Showing 39001 words to 42000 words out of 411050 words
Chapter 14 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
saukin tafiyar da dukkanin lamurana idan naje cikin su ," ba akan mutum guda zaki sanya ido ba akan duk wasu makusanta biyamuradi youssouf , nasan tsawon shekara guda zai ishe ki kammala aykin da na aike ki ," idan na zo babu wahala zan sauyawa siyama ke da wata baiwa daban ,amma a yanzu ke yafi chanchanta da ki tahi ," ki kula sosai bana so a samu matsala zan dunga tuntuɓar ki lokaci zuowa lokaci ,"
Cikin girmamawa da miƙa wuya baiwa gnala ta amsawa uwargijiyar ta ,"cikin ran ta kuwa tana tunanin wanne lamurra uwargijiyar ta ke son aiwatarwa a masarautar na maraɗi da har zai kai ta zaman aure da magajin garin ,????????
Kafin karfe baƙwai na safe siyama ta gama shirin ta ,an yi mata jagora zuwa sashin matan sarkin ɗaya bayan ɗaya ta kai gaisuwa inda a karshe tayi zango a fadar mai martaba sarkin agades inda nan ma ta kai gaisuwa tare da biyamuradi youssouf wanda shima yake shirye tsaf cikin shirin sa na tafiya,"
Ƙarƙashin rakiyar dogarai suka sadu da wurin da motocin su suke batare da bata lokaci ba suka shiga , sai dai a yau saɓanin jiya baiwa gnala ita ce a mazaunin mai zaman banza yayin da siyama take maƙale daga jikin kofa gefen biyamuradi wanda tun bayan gaisuwar su da ya amsa ita da gnala ɗin bai sake bi ta kan su ba bai kuma tambayi siyama wacece gnala ɗin ba ,"domin gimbiya maimouna ta gama yi masa bayanin kome ,"inda ta bayyana masa ayken ngla ɗin tayi zuwa niamey ,???( koh meyasa ta boye masa gaskiya )
_______
Tafiya yankin azaba tabbas haka ne domin ba su suka sami isa niamey ba sai bayan magarib ," yayin da kai tsaye ya sa suka wuce gidan "ubboh" wacce tun jiyan take ɗokin zuwan ƙanwar ta mafi soyuwa agare ta ,"
Da gudu-gudun su suka fito ita da ƴan kyawawan yaran ta huɗu ," suka tarɓe su tare da jagorantar su zuwa ciki , inda ta miƙawa mai kula da hidimar gidan namiji ,"mukullin sashin da suke sauƙar baƙi ya buɗewa youssouf da muƙarabban sa sai dai biyamuradi youssouf ɗin ya dakatar da ita ta hanyar sanar mata da cewa karfe takwas suke da taro (meeting) kuma zuwa asubahin yau jirgin su zai ɗaga zuwa nigeria dan haka basu da isashen lokaci ," hakuri ya bata ganin yadda tayi kicin-kicin da fuska tana mitar bata lokutan da aka yi wurin shirya musu abinci shi da muƙarabban sa ,"ƙarshe dai dole ta sa suka kwashi abincin bayan ta sa anfito musu da shi ,suka yi sallama cike da ƙaunar junan su ,"domin duk da kasancewar su abokan faɗan juna amma wannan tsabtatatciyar ƙaunar ta tsakanin saƙo da saƙo tana nan tana gudana a tsakanin su ," koh sun yi faɗa basa jimawa suke shiryawa ba'a shiga tsakanin su ,"
Har ta ga ficewar motocin sa daga gidan tana ɗaga masa hannu zuciyar ta cike da ƙauna tare da tausayin ƙanin nata ganin irin aikin wahala da bautawa ƙasa da ya zaɓarwa kan sa ,"
Gefe guda kuma tana tinanin damuwar da ta hango kwance a ƙwarar idanun siyama cikin sassarfa ta juya gami da nufar cikin gidan ," koma meye dole zata magance mata matsalar ta saboda ita kam duniya bayan mahaifan ta bata da kamar mahaifiyar siyaman har abada baza ta mance da ƙaunar ta ba ,"
_____
Karfe huɗu da rabi na asubahi agogon niamey jirgin su biyamuraɗi youssouf ya ɗaga Daga "Diori Hammani international airport " zuwa nigeria ,inda karfe shiddah da mintuna arba'in suna cikin tashar jirgin sama na "Nnamdi Azikiwe international airport Abuja Nigeria ",......
