Showing 348001 words to 351000 words out of 411050 words
Chapter 117 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ta sa hannu a hankali ta tsinto su , ta zube su a gaban ta tana kallo cikin ran ta tana tunanin me ake yi da su kuma ?
Jingina kanta tayi da jikin barandar tana rintse idanun ta saboda iskar wajen da take jin ta mata yawa kamar tana ƙara mata ciwon idon .
Da ta rufe idon sai taji daɗi sannu kan hankali taji zaman ya fara mata ba daɗi saboda bayan ta da ya fara ƙagewa , bata damu da ta buɗe idanun ta ba da daman tafi sabawa da duhun dake cikin su.
sai ta kishingiɗa kaɗan da nufin bawa kanta hutu na wani lokaci , sassanyar iskar wajen haɗi da shirun da wajen yake da shi da kuma yanayin jikin masu ciki yasa bata jima ba baccin da bata san yaushe ne ya kawo mata ziyara ba ya ɗauke ta a wajen .
Lokacin da Biyamuradi Youssouf ya iso baki ɗayan Masarautar sai ta ɗauki murna da kiɗe-kiɗe tamkar wanda ake gagarumin biki .
Da kyar ya samu ya zille daga fada nan ma domin uzurin da Tafeeda ya shigar ne na cewar da yayi ya kamata ya samu hutu tunda bai cika lafiya ba har yanzu .
Da ya shigo gida sashin Hajiya Umma nan ɗin ma a cike ya tarar da sashin da katafainin 'yan uwansa waɗanda dai suke cikin ƙasar kama daga waɗanda suke ciki ɗaya har 'ya'yan Hajiya Mama da suke gidan tuni sun yi zangon a ɗakin mamar su labarin tabbatuwar shigowar sa yasa suka yi ɗango zuwa sashin Hajiya Umma.
Haka ya dunga gaisawa da wasu wasu na rungume shi wasu har 'yar ƙwalla suke na jin dadin sake ganin sa a tsaye kyam bisa diga-digan sa irin taryar da suka masa ya sanya shi jin hawaye bai taɓa sanin haka yake zakara a cikin 'yan uwansa ba sai yau , babu shakka da mutuwa yayi da ya bar musu miƙin da bazai gogu ba a zuci .
Daga can lungu ya hango Siyama ita ma ƙwallar farin-cikin ganin sa take tare da tasowar ciwon kewar sa da take yi , ɗan bakin nan nata yaƙi rufuwa daga murmushin da take kamar yadda ta kasa janye idanun ta daga kan sa.
da hannu ya yafice ta yana 'yar dariya tare da jin raguwa ciwon da yake ji a cikin ran sa kan abunda ya same shi yana yin ƙasa da kusan kaso 50% ganin soyayyar 'yan uwan sa ya ishe shi farin-ciki .
Tana murmushi ta ƙaraso zata tsugunna daga gefen sa ya sa hannu biyu ya ɗago ta ya matsa tare da yi mata wajen zama daga gefen sa da fara'a cikin sautin sa yace " Mata ai geufen Mijinta take da mazauni ƙaƙa za ki ɓuya bayan Aicha kina leƙe na ? Ina ɗiyata ban ganta a masu tarɓa ta ba .
" tana bacci' ta bashi Amsa tana sake riƙe hannun sa da yasa cikin nata a lokacin ji take kaf duniya ba wanda ya kai ta jin farin-ciki har wani narkewa take jin zuciyar ta na neman yi bata ƙi ba kowa ya watse a bar su tare .
Wajen ya ɗau dariya wasun su na tsokanar Siyama suna cewa kunyar kinibibi take yi bayan tun ɗazu ta ishe su da leƙe-leƙe .
A cikin su duk babu wanda ya tado da batun abunda Maimounatou tayi masa da wannan kuma umarni ne daga Maimartaba da kan sa da yace " kada a maida zancen labarin tattauna akai .
