mutum.
Ajiyar zuciya tasaki ahankali sbd ganin macece tayi karo da ita ba namiji ba.
Da sanyin muryarta tace,
Sorry..
'Dif gurin sukayi sbd yau shine karo na farko da wani yaji muryarta a makarantar.,
Zaqi da sanyi tareda laushin muryar yasa kowa qara kwa'daituwa dason ganin fuskarta
musamman ma zeey(zeey is back)í ½í¸œ Wadda tafi kowa takura da tsangwama Mata ko a
wancen karon itace sanadin fadowarta stairs harta fadawa 'dan hutu.
Kallonta zeey tayi tareda sakin wani shu'umin murmushi tace,
Yaudai Kam dole muga abinda ke lullu6e cikin niqaf 'din Nan Dan jikina nabani kilama aljana ce
muke tareda ita.
Danne niqaf dinta tayi ta ra6ata zata wuce taji ta riqo hannunta tareda dawo da ita baya da
qarfi.
Wani qaramin flask taga ta bu'de ba zata ta watso Mata ruwan ciki da qarfi saitin fuskarta tayi
saurin juyarda fuskarta gefe daidai da kawowarsa gurin ba zato yaji saukar ruwan zafi a
qirjinsa..
Da gudu suka bar gurin shukuma want azababben ihu yasaki tareda sakin wayoyinsa
Da sauri ta juya Dan ganin wanda aka qona shima 'dagowa yayi Dan ganin wanda ya qonasa
sunayin four eyes kawai saiya yanke jiki ya Fadi a sume.
Mamuhí ½í²‹
_dont forget to follow, vote and comments_
[7/8, 8:41 PM] 0mmer Farouk: *_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU....*_í ¼í½’
_Mi amor-mi vida_....
_viawattpad@mamuhgee_
*5&6*
Mummunar fa'duwa gabanta yayi ganin wanda abin ya sama juyawa tayi da sauri tabar gurin
sbd Murphy dayayi mata alamar ta ta tafi,
Cikin tashin hankali da fargabar masifar mum ya kinkimesa Sai asibiti.
Koda su mum suka iso asibiti Banda tashin hankali babu abinda take ciki sbd Murphy cemata
yayi coffee mai zafi Nik 'din yaje Sha ya zube Masa.
Koda Dr yafito yayi musu bayanin ba wata qonewa bace dan da alama ruwan basuda wani
mugun zafi kawaidai yaji tsorone dakuma qila rashin sabo.
Fita mum tayi Dan Kiran waya hakama Finn bayanta yabi Davina kuwa kujerar 'dakin ta zauna
tana chatting tana taunar chewing gum 'dinta.
Kallonta Murphy yayi lokacinda Nik 'din ya farka yaga hankalinta nakan wayarta ya maido
kallonsa kan Nik murya qasa qasa yace,
Ninja lady....
Manyan fararen idanuwansa ya ware cikin tsoro,,
Murphy yayi saurin dafesa yace,
Easy Mama's boy,she's not hia but she'll soon be if you tell your mum that she is responsible for
this.
Kallon wat do you mean yayi Masa,
Yace,
Yes bcox your mum won't let it go in vain so she's probably coming to take her revange and who
knows h....
A tsorace ya katseshi da cewa,
No no no no i won't tell my mum and you too won't tell her anything...
Murmushi Murphy yasaki ganin ya ku6utarda ninja lady cikin sauqi sbd yasan duk mum taji the
poor girl will lose everything.
Koda mum takuma tambayarsa akan qonewar yawu ya ha'diye tareda tuno abinda Murphy
yafada saiya shagwa6e Mata batareda yabata amsa ba.
Aiki ja yasamesu Dan kuwa jinya ake ba sauki 'dan lele ya qone qiri qiri akasa Dr treatment 'din
dole sbd dai shi baiga wata qonuwa ba Amma tunda Mama's boy ya lafe yace yanajin zafi
agurin hakanan ake jinyar harkusan sati biyu a asibitin kafin suka dawo gida nanma wata
sabuwar kulawar ta tashi masu aikin gidan basuda hutu Sai hidima suke.
Koda yaji sauqi qara lafewa yayi Dan karyaje makaranta mum ta takurasa saiyaje sbd duk son
'yayanta bata wasa da karatunsu.
Shika'dai yau yazo makarantar sbd Murphy na gurin wani program.
Zaune yake kan motarsa bayan ya fito lectures
sanye yakeda black dress da black speck Sai kyau da hasken fatarsa suka qara fitowa sbd
duhun kayansa.
Waya yakeda dad 'dinsu saiga wasu friends 'dinsu dake shige Masa Amma shi Sam bai cika
son mu'amala dasuba sbd sun cika neman Mata Dan ko acikin mota suna iya having sex da
Mata Sam basuda class ko agurin za6ar matan shikuma mutum ne Mai son Abu Mai kyau
tsaftatacce danshi qyamarma wasu matan yake shiyasa bai cika wani shiri dasuba.
Datse Kiran yayi Yana kallon 'daya daga cikinsu Mai suna Josh.
Murmushi Josh 'din yayi tareda Hawa tasa motar ya zauna yace,
Unbelievable Niklaus Aiden...
