Showing 324001 words to 327000 words out of 411050 words
Chapter 109 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ki zuba min , yace da sauti marar ƙarfi , kanta a ƙasa ta juyo ta ɗau daya daga cikin plate biyu da suke kan faranti ta fara ƙoƙarin zuba aɓincin ,
Da sauri ya dakatar da ita , " kar ki zuba , chak ta tsaya zuciyar ta na harbawa , jinsa tayi daf da ita ya kai hannu a hankali ya zare plate ɗin daga hannun ta , banɗakin sa ya koma ya ɗaureye plate ɗin tare da chokula biyu , ya dawo ya miƙa mata, ta miƙa hannu biyu ta karɓa , da ido ya bi hannun ta da ya sha ƙunshi .
" Ya isa yace , lokacin da ya ga tana ƙoƙarin cika masa Plate har ya tunbatsa , kan ta a ƙasa ta miƙa masa , ya karɓa yana kallon fuskar ta , kafin tayi wani yunƙuri yace mata " ki dakata na gama ci kar ki tafi ,
A ɗarare ta zauna daga gefe a ƙasa ta sunkui da kai , yana daf da kammala cin abincin Amnee ta ƙira wayar sa , yayi hanzarin ɗauka ," tambayar sa tayi ina Yakaka ? Ka turo ta yanzu ta gama shiri kowa ya shirya ita ake jira har wasu sun tafi ,
Cike da nutsuwa da kwantar da kai yace " Amnee wani wajen za'a tafi ne ?
A gaggauce ta amsa masa da " eh wajen Dinner ɗin Rahima zamu tafi tare baki ɗaya , ta ƙarasa da cewa " ka turo ta yanzu kaji ko ,"
"Amnee , amm Amma kuma zuwa dinner har da ita ? Da dai ita ta zauna a gida Amnee ba wani amfanin fitar ta a daren nan tun...
Muryar ta a ɗan sama Amnee tace "kai kar ka min tsarin wofi ka turo ta mu tafi yau dai ɗaya tal taje , tunda ita ba'a shirya mata nata bikin ba .
Zai sake yin magana ta kashe wayar tana cigaba da yiwa Khaalty Rahima mitar meyasa ta aiki Yakaka sashin Doctor Hamza ? Ga shi zai kawo mata wani iyayi irin na shi .
Murmushi kawai Amnee tayi tana mamakin rigimar Amnee marar tushe , mutum da matar sa a hana ta yi masa hidima ?
Hankalin sa kwance ya ƙarasa cin abincin sa , cikin ran sa neman hanyar da zai hana fitar Yakaka zuwa wajen wani taron can daban yake , a haƙiƙanin gaskiya baya son ta fita da auren sa cikin wasu ƙattin wofi ,su gama ƙare mata kallo , wanda aka kalla a da ma ya isa , duk da cewa dai wasu maganganun da Suleiman ya faɗa masa sun saɓa sosai da zaton da shi yake mata .
Yakaka ta durkusa ta tattara wajen ta haɗe kome yadda ta zo da shi , a hankali ta miƙe zata fita , cikin rashin sanin ta ta taka bakin dogon Hijabinta , saboda sauri da take ta bar inda yake ,
bata ƙarasa miƙewa ba Hijabin ya taɗile ta tayi ƙasa baki ɗaya farantin hannun ta ya bigi ɗan teburin gabanta , miyar da bata rufe sosai ba ta buɗu cooler ɗin yayi ɗan tsallen da yasa miyar tankwaɓewa ta fallatsuwa har cikin idon ta kafin ta kwaranye mata baki ɗaya a jikinta .
Ɗumin miyar tare da zafin attaruhun ciki da ya shiga mata ido yasa bata san lokacin da ta saki wani ɗan ƙaramin ihu ba .
