Showing 276001 words to 279000 words out of 411050 words
Chapter 93 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
karɓi ɗiya mu tai da itta ina ? Muyi me da itta ? Mu 'yan nasaba ne , ɗiyan asali ɗiyan halak ba zamou taɓa yadda da zouwanta cikin mou ba ai daman ɗiyan zina na uwattai ne , can zaku koma da itta ,
Da rishin kuka Falmata ta miƙe tsaye ta tsaya akan su ,
"ƙarya kuke yi Yakaka ba ƴar iska bace bata taɓa zina ba , dan haka Mama ba shegiya bace ,
Juyawa tayi ta ɗago Yakaka da ruwan hawaye ya jiƙa mata gaban riga , ko kusa bata san wannan ranar da zasu shiga tozarta ita da "yar uwar ta a sanadin kuskuren da ta aikata zata zo ba ,
Kuma bata so ba wasu suka riga ta sanar da Falmata ta irin hanyar da ta samar da Mama ba ,
jijjigar da Falmata ta yiwa kafaɗunta da ta riƙe duk biyu shi ya tsorata ta ,
"Yakaka kina jina ki je gaban su ki faɗa musu ƙarya suke miki sharri suke muku ke da Baban Mama ba zina kuka yi ba , ki faɗa musu Mama ba shegiya bace , ki ce musu ƙarya suke yi , Mama ƴar halak ce kamar su ,
Ta karasa zancen tana fashewa da kuka ,
Kukan da ya hargitsa duk wata guntuwar nutsuwar da ta ragewa Youssouf , ya miƙe a ɗimauce , lokacin da muryar Yakaka ya ratsa wajen ,
" Gaskiyar su ne Falmata , Mama shegiya ce , ba muyi aure ba ni da Baban Mama muka haife ta ,
tamkar an harbi ƙwaƙwalar ta haka Falmata ta ji zancen , sai ta wara idanun ta fes akan fuskar yar uwar ta muryar ta babu ƙarfi irin na ɗazu illah tsantsar tashin hankali ta ce
" Yakaka tsoron su kike ji ? Dan kina tsoron su shine kema zaki ƙira Mama shegiya dan kawai bakya son ta ? ,
sai ta tunkuɗe ta baya , ta wuce kai tsaye wajen Youssouf da ƙafafun sa ke karkarwa ta tsaya daf da shi ta ɗaga kai tana hangen farar fuskar sa
"Baban Mama ka cewa Yayar ka ƙarya take , ka faɗa musu kai mutumin kirki ne bazaka cutar da Yayata ka ɓata asalin Mama ba ? Ka faɗa musu ba zaka yi zina da Yayata kuma ka aureni ba .
hannun sa dake rawa ya miƙa ya rike kafaɗar ta , sai dai hannun sa yana sauƙa a jikinta ta doke hannun da wani irin matsanancin fushi , tace "kaima zaka ce gaskiya ne ? Eh ?
Ubbo wacce abunda Falmata take yi ya fara bata haushi a ganin ta tsaurin idanun Falmata ya wuce iyaka da har take ƙaryata su kai tsaye ,ta kuma tsare Youssouf ɗin a gaban idanun su dan haka sai ta miƙe tsaye ta ƙaraso wajen ,
Ta fuskance shi tana cewa
" Youssoufa menene haka nake kallo ? Macce ke tsare gaban ka Youssoufa ? A gaban ka take ƙaryata Adda Ammi ? Ka sake ta Youssouf a yanzou , ka sau amrenta nace wacece itta da bata wuce bayun mu ba ?
Da dukkanin Fushin sa ya juya gare su muryar sa da Amo mai ƙarfi laɓɓansa na karkarwa yace.
"Adda Ammi, Adda ubbo , Tafeeda , domin Allah ku tafi abunku , ku fita dagga Rayuwa ta , Rayuwata tawa ce ni ɗaya ba tare da ku ba , duk kome nayi a cikin ta domin kai na ne ,
" ba zan saki Matata ba haka kouma ba zan rabu da ɗiya ta ba , naji ban samar da Mama ta halastatciyar hanya ba , amma ina ƙaunarta fiye da yadda nake kaunar kaina , ni nake da laifi Mama ita wankakkiya ce tsaftatatciya ,
"ba zan danganta Mama da ku ba asalinta ya tsaya ne daga kaina ni kaɗai , ba zan raɓa ta da ku ba , samuwar Mama a wajena wani kaddara ne Maigirma daga ubangijina ,don Allah Adda ku tafi nace ,
"to maras kunya fitsararre , idan kai ka zare mu dagga rayuwar ka mou ba mou fita ba , asalin mu gouda da kai sannan akwai hakkin 'yan ouwantaka da na iyayen mu akan ka ,
Ubbo tace haka ,
Bata saurare shi ba ta juya ga Falmata wacce ta durƙushe a wajen tana wani irin kuka marar sauti ,
"ke yarinya tunda baki da alkunya ku tattara yanzou ku fita zouwa wani wajen cen , ku tafi kuyi nesa da ƙanina shi ba tsaran amren kou bane ɗiyan matsayitta masu gajeren assali ƴaƴan titi....
