Showing 375001 words to 378000 words out of 411050 words
Chapter 126 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
nata taƙaitattu ne amma masu faɗi ne a wajen sa da zai yi zama na musamman domin yi musu fashin baƙi ,
" I appreciate that and I cherish yours even more, integrity you're worth-valuing, worth-treasuring and worth-cherishing. Your value is such unfathomable Wafaa.
zamewa ƙafar Sofia tayi da ƙiris ya rage ta gangaro daga ƙafar bene, bata taɓa sanin ƙeyar mutum na da ido ba sai da ta ji tana taka matakalar bene ta baya , kalaman na mata amsa kuwwa suna mata rakiya har ɗakin baccin ta da ta na shiga ta zube a ƙasa kan ta na juya mata tana ganin kome na dakin yana tafiya da kafafun sa.
A narke Yakaka take kallon sa lokacin da yake furta mata kalmomin da suka mata zurfi wajen fassara har ya sunkuyo ya sumbanci goshin ta, " ni zan tafi Wafaa .
Ya furta haka yana ɗaga taku ya nufi hanyar ficewa daga falon har ya kai ƙofa ya waigo ta , kallon sa take da murmushin da yafi so a tare da ita a hankali ya ƙarasa ficewa a falon ran sa cike taf da ƙaunar ta fuskar ta tana zanuwar masa a cikin rai yana jin zata ishe shi farin-cikin yau har ya je ya dawo .
Ya tada motar sa a hankali yana ficewa a gidan zuciyar sa na daɗa hasko masa yanayin da ya bar ta a ciki " she's smiley, she is smile just like the sunflower. Ya furta hakan a sarari.
Cike da zumuɗi Yakaka ta kunna wayar da cikin sa'a ta tarar da sabon Sim a ciki , duk da bata taɓa riƙe babbar waya ta kan ta ba amma bata gagara sarrafa wannan ɗin ba saboda Lubna tana riƙe irin su a wasu lokutan tana karɓa tayi 'yan taɓe-taɓen ta saboda sosai manyan wayoyi suke burge ta dan dai kawai bata da damar mallakar su ne .
Ta kwashe tsawon lokaci tana wasa da wayar cikin taka tsan-tsan ta shiga nan ta fita can kafin ta miƙe tana riƙe da wayar duk hankalin ta na kai ta tafi ɗaki ta ɗauko tsohuwar wayar ta ta kunna ta cike da zumuɗi ta kwafi number Hajja akan sabuwar wayar ta ta fara ƙira da ɗokin son ta yiwa Falmata albishir .
Bugu ɗaya Hajja ta ɗaga tana ɗauka da ta ji muryar Yakaka sai ta sa dariya "Ah ka ga manya a baku naku daban Babba Uwar Mama uwargida kuma Amarya a gidan Babban likita , ai yau kwana uku kenan uwarɗakina tana nacin ƙiran wayar ta ki bata samu tun ranar da muka samu labarin kin tare da fatan ana Amarci yadda ya dace ?
'Yar dariya Yakaka tayi ta fara sabo da halin Hajja na jaan zaren magana tayi ta tsawo , "Hajja kenan muna lafiya ya ya wajen ku ?
"Mu ma lafiya ras muke bari na miƙawa gimbiyar wayar ku yi magana tana ɗaki .
"To Hajja nagode .
"Ince da kuɗi a wayar ta ki ? Kar ki katse yanzu zan ba ta
A zaune ta tarar da Falmata ta tasa cikin ta a gaba da cikin kwanakin nan yake wani irin girma na ban mamaki daga gefen ta faranti ne a cike da warmers ɗin da aka shaƙe cikin su da kayan cimaka .
Miƙa mata wayar Hajja tayi tana cewa "Uwar biyu ma za riƙe waya Babba Uwar Mama ce ke kai .
Zunbura baki Falmata tayi kafin ta karɓi wayar tana cewa "Hajja ina faɗa miki bana son sunan nan wai Uwar biyu dan Allah Hajja ki daina .