Naso chapter nan tafi haka yawa, "amma ban samu dama ba, "kuyi manage da wannan din insha Allah mai yawan yana tafe, "
Koh kun San comments din ku suna kadan? 😕ku Kara ku yunkuro a tattauna ku fada min ra'ayoyin ku akan abun da yake faruwa, da ma Wanda kuke hasashen zai faru a nan gaba, Domun nishadin ku nake yi. 😍
#vote
#comments
#share
#son so
#fkrh
[6/24, 9:59 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: Fikrah writers association
*MAFARI........*
( _Hargitsin Rayuwa_ )
*Ummu'muaz*
9
Misalin karfe biyu na rana ya kammala da kome da ya shafi sabon wurin da zai fara aiki inda aka tura su shi da sojojin dake ƙarƙashin sa chan tsakanin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno ,"
Karfe huɗu jirgin su na sojoji ya ajiye su a cikin garin maiduguri inda zasu kwana zuwa washegari su wuce inda suka nufa ,"
Tun isar sa babbar hedkwatar soji na birnin na maiduguri , hankalin sa ya tashi da ganin irin taron mutane maza da aka gaggarƙame cikin ɗakunan horo , a galabaice matuka , cikin azabobi da horo mai tsanani wanda a gaban idanun sa ma yaga an fidda gawarwakin jama'a daga cikin ɗakin horon da azaba ta kashe su ,"
Duk da cewa a matsayin sa na babban soja hakan ba bakon abu bane ,toh amma zuciyar sa ta taɓu da yaji daga bakin wani sojan nigeria cewa waɗannan mutanen , mutane ne waɗanda aka kama akan zargin suna da hannu wurin tada tarzomar boko haram da ba'a kai ga tabbatar da laifukan nasu ba ,sune a jibge a garƙame cikin horarwa da azabtarwa , yunwa da ƙishirwa ,rashin isashen muhalli ta yadda wasu a tsaye suke wuni , wasu a tsugunne ,wasu a tanƙware , wanda yawan su ya tasamma dubunnai ,"
Gagara samun nutsuwar zuciya yayi bayan ya koma masaukin sa ,zuciyar sa sai kai kawo take da tunanin san samar da mafita ga waɗannan bayin Allah waɗanda a zahiri akwai zalinci cikin irin wannan ajiyar da ake musu ,kamata yayi a miƙa su ga kotun ƙasa ta yankewa kowa hukuncin sa dai-dai da shi waɗanda basu da laifi a sake su , wannan hukuncin ajiye su ana gana musu azobobin da suke kai su ga rasa rayukan su yayi tsanani da rashin dacewa ,"
Har gari ya waye bai sake marmarin fita ba sai da suka tashi barin ainahin cikin garin maidugurin zuwa bakin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno , a tare da shi da tawagar sojojin su na niger da kuma ƙarin wasu sojojin nigeria , zuciyar sa cike da tausayin al'ummar da sanadin boko haram ta ɗaiɗaice suka bar ainahin cikin garin na maiduguri .