Kalamanta sun ƙona zuciyar Yakaka , dan haka ta tako gabanta tana jin duk wata shakkar su na ficewa daga ranta tace ,
" Ya isa , Ya isa nace Ya isa kar ki zagi iyayen mu , da basa raye a duniya , ko daman baki faɗa ba Falmata ba zata cigaba da zama da azzalumin ɗan uwanku ba , wanda tushen sa da asalinsa tare da girman da kuke fariya da shi bai katange shi ba daga aikata alfasha , kamar yadda kuka faɗa ya zama dole ya saki ƙanwata ya kuma ba ni ɗiya ta ,
" Nima bazan taɓa yadda ta zauna atare da ku ba , idan kun so a yau ku ɗora shi ya zama sarki , har abada Mama baza ta sake nuna shi a matsayin Uba ba ,
Takawa tayi ta ƙarasa gaban Youssouf , idanunta jazir da ɓacin rai tace
" ka saki auren Falmata na sake maimaita maka , ka kuma fita daga rayuwar mu Youssouf ...
Assalamu Alaikum masu karatu , da fatan duk kuna lafiya ??
Wannan shafin kachokam ɗinsa tukuici ne ga duk wasu masoyan MHR a duk inda kuke alherin Allah ya iske ku , ina ƙaunar ku domin Allah 😍❤
Nagode
[12/16, 1:06 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
43
Ƙiran wayar Youssouf da aka yi ƙarar ita ta ratsa shiru mai ɗauke da tashin hankalin da ya biyo bayan martanin Yakaka ,
Baya cikin nutsuwar sa ya dubi fuskar wayar da take riƙe a hannunsa , ganin wacce take ƙiransa ya sa zuciyar sa ta tsinke ,
Hannunsa na rawa ya ɗaga ƙiran wayar da ya zarce da sanya ta a hands-free batare da ya ankara ba ,
Muryar Hajja ciki kuka ta karaɗe falon , da take cewa
"Babban soja , ku zo Dan Allah, ku zo wajen Mama ku ga jikin nata , jikin Mama babu daɗi...
Rige-rigen ficewa daga falon aka yi tsakanin Youssouf ,Yakaka da Falmata da babu wanda ya saurari kansa bare waninsa burin su kawai su isa wajenta ,
Kuma a tsakanin Falmata da Yakaka babu wacce ta nufi motar Youssouf da ya shiga ya tayar dukkanin su biyu kai tsaye mafitar gidan suka nufa ,
Suna fita ya sha gabansu da Motar ,"ku shigo ,
Yace da wata irin murya
Dukkanin su a lokacin ganin Mama shine burin su , dan haka suka shiga motar ya jaa da gudun gaske ,
A lokacin hawayen fuskar Yakaka da Falmata sun ƙafe kamar yadda yawun bakin su ya ƙafe ya daƙile fitowar wata kalma daga gare su , bayan addu'o'i babu abunda kowannen su yake yi a zuciya
Suna ficewa daga layin gidan motocin da suka yi jerin gwano su kimanin guda biyar suka shiga layin .
Gudun da yake yi ya wuce ka'idar tuki , kiyayewar Allah kaɗai ta kai su asibitin , ba inda ya kamata ya ajiye motar ya ajiye ba , bai ko lura da securities da suke masa magana ba , ya fito daga motar sauƙar ƙarfar sa akan titin da ya ɗau zafin rana shi ya ankarar da shi cewa fa ko takalma babu a ƙafafunsa ,
da gudu-gudu suka nufi ɗakin da suka san Mama tana ciki suna rige-rigen kutsa kansu ,
Turus suka yi ganin babu kowa akan gadon nata , da sauri ya fita suka bi bayansa , ma'aikaciyar jinyar da ya fara cin karo da ita zata wuce ya tambayeta ,"ina ɗiya ta ?
Ta san shi sosai a saboda yadda suke yawan zaman asibitin da kuma kasancewar sa babban Mutum , sai ta nuna musu ɗakin da aka mayar da Mama wanda yake daga ciki sosai ,
Bai saurari me zata sake faɗi ba ya nufi inda ta kwatanta masa da sassarfa ,
Bankaɗa ƙofar ɗakin yayi ya danna kai su Yakaka suna bin sa ba tare da sun bi ta kan Hajja wacce take tsaye daga bakin ƙofar tana sharar hawaye da gefen mayafin ta ba ,
Shigar su ya zo dai-dai da lokacin da likitan yake zare trach tube ɗin da yake fuskar Mama ,
Da gudu Youssouf ya ƙarasa ya ratsa ta tsakankanin Likitocin da suke zagaye da ita , fuskokin su cike da Alhini ,
Ya tarairayo ta bayan ya zauna a bakin gadon ya ɗagota lokacin da take jaan wani irin numfashi mai tafe da gurnani ciki-ciki , idanunta a buɗe akan fuskar sa ,
Hannun sa ya kai yana goge mata tsinkakken yawun da yake zuba a bakin ta , muryar sa tana karkarwa yake kallon likitocin yana cewa,
" Doctora yaya hakka ? Kuyi wani abu mana , Mama tana hakka alhalin kuna tsaye ?
"Mama, kar ki barni ki dubeni Mama ,
ya ