Showing 30001 words to 33000 words out of 50455 words

Chapter 11 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf

08 Jul 2025

2471

duka baban yayi Mata ba Amma haka ta miqe baki na jini ta qara rarrafowa gaban
malam babba cikin tsananin kuka tace,

Wallahi baba banyi watsi da tarbiyar da kuka bani ba wannan al'amarin qaddarace daga Allah
wlh baba na yarda danayi babban kuskuren barin soyayya ta rufemin Ido nayi aure batareda
saninku ba....

Shaqota Umar yayi ahasale yace,

Da wa Kika 'daura auren?

Cikin tsananin kuka tace,

Niklaus..

Wurgi yayi da ita da qarfi cikin 6acin saida kanta ya daki dutsin da aka tare qofa dashi Nan take
goshinta ya fashe duk da haka Bata tsayaba saima kukanta daya tsananta ta rarrafa taqara
zuwa gaban malam babba da har lokacin numfashinsa bai daidaita ba ta riqo qafafunsa cikin
tsananin kukan dayake jijjiga jikinta tace,
Baba wlh da gaske nake ban aikata zinaba na samu wannan ciki wlh aure.....

Hannu ya 'daga ba zato kowa yaji kukan Marin daya sakar Mata.

Tsit sukayi cikin mamaki da tsoro sbd malam babba bai ta6a 'daga hannunsa akan kowaba Sai

yau.

Miqewa yayi su abbakar na riqe dashi numfashinsa na sama sama ya rintse Ido cikin kakkausar
murya da bai ta6a magana da itaba yace,

Daga yau nacire ayshah daga cikin zuri'ata,,,

Daga yau ayshah Bata cikin zuri'ar gidan Nan,,,

Daga yau na Kori ayshah daga cikin gidan Nan har abada bana buqatar sake ganin fuskarta,,,

Daga yau ko sunan ayshah karna kumajin wani ya furta acikin gidan Nan,,,
Kuma ban yafe ta ra6i ko 'daya daga cikin zuri'ar gidan Nan ba haka Kuma ban yafe taje gida
nijar ba da wannan mummunan abin kunyar.....

Cikeda tsoro da fargaba baba qarami ya matso zaiyiwa malam magana akan Kar akoreta
ayimata duk wani hukuncin cikin gida...

Malam ya 'daga Masa hannu idanuwansa na qarasa rufewa Nan hankalinsu Yakuma tashi...


Kasa motsawa tayi sbd babban tashin hankalin dataji...

Cikin zafi da 'daga murya babanta yace,

Umar fitar Mana da ita daga gidannan Kuma koni duk ranar data Kuma waiwayar gidannan ban
yafe haihuwar danayi mataba...

Hannu ta 'dora akai tareda fashewa da wani sabon kukan tashin hankali ta rarrafo gurinsa da
sauri tana want irin kuka hartana shaqewa ya janye qafafuwansa tareda barin palon jininsa na
hayewa danshima daqyar yake gani.

Gurin baba alhaji ta rarrfa tana kuka Mai ban tausayi da tsananin nadama shima yabar palon ta
koma gurin baba qarami kukanta ya ta6a zuciyarsa matuqa sbd kukan datake ya wuce tunani
dan komai na jikinta rawa yake...

Cikin tsananin tsawa baba yace,

Ka fitar da ita Umar...

Matsowa yayi jikinsa a sanyaye idanuwansa jajir Dan tun 'dazu shima kukan yake kamar ransa
zai fita sbd yasan ya rasa ayshah kenan tabbas daya sani tun farko zaice cikin nasane kodan
ya sameta.

Idanuwansa a rufe yake janta,
Kuka take tana kiran sunayen su baba tana bayyana tubarta da Basu hakuri amma Saida Umar
yakaita waje ya kalli cikinta wani baqin ciki ya taso Masa ya jefata da qarfi kan qaton dutsen
dake qofar gidan cikinta yayi mummunan buguwa Nan ta dafe ciki cikin wata mummunar azaba
sabbin hawaye na bin fuskarta...
Jitayi wani sanyi nabin cinyoyinta tasa hannu ta shafo saitaga jini...

Rintse ido tayi cikin tsananin azaba da kuka ta miqe da qyar goshinta da bakinta na jini ga
Wanda yake bin qafafunta ta tsaya ta kalli gidan sabon kuka na zuwar Mata ta juya jiri na
'dibarta tayi titi.

