Showing 36001 words to 39000 words out of 50455 words

Chapter 13 - Taura Biyu Book Complete Hausa Novels by Mamuh Gee..pdf

08 Jul 2025

2464




_mugun mafari_,,,

Sannu ahankali saiga ayshah ta warware Ras kamar ba itaba tuni aka sallamesu suka dawo
gida duk da anty fannah tayi mamakin ganin sauyin gaggawa daga ayshan Amma saita
dangana hakan da adduar datake kwana tanayi Mata.


Ayshah kuwa sabuwar duniyar sha aka shiga Dan kuwa tuni takoma school duk wata mashaya
yanxu tare suke zuwa da shanty Wanda Nan take idanuwanta suka qara bu'dewa ta qara
zanzarewa Dan yanxu ko Zama gida Basu cika ba kullum suna club suyi nis su lalla6o gida su
kwanta,,,,,
Lokuta da dama tana idan tana cikin hayyacinta zaunawa take tayi kuka kamar ranta zai fita sbd
ganin mummunar rayuwar data tsinci kanta sanadiyar iyayenta da Deen,,,
Tanason dainawa Amma abin yayi matuqar shiga jikinta Bata iyawa Dan yanxu shiga kowace iri
taga dama yitake ta fita sbd abin ba qaramin fara shiga cikin kanta yayiba Dan ita Shan hauka
takeyi harsaida shanty tafara Dana sanin sata aharkar.


Anty fannah alamarin duniya ya taru yasata gaba tayi kukan harta gaji Amma ayshah ta zare ko
maganarta ba wani jitakeyiba saidai idan abin yasaketa tazo tana kuka tana Bata hakuri.,,,

Tun anty fannah na 'daukar abin da sauqi harta gaji tafara tsanantawa ayshah Amma maimakon
sauqi saima ayshah ta qara zarewa danko gida Bata dawowa wataran idan sukayi dare saidai
takwana gidansu shanty.

Rama da ciwo yafarasaka anty fannah gaba danko fita office Bata iyayi tayi kuka tayi addua tayi
fa'da Amma ba wani sauqi Sai kawai ta tattara kayanta tabar gidan bayan ta rubutawa ayshah
wasiqa.

Yau da wuri tadawo Qarfe bakwai parking tayi taga ba motar anty fannah gabanta taji ya'dan
fa'di sbd tasan anty fannah batada lpia Bata fita ko'ina tunda da'dewa,

Fitowa tayi riqeda handbag dinta cikin shigar doguwar straight gown ta English wear black Sai
blue Vail 'daure akanta da blue designer takalmi masu tudu sosai.,,,

Tayi haske saidai Rama dake tattare da ita dakaga idanuwanta zakayi zargin tana kora qwayoyi
sbd a wani lumshe suke.

Palon tashigo Kai tsaye cikin sanyin jiki Sai ganin Nana tayi rakube tanata darzar kuka...

Rass gabanta ya buga cikin tsawa tace,

Can you please keep quiet,,,ke kullum bakida aiki Sai kuka..

Sharce hawaye Nana tayi tareda miqewa ta miqa Mata doguwar letter.

Kallon Nana tayi ta kalli lettern ta kar6a tana yamutsa fuska ta bude tafara karantawa...



Jikintane yayi mugun saki ta zube gurin jikinta na rawa Sai kawai tasaki kuka cikin mummunan
yanayi na tashin hankali...

I've lost another part of my life today,,,
Once again rayuwa ta nunamin I will never be happy in my life again..,,

Kuka takeyi cikin mummunan yanayi Dan har wani qanqamewa take..

Sunanta taji Nana takira ahankali ta 'dago da jajayen idanuwanta saitaganta tsaye da kayanta ta
rintse ido cikin ra'dadi da quncin zuciya tace,

Kema tafiya zakiyi bazaki iya rayuwa daniba...

Dama wazai iya rayuwa Dani iyayen dasuka haifenima sun gujeni mijin danake tsananin so ya
gujeni,
Mahmud ya tafi,,anty fannah ta tafi kema kitafi dama ni nasan bani ba farin ciki arayuwa sbd
rayuwata tagama lalacewa bamai iya tolerating din mugayen halayen danake dasu yanxu,,,.

Tana gurin zaune tana kuka Nana ta wuceta tabar gidan cikin tsananin kuka da damuwar
halinda tabar ayshah aciki Dan tasan ayshah ada Mai sanyin Hali da hkr tareda nutsuwa Amma

yanxu takoma Banda tsiwa da masifa tareda rashin mutunci ba abinda ta iya.