A ruɗe Doctor Hamza ya miƙe yana jera mata sannu , amma azabar da take ji a idanun ta yaƙi barin ta nutsuwa bare ta ji me yake cewa , ihu ta shiga yi tana cewa " wayyo idona ,
Da sauri ya riƙo ta ya kama hannuwanta duk biyu zuwa cikin ɗakin sa ya zarce da ita cikin bathroom , gefen Bath ya zaunar da ita , duk a ruɗe yake da ihun da take yi ya kunna fanfo lokacin da ya ɗauki handle ɗin shower yana tara ruwa a hannun sa , ruwan ya kai ya wanke mata fuskar da shi ya sake cika hannun sa ya wanke mata ,
Yayi hakan sau kusan huɗu amma bata daina kukan da take yi ba , sai kawai ya juya shower ɗin ya shiga fesa mata ruwan a fuska yana haɗawa da wanke mata idon sosai da ma fuskar ta baki ɗaya ,
Hannun sa ta ture lokacin da ta ji raɗaɗin ya ragu sosai , ta fara ƙoƙarin buɗe ido ,
" ya ya ? Ya fita ? Ya tambaye ta cikin taushin murya bayan ya ɗan yi durƙuso a gaban ta yana leƙen idon nata so yake ya ga ta buɗe su ,
Tana buɗe idon ta runtse su da ƙarfi jin har yanzu da sauran raɗaɗi , bata ankara ba ta ji ya ɗago haɓar ta ya matso da fuskar sa daf ta ta , hannu ya sa ya tallafe ƙeyar ta ya fara hure mata idon a hankali
Sassanyar iskar bakin sa tayi tasiri sosai wajen rage mata raɗaɗi , ta kuma taimaka wajen dawo mata da nutsuwar ta , har ma ta fahimci irin kusancin da yake tsakanin su , zuciyar ta ta ji ta buga ɗas!
Da hanzari ta buɗe idanun ta da suka ɗan rine suka kunbura kaɗan , suka yi musayan kallo da ita da shi , nitsar da idanun sa yayi cikin nata yana yawo da ƙwarar idanun sa a tsakanin nata , ji yake tamkar wata dama yau ya samu na gano tare da tsamo abunda yake hangowa a cikin ƙwarar idanun ta da yake kashe masa jiki a duk lokacin da ya fiye kallon su ,
Tsintar kan ta tayi da gaza janye idanun ta , fuskar sa dake daf da ta ta take ƙarewa kallo , sajen da ya bari da yake ta sheƙi a hasken lantarki ya ɗau hankalin ta , kamar ta kai hannu ta taɓa ,
Ganin yadda ta shagaltu da kallon fuskar sa yasa shi hure mata ido , da sauri ta sake rufe idanun nata ,
Kamar an farkar da ita sai ta miƙe tsaye da sauri , ta ɗan matsa daga kusan shi sosai sai lokacin ta ankara da jiƙewar da kayan ta yayi sharkaf ,tundaga kan hijabin jikinta har rigar ta ta ciki .
" shine ka jiƙa ni haka ? Yanzu ya zan yi ?
Ta furta hakan muryar ta cike da shagwaɓar dake nuni da damuwar da zuciyar ta ke ciki ,
Miƙewar shima yayi ya ɗan wara hannu kafin ya nuna mata nasa jikin da yake jiƙe shima , yace
" ku ji ta kamar ba ke kika ruɗani ni ba kika sa na jiƙa jikina , raguwa kawai kin sa yanzu dole na sauya kaya .