*******
Cikin kwanaki biyar ɗin da su yakaka da falmata suka ƙara cikin sansanin su basu tsinci kome ba sai tarin wahalwalun da suka sake jikkata gangar jiki da ruhin su ,"
Domin zuwa yanzu karfi da yaji su yakaka sun zama ƴan aikin matayen nan da aka haɗa su rayuwa a ɗakuna ɗaya da su,"
Ta bangaren yakaka matar da suke kwana tare wacce ake kira "fanne" ta maida ta baiwar ta wacce take yi mata bauta nata da na ƴaƴan ta , tun daga kan wankan yaran biyu har zuwa wankin bargunan su da kullum ta Allah sai yaran sun zabga fitsari , wankin ƴan tsirarun kayan yaran da koyaushe ba'a rasa shi da guntun kashi da fitsari wanda yakakan take shan wahala wurin wankin saboda rashin isashen ruwa da sabulun wankin ,uwa uba rainon yaran da suke kusan yini goye bisa bayan ta duk wata jigila da su take yi suna ɗane a baya , ta sauke wannan ta goye wancen ,uwar su kuwa tana chan cikin yaran mata tana zuba hira da ɗinkin hular ta ,"bata chas bata ass ,
Ga falmata kuwa duk da kasancewar ta miskiniya amma hakan bai sa ajus ta ɗaga mata kafa daga sanyata ayyuka ba ," tun farar safiya idan ta tashi daga kan shimfiɗar da a yanzu ita kaɗai ke kwana a cikin gidan sauron sakamakon irin azabar da take ganawa falmatan cikin dare ya sa ta hakure ta samawa kan ta salama daga ,zagi hantara ,hauri , mangari da mintsinin da ajus take buwayar ta da su cikin dare , ta bar kwana a gidan sauron ta komo bakin kofa tana shimfiɗa zanen ta tana kwanciya bisa ,"
amma duk da hakan ita ke lalubawa ta naɗe gidan sauron ta kuma ninke kayan shimfiɗun da ajus ɗin ta kwana a kai , bata bar ta haka ba kullum ita take ɗebo mata ruwan wanka a bokiti da na tsarki a buta , daga bakin famfo inda anan suke samun damar haɗuwa ita da yakaka wacce ita ma take zuwa ɗibo ruwan hidimar fanne da ƴaƴan ta , famfon baki uku ne rak da shi kuma idan aka tayar da injin bada ruwan karfe biyar na asubah zuwa karfe bakwai na safe ake rufewa sai kuma lokutan sallah da shi ma na ɗan kalilan ɗin lokaci ne sakamakon rashin man tada injin tare da rashin wutar lantarki ,"
dan haka yaƙi ne tukuru yake tashi wurin kokowar ɗibo ruwan wanda mai karfi ke ture na ƙasa da shi ya samu ya ɗiba ,"ire-iren su yakaka kuwa da kƴar da suɗin goshi da faɗawa cikin dagwalo tare da jin ciwo take samu ta cikawa falmata nata kayan ɗiban ruwan "da yakakan take tsaida ta a gefe ta hana ta shiga turmutsutsun ɗibo ruwan" ta kuma ɗibo nata , wanda mafi yawancin lokuta ake kashe injin bada ruwan akan bokitin ta ," hakan ya sa har yau da suke cika kwanaki shidda wanda yake dai-dai da kwanakin su bakwai da barin mahaifar su ,fatar jikin su bata ga ruwan wanka ba sai dai ɗaurayar kafafu da hannaye zuwa fuskokin su da suke yi da ruwan alwala ," dan haka duk suka bi suka sake hautsinewa tare da ficewa daga kamannin su ,suka zama yarkace yarkace tamkar sabbin mahaukata.
