Showing 366001 words to 369000 words out of 411050 words

Chapter 123 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

8141

ta miƙa hannu a hankali ta ɗau wayar ta ta fara dannawa ba tare da tasan me take yi ba '

Hakan da tayi ba ƙaramin tunzura Sofi tayi ba a fusace tace "Dan Ubanki watau ga mahaukaciya tana magana kin wani yi banza dan....'

Kamar an safure ta Yakaka ta miƙe daf da Sofi ta zo ta tsaya idanun ta ƙyar akan ta cikin muryar ta da bata cika ƙarfi ba tace "Duk wani cin mutumci da zage-zagen ki ya tsaya a iyakar kaina , kar domin kin ga ina yin shiru kiyi zaton za ki iya zagin iyayena na ƙyale ki .

" ban ajiye iyayena kurkusa ba idan ke kin raina naki iyayen na.....

Turo ƙofar da aka yi yasa su duk biyun waigawa .

Doctor Hamza turus yayi yana kallon su kafin ya ƙaraso fuskar sa cike da mamaki ya tattara ganin sa kan Sofi wacce har kawo lokacin bata farfaɗo ba daga ruɗanin da ta shiga kan ji da tayi Yakaka ta mayar mata da Martani har ma tana ƙoƙarin rama zagin da ta mata.

"Sofia me ya faru ? Me kika zo ...

Sai yaƙi ƙarasawa ya ɗan riƙo hannun ta ganin wani irin huci da take yi ,so yake ya jaa ta waje .

Amma sai ta ƙi da ƙarfi ta warce hannun ta kafin ta fashe da wani irin kukan baƙin-ciki .

"Na shiga ukuna Yakaka ni kike zagi ? Iyayena kike zagi Ni-ni kika zaga ? Yakaka uwata da ubana kike zagi ? Daga kawai na shigo na tayar da ku Sallah ?

Yakaka wacce ta cika da mamaki da tsoro ta ɗago kan ta fuskar ta ɗauke da mamakin makircin Sofi da bata saba da irin sa ba tayi rau-rau da ido tana kallon Doctor Hamza wanda shi ma ita yake kallon fuskar sa a ɗaure , ta juya ga Sofia tace "ki ji tsoron Allah ni na zage ki ? Ba ke kika zage ni ba ? Ina ke ce kika shigo kawai kika fara zagi na har da Babana ?

Sofia ta zaburo zata yi magana Doctor Hamza ya dakatar da ita da cewa "saurara Sofia wai me yake damun ki ne ? Ya za ki shigowa mutane ɗaki haka da sassafe ?

Zata yi magana ya sake katse ta wannan karon muryar sa a kaurare yace "Sofia bana son tashin hankali da fitina , ran ki zai yi mummunan ɓaci muddin kika ce ...

Sofia wacce take jin zuciyar ta kamar zata fashe ganin Doctor Hamza yana shirin birkice mata kuma a gaban Yakaka .

Nan take ta haɗiye kukan kissar ta ta murje ido cikin salon ta na goggagun matan da suka raina mazajen su kunya kuma ta mata nawin ɗauka ta gatsina fuska da buɗaɗɗiyar murya tace

"Wannan wane irin rashin adalci ne kake fara rabawa a tsakanin mu tun yanzu ? Kenan dan tana ɗakin bani da ikon shigowa ɗakin ka a duk lokacin da na so ?

"Sofia ki wuce ki koma ɗakin ki kar ki ɓata min rai ki ɓata min lokaci .

Buɗe baki tayi kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa tana mayar da ganin ta kan Yakaka wacce ita ma ita take kallo , da haƙoran ta ta cije leɓen ta na ƙasa tana yiwa Yakaka wani irin mugun kallo tayi ƙwafa kafin ta juya a fusace ta fita a ɗakin tana wani irin bugo ƙofar da har sai da Yakaka ta firgita .