Kewaye ta yayi ya fita kai tsaye wardrobe ya nufa ya zaro wata jallabiyar ya tuɓe ta jikin sa yana warware ɗayar Yakaka da ta matse ruwan jikin kayan ta ta murɗo ƙofar a hankali ta fito ,
Da fitowar ta da hango shi ba riga da komawar ta cikin banɗakin ta rufo ƙofar da ƙarfi duk cikin abunda yake ƙasa da minti guda ta yi su ,
Doctor Hamza da duk abunda tayi akan idanun sa , har A'uzubillah da tace kafin komawar ta cikin banɗakin duk ya ji ta ,
Ɗan wani guntun murmushi yayi lokacin da wani tunani ya gifta masa nan take , rigar da yayi niyyar sawa ya ajiye a gefen gadon , a nutse ya nufi ƙofar banɗakin , ba tare da ya taɓa ƙofar ba yace ,
" ki fito ki tafi kar a gaji da jiran ki .
Daga ciki ta ce " to ka gama shiryawa ko ? Dan Allah kayi haƙuri ɗazun ban san kana shiryawa bane ,
Ɗan mitsitsin murmushi ya kuma yi yana cije leɓensa na ƙasa a taƙaice yace " eh na shirya ki fito .
Kan ta a ƙasa ta fito , a ɗan sace ta ƙyallo sa ,ta gan shi yadda yake a ɗazu da sauri sake juyawa sai dai kafin tayi wani yunƙuri ya naɗo ta ta cikin jiƙaƙƙen Hijabin ta ya haɗa ta da jikin sa ,
A ruɗe Yakaka ta fara ƙoƙarin ƙwacewa , bakin ta ya gaza furta ko kalma guda , matsera kawai take nema ,
" Meye kike haka , kamar wacce bata saba ganin Maza a tuɓe ba ? Kar ki min kinibibin ku na mata .
Doctor Hamza yace haka laɓɓansa ɗauke da murmushin da yafi kama da na mugunta , cikin zuciyar sa yana sake haƙaƙewa da abunda yayi niyya , ya juyo da ita da ƙarfi ya ɗago fuskar ta da idanun ta ke runtse , hasken da ya haske fuskar shi ya bashi damar ganin hawayen da suka jiƙa mata fuskar ta ,
Shagala yayi da kallon kowanne ɗigo na tudu da ƙwarmin da yake fuskar ta , kallo yake mata irin wanda bai taɓa yi mata irin sa ba , a idanun sa kome na fuskar ta tsararre ne da ya dace ƙwarai da muhallin da Ubangiji ya ajiye mata shi .
Zuciyar sa take buɗuwa tare da tashin tsikar jikin sa, bai san lokacin da ya haɗe tazarar da bata wuce tudun yatsa guda da yake tsakanin fuskokin su ba , ya haɗe fuskokin su waje guda , tare da ratsa hannuwan sa ya kewaye ta da su sosai ,
Da wani irin yanayin da ya zarce yadda yake da nufin yi , ya shiga yin abubuwan da zuciyar sa ta raɗa masa da ya yi a matsayin gwada Yakaka ya ga ko kalaman Suleiman gaske ne Yakakar kamilallar mace ce , tsautsayi tare da kaddarar rayuwa ce suka faɗa mata ?
Sai ga shi ya gaza tantance Yakaka yake son gwadawa ko kuwa martabar sa ta ɗa Namiji yake aunawa ? Domin kuwa a tsakanin lokacin jin sa yake kamar wannan ne lokaci na farko da gangar jikin sa ya fara raɓar na wata ɗiya Mace .
Yakaka da ake yiwa gwaji ita ta yunƙura ba tare da tayi amfani da ƙarfin kirki ba , ta zare jikin ta daga na shi , bata tsaya ba kamar yadda bata yadda ta bari idanun su sun haɗu ba ta taka da gudun gaske ta fice daga ɗakin da sashin nasa ma baki ɗaya ,
Bata tsaya daga gudun da take yi ba sai da ta tabbatar ta bada tazara mai ɗan yawa daga sashin sa .
Zama tayi akan wani ɗan tudu tana mayar da numfashi harabar wajen babu mutane alama dake nuna an riga an tafi Dinner an bar ta .