Hajiya umma ta miƙe tana barin wajen zuwa cikin ɗakin ta a lokacin Allah kaɗai yasan Halin da zuciyar ta ke ciki tayi rauni bata taɓa zaton zai dawo haka ras da shi da lafiyar sa ba babu shakka Allah shine mai yin yadda yaso da bawan sa wani ɗan Adam can bai isa tasiri ba.
Bayan Miƙewar ta bai fi mintoci uku ba shima Youssouf ya mike cikin ran sa ya fahimci Mahaifiyar sa na son ganawa da shi dan haka ya bi bayan ta zuwa cikin ɗakin .
Bayan yayi Sallama ya tura kai ciki , bisa sallaya ya hango ta riƙe da Alkur'ani , ta ɗago kan ta tana saita ganin ta a kan shi fuskar ta ɗauke da Murmushi ya ƙaraso daf da ita ya zauna yana riƙo hannuwanta baki ɗayan raunin da yake ji a lokacin shine ya taso masa " Umma Allah shi min dawowa ban mutu ba kamar yadda suka so .
.. ya furta hakan hawayen da suka cika idanun sa na sauƙa , yana jin yadda zuciyar sa ke yin kuka.
a take ita ma zuciyar ya ta karye tun faruwar lamarin yau ne rana ta farko da Youssouf ɗin yace wani abu yau ne kuma rana ta farko da ta ga kukan sa a tunda ya zama cikakken mutum.
Kan shi ta ɗora hannun ta kafin tace " ka dawo Youssouf ita cuta ai ba mutuwa ba wani kuma bashi da tasirin datse rayuwar wani sai fa idan kwanaki sun ƙare ka yi godiya ga Ubangiji doumin shi ya baka kariyar da basu idda nufin su ba Allah ya sa hakan ya zama kankara na daga zunuban ka .
" Amin-Amin Umma, ya amsa yana goge ƙwallar sa da hannuwan ta duk biyu ta taya shi tamkar dai lokacin da yake ɗan yaron sa.
" Kar ka yiwa maƙiya kuka kamar kai ba jarumi bane ? Hakan zai iya barantaka da matsayin da kake kai na Soja mazan Fama sannan kuma Yarima sarkin watarana jarumi bai yiwa maƙiya kuka idan sun kai shi ƙasa ya samu dama miƙewa yake ya gyagije a cigaba da fafatawa .
" hakan ba kome bane da ya wuce ƙarin ilmi cikin zaman duniya ka lura ka gane ba kowanne so bane yake zama na gaskiya , ba kowanne murmushi bane yake zama na ƙauna wasun ai shiga suke irin ta burtu suyi aron halayya da kamanni domin cimma wata mummunar manufa tasu su idar da mugunta ka kiyaye Yossoufa .
Kallon ta yake bai ko ƙifta idanun sa zuciyar dake ƙirjin sa ya buɗe yana ƙarbar duk wasu kalmomin ta yana musu adana saboda dayawa daga cikin zantukan ta bai kai ga gane me take nufi ba a yanzu ? Har kawo yanzu cikin ruɗani yake mai yawa '
har kawo yanzu zuciyar sa bata bar nacin tambayar sa me yasa Maimounatou tayi masa haka ba ? yana son ganin ta domin ita kaɗai take da amsar tambayar nan .
Ga mammadou ya kasa amincewa kiyayyar da yake masa har ta kai ya kashe shi ? Mammadou ɗan uwan sa ne da yake kusa da shi a haihuwa cikin jerin 'ya'yan gidan mutane biyu ne kaɗai a tsakanin su Bilal da kouma Yacouba da suke ɗaki guda.
Hajiya Mama kouwa da ɗai ba zai yafe mata ba da ta zama jagora na lalacewar rayuwar sa da zama tsanin faɗawar sa a duk wasu munanan aiyuka da yayi a baya.