Tsoron Sofi da ya ɗan yi ƙaura saboda zuciya da tayi da ta zagi Baban ta taji yana dawowa sabo fil ,ta tuno da zaɓin da tace ta bata kan ta zauna ta yini da kare a ɗaki irin na jiya ko kuma ta fita ta bar gidan to ta tafi ina ?? Yaya dacta ma ai ba zai bari ta fita ko da ƙofar gida bane kuma a can ma an mata nasiha kan fita ba mutumcin matar aure bane a dunga ganin ta a titi haka siƙau muddin ba lamarin zumunci mai ƙarfi ko aiki ko kasuwanci zata fita yi ba .

Hannun sa da ta ji a ƙugun ta shi yasa ta sauƙe ajiyar zuciya , tana jin lokacin da ya sako fuskar sa ta gefen wuyan ta ƙamshin turaren sa na game mata hanci , muryar sa kamar ba shi ya gama kurara Sofi yanzu ba yace "tunanin me kike yi Wafaa ? Bana son kina yawan tunani na faɗa miki .

A hankali ta juyo ba tare da ta fita a tsakanin hannuwan sa da ya kewaye ta da su ba tana yin ƙasa da murya tace "Yaya Dacta wallahi ban zage ta ba ku....

"Shitt yace yana ɗaura hannun sa akan laɓɓan ta da yasa ta ɗago kan ta tana kallon ƙwarar idanun sa da suke cike da tausayin ta

"Ba sai kin min bayani ba Wafaa na san halin Sofia , kiyi haƙuri zan ɗauki mataki ba zan bari ta ci zarafin ki ba da ke da ita duk matan Aure na ne kiyi haƙuri kin ji ko ?

Wata sassanyar ajiyar zuciya tayi jin daɗin bai yarda da sharrin da ta so ƙulla mata ba " Nagode Yaya Dacta .

Murmushi ya yi mata kafin ya sake matso da ita jikin sa kamar mai raɗa yace "mu je mu kwanta kafin lokacin tafiya ta aiki .

Da sauri ta girgiza kai kafin tace "Yaya Dacta kitchen zan tafi na yi girkin abin karyawa kafin ka tashi bacci.

Zama yayi a bakin gado yana zaunar da ita a cinyar sa yace "No Amarya ce ke Wafaa bai ma kamata kina shiga kitchen ba har sai mun gama amarcin mu ko ?
Ya ƙarasa da sigar tsokana yana ɗaga mata gira .

Ɗan murmushi tayi tana miƙewa tsaye "zan tafi kitchen Yaya Dacta bana so ka tafi office baka yi breakfast ba .

Da gama faɗin haka ta taka tana barin ɗakin , fuskar sa ɗauke tattausan murmushi ya bi ta da kallo salon kulawar da ta gwada masa ya burge shi daban da na Sofi wacce bata iya kula da duk wasu lamuran nasa ba sai fa gwada haukar So a sarari .

Bai kwanta ba sai ya jawo littatanfan sa na addini ya shiga karatu.


A kitchen cike da azama irin na matan da suka gogu da aiki Yakaka ta ɗora ruwa kafin ya tafasa ta kwaɓa fulawa da baking powder sai 'yar zuma da ta sa a madadin sugar .

Lokacin da ruwan ya tafasa ta wanke shinkafa fara ƙal ta tuwo ta zuba tare da Sugar sannan ta zuba spices da ake amfani da su wajen haɗa shayi .

Kafin shinkafar ta nuna , ta ɗora mai ta fara soya pancake da har ya fara tashi saboda ɗumin wajen '

kafin ta gama shinkafar ta tayi ligib dan haka ta dama madarar gari mai yawa ta juye akan shinkafar ta da tayi ligib tana juyawa yayi kauri kamar talge shinkafar kuwa tabi cikin madarar, ɗan manshanu kaɗan ta zuba aiki ta kashe Sugar ta bari.

Da ta gama soya pancake bata bar kitchen ɗin ba sai da wanke kwanukan ta goge ko'ina tsaf .

Sannan ta buɗe fridge ta ɗauko Strawberry ta wanke shi tsaf ta yanka shi a tsai-tsaye bowl ta ɗauko mai kyau tazuba basisen da yayi nar-nar da shi ya kwanta fari ƙal , sai ƙamshin man shanu da kayan ƙamshi yake yana ɗaukar Ido .