Kalaman Doctor Hamza ta tuno ," me yake nufin da cewa ta saba ganin maza a tuɓe ? Kenan nufin sa ita wata ƙasurgumar karuwa ce da ta saba cuɗanya da Maza , shi yasa ya mata abunda ya yi mata yanzu .
Hawayen ɓakin ciki ya zubo mata , tayaya zata yi rayuwa da mijin da yake zargin ta irin wannan mummunan zargin ?
Da jaan ƙafa ta nufi cikin gida , kai tsaye ta zarce ɗakin su inda ta tarar da Falmata ita ɗaya ƙwal tana kwance lamo akan gado
Bata ce mata ƙala ba kamar yadda ita ma Falmatan bata nuna alamun ta san da shigowar ta ba , ta cire jiƙaƙƙun kayan jikin ta sauya da wasu , a hankali ta zo bakin gadon ta zauna , ta ɗan dubi Falmata da jikinta yake bata ba bacci take ba ƙoƙarin haɗiye damuwar ta take lokacin da tace , " Falmata baki tafi wajen Dinner bane ?
Ba tare da ta motsa ba muryar ta can ciki tace " Ban tafi ba Yakaka Amnee tace na zauna nima tunda ke ma Yaya Dakta ya hana ki tafiya , kuma ma bana jin daɗin jikina bayana ciwo yake min .
Shiru su dukkanin su biyun suka sake yi , zuciyar kowaccen su na sake ƙuntata da damuwar dake cin ta a rai , can ta tsinkayi muryar Falmata tace , "Yakaka yau kwanan mu ishirin da ɗaya da dawowa daga Niger ko ?
Ɗan waigowa Yakakar tayi ta dube ta , ba tare da ta bata amsa ba tausayin ta ta ji ya kama ta , babu shakka tasan damuwar Falmata ba zata wuce akan Youssouf ba da shima yake gwada nashi walaƙanci a zaton ta ta hanyar yin shaƙulatin ɓangaro da ƙanwar ta .
Washegari duk baƙi na nesa suka fara watsewa ciki har da Malama maryam da duk wasu dangi na nesa suka yi tafiyar su bayan Amnee ta cika su da kayan biki fal .
Zuwa yammaci gidan ya rage sai su isu 'ya'ya da dangin Amnee , lokacin ne kuma Baa ya aika aka ƙira masa Doctor Hamza , bayan sun gaisa nasiha ya shiga yi masa mai ratsa jiki tare da tarin tunasarwa akan nawin da ya ƙaru akan sa , da kuma wuyar da yin Adalci yake da shi wanda kuma dole ne ya tsayar da shi a tsakanin matansa muddin yana son dacewa da samun Rahamar Ubangiji .
Bayan ya gama masa nasiha da hannu ya masa nuni da saitin akwatuna biyu da adadin su yake kai ɗaya kawai launi da sumfurin su ne ya shabanba , kowanne guda takwas , ya ɗora da cewa " Wannan lefen Matan ka ne ɗayar ka kaiwa Safiya da hannun ka , ɗayan kuma na Amina ne , kamar yadda muka yi da kai nan da ƙasa da watanni biyu nake so ka samarwa da matar ka wajen zama a kusa da kai , idan ma kuma wajen zaman ya samu a yau
ko gobe ne ka dawo ka ɗauke ta ku tafi abun ku Allah ya bada zaman lafiya .
Godiya Doctor Hamza ya dunga yi ƙaunar Mahaifinsa na daɗa ratsa shi tare da ƙarin ganin ƙima da darajar sa , har ya miƙe zai tafi Baa ya sake dakatar da shi wata ɓakar leda da take nannɗe ya miƙa masa "wannan kuma wasu kuɗaɗe ne da aka bani na baka a matsayin gudumawa , ka ƙara wajen kula da gida ,
Da sauri Doctor Hamza ya noƙe hannun sa ," Baa ka bar su ayi amfani da su anan , ni ina da kuɗin da zasu isa nayi kome da su Nagode Baa nagode .