Ɗan dama-daman yagana ce wacce daman ita ta ɗan fi su wayewa da buɗewar idanu saboda ta tashi a alkaryar da take da wadatuwar wayewa , dan haka bata yadda kowacce mace ta nemi taka ta, bata yadda tayi aikin bauta ga kowa , sannan kuma abokiyar kwanan ta ma yarinya ce budurwa sa'ar ta dan haka suke yin chanjaras daga ta nemi kawo mata wargi ," damuwar ta yanayin rayuwar da take gudana ne a wurin da yanzu ta tabbatar ba gidan gwamnati bane , wuri ne na kazo na zo rayuwa ce irin ta daga ƙwari sai gwaiwa ,kowa kan sa ya sani rayuwa ce ta nafsi-nafsi ,uwa uba rashin wadatatcen abinci ,da ruwan sha ba'a maganar kayayyakin gudanar da rayuwa irin ta yau da kullum kamar su sabulan wanka da na wanki ,suturu da sauran su ,"
wanda tun zuwan su bata ga alamun za'a taimaka musu da waɗannan ba ," ga fatara da ta addabe ta saboda rashin koh kwandala da take matsayin mallakin ta ,"
gefe guda na zuciyar ta tana tausayawa abokan tafiyar ta da a yanzu ta fisu ƴanci , ta kuma sha zama ta gwada musu yadda zasu ƙwaci ƴancin kan su daga hannun ƴan iskan mata azzaluman da suka maishe su bayin su ,
sai dai daga yakakan har falmata babu mai kumajin iya kwatarwa kan sa ƴancin saboda rangwamen wayewar kai tare da ƙarancin shekaru ,
ɗan gwara ma falmata idan ƙumu ta ƙuma mata kai ta kan iya yin hobbasa ta nemi matsera daga hannun ajus ɗin ta hanyan yi mata batar dabo ta gudu bayan ajujuwa cikin datti da guntun najasa tayi zaman ta ,"
amma ga yakaka babu fuss , akan ga ƙwanjin ta ne kadai idan aka taba mata sanyin idaniyar ta falmata a gaban idanun ta , amma akan kan ta kam raguwa ce ta kin ƙarawa ,"
Dan haka kamar yau da suke zaune su ukun turmus a cikin rairayin da ganyayyakin bishiyar darbejiya ya lulluɓe ,yagana ta dubi fuskar yakaka da take duk jirwaye da lollori "( abun ka da farar fata )
"Nikam yakaka wannan mawuyacin halin da muke ciki a sansanin nan namu ya isheni , domin ban hango ranar yankewar wahalar mu ba a haka muna zaune cikin rashin sanin makomar rayuwar mu ya kamata mu samarwa kan mu mafita tun kafin ta ƙure mana ,"
dan zunkuɗa goyon yaron da ke ɗane baƙe-baƙe akan bayan ta wanda iskanci ne irin na yara ya sanya shi sanya kukan sai an goya shi domin yana yawon sa da gudun sa ko'ina ,"
"Hmm yagana kenan toh wace mafita kike tunanin muke da ita , mu da bamu da kowa kuma bamu san ko'ina ba sai nan ɗin ? Ai ina ganin haka zamu cigaba da hakuri har zuwa lokacin da ubangiji zai sauƙaƙa mana domin nasan yana sane da mu ," ta karashe zancen tana mai kokarin maida ƙwallar da ta ciko mata a ido
Yangana ta nisa cikin kallon sashin da falmata take wacce gaba ɗaya ta maida hankalin ta ga gefen su tamkar dai idanun ta suna kallon wani wajen , da azahiri kunnuwan ta tarwai suke tana kuma sauraran tattaunawar tasu ,kawai bakin ciki da damuwa ne suke danƙare a kahon zuciyar ta
",Amma ai kina ganin yadda wasu mutane dayawa a sansanin suke taɓuƙawa kansu wasu abubuwan ta hanyar kula da rayuwar su da ƴan kananun sana'o'in da suke , me zai hana muma mu yunƙura mu gwada sa'ar mu koh zamu samu damar taimskon kan mu da kan mu yakaka rayuwa a haka bazai yiwu ba ,"
Murmushin takaici yakaka tayi ganin yadda yagana ta hakikice akan batun neman sana'a
Yagana kin manta da ruwan ciki ake jaan na rijiya ? Ita kan ta sana'ar ai sai da jari ,mu kuwa bamu da ko sisi bamu da kadara toh aina kike tunanin zamu samu jari bare a kai ga batun fara tunanin sana'ar yi
Nasan bamu da jari yakaka toh amma ai ga "kolo"(abokiyar kwanan ta ) ita ma bata da jarin amma tana bi tana neman aikin kwangilar yin ɗinkin hula ,ana biyan ta muma mai zai hana mu nemi kwangilar mu dunga yi koh zamu samu ɗan kuɗin biyan kananun buƙatu ?