Bayan ta zuba iya adadin yadda ta ke ganin yayi sai ta jera Strawberry ɗin a kai , ta rufe , ta ɗau wani bowl daban kuma ta zuba pancake .

Bata juya ba amma jikin ta ya bata da tsayuwar mutum a bayan ta dan haka ta juya da sauri ,

Ajiyar zuciya tayi ganin Doctor Hamza ne shirye yake tsaf cikin shirin sa na zuwa wajen aiki a hankali ya tako har inda take yana bin fuskar ta da kallo da ita ma shi take ta kallo cike da burge ta da yayi kamar wani bature ya tsuke cikin lounge suit launin shuɗi Mai duhu .

Yana mata murmushi ya shafa kumatun ta , "Wafaa wannan kallon fa ? Yace da sautin da yake tsakanin maƙoron sa .

Sunkuyar da kai tayi a dan kunyace da 'yar ƙaramar murya tace "ba kome har ka shirya ? Nima na gama girkin .

"Naso na makara ma wafaa , me kika girka mana ? Ya furta hakan yana zarcewa da hannun sa ya buɗe abincin da ta haɗa , da kallo ta bi fuskar sa cike da son ganin yanayin da zai nuna .

Buɗe baki yayi cike da jin daɗi sai kuma yayi murmushi "Basisee ? Wow Wafaa ashe kin iya girki ? Kamar kin san na daɗe rabo na da na ci Basisee .

Murmushin jin daɗi tayi tana ɗaukar farantin da abincin ke kai tace "Yaya Dacta to muje ka ci tunda ka ga har ka makara .


Bayan ya zauna a kujera ta Zuba masa basise a Plate ta ɗeba masa pancake ɗin ta zuba a gefe.

Duk abunda take yana bin ta da kallo cike da so da sha'awa komen ta a tsaftace dai-dai da yadda yake so .

Bayan ta zuba masa yayi bismillah ya ɗau pankcake ya dangwali Basisen ya kai bakin sa ya gutsura

Daɗi da ƙamshin girkin ya ratsa shi , a karo na biyu Yakaka bata tsammata ba ta ga ya nufo bakin ta da Pancake ,

Noƙewa tayi tana kallon shi tace "idan ka gama nima zan ci ,

"Buɗe bakin ki Wafaa, yace muryar sa da sanyi amma ƙwarar idanun sa na mata umarni .

A hankali ta buɗe baki ya saka mata yana bin ɗan ƙaramin bakin ta da kallo yadda take cin abincin a kunyace ya so ba shi dariya "yarinya za ma ki sauƙe wannan kunyar ta ki ne a hankali "

sannu kan hankali ya ciyar da su iya cin su da su duk biyun sun yi mamaki domin kusan duk suka cinye sai fa kaɗan suka bari da bai wuce cin ɗan yaro ba .

Sauƙowar Sofia ya ɗau hankalin Yakaka da ta hango ta sai ta ji wani abu ya ɗan taɓa ran ta da bata san mene ne ba , ta sai ji kamar ta muzanta ganin irin kwalliyar da Sofia tayi cikin wani yadi da aka yiwa kyakkyawan ɗinkin Riga da Siket da suka kama ta ɗam.

Tayi ɗaurin ɗankwalin zamani ƙamshi turaren ta ya riga ta isowa .

A hankali Yakaka ta saci kallon Doctor Hamza ta ga yadda yake bin Sofia da kallo da alamun kwalliyar ta ta ɗau hankalin sa , ganin ta ta mayar kan ta , ta ga tun atamfar jiya da daren nan ce a jikin ta sannan ba wata kwalliya a tare da ita , duk sai ta fara ganin laifin kan ta "Amnee cewa tayi kullum ki dunga ƙwalliyar Safe daban ta rana daban ta dare daban ta kwanciyar bacci daban . Zuciyar ta ta tunasar da ita .