How could you let yourself get embarrassed by letting people know you're scared of some
stupid mask lady afterall you're a man..
Kallonsa yayi da fararen idanuwansa ya lumshesu batareda yace komai ba sbd shima Sam
bada son ransaba yake tsoronta gashi yanxu zancen yafara ya'duwa acikin makarantar.
Matsowa Josh yayi daf fuskarsa yace,
Let's do one,, let's get rid of this problem..
How?
Yace Yana Danna wayarsa.
Let's scare her....
Meaning?'''''yakuma fa'da Yana kallon fuskar Josh 'din.
Kashe Masa ido 'daya yayi Yana murmushi.
Shiru yayi Yana nazarin shawarar Josh 'din sbd zuciyarsa tayi na'am da zancen.
Murmushi yasaki tareda dirowa motarsa yashige Yana cewa,
I will see you guys tomorrow.
Washe da hadari sosai aka tashi shiyasa jiki ba qwari ta shirya ta wuce makarantar.
Tana Isa makaranta ruwan ya 6arke masu qarfi Nan kowa yafara gudu Dan fakewa.
Fixgota taji anyi tareda jefata cikin mota akabar makarantar a guje da ita batareda kowa ya
luraba sbd qarfin ruwan.
Babban filin qwallo ne daya ha'du,
Tsakiyar filin yake zaune kan kujera sauran abokanansu biyu na tsaye riqeda umbrella sun Kare
Masa ruwa.
Three quarter jins ne a jikinsa da boot Sai wata jibgegiyar rigar sanyi Mai laushi da hula.
Tsakiyar gurin motarsu ta tsaya suka bu'de tareda jefota inda yake zaune gabansa.
Qanqame jikinta tayi tareda sakin kukan tausayi da fargabar masifar dake gabanta ga ruwan
saima tsananta qarfi suke.
Fa'duwa gabansa yayi ya miqe tsaye tareda juya musu baya Dan har lokacin akwai sauran
tsoranta a ransa.
Zagayeta su Josh sukayi suna qyakyata dariya.
Rintse idanuwanta tayi tareda qanqame jikinta tana sake sakin Wani sabon kukan.
Niqaf 'dinta Josh ya fixgo tareda wurgi dashi tayi saurin duqar da kanta tasa tafukan hannayenta
ta rufe fuskar.
Hijab 'dinta yakuma fixgowa da qarfi Saida ya 6arke tundaga sama har qasa.
Doguwar rigar wani red shaking material ne ajikinta ruwan dake dukanta yasa tuni ya lafe ya
kwanta ko ina a jikinta.
Wani yawu dukkaninsu suka ha'de sbd wata irin kyakkyawar surar fuxgar hankali dasuka gani.
Hannu Josh yakai zai janye hannuwanta don ganin fuskarta sbd shi tuni yagama kwa'daituwa
Dan idanuwansa harsun fara wani Jan kwa'dayinta.
Caraf yaji anriqe hannunsa da qarfa.
Dagowa yayi sukai ido hu'du da Murphy.
Murmushi yasaki yace,
What is the rush Murphy?
We're all gonna enjoy so let me go first.
Turesa Murphy yayi da qarfi
Jin sunan Murphy yasa Nik juyowa ahankali idanuwansa Basu sauka ko inaba Sai kanta
Gabansa yayi mummunar fa'duwa...,
Fuskarta soke take tsakinin qafafuwanta babu Wanda yaga fuskarta Sai kyakkyawar farar
fatarta da surarta data bayyana.
Kuka take sosai Amma ba'anjin qarar kukan sbd qarar ruwan saman dake sauka Dan
dukkaninsu akansu ruwan ke sauka idan kacire shi shida baya shiga ruwan sama Dan yanxun
ne zai kwanta ciwo.
Qura Mata ido yayi Yana kallon yanda jikinta ke girgixawa sbd sheshekar kukan datakeyi,,
Duk qarar ruwan saman masu qarfi dasuka hana kowa Jin kukanta shi tsaf yake Jin sautin
kukan na shiga kunnuwansa suna amsa amo.
Cak ya qame agurin dukan zuciyarsa na tsananta.
Hijab 'dinta Murphy ya 'dauka ya yafa Mata
'dagowa tayi akaro na farko ta takallesa da manyan idanuwanta dasukai jajir.
Bugawa gabansa yayi da qarfi yaja Baya da qarfi Yana kallon fuskarta.
Dukkaninsu ja da baya sukayi cikin tsoro sbd ganin Murphy ya tsorata da ganin fuskarta sbd
dukkaninsu babu Wanda yagani Dan baya ta Basu.
Rintse idanuwanta tayi hawayen ciki suka gangaro takuma kallonsa.
Niqaf 'dinta ya wawuro ya miqa Mata sbd shi kansa bayason yacigaba da kallon wannan
kyakkyawar fuskar da baita6a ganin irinta ba Dan zai iya zaucewa.
Kar6a tayi tasaka tareda gyara zaman 6arkaken hijab 'dinta tabar gurin tana tsiyayar hawayen
baqin ciki.
A tsorace suke kallon Murphy Dan son yafada musu abinda yagani a fuskarta daya