Tunda Nana ta tafi takasa tashi agurin har tsakar dare da shanty tazo suje mashaya ta tararda
ita cikin tashin hankali tayi kuka har kukan ya daina fita...

Acikin Daren shanty ta kwashe Mata kayanta suka koma gidansu shanty 'din sbd iyayenta basa
qasar zaune ita kadaice Sai tsohuwar dake tayata Zama sbd karatunta.

Duk iya wani farin ciki tarigada tasan ya qare Mata damuwa da baqin cikin rayuwa sun rigada
sun yiwa zuciyarta mummunan kamu sai rayuwa ta qara lalace Mata sbd rugujewar da rayuwar
ta ida yi.




_Years back_.....
Lokacinda manyan doctors suka gama iya bincike da nuna qwarewarsu akan matsalarsa sun
gano yasamu shafewar qwaqwalwa,,
Sunyiwasu mum bayanin komai maimakon nuna damuwa Sai mum ta nuna farin cikinta akan
hakan Dan ko ba komai she'll get her son back yanda takesonsa...

Davina kuwa hakanan taji hankalinta yatashi zuciyarta taqi yarda da amincewa da karsu
fa'dawa Nik komai akan abinda yasamesa dakuma auren dayayi,,,

Sam bazata iya 6oyewa 'dan uwanta yanada Mata da ciki ba Dan gwara yasani yaje ya ceci
matarsa da 'dansa daga baqar wuya.


Tunda ya warke yakomawa normal life 'dinsa as a Christian Davina takasa zama saidata fa'da
Masa komai da farko bai yardaba harsaida yaga nacinta da dagewarta yayi yawa qarshema
wayarsa dake 'daukeda hotunan ayshah dashi ta nuna Masa Nan yaji jikinsa yayi sanyi amma
ackin zuciyarsa bayajin tsananin sonta kaman yanda Davina tace yana tsananin yi.. Saidai tausayinta daya mugun shigarsa na yanda tayi sacrificing komai kan sonsa shiyasa yayi
alqawarin nemota ya inganta soyayyarta garesa.

Cikin sirri suka shirya tafiya Nigeria shida Davina ta hanyar yiwa mum qaryar Mexico zasu
auren wani friend 'dinsa.
Ba musu mum ta amince suka taho Nigeria tashin farko gidansu ayshah suka nufa Kai tsaye.

Su baba alhaji suka fara cin karo dasu a qofar gida.
Gaidasu yayi cikin mutuntawa Dan Koda yake cikin yanayi na shafewar qwaqwalwa wannan
mutunci da tsarkin musulunci har lokacin suna taredashi.

Kallo 'daya sukayi masa jiki duk a sanyaye suka amsa Nan yaso fara yi musu bayanin abinda
ke tafe dashi suka dakatar dashi tareda kallonsa dakyau sukace yabar gidan idan ayshah yazo
nema batanan sun koreta basusan inda takeba.

Kallonsu yayi cikeda mamakin yanda suka iya rufe Ido suka Kori yarsu batareda Duba
yanayinta na 'ya mace ba Kuma harda juna biyu ajikinta.


Gida suka koma cikin ikon Allah da zallar mamaki saisuka tararda Murphy a qofar gidan cikin
shiga ta alfarma ta cikakken musulmi.

Davina ita tayiwa Nik bayanin waye Murphy agurinsa Nan dai suka tattauna ya sanardasu shi
yanxu musulmi ne sunansa muh'd nandai suka ha'da Kai suka duqufa gurin bincike akanta
Amma ba wani lbr.,

Mum kuwa tuni hankalinta yatashi sbd antabbatar Mata dasu Nik 'din basa Mexico.

Davina tun dawowar Murphy taji duk duniya ba abinda takeso kamarsa Dan nutsuwa da tuninta
tuni suka qwace Mata Wanda Sai alokacin take qara jinjinawa ayshah Dan yanxune takejin
abinda taji Kuma itama a shirye takeda ta kar6i musulunci akan soyayyar datakewa muh'd.

Tun mum na 'daukar abin wasa saigasu sun shafe kusan wata hudu a Nigeria wanda tuni sukayi
Nisa tareda maida hankali gurin koyan karatu da sani gameda addinin musulunci Dan kuwa tuni
Davina ta musulunta.