Hakan yasa tayi saurin miƙewa kunnen ta na toshewa daga jin zantukan Doctor Hamza da Sofia da suka fara sabuwar gaisuwa ba'a ce sune ɗazu suke hayaniya ba .

Sofia ta shafe fushin ta kamar kome bai faru ba .

Taku biyu tayi ta ji hannu Doctor Hamza cikin nata ɗayan hannun sa kuwa riƙe da briefcase .

"Wafaa ni zan tafi ba za ki min rakiya ba ?

Murmushin yaƙe tayi tana ɗan kallon Sofia tace "zan tafi nayi wanka ne .

Wata 'yar dariya Sofia tayi kafin tace "anya kya yi wanka yanzu ? Ko da ...

Da sauri Doctor Hamza ya katse ta lokacin da yake sakin hannun Yakaka yace "Sofia na jima ban ji daddaɗan girki irin wannan ba ba domin Amnee kar ta hukunta ni ba zan ce ma ban taɓa cin basise mai daɗin wannan ba Sofi ki koyi girki ke ma zan ji iri..

Taɓe baki Sofia tayi tana hararar bayan Yakaka wacce ta riga ta juya tana barin wajen zuwa ɗaki kafin ta dawo da ganin ta kan Doctor Hamza .

Fuskar sa a ɗaure yace "na faɗa miki ki daina neman fitina hakan ba kome zai jawo miki ba illa raini yarinyar nan dai a haife ma kin kusa haihuwar ta.

Kamar an soke ta da tsinin mashi haka Sofia ta ji , "ita zai ce ta haifi Yakaka ?

ƙanƙance ido tayi zata fara jaraba yayi wucewar sa cikin ɗaga taku yana barin falon ran sa cike taf da jin haushin korar masa Wafaa da tayi bata bari sun yi sallama ta masa rakiya ba .

Ta jima a tsaye a wajen tana rarrashin zuciyar ta da take ingizata akan ta je ta yiwa Yakaka dukan tsiya idan ya dawo ya ga banbancin shekarun a zahirance '

Sai dai ɗaya ɓarin zuciyar ta da yake cike da tsoron abun da hakan zai jawo ya hana ta aikatawa.

Sai da ta furzar da wata iska mai zafi sannan ta juya ta nufi ɗakin da take ɗaure Sam .

Yana kwance magashiyan kamar gawa , ƙafar ta tasa ta haure shi amma bai motsa ba " Dan ubanka kai ma ka tashi haka kaje kayi aikin da na kawo ka domin yi , ni inaga wannan maganin ma kamar ya maka ƙarfi yau ba zan baka shi ba .

Yakaka wacce har ta shiga wanka ta tuno da abincin ta na rana da ta ɓoye a kitchen cikin dabarar da take son yi , dan haka ta ɗaura towel ta zura hijabin ta ta murɗa ƙofar ta fito sai da tayi dube-dube ta samu tabbacin Sofia bata nan sannan da sassarfa ta tafi kitchen ta ɗauko sauran Basise da pancake da ta juye a warmer ta rufe ta nufo ɗaki.

zuwan ta tsakiyar falon yazo dai-dai da fitowar Sofia jaye da karen ta da yake ta turjewa yana wani ɗan kuka .

Kallon-kallo suka yi a tsorace Yakaka ta jaa baya tana neman hanyar gudu cikin daƙiƙu kaɗan Sofia ta fahimci abunda Yakaka take shirin yi .

Dan haka ta zaburo bayan ta saki karen, da ganin haka Yakaka ta zuba a guje ta faɗa ɗaki da bata nesa da shi sosai tana shiga ta dire warmer ta danna ƙofar ta murza key bayan ta kulle ta zare shi daga jikin ƙofar dai-dai da ƙarasowar Sofia .

Wani irin duka Sofia ta kaiwa ƙofar kamar wacce ta sha giya ta shiga ƙundume-ƙundumen zagi tana cewa sai ta ga bayan Yakaka .

Yakaka wacce take jingine da jikin ƙofar daga ƙasa da ta zame ta zauna ji tayi hawaye na sauƙa a idanun ta wacce irin masifa ce wannan ?