Napep ta tsayar ko gani sosai Bata iyayi sbd jini daya daketa ga kukan datasha kamar na hauka
Kuma har lokacin Bata daina kukanba.


Qofar gidansu Deen aka ajeta ta fito a dudduqe ta nufi gate maigadi na ganinta ya bu'de Mata
sbd tun wancan zuwan datayi Deen yayi Masa kashedin datazo ya bu'de Mata kofa.


Aharabar gidan ta tarardasu mum sun rufe ko'ina zasu shiga mota Sai ganinta sukayi.

Tana zuwa gaban mum ta zube tana wani irin kuka Mai tsima Rai Dan nantake ya ta6a zuciyar
Davina Da tsananin qaunar datakewa 'dan uwanta tasa tafara qaunar ayshah 'din.

Bu'de mota mum tayi zata shige tayi saurin riqe qafarta cikin tsananin kuka tace,

Mum pls I need to see him..I want to talk to him,,,I was thrown out of my house,my family,,,,
I have no one now,,,he is my only hope now....

Fusge qafarta tayi tareda damqarta tafara janta cikin masifa takai wajen gate ta watsar tareda
nunata da yatsa cikin tsananin baqin ciki tace,

I've never hated something or someone so badly the way I hate you,,,

I hate you to the last core that I can strangle you to death...

My son Nik will never see you or be with you again because he's already in somewhere else,,,

You'll never set your eyes on him for the rest of your miserable existence...
So go, leave,stay out of our lives....

Cikin karaya da tashin hankalin Jin zancen mum 'din hawaye nabin fuskarta tace,

Mum please don't do this to me,,,if not for me please let me see him for sake of his unborn
child.....

Cikin tashin hankali dukkaninsu suka zaro idanuwa musamman ma Davina da wani irin da'din
zancen ya kasheta kafin tayi magana mum ta tura ayshan baya da qarfi ta fa'di kife Nan tasaki
qara tareda dafe cikin Nan sauran jinin daya tsaya ya qara 6alle Mata ta kalli qafafuwanta da
sauri taga yanda jinin ke gudu kafin tayi want motsi ruwan sama suka 6alle mum takalli su
Davina ta nuna musu mota da Ido kafin ta bu'de jaka ta Ciro bundle 'din one one thousand ta
jefawa ayshah ta fa'da mota sukabar gidan aguje Sai airport suna Isa ko minti ashirin basuyiba
jirginsu ya tashi sukayi bankwana da Nigeria..



Qurawa jinin cikinta dake bin ruwan sama Yana gudu tayi zuciyarta na Mata wani irin nauyi,,,,

Jinin tacigaba da kallo har ruwa yagama wankesa yatafi dashi ta rintse ido tareda sakin wani ihu
tareda kuka...

Har aka gama ruwan saman tana duqe gurin tana kuka irin Wanda Bata ta6a yinsa arayuwaba.


Rarrafawa tayi qoafar gidan ta ra6e jikin gate tana rawar sanyi da wani zazzafan zazza6i har
haqoranta na ha'duwa.


Da safe Mai gadi na fitowa yaganta kwance a gurin kamar batada Rai yayi saurin komawa ciki
ya 'debo ruwa ya antaya Mata tasaki ajiyar zuciya ahankali tareda bu'de Ido daqyar.

Durqusawa yayi gabanta cikin tausayi yace,

Kiyi hkr ki koma gida ko kitafi wani guri Dan maganar gaskiya itace Nik yatafi,anvar qasar dashi
Kuma bazai ta6a dawowaba.

Kamar wawiya take kallonsa zuciyarta na wata irin tafasa tabbas tayi ganganci tareda babban
kuskuren barin soyayya ta rufe Mata ido tayi aure bada sanin iyayenta ba gashi yanxu yasamu
abinda yake so ya gudu ya barta da ciki gashi gidansu ankoreta....