Jimm yakaka tayi cikin tunani a zahiri ita bata wani iya ɗinkin hula ba sai dai tana ganin bata da wata mafitar taimakawa kan su ita da falmata idan ba ta wannan hanyar da ƙawar kirki yagana ta zo da ita ba ," dan haka ta ɗago da murmushi dai-dai lokacin da falmata ta waiwayo su tana me kafe gefen da take jin muryar yakaka da ido ,"
Yakaka bata iya ɗinkin hula ba koh riƙe allura a soka bata iya ba, asalima a cikin wannan halin bautar da muke ciki ina yakaka zata samu damar da zata zauna ɗinkin hula , yakaka kar ki ƙarbi abun mutane ki zo ki ɓata musu abu ya zo ya zama rigima da muguwar rawa gwamma ƙin tashi mu cigaba da addu'a Allah zai kawo mana mafita ,"
Falmara ta furta hakan karon farko tana me jin ciwon rashin idanun ta da babu abun da zai hana tayi ɗamarar karba kwangilolin ɗinkin hula har sai ta samar musu rayuwar da ta fi wacce suke yi yanzu inganci ita da yayar ta domin babu dare ba rana zata duƙufa soka allura da zarewa koh da zata tsire ƴan yatsunta da allura ," sai dai tana jin baza ta iya barin yakaka ta yi ba saboda sanin irin tarin ayyukan da suke jibge akan yakakan wanda mafi akasarin su na wannan azzalumar matar ne fanne " idan dai ba tsakar dare yakakan zata tashi yin ɗinkin hular ba bata hango tana da lokaci ba , tsakar dare kuma da wanne haske zata soka allura a matsayin ta na ƴar koyo ? Su da basu da koh ashana bare tocila ? Zata fi so yagana ta zo da shawarar wata sana'ar da ita ma za'a iya haɗuwa da ita ayi .
Shiru ne ya biyo bayan katse musu hanzari da falmata tayi ,kafin yakaka ta yunƙura cikin karfin zuciya
" zan iya falmata , yagana yaushe zamu samu kwangilar ɗinkin hular kuma aina zamu samu ? Wallahi zan yi koh da a tsaye koh a durƙushe ne zan kuma koya na kware cikin karamin lokaci ni dai fatana mu samu na kan mu ,"
ta ƙarashe zancen tana mai kamo hannun yagana wacce tayi shiru tana jimamin bahagon halin falmata ,
Toh bari mu fara tuntuɓar kolo koh zata shige mana gaba domin ita ta san masu bada kwangilar saboda ta fimu daɗewa a sansanin ,"
_____
Saɓanin tunanin su yakaka akan saukin samun kwangilar ɗinkin hula sai ga shi har yau da suke kwanaki huɗu da fara neman aikin kwangilar ɗinkin hular ,amma koh hula ɗaya ta gagara samuwa a gare su , daga ita har yagana ,saboda kowa shakkar basu ɗinkin hular sa yake domin gudun kar su ɓata masa dan babu wanda ya tabbatar da ƙwarewar su , kamar yadda ita kolo tayi suna wurin ƙwarewa da saurin ɗinkin hula hakan yasa take samun kwangila sosai,"
Har dai yanzu da suka gama hakiƙancewa baza su samu ba ,"kolo wacce ita ma ƙwarai ta so su samu ɗinkin koh dan ɗasawar da suke ita da yagana a yanzu ,"
Mai zai hana toh ku nemi wata hanyar neman kuɗin yagana ? Cewar kolo
Kolo kenan ina muka ga jarin neman kuɗi ? kina ganin aikatau ma mun gagara samu .inji yagana wacce duk mamakin halin mutane na rashin taimako ya cika ta,
Akwai hanyoyin neman kuɗi mana ba iyaka ma mu da muke cikin birnin maiduguri ,"
Tun kafin ta ƙarasa yakaka ta tari numfashin ta toh ai kolo bakya ganin mu a kulle muke cikin sansanin mu ba'a kuma fita sai da dalili mai karfi kamar idan kana saye da sayarwa koh kuwa ka nemi iznin zuwa ganin wani naka cikin gari ka ci sa'a an bar ka
Idan dai har kun tabbatar kuna