Muryar Hajiya Umma ta katse masa zurfin da yayi cikin tunani inda take miƙa masa 'yan mukullin ɗakunan sa tana cewa "Magarib ta gabato ka tai kayi haramar Sallah nasan Maimartaba zai nemi ganin ka doumin ku tattauna ya ji ra'ayin ka kan duk waɗanda suka maka ƙeta kada ka cutar da kan ka wajen hanawa a bi ma hakkin ka , ka yafewa wanda duk zuciyar ka ta amince da yi masa yafiya , kada kouma ka ɗaukarwa kanka aniyar zama da wanɗanda zuciyar ka bata aminta da su ba ka saukakewa kanka sake faɗawa ga hatsari irin wanda ka fito a baya Allah ya ƙara ƙiyaye mouna kai sannan ka tsanan ta addu'a .
"Amin Umma na kouma gode sosai Allah ya ƙara nisan kwana tare da lafiya .
Lokacin da ya fito mafi yawan 'yan uwansa sun watse sun tafi hidindimun su wasu kuma suna haramar sallah Ubbo ce kaɗai a zaune da ya fito dariya suka yiwa juna shi da ita yana wucewa tace " Fita kake yi Yarima ?
" zan tai Sallah , ya ce mata yana ƙarasa ficewa .
Bayan ya idar da Sallah gajiya duk ta taso masa tun yana sallar yake hamma dan haka bai tsaya sauraran masu son gaisawa da shi ba ya nufi cikin gida sashin sa ya tasamma saboda so yake yayi wanka da ruwa mai ɗumi ya ɗan huta kafin lokacin isha'i da yasan bayan sallar isha zasu gana da Maimartaba .
Masu gadin shiyar sa suka buɗe masa ƙofa ya shiga , haske ya wadaci harabar da taimakon security lights dan haka ya nufi sashin sa kai tsaye yana janye ganin sa daga shiyar da Maimounatou tayi zama da ƙoƙarin son raba zuciyar da damuwar da take rufto masa ya hau kan 'yar barandar sa ya kai hannu yana kunna wuta domin ya samu damar buɗe ƙofa .
Zuciyar da tai masa wani ɗan ƙaramin tsalle lokacin da ya lura da wanzuwar mutum kwance akan barandar kusa da ƙafafun sa ,
"Wanene nan ? ya tambayi zuciyar sa yana yin baya kaɗan cike da mamaki yana kure kallo zuciyar sa a dake da ƙoƙarin ganin fuskar ta da ta juya baya tana baccin ta hankali kwance
Motsin sa da yayi da ɗan ƙarfi yasa ta motsawa ta juya zuwa rigin-gine tana motsa idanun ta da suka yi nawi .
Saƙare yayi yana duban ta karo na farko da ya ji ya yarda cewa akwai Mafarkin ido biyu domin shi yake yi a yanzu.
. "Fatima-zahra ya ƙira sunan ta a can ƙasan maƙoshi bata amsa ba saboda baccin da yake son sake danne ta .
Tsugunno yayi a hankali kamar mai tsoron kar ya taɓa ta ta ɓace ya kai yatsun sa biyu kan fuskar ta ya shafa .
Da sauƙar hannun sa a fuskar ta ta buɗe idanun ta da suke luf-luf cike da rauni ta ɗora ganin ta akan fuskar sa da
"Fatima-zahra est-ce vrai ? Ehm ? est-ce vrai ? Ya furta hakan muryar na 'yar ƙyarma .
Hannun sa da yake cigaba da mata yawa a fuska ta riƙe da nata hannun kafin ta fara yunƙurin tashi sai dai kwanciyar da tayi a kan floor ba tare da shimfiɗa ba yasa jikin ta yin ciwo musamman haƙarƙarin ta .
Lura da yadda ta kasa tashi farar ɗaya yasa shi tallafar ta gaba ɗaya ya zaunar da ita lokacin da shima yake yin zaman dirshan a ƙasa ya jingina ta da jikin sa kamar wanda ya tuno sai ya ɗaura dukkanin hannuwan sa biyu akan tudun cikin ta yana shafawa da buɗaɗɗiyar muryar sa yace
"Fatima ki min magana mana don Allah , kece kuwa ?