Wani mummunan nauyi taji zuciyarta tayi Mata idanuwanta sukai wani mugun ja ahankali taji
tsanar kowa da qiyayyar kowa na shiga dukkanin ga6obin jikinta ta miqe tsaye tareda
durqusawa ta 'dau ku'din da mum ta jefo Mata cikin wani irin yanayi tace,

Zanbawa kowa mamaki,,,
Gidanmu sun rufe idanu sun koreni batareda bani damar gyara laifina ba ko bani uzuri
amatsayina na mace,,,
Sunan dasuke gudun ya lalace har suka koreni saina lalata musu wannan sunan ta yanda ko
qofar gida Babu Mai sha'awar fitowa....

Ku'din da mum ta jefo Mata takalla da jajayen idanuwanta tace,

You'll pay for this queen...
I promise to make all your lives a living hell....
I hate you all..
You'll all pay for my poor unborn childs blood..

Kuka tasaki tanajin zuciyarta na karyewa ahankali tace,

Meyasa duk zaku gujeni adaidai lokacinda nake tsananin buqatarku,,,meyasa Zaku barni
rayuwata ta lalace akan titi....

Wata qatuwar lafiyayyar black Jeep ce tashigo kwanar layin da gudu daga gani matuqin motar
ransa a matuqar 6ace yake kafin tayi wani motsin arxiki motar tayi sama da ita ta watsar.


A rikice kyakkyawar budurwar dake tuqin ta fito Mai gadi yakama Mata ita suka saka mota tayi
asibiti da ita Dan ita batacika son 6ata lokaciba akomai afterall tanada gurin zuwa..


Cikin qanqanin lokaci akayi gama treatments din komai sbd ba wani ciwo tajiba kawai
buguwace a hannu Sai maganin qarin jini Dana masu 6ari daya rubuta musu.


Kallonta fannah tayi cikin yanayin 'dan tausaya tace,

Ya sunanki?

Ayshah"""""tafada ataqaice sbd lurada datayi da fannan idanuwanta a bu'de suke matuqa duk
da tanada 'dan banxan kyan 'daukar hankali.


Ayshah Ina ne gidanku nakaiki sbd ni Nan tafiya zanyi zankoma inda nake Dan ni baqunta nazo
Kuma yau zankoma.


Banida gida Kuma banida gurin zuwa.,kitafi kibarni anan.

Batayi mamaki ba dantaga alamar korarriyace kamar ita awancen lokaco Dan haka kai tsaye
tace,

Korarki akayi daga gida?

'dagowa tayi ta kalli fannan idonta na qoqarin 6oye hawayenta..

Murmushi Mai ciwo fannah tasaki Dan itama ta 'dandani irin wannan ciwon na korar iyaye Kuma
haryau Tanakan 'dandanar ciwon..

Kallon ayshan tayi tareda cewa ta tashi sutafi.

Motarta suka shiga suka baro asibitin tana Hawa titi takalli agogo tareda juyowa ta kalli Ayshah
tace,

To ayshah ni Zan tafi Zaki bini ne ko kuwa kinada gurin zuwa..

Danne karayar zuciyarta tayi tareda sauke idanuwanta Kar kan titi tace,

Muje ni 6arnar suna nafito yiwa zuriata tareda 6ata rayuwar Deen da zuriarsa.


Wata dariyar farin ciki da samun 'yar uwa fannah tayi tareda bawa motarta wuta suka Kama
hanyar barin gari.






*Nasiha,,,,,,iyaye da abokan zaman rayuwa akoda yaushe yiwa dan Adam uzuri abune Mai
mahimmanci sbd rashin bada dama da uzuri shike qarasa ta6ar6arar da alamari qarshe ayi
aikin jahilci da Dana sani ta biyo baya Wanda hakan baida kyawu kwata kwata a addini...*
*Iyaye komai girman laifin da 'yaya zasu yimuku Kar ku kasance masu rufe Ido ku aikata abinda
zai dawo ya zame muku abin Dana sani Don kuwa qeya ce.*

*Allah ya tsare yakuma Kare zuri'ar mu gabaki 'daya*...