Ganin sunyi neman Amma ba lbari yasa suka koma Amma batareda muh'd ba daya koma
Abuja bakin aikinsa.


Lokacinda suka fuskanci mum haukace kawai batayiba ganin 'yayanta datafi so cikin inuwa da
arzikin musulunci..,,

Rufe idanuwanta tayi ta koresu fata fata a rayuwarta dadynsu kuwa bai tauyesuba yabasu
damar bin addinin dasuke ra'ayin bi.

Ba 6ata lokaci Deen ya Nemo musu admission a makarantar Madina shida Davina cikin ikon
Allah suka samu suka koma Madina suka maida hankali kan karatunsu batareda wata damuwa
ba.

Lokacinda suka kammala karatun Davina takoma gida shikuwa zurfafa karatun nasa yayi Sai
gashi allah yayi Masa baiwar sanin addini Nan take yayi fice yazamo matashi lamba 'daya daya
haddace alqur'ani da littafai da dama akan addini Dan kuwa duk wani taron musulunci da

da'awa Yana cikin manyan baqi da musulunci keji dasu ayanxu,,

Hutu, kwanciyar hankali da arziki Mai tarin yawa sun samu Zama sosai arayuwarsa shiyasa
Mata da dama ke sha'awarsa musamman kyawunsa da class 'dinsa dake fuzgar duk wata mace
Mai sauraron fatawarsa.

Siyama salees shine cikakken sunan yarinyar data maqale Masa tun ranar farko data fara
ganinsa a wani taro dayazo Nigeria a Abuja tun Yana share Mata hardai ya amince akayi
aurensu Wanda ranar 'daurin aurensu a ranar mahaifinsa ya musulunta Kuma a ranar mum
tagano ayshah hartasa aka sato Mata Mahmud takaisa qofar gidan Deen ta aje tareda doguwar
wasiqar cewa ayshah ce takawosa akan Bata buqatar sake ganinsa ga dansa Nan yariqe...

Sosai yaji zafin hakan datayi Sai kawai ya 'dauke yaron ya bar qasar dashi bayan yayi dna ya
tabbatarda dansa ne,


Murmushi mum tayi cikin farin cikin ganin tasamu hanyar fara cusa tsanar ayshah cikin zuciyar
Deen kamar yanda tasan ayshah ta tsanesa yanzu danso take ko kallon juna karsuyi da
mutunci duk ranar dasuka ha'du


Muh'd kuwa duk wani tunaninsa ya karkatasa ga binciken inda zai gano ayshah Dan kuwa
lokaci yayi da zai kar6i abarsa kamar yanda ya qudurta.







Mamuh



_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_
_Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_




*30*



*_gskia I really appreciate_*
*_masoyan taura biyu_*




Zaune take gaban mum Banda tsayayar hawaye ba abinda take sbd duk duniya batajin zata iya
abinda mum 'din tace na cewar ta cire muh'd cikin ranta sbd tasan ba abune Mai yiyuwa ba,

Cikin baqin ciki da damuwa mum 'din tace,

I will never forgive that horrible ninja lady for wat she has done to my family,,
The family I build with so much love,
She distroy everything for me,,,,

Cikin hawaye Khadija (Davina) tace,

Mum please stop blaming ayshah sbd mu muka dama muka za6i rayuwar datafi, rayuwa Mai
'dorewa ta gobe a qiyama,,

Tashi mum 'din tayi jiki a sanyaye sbd gabaki 'daya yanxu Bata iya zaman mintuna da 'yayanta
sbd zancen addininsu dasuke yimata akoda yaushe.


Cikin sallama yashigo qayataccen palon Yana tashin qamshin turaren Arabian oud cikin farar
tsadaddiyar jallabiya fara blue Sai Kyau da hasken fatarsa ya da'da bayyana.

Kallo 'daya mum tayi Masa ta 'dauke Kai ta nufi hanyar bedroom 'dinta yayi saurin Shan
gabanta tareda riqo hannunta fuskarsa 'dauke da wani lallausan murmushi yace,

My sweet mum please don't stop ignoring me like this,,
I love you so very much mum so will you please stop ignoring me mum,,

Kallonsa tayi tayi son 'danta da kewarsa na 'dawainiya da ita ta rintse ido tareda juyawa zatabar
gurin..