Ta ƙarasa zancen tana kara wayar a kunnen ta dariyar da Yakaka take yi ita ta fara sauƙa a kunnuwan ta da yasa ita ma ta saki 'yar sassauƙar dariyar jin daɗin sauraron tashin muryar 'yar uwar ta da cikin kwanakin nan take jin kewar ta matsananciya .
"Yakaka na .
Ta ƙira ta da dariya , bata jira ta amsa ba ta ɗora da cewa "wallahi nayi fushi Ya yanyi3 ki ka koma Abuja ba muyi Sallama ba kuma bakya ko nema na yaya Dakta ya mantar da ke ni ko.?
Dariya Yakaka tayi tana rufe bakin ta da hannu ta ce "Falmata sharrin da za ki min kenan ? Haba Falmata na tayaya zan mata da ke 'yar uwa rabin jiki , kiyi haƙuri tunda na zo bana cikin kwanciyar Hankali ne Falmata na ....
Da sauri Falmata ta katse ta "Yakaka bakya cikin kwanciyar hankali ? Me yake damun ki ? Sofi ce ko ? Me take miki ?
"Falmata , abunda Sofi take min ba kyau ta takura min ta hana ni sakewa har fa kare take kawo min cikin ɗaki'....''
"Me ...? Kare ?
Falmata ta katse ta hankalin ta a tashe har tana wani ɗan yin zillo da hakan ya jaa hankalin Hajja da take shirin barin ɗakin dan ta basu dama suyi hirar su ta 'yan uwa ta ɗan dawo da baya tana cewa "Uwarɗakina ince dai lafiya ?
"Wallahi Falmata kare Sofi ta kawo gidan nan take kulle'....
Chak ta tsaya da bayanin da take sakamakon bugo ƙofar da Sofi tayi ta shigo a haukacen ta daga yadda take gama hanya na nuni da alamun ta shawu .
Cikin Yakaka yayi wani ƙugi ƙululu , ba tare da ta katse wayar ba ta sauƙe ta daga kunnen ta ta riƙe ƙam a hannu lokacin da take miƙewa ta tsaya akan ƙafafun ta .
Daga can Falmata ta ji shiru Yakaka ta katse zancen da ta faro yi mata zare wayar tayi a kunnen ta ta duba ta ga cewa Yakaka bata ajiye wayar ba , sanya wayar tayi a handsfree da zaton ko network ne da ɗan ƙarfi tace "Hello Yakaka kina jina ? Ki min magana..
Sautin da ta ji ya fara fitowa daga cikin wayar ya sa tayi saƙare tana kallon wayar .
"Yakakaakaa ko ? Ko Wafaaaa in Doctor voice ? Ko Aminaa Aminaa , whatever dan ubanki me na faɗa miki akan rayuwa ta da kika shigo kin manta alƙawarin da na miki dan me koyawa tsohuwar ki darasi ? Da har ki ka iya yin tsaurin idon yi min rashin kunyar da ta sa aka mare ni akan ki Kin yi kuskuren da ba zan bari ki maimaita makamancin sa ba .
Girgiza kai Sofi tayi kamar lokacin aka mare ta ta riƙe ƙuncin ta "Mari ni Sofi aka mara akan ki.?
Taku ta fara yi tana kusantar Yakaka wacce ko ba'a faɗa mata ba ta fahimci manufar Sofi , kuma tuni ta fara neman hanyar tsira .
Laɓɓan ta na rawa ta fara jaa baya tana cewa "Anty Sofi Dan Allah kiyi haƙuri walla.'..
Wata waftar da Sofi ta kawo mata ya sa ta daka tsalle ta tsallaka kan gadon ta hau ta tsaya..
"Zan kashe ki Yakaka na ga abunda zai faru ba dai kin gwada min naci ba ? Kin nuna a dole Mijina naki ne ko ? To sai na kashe ki kamar yadda na sha alwashi.
Daga can kuka Falmata ta sa ta yunƙura da ƙyar ta miƙe jikin ta na rawa ta miƙawa Hajja wayar da duk abunda Sofi take cewa a kunnuwan su muryar ta na rawa tace "Hajja , Hajja kin ji wai Sofi za ta kashe min Yakaka wallahi kuma za ta iya dan Allah ki bata hakuri Hajja.