"Ai kin kulle ƙofa a banza ki jira zan nuna miki iyakar ki zan nuna miki cewa nan gidana ne da baki isa min shamaƙi da wani ɓangare a cikin sa ba.

Tana jin lokacin da ta juya ta bar wajen bayan ta gama faɗin haka , ajiyar zuciya tayi ta miƙe tana ɗauke warmer ɗin daga wajen ta ajiye a gefen gado ,

Duk da ran ta na mata ciwo da irin yadda take rayuwar rashin ƴanci amma ta ji daɗi da yau Sofia ba zata samu nasarar turo mata kare kamar yadda ta ɗau alwashi ba ita daman ko babu kare a gidan ma yinin falo ba nata bane muddin Sofi na shawagi a gidan .

Wanka ta shiga ta ƙarasa ta kusa fitowa ta ji kamar an buɗe ƙofar an shigo ta ɗan kasa kunne bata ji motsi ba sai dai ƙarar rufe ƙofar da ta sake ji yasa a tsorace ta ɗauraye jikin ta ta fito .

Abun da ta gani yasa numfashin ta yin gargada 'Sam ne Sofia ta sake kawo mata shi kenan tana da makullin ɗakin ? Yau ma so take tayi yini makamancin na jiya ?

Wani irin daskarewa take ji zuciyar ta na yi tsanar Sofi na ratsa kowanne lungu da saƙo na ran ta "sofia wace irin Azzaluma ce haka ? Da gaske idan bata bar gidan ba watarana Sofi zata kashe ta .

Kallon karen take yi tana jin yadda bugun zuciyar ta ke sauyawa tamkar jinin jikinta ya tsinke .

Laɓɓan ta na karkarwa ta fara jaan ayoyi tana yin baya-baya ta koma cikin banɗakin ta rufo ƙofar , sai kawai ta fashe da kuka ,ita tun da ta san kan ta a matsayin mutum babu wani abun da take jin tsoro sama da kare ,

Bata son kare ta yadda ko da takun ƙafar sa ta gani a cikin ƙasa sai ta ji bugun zuciyar ta ya sauya Allah ya ratayawa ruhin ta tsoron kare .

Ta jima a zaune cikin banɗakin tana tunanin mafita "shin haka zata zauna kullum Sofi na azabtar da ita ta hanyar turo mata kare ? Ba zata iya ba domin watarana zuciyar ta zata gaza jurewa tsoron da take shiga sanadin haka sai ta mutu .

"To kuma idan ta faɗa me zai biyo baya watakila Sofi ta kashe ta da wuƙa da kuma ta san ba wanda zai san ita ta kashe ta domin daga jiya zuwa yau ta hango wani lamari tattare da Sofi da ya zarce mugunta sai dai a ƙira shi rashin imani.

" Wai kuma da gaske Yaya Dacta bai san da kare ba a gidan ? Anya gaskiya ne ?

Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji karen na wani irin kuka ciki-ciki kamar gurnani , can kuma ta ji yayi shiru sai ta ɗan matsa kaɗan ta leƙa ta ƙafar makulli inda ta bar shi a kwance a can ta hango shi ya yada kai gefe .

Ta koma ta zauna tana tunanin yau kuma baya tsalle-tsallen ?

Har azahar tana cikin banɗaki har gyangyaɗi tayi ta farka lokacin ma ana ta sallah , ta sake leƙawa ga mamakin ta har yanzu fa Sam a inda yake anan yake kwance .

Shiru tayi tana nazarin sa da ta ƙura ido sosai sai ta ga kamar ma bacci yake .

yunwar da take ƙwaƙwular ta ita ta tunasar da ita cewa fa lokacin cin abincin ta na rana yana ƙoƙarin wucewa .

Tunanin da ya ɗarsu mata a rai a dai-dai lokacin ya sa tayi wani ɗan zullo tana dafe ƙirji a fili tace "wallahi bazan iya fita ba watakila idon sa biyu .

Can bayan kamar mintoci talatin da ta gama nazarin Sam ta haƙaƙe bacci yake yi sai ta buɗe ƙofar a hankali

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login