Da murmushi a fuskar sa yace" karɓi mana ai ni na baka .
Ƙarfe biyun rana Doctor Hamza yayi Sallama da iyayen sa zai koma Abuja a yau ɗin saboda gobe yana da tarin aiyuka a office da bashi da damar ɗaukar musu uzirin jinkirta yin su .
Dangin Amnee ma ya musu Sallama bayan ya bada kuɗaɗe masu yawa da yace ayi musu sayayyar duk abunda suke so kafin tafiyar su , sannan ya tsawaita godiyar sa a gare shi .
Da Khaalty Rahima ma sallamar su ta musamman ce da suka keɓe suna yi ta inda ita ma ta ɗora masa 'yar nasihar ta a ƙarshe ta ba shi shawara kan ya lallashi Safiya sosai kar ya bari ƙarin auren da yayi ya ɓata zamantakewar su .
Ƙannen sa mata ma duk Sallamar yayi da su har da Rahima amarya da ba'a riga an miƙa ta gidan mijin ta ba saboda iyayen sa ba 'yan nan bane 'yan ƙasar katsina ne , kuma a halin yanzu duk suma shirye-shiryen komawar su suke can ƙasar America inda suke rayuwar su a can , nan da ƙasa da sati biyu zasu tafi tare duk har da Rahima .
Lokacin da ya gama Sallama da kowa da ya dace , ciki har da Falmata, sai ya shiga ɗan jefa ido waje-waje ya gagara tashi ya tafi , sai daɗa jaan hirar su yake shi da ƙannen sa .
Hajja wacce ita ma tun a waje da ita ya fara cin karo tana tattara harabar gidan suka gaisa har ma ya mata sallamar tafiyar sa ta jero masa addu'o'in da yake jin daɗin irin su ,
Ita ce ta shiga tana ganin sa tace ," Babban likita har yanzu baka tafi ba ? Kai kuwa na ga baka saba tafiyar dare ba garin Abuja ai ba kusa ba , dan ma dai ku manya ne .
" yanzu zan tafi Hajja , yace yana ƙoƙarin miƙewa , Hajja ta shige ɗakin ta tana cewa " Allah ya tsare hanya Babban likita .
Tana shiga ɗakin tayi turus ganin Yakaka kwance akan katifar ta tana buga game da wayar Rahima ,
Salatin da Hajja ta ɗauka sai da ta dire shi da tafa hannuwa sannan ta ɗora da cewa " ni hauwa'u me zan ji me zan gani ? 'yar nan kan ki ɗaya ?
Yakaka ta ɗago kai tana kallon Hajja ,
" me nayi Hajja ko dan na hau 'yar katifar ki ? to bari na tashi , ta ce tana miƙewa ta sauƙa daga katifar ,fatan ta shine Hajja tayi shiru kar a jiyo muryar ta a san tana nan .
Hajja ta ɗora da cewa " tambayar ki nake kan ki ɗaya ? Yanzu ace Mijinki na can shirin ɗaukar doguwar hanya ke kina nan kina latse-latsen wofi ? Bawan Allah shi yasa mana ya gagara tafiya ashe ke ce baki masa abunda ya dace ba wanda zai ƙara masa kuzari da nishaɗin tafiya , tashi nace sakaryar mata , tashi ki fice min a ɗaki , ki fita ga mijinki can yana jiran ki kuyi sallama .
Hafsa da zainab da duk abunda Hajja ke cewa daga ɗaki suna jin ta sarai saboda sama-sama take maganar sai suka haɗa ido kafin su duka ukun su kwashe da dariya , Falmata ma sai da ta ɗan dara , a ran ta tana aiyana wannan kaɗan ne daga halin Hajja , yadda aka san bata da wani aiki sai na faɗin yadda mace za ta farantawa miji Ho Hajja , ya dace a bawa Hajja shugabantar wata ƙungiya ta faɗakar da mata kan