Karɓar wayar Hajja tayi ta shiga cewa "alo 'Alo babba uwar Mama ba wa mahaukaciyar kishiyar ta ki wayar dan ƙunduƙurin ubata yau ji min tsinannana? Kishi hauka ne?
Jin shiru yasa Falmata ta sake rikicewa da muryar da take gaf da fara kuka tace ,
"Yakaka , Yakaka Dan Allah kiyi magana , Yakaka ki gudu dan Allah kar ta kashe ki..
"Ke jaa can ar kishiyar za ta guduwa ? Zancen banza ma kenan ,mugun nufi ai baya kashe ɗan barewa Babba uwar Mama zage ki taushe bakin akuyar wofi ki ɗaga ta sama ki doka ta da ƙasa kika yadda kika gudu ni da ke ne , nace ki zage ƙwanji 'yar nan ki kwaci 'yancin ki ta isa ne ma ta kashe ki ? Naushe ta a ƙahon zuci nace.
Hajja ta furta hakan har tana kaiwa iska duka tana cije baki cike da jin wani irin takaici na rufe ta .
Daga can kokawa tuƙuru ta sarƙe tsakanin Yakaka da Sofi da take neman shaƙe Yakaka amma ta kasa samun galaba abun mamaki wani irin ƙarfi ta tarar Yakakan na da shi da ko kusa ba ta yi zaton sa ba dan haka bata ankara ba ta tunkuɗa ta baya bata yi aune ba tayi baya ba shiri daɓas ta zauna da manyan mazauna ta akan wata ƙwalbar turaren da ta faɗo sanadin kokuwar da suke nan take kwalbar tace fusss! Ta fashe a take ta soki ɗuwawun ta.
Lokaci ɗaya wani irin raɗaɗi ya ratsa mata ƙwaƙwalwa da yasa ta saki ihu kafin ta dawo hayyacin ta Yakaka da daman matsera take nema ta tsallaƙe ta da gudu ta fice daga ɗakin bata tsaya ba ta buɗe ƙofar falon ta fita daga ita sai kayan jikin ta ƙafar ta ko takalmi babu sai fa wayar ta da take riƙe ƙam a hannun ta .
Sofi wacce bata saurari azabar da mazaunan ta ke mata ba ta fito gaba gaɗi tana ganin ƙofar falon a buɗe ta fahimci Yakaka ta fice a gidan abunda daman take so kenan .
Dan haka ta tura ƙofar falon da ƙarfi ba tare da ta kulle ba ta juya ta hau sama saboda raɗaɗin da take ji a mazaunan ta tana son ta duba irin raunin da ta ji.
Yakaka wacce take tsaye daga harabar gidan ta hango rufo ƙofar da Sofi tayi dan haka a galabaice ta samu waje daga gefe ta zauna baki ɗaya bugun zuciyar ta ba dai-dai yake ba .
Sofi ta kulle mata ƙofa ta bar ta a waje da tazarar tsakain ta da titi bai wani cika nisa ba sauran mutanen da suke makwaftaka duk za su iya ganin ta haka babu mayafin kirki wannan wane irin rayuwa ce take yi ?
Kiran wayar ta da aka yi yasa ta duba fuskar wayar sunan Hajja ta gani dan haka ta ɗauka tana ɗagawa daga can Falmata da ta kasa zaune ta kasa tsaye ta ce "Yakaka ke ce ? Bata mi ki kome ba ko.? D''
"Falmata ni ce eh na samu na gudo ki....'
"Kika gudu ? Gudu fa kika ce ?
Hajja take tambayar ta daga can kafin Yakaka ta ce wani abu Hajja ta karɓe wayar daga hannun Falmata tana cigaba da cewa
"Ke wacce irin Solobiya ce ? Kishiyar ke bin ki kina rugawa da gudu dan ragwanta da mutuwar zuciya kenan ko me ? Bakya tsayawa ki nuna mata banbancin ƙwarin jikin tsohuwa da na yarinya ? Wai ko ba wannan fantekar matar ta babban likita me jemammiyar fuskar nan ba ce ? Yanzu ita kike gudu ? Ita kike tsayawa tana cashe miki haka ba ki rama ba ? to wallahi kin rako mata 'yar nan ah lalle fa kina ina yanzu ?