Kewar sa mai girma da take ta faman yaƙa tsawon watannin da suka yi basa tare ita ce ta taso mata baki ɗaya a yanzu ta kassara duk wata juriyar ta sai ta juyo a hankali rana ta farko da ta ɗaro hannuwan ta a fuskar sa ta riƙe shi da sanyi murya tace " Baban Mama est-ce vrai ? Meyasa ka tafi ka barmu tsawon lokaci baka neme mu ba ? meyasa ? Ka sa min ciwo a zuciyata ta , kasa kullum ina ta kuka . ƙarasa zancen tana janye hannuwan ta daga fuskar sa hawayen ta suka fara sauƙa .
Riƙo ta yayi lokacin da ya lura tana jaa baya daga kusan sa cike da tsoron kar ta sake tafiya ta bar shi ya shiga share mata hawayen ta yana cewa " ke kika bar ni Fatima kin manta ke kika tafi ba tare da izni na ba , baki ko min sallama ba kika bar ni ? Fatima ke ma bakya sona ko ?
Kan ta ta mayar kirjin sa da ƙarfi tana jin farin-cikin sake ganin sa tana jin kamar an bata maganin wata cuta dake cinye mata nishaɗin ta , ta kewaye shi da hannuwan tana riƙe shi ƙam-ƙam .
"Oshh , yace yana ɗan ɗaga ta daga jikin sa saboda raunin sa da ta fama .
"Fatima ina da rauni a jiki , baki san nayi jinya ba kou ?
Idanun ta suka yi rau-rau tana kallon a hankali ta motsa bakin ta tana faɗin "sannu ,
Da ido ya amsa mata da yasan ba lalle ta gani ba da nishaɗi cikin muryar sa yace "Ya babyn mu ? Lafiyar shi lau kou ? Naga yayi girma , ya zama babba alhalin bana ganin sa .
Bai jira ta ba shi amsa ba ya ɗaga ta suka miƙe tsaye yana ɗora faɗin " mu tai ciki ki bani labarin yadda kika zou nan kuma ki nuna min Baby na na gan shi sosai .
Ƙin motsawa tayi a hankali ta zare hannun ta daga cikin nashi kafin tace " nan ba shine masauƙin mu ba a can wajen Umma muka sauƙa can zan koma .
Sake riƙo hannun ta yayi ya ja ta jikin sa ɗan tunbin ta ya tokare haɗuwar fuskokin su muryar sa a ƙasa da wani irin yanayi yace "to ai nan ne gidan ki nan da muke tsaye nan ne shiyar gidana nan shine ɗakina ya mata nuni da ƙofar ɗakin su .
Cike da son samun haɗin kan ta ya cigaba da cewa ko kin koma yanzu tunda na dawo gobe nan za'a kawo ki , kin ga nayi rashin lafiya ma baki ko min ya jiki ba , muje ciki na nuna miki inda aka min fiɗa .
Da sauri ta ɗago kan ta muryar ta tana rawa tace "yanka ka aka yi ? Aina ? Amma ka warke yanzu ? Ni fa ban san kana rashin lafiya ba sai da suka je tahowa da ni suke faɗa .
Langwaɓe kai yayi da son ta tausaya masa yace " nayi jinya iriyar wacce ban taɓa makamanciyar ta ba Allah shi ɗagga ni da war haka na daɗe a kushewata .
Ta buɗe buɗe baki zata yi magana suka fara jiyo muryoyi ana hira da dararraki ana kusanto su ,
A tsorace Falmata ta zare jikinta daga nashi a kunnuwan ta masu saurin ɗaukar sauti ta tsinkayo muryar Ubbo cikin masu maganar ,
Muryar ta tana ɗan rawa tace " ni ni zan tafi ga mutane suna zuwa kar a ganni ace kuma na biyo ka .
Yana ƙokarin sake riƙe ta taƙi yadda da sauri ta sauƙa daga barandar tayi bayan shuke-shuken da suke kusa da ita .
Da wani irin yanayi yayi tsaye hannuwan sa biyu zube cikin aljihun wondon sa har Siyama da Ubbo suka ƙaraso wajen bayan su bayu ne su uku suna bin su ɗayar saɓe da Yumna a ƙafaɗar ta biyun suna riƙe da manyan tire-tire da aka jera abinci bisa .