_masu cewa wannan yayi, wannan baiyiba wannan yakamata ayi, wannan bai kamata ba
kokuma ga abinda sukeso ace anyi to duk wannan bashine ba idan kun nutsu kunbi labarin
ahankali to ahankali Zaku fahimci yanda labarin yake dakuma darussa tareda alajabin dayake
cikinsa._

*Nagode da qauna*💋







Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comment_






Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_


*28*



_*A zahirin gskia banajin da'din yanda wasu da dama suka dameni da zancen wani bai

kamataba ace ayshah tayi karuwanci da aurenta ba,,*_
*_kusani nimafa musulmace Kuma gwargwado inada ilimi da sani akan addina nakumasan me
nakeyi Kuma ni nasan abinda nake rubutawa amma ku masu karantawa Sai ku kasa hakuri
kuga yanda labarin zai kasance wasuma harda zagi da munanan kalamai to Wanda hakan ba
tunani bane Dan haka please and please for god sake idan Kunga abinda bakwa iya karantawa
to ku barshi ba dole bare zagi da cin fuska yashigo._*😠




Tsakar dare suka shiga garin Abuja Kuma zuwa Time 'din ayshah gaf take da ficewa hayyacinta
sbd mugun zazza6i da ciwon marar datakeji.

Sannu fannah ke Mata cikin tausayawa da damuwa tareda tsoron Kar 'yar mutane ta mutu a
hannunta.

Wata 'yar babbar private hospital dake kusada anguwarsu ta nufa Kai tsaye batareda sun Isa
gidaba Nan aka kar6eta tareda qoqarin fara Bata treatment 'din gaggawa sbd tashin farko suka
gano cikin dake jikinta ne ke qoqarin qarasa zubewa Nan suka fara qoqarin tsayar da jinin.


Tun fannah na 'daukar abin da sauqi saigasu da kwana asibitin.,,

Koda ayshah ta farka abun farko da fannah tace Mata shine azubar da cikin.

Kallon mamaki ta aiketa dashi fuskarta na qoqarin bayyana farin cikinta tace,

Cikina yananan bai zubeba?

Cikeda mamakinta fannah tace,

Yana Nan amma banga amfanin barinsa ba gwara ki zubar tunda shege n....

Cikin tsawa ta dakatarda ita hawaye suka gangaro Mata tace,

Cikina ba shege bane 'dan halak ne,
'dan sunna Kuma Koda shegen ne ta bazan ta6a zubarwaba sbd shika'dai ne abinda Zan riqa
gani naji sanyi arayuwata zuwa Nan gaba,,,,
Bansakaki Zama Dani doleba idan kinajin bazaki iya Zama Dani Dan inada cikiba to ko anan
Zaki iya tafiya kibarni ahakanma nagode..

Ajiyar zuciya fannah tasaki tareda miqewa tsaye cikin kulawa tace,

Ayshah bance lallai saikin zubarba shawarace nabayar a tunanina ba cikin aure bane Kuma
kince bazaki zubarba ba shikenanma ki daina kukan ya Isa haka...Bari naje na kar6o Mana
sallama muje gida Dan gskia nagaji da zaman asibitin.


Tana fita ayshah tabi bayanta da kallo cikin mamakin sanyin halinta sbd yanda ta gasa Mata
maganganu Amma bataji haushiba..

Fannah ta girmeta zaikai kamar da shekaru biyar,,
Fannah kyakkyawar chocolate mace Mai kyan jiki,,Sam batada zafi tanada hakuri da tausayi
Amma a gurin maza labarin bambam ne don kuwa Bata raga musu Bata 'daga musu qafa
hakama batajin wuyar ci musu mutunci sbd namiji ne sanadin qorar da iyayenta sukayi Mata,,

Ahankali tariqota suka fito tashigarda ita mota suka bar asibitin.

A wata anguwar masu Hali gaban wani qaton flat Mai kyau da tsari taga sunyi horn Mai gadi
yazo da saurinsa ya bu'de musu gate suka shiga harabar gidan sukayi parking..

Kallonta gidan tayi zuciyarta na karyewa idanuwanta na qoqarin kawo hawaye sbd tunanin
iyayenta daya fa'do Mata Dan tabbas tafi sha'awar Zama taredasu Koda acikin ruga suke akan
irin wannan daular da aka Tara ta hanyar 6arna.

Qofar shiga babban palon sukayi fannah ta fiddo keys ta bu'de suka shiga.

Zaunar da ita fannah tayi tareda Zama kusada ita cikin sanyin murya tace,

Ayshah Kinga gidana Kuma nikadaice nake rayuwa acikinsa shiyasa ban cika zamaba kullum
ina gurin tafiye tafiye Amma ayshah nayi Miki alqawarin 'dage duk wasu tafiye tafiye na na
zauna na kula dake har lokacinda Zaki haihu Insha allah.