A sanyaye Yakaka tace "ina waje harabar gidan Hajja ta koro ni wallahi tsoro nake ta ɗau wuƙa ta soka min dan haka ta ce min wai wallahi za ta kashe ni kuma ni wallahi bana son tashin hankali Hajja ni fa ko musu na fatar baki ciwon kai yake saka ni bare danbe hajja....
"A ah ai fa lalle abun nayi ne wai an biyawa bazaura Hajji , na gani na kuma shaida haka waliyya to kina jina ko ?
"Ba dai ita ta ce 'yar iska bace? Zata hana ki rawar gaban hantsi ke da gidan Mijin ki da ke kuma ta same ki solobiya kike biye mata ?
"Hajja .....
"Yi min shiru 'yar nan barni da ita ke dai bin umarni ne na ki , ince dai can layi ta koro ki ?
"Eh Hajja .
"Da mutane a wajen ko kuwa ?
"Eh da mutane dai kaɗan .
"A yaya kika fito titin ?
Yakaka ta ɗan yi jim ita fa bata cika son biyewa subaɗaɗin Hajja ba muryar Hajjan ta katse ta da ta ji tana sake cewa
"Nace da kayan arziki a jikin ki ko kuwa ɗan diras ne a jikin naki ?
"Hajja da kaya a jikina .
"To yaga su
"Eh Hajja?
"Nace ki yage kayan ki musu mummunan yagu .
"Haba Hajja ya kuma za ki ce ta yaga kayan ta a waje fa take ?
Falmata ta furta hakan tana zaro ido da mamaki
" kar ki katse ni ki min shiru '.
"Babba uwar Mama kina jina?
"Ina jin ki Hajja ki saurareni da kyau 'yanci nake son taya miki ki kwato , shi maganin biri karen maguzawa dan haka duk abinda nace miki kiyi , kiyi kawai ina mai tabbatar miki daga yau bata sake chakumar ki da dambe bare har ta kora ki layi .
"Ince kina da layin wayar shi Hamzan ?
"Ina da shi Hajja
" You katse ƙiran nan ki ƙira shi ki tabbatar kina gunjin kuka za ki ƙira shi kice ya taho yanzu ga matar sa za ta kashe ki kina faɗin hakan idan kin tabbatar ya ji sai ki kashe wayar daga nan ki sake ƙira na.
Doctor Hamza ya gama round kenan misalin sha biyu saura ya ga ƙiran Yakaka , fuskar sa cike da annuri ya ɗaga ƙiran yana jin 'yar guntuwar gajiyar na barin jikin sa .
Sai dai me ? Muryar ta da ya ji cikin kuka ya sa zuciyar sa yin tsalle hankalin sa a tashe yake tambayar ta me ya faru ? Tana kuka ta fara masa bayani bai gama saurara ba ma ya katse wayar hankali tashe ya fara ƙoƙarin barin asibitin .
Yakaka tana sauƙe wayar ta ƙira Hajja da daman tsumayar ta take dan haka nan take ta ɗaga "na ƙira shi Hajja . Ta ce a sanyaye .
"Yauwa ta farka rigar ta ki ta waje-wajen wuyan sannan ta ƙasa ma ki yiwa zanin naki ko siket mummunan yagu ta wajejen cinyar kina jina ?
"Hajja dame zan ya ga ? ba zai ji daɗi ba idan ya gan ni haka jiki a buɗe a waje .
"Kin ci gidan ku ana son ƙwatar miki ƴanci kina gardama cewa nake fitinannar matar sa ta koro ki ? Yi maza ki yage kayan nan dan a kori gaba .
Ba yadda Yakaka ta iya haka ta ɗan yiwa kayan jikin ta rauni da ƙyar saboda ƙarfin su .