Granny,,,,

Cak ta tsaya tareda sakin tareda juyowa Nan take tasaki fuska kamar ba itaba da gudu ya
qaraso gurinta ta 'daukesa sama duk da yaqara girma sosai tace,

I miss you so much my beautiful boy..

Kumatunta yaja cikin dariya kamar yanda taja nasa yace,

I miss you too granny but I won't stay with you today since you're angry with my daddy.

Bedroom 'dinta ta nufa dashi tana cewa,

Your daddy is a stubborn man he doesn't care for me now....


Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka 'dan bayyana sbd yasan mum ta sauko sosai sbd
tsananin sonda takewa mahmud Amma yakasa gane meyasa ta tsani ko sunan uwar Mahmud
'din afada.


Juyowa yayi gefen Khadija dayar kolacin take zaune tana kuka ahankali ya zauna a sofa Yana
kallonta yace,

Menene Kuma Khadija?

Ahankali tace,

Shaikh just pray for me sbd naji ajikina nice Zan biya dukkanin haqqin ayshah da aka zalunta
Dan kuwa tun yanxu nafara ganin ishara Kuma na tabbatarda duk inda ayshah take Bata cikin
kwanciyar hankali tunda Bata tareda iyayenta da 'danta duk sbd soyayya.,,,,

Katseta yayi cikin 'dan yamutse fuska yace,

Karki ha'da kanki da ita sbd ita itace ta za6i kawo 'danta dantayi rayuwar dataga dama afterall
tasan inda nake tunda harta kawomin 'dana so inda tanada niyyar Zama Dani da tuni ta
bayyana kanta Amma she chooses to stay away and wani gefen zuciyana is telling me we are
better without each other.....

Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta tana girgixa Kai cikin kuka tace,

Shaikh kaiba butulu bane karkayi butulci da raharamarda Allah yayi maka ta musulunci ta
dalilinta,
Shaikh kome ayshah tazama arayuwa Kaine sanadi,
Koda yake basai nafada ba Zaku gani akaina duk da banjiba banganiba Amma haqqi zai sauka
akaina.

Miqewa yayi batareda yakuma tanka zancentaba yace,

Maganar zuwana Nigeria ne yataso sbd gobe Zan wuce insha Allah if you're still interested in
coming with us ki shirya.

Wucewa yayi yabarta farin ciki na ratsa zuciyarta najin maganar zuwansu Nigeria zataje taga
muh'd dinta.


Washe gari shida matarsa siyama da 'dansu mahmud tareda Khadija suka diro Nigeria suka
baro mum cikin 'dibbin damuwar ganin gabaki 'daya yayanta yanxu kamar ba nataba nantafara
tunanin mezai Hana tabi nasu addinin matuqar familynsu zai qara Zama Happy family kamar
da.

A qaton lafiyayyan gidansa dake asokoro suka sauka Wanda Nan aka qaro securities agidan
Siyama hankalinta ya qara kwantawa Dan dama tafison zamansu a Nigeria akan can Paris 'din,,

Babbar damuwa da tashin hankalinda take ciki shine rashin haihuwarta har yanxu,,
Tayita yimasa compain akan hakan Amma bai damu ba sbd ganin mahmud dayake jinsa cikin
jinin jikinsa Dan ba qaramin so yakewa yaronba.
Hakan yasa gabaki 'daya hankalinta ya tashi dason haihuwa sbd batason Koda wasa yayi
tunanin maido karuwarsa tada Dan ita Bata 'dauketa matarsaba saidai karuwa Dan bataga
dalilin ha'da shimfida da kafiriba tunda alokacin yanada sauran dabiar kafirai ataredashi.







********
Wani qaton babban hotel daya amsa sunansa na manyan mutane,

Acikinsa akwai manyan halls na alfarma dan meetings ko taron manyan mutane.,

Hakama akwai club na 'yayan manya dake cikin gurin Wanda ya tsaru ya ha'du ba kadanba.,,

Zaune take cikin club 'din tayi crossing legs tana sanye da wata designer English gown red
datayi masifar yimata kyau sbd kwantawar datayi ajikinta Sai wani siririn black scarf Mai adon
red data 'daure gashinta gefe dashi Wanda duk Rabin gashinta a waje yake sbd tsawonsa Sai
hakan ya qara Mata kyau,,
Abuge take banda lumshe idanu ba abinda take shanty dake zaune gefenta waya take tana
kur6a ruwan qwayoyi ahankali tana lumshe ido,,,

Wani kyakkyawan saurayine ya qaraso gurinsu cikin qasaita na kasancewarsa 'dan senator ya
kalli Ayshah dako kallo bai ishetaba yace,

Eshaah my love look at me please,,,,look wat your love has done to m..