Kallon su yayi kafin ya ɗauke kai ya juya yana buɗe musu ɗakin
"Biyamuradi daman kana ta tsayuwa nan ? Ko kouwa yanzou kaima kake isowa ?
Ubbo ta tambaye shi ,
Bayun da suke gaishe shi ya amsawa gaisuwar kafin su wuce ciki Siyama na gaba tana musu jagora.
"Tun-tuni na zou Ubbo , ya amsa mata yana satar kallon inda Falmata take maƙale ran sa sam babu daɗi damuwar sa kar wani ƙwaro ya cije ta .
" To ni zan koma sai da Safe ku kula da kan kou .
Gyaɗa mata kai yayi lokacin da take juyawa Bayun da suka ajiye sakonni hannuwan su suna rufa mata baya bayan Siyama ta sallame su daga ciki .
Suna ɗan bada tazara ya sauƙo daga kan barandar da sauri ya nufi inda Falmata take kafin ya ƙarasa daga bayan sa Siyama tace " Baban Yumna wani wurin kake tahia ? Na haɗa ma abinci fa kouma ga wanka ma na tsumayen ka .
Juyowa yayi yana kallon ta ya ga yadda ta ƙarya wuya tana tsare shi da idanun ta , a dai-dai lokacin ya rasa takamaimai amsar bata yana ganin ta ta taho har gaban sa tana murmushi ta saƙala hannun ta cikin na shi .
"Ka bar koume zouwa gobe yanzou lokacin hutu ne Maimartaba da kan shi yace Umma ta sanar da kai ka huta yau sai daren gobe za ku gana .
Jan hannun sa tayi tana 'yar dariya ta sake cewa "mu tai ciki na kula da kai Vous êtes mon patient pour aujourd'hui et je suis votre médecin.( kai marar lafiyan da zan kula da shi ne a daren yau nice likitar ka )
Cikin idanun ta ya mayar da duban sa yana lalubo fassarar kalmomin ta a cikin su, murmushi ta sake yi masa tana kashe masa ido da yasa shi yin dariyar da bai shirya mata ba , cikin ran sa yana mamakin yaushe Siyama ta falle ya haka ? ya jaa ta jikin sa hannun sa riƙe da kugun ta suka juya tare muryar sa ƙasa-ƙasa yace mata " Fille, es-tu sûre que tu peux prendre bien soin de ça, ta patiente? ( Yarinya kin tabbatar za ki iya kula da wannan marar lafiyan naki da kyau ?
Dariya ita ma ta saki tana rufe fuskar ta da tafukan hannun ta cike da jin kunya gefe guda zuciyar ta na madallah da 'yar uwa irin Ubbo da duk wasu shawarwarin ta basa wuce akan yadda zata yi ta karkato da hankalin mijin ta kan ta.
Sun kai kan barandar sa ya juyo yana sake kallon inda Falmata take a idanun sa ya ga motsawar ta a wajen .
Siyama ta jaa hannun sa zuwa ciki suka turo ƙofar .
A hankali Falmata ta fito daga inda tayi maɓoya idanun ta shaɓe-shaɓe da ƙwalla zuwa yanzu ta tabbatar ita 'yar karo ce a wajen sa da kaddara ta haɗa su marar yanci ce ita da koyaushe take duƙunƙune a gefe.
Siyama ita ce matar da take da 'yanci na yin duk yadda ta so da shi a lokacin da duk ta so amma ita ai a ɗosane take da kuskure kaɗan zata yi dangin sa su tunɓuke ta .
Idanun ta suna ruwa ta baro sashin da kyar saboda bayan ta da yake rirriƙewa sai dai lokacin da ta tasamma komawa masaukin ta sai ta rasa hanya ,
Sai lokacin ta lura da sashi-sashi ne a ainahin gidan da duk gine-ginen su iri ɗaya ne sai ka lura da kyau zaka iya tantancewa ko kuwa idan daman ka san gidan sosai .
A idanun ta da suke da rangwamen lafiya ga kuma duhun dare ba zata iya tantance ina ta fito ba sai dai