Hajja tana iya jin ƙarar ɓarkewar kayan tace "Yauwa to sai abu na gaba da kin dai-daici ya kusa zuwa ki cisge ɗankwalin kan ki ki yasar , kuka kuwa kar ki ƙaƙƙauta har sai kin ga nata hawayen ita ma ba dan kome nasa kiyi haka ba sai dan a kori gaba kin fahimta ko.?
"Naji Hajja .
"Madallah.
Ba'a rufa mintuna goma ba sai ga Doctor Hamza a guje da motar sa da Yakaka tana hango shi ta fara kukan da daman yana cin ran ta kan irin tozarcin da Sofi ke mata.
Ƙafafun sa kamar ba za su iya ɗaukar sa ba ya fito a motar idanun sa da suke bayyana tashin hankali akan ta yana bin duk saassan jikin ta da kallo .
Yana ƙarasowa Yakaka ta faɗa jikin sa shi ma ya riƙe ta gam da wani irin yanayi a muryar sa yace "wa ya mi ki haka ?
Tana shiƙar kuka tace "auntie Sofi .
Hannun ta kawai ya kama suka nufi ƙofar shiga gidan yana murɗawa ya ji ta a ɓude '
"Sofi Wacce take baje akan kujera tana zuƙar shisha daga ita sai 'yar doguwar rigar shan iska gefen ta Sam ne a kwance daga ƙasa ta tasa masa abincin sa a gaba yana ci .( irin ita Bosslady )
Lokacin da ta ɗago kan ta tayi zaton Yakaka ce sai kawai tayi ido huɗu da Doctor Hamza da yake tsaye yana mata wani irin kallo na tsana daga bayan sa kuwa Yakaka ce take rakuɓe .
Assalam Alaykum masu karatu da fatan alkhairi.
Ina dai neman afuwar ku yau da gobe ta fi ƙarfin wasa jiki kuma da jini .
Ina kaunar ku domin Allah.'
Nagode
[4/15, 10:16 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: Mafari
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
52
Ƙarar Turo ƙofar daƙin da Yakaka ta ji yasa ta tashi da sauri daga inda ta rakuɓe tana kuka ta zo jikin ƙofar ta ƙafar ɗan makulli ta leƙa .
Sofi ta hango ta shigo, duk da halin firgicin da take ciki bai sa ta kasa ganin irin kwalliya ta ɗaukar magana tare da jaan hankalin duk wani ɗa namijin da ya ɗora idanun sa akan ta ba da Sofia tayi .
Wani ɗan fito Sofi ta yiwa ɗirkeken karen nan ( Working dog ) sai ga shi ya dako tsalle daga kan gadon da Yakaka bata san yaushe ya haye ba , ya taho jikin ƙafafun Sofi yana kaɗa jela tare da sunsuna ta .
Ƙaramar dariya Sofi tayi kafin ta ɗan yi sunkuyo ta shafa kan karen da farin ciki a sautin ta tace " oh Sam do you know how handsome you are ? You've got the best underbite, and the best butt muscles , Oh Sam I Love you , you really did a good job baby.
Lokacin da ta ɗago kan ta wata ƙatuwar harara ta wurga a saitin ƙofar banɗakin kafin ta jaa wani dogon tsaki tana juyawa akan ƙafafun ta Sam ya bi bayan ta da ɗan gudun sa suka ƙarasa ficewa a ɗakin.
Wata doguwar ajiyar zuciya Yakaka ta jaa tana dafe ƙirjin ta kafin ta ƙarasa zama a ƙasa tana jin wata 'Yar nutsuwa na safko mata, "Anty sofi Muguwa ce , ta aiyana hakan a cikin ran ta lokacin da ta tuno yadda tsakanin su yakasance a ɗazu da safe bayan fitar Doctor Hamza da yayi sammako ƙarfe shida na safe ya bar gida .
Bayan fitar sa ta tashi tana son tattara ɗakin kafin ta fita gaishe da Sofi ta dawo ta hau gado ramuwar baccin gajiyar hanya da suka sha saboda a jiya basu iso gidan ba sai wajen ƙarfe sha biyu na dare dan haka ko da Matar gidan basu gaisa ba .
Ƙarar turo ƙofar