Kallon palon ayshah tayi taga ya ha'du matuqa Dan komai najin da'din rayuwa an zuba Masa
kafin ta maida kallonta ga fannah cikin hawaye batareda tace komaiba sbd ita duk ba wannan
takeso iyayenta da Deen takeso..kuka tasaki ahankali tana shesheka.

Dafata fannah tayi cikin son danne Tata damuwar da kullum take dannewa tace,

Ayshah dole hakuri zakiyi for now har lokacin da Allah zai kawo qarshen damuwar.

Kukanta Tasha Mai isarta kafin fannah ta riqo hannunta takaita bedroom 'daya daga cikin two
bedrooms 'din dake palon..

Qaton 'dakine Mai 'dauke da lafiyayyan makeken gado da wrdrope 'dinsa da qaton mirror Sai

lafiyayyan toilet.,komai na room 'din is blue and white shiyasa 'dakin yayi masifar ha'duwa.

Zaunar da ita bakin gado fannah tayi tareda cewa,

Ayshah ga room Nan kishiga kiyi wanka kifito kici abinci saiki kwanta ki huta zuwa anjima idan
na huta Zan fita nasiyo Miki 'yan kayanda Zaki riqa sawa..

Bedroom 'dinta takoma Wanda ya'danfi na ayshan tsaruwa sbd tsadaddun designers perfumes
da kayan kwalliya masu tsada da mayukan dake jere gaban mirronta hakama.


Ayshah kuwa saidata shaqi sabon kuka kafin ta lallashi zuciyarta ta shiga toilet 'din tayo wanka..

Doguwar riga Mara nauyi ta tarar a kan gado data fito saita 'dauka ta saka Dan tasan fannah ce
takawo Mata.

Abinci fannah tashigo dashi cikin plate ta aje Mata agabanta tareda ruwan faro da
magaungunanta.

Dafa cikinta tayi cikin yanayin sonyin kuka tace,

Sbd Kai ko ke zanci abinci Nasha magani...

Murmushi fannah tayi cikin nutsuwa tace,

Na tabbatarda sonda kikewa wannan cikin ba qaramin so kikewa ubansa ba.

Hawayen datake tarewa ne suka gangaro tace,

Ada kenan,,

Miqewa fannah tayi tareda tattara kayan ta Fice dasu batareda tasake mgnba.

Da daddare fannah taje tayowa ayshah siyayyar kayan sakawa Mai 'dan yawa.




**********
Sannu ahankali tafara sakewa sbd yanda fannah ke kulada it's sosai gashi itama ta 'dauki son
duniya ta 'dorawa cikin kaman yanda ayshah ke matuqar son abinta,,

Lafiya tasamu gareta sosai Dan tuni fatarta ta canxa sbd hutu daya ratsata danko fita Bata

ta6ayiba harsaida cikinta yafara tsufa kullum Sai sun fita shopping kayan baby..

So da dama ayshah najin matuqar tausayin fannah na irin rayuwar data jefa kanta aciki
musamman yanxu datake jinta kamar Yar uwarta ta jini.,

Duk wani Jin da'di da kulawa Babu Wanda fannah Bata Bata hakama duk sati take kaita awo
asibiti.




Zaune take a Palo ta miqarda qafafuwanta dasuka matuqar kumbura sbd tsufan da cikinta yayi
tanacin guava da fannah tasiyo mata tana kallon wani shirin larabci a tasar salamtv.

Fannah ce tashigo palon riqeda handbag wata yarinya kimanin shekara goma Sha bakwai tana
bayanta riqeda 'yar Viva bag.

Kallon fannah tayi cikin murmushi tace,

Anty baquwa Kika kawo Mana.

Zama tayi kusada ita tareda 'daukar yankan guava 'daya taci tana cewa,

Eh 'yar aiki ce nasamo sbd abubuwa sunyi yawa gashi kina gaf dashiga watan edd 'dinki so
Dole muna buqaran helper.. she'll be the one gyaran gida da girki so that I will be able to take
good care of our prince or princess...

Murmushi tasaki tareda kallon cikin tana danne 'dacin zuciyarta da haryau takejinsa kullum
kamar sabo Amma ta koyi danne abinta tun kafin ta haihu abin yashafi 'danta.

'dakin dake gaf da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login