Banza tayi dashi tareda 'daka cup 'din dake gabanta ta shanye zuciyarta na tafasa taji Bata
dainajin qunar zuciyarba ta 'daga wani cup 'din takai bakinta yayi saurin Kai hannunsa zai riqe
cup 'din ta miqe tsaye ta 'daga hannu ta sharara Masa wani lafiyayyan Mari Nan take 'yan
koransa sukayo kanta kafin suyi wani yunqurin takuma yanka Masa wani Marin Nan take guri ya
kaure da hayaniyar fa'da sbd wani 'dan governor dayake matuqar son ayshan ya shiga fadan
dama yanajin haushin Abbas 'din sbd yanason ayshah Nan suka hau fa'da harda fasa kwalabe.

Shanty datafi ayshah qarfin jini Dan yanada wuya ta bugu duk abinda Tasha kuwa,
Kamo hannun ayshar tayi suka fito harabar hotel 'din inda Nan take gurin yacika sbd fadan Nan
yadawo.


Fixge hannunta tayi cikin maye tace,

Let go of me shanty,,,I'm not done,,,let me teach the bastard a lesson...

Fitowarsa kenan daga meeting 'din dasukayi agurin yayi mamakin ganin mutane agurin tunda
ko hayaniya ba'ayi sosai agurin.

Kamar a mafarki idanuwanta suka sauka akansa ta lumshesu tasake bu'dewa sai kawai tasaki
dariya Mai qarfi cikin tsananin maye tareda nunasa tace,

There he is,,,,the one and only Niklaus Aiden,
The greatest cheat so far...

Kanta securities dinsa sukayo sbd tuni gurin yayi tsit kallo Yakoma kansu ganin tana qoqarin
6atawa shaikh suna cikin bainar jama'a Amma Abbas yayi saurin Shan gabansu cikin rashin

mutunci yace,,,,.

Karku fara ta6amin babe okay...


Dariya takuma saki tareda nunasa cikin maye tareda kallon shanty da juyayun idanuwanta tace,

Look at him shanty my sweet friend,,,
He is the father of my poor son Mahmud...

He is nothing but a cheat,,,,he uses me and run away like a,,,,, like a,,,
Yesssss like a mosquito..hahhhhhhh

Rintse idanuwansa yayi zuciyarsa na mugun tafasa gashi tuni yafara ganin hasken cameras na
tashi ana 'dauka koba'a fa'daba ya tabbatarda itace ayshah uwar 'dansa,,,


Kanta securities sukayo tayi saurin zillewa tana dariya ta isa gabansa takallesa from head cikin
dariya ta ta6a Masa tana cewa,

Wow Mama's boy yatara muscles bayan yasha duka agunsu ummmmnnn Yama
sunansa,,,,,yesss ya Umar the great heartless parson of the universe,,,,look shanty everyone
look"""""tafada tana qoqarin Kai hannunta kan damutsansa cikin tsananin 6acin Rai da baqin
ciki ya watsa Mata Marin dayasa Rabin mayen dake tareda ita sakinta ya fa'da mota da qarfi
driver yaja sukabar gurin wasu na tir da halinsa na 6oye da yau tsohuwar karuwarsa ta tona..

Ita kuwa baqin ciki takaici da danasani ne suka shigeta na abinda tayi cikin mayen shanty tajata
sukabar gurin..

Koda ya Isa gida Zama yayi a kujera zuciyarsa na tsananin tafasa he can't believe he once fall
for that shameless crazy lady,,,no I can't love that thing'''yafada da qarfi Yana miqewa tareda
fadawa toilet yasakarwa kansa ruwa Dan ji yake kaman zaiyi bindiga sbd baqin ciki da takaicin
ganin Wadda ake cewa yaso abaya.


Qin fadawa Khadija yayi yaga ayshah sbd bayajin zai iya cigaba da Zama da mace kamarta,,,
Koda yafadawa muh'd kuwa ganin yayi hankalinsa yatashi Nan yaqara labarta Masa halayen
ayshar nada shidai shiru yayi Dan baiga duk wasu gud qualities dake cewa tanadasu ba
atareda ita.

Kwana biyu da faruwar hakan sukaje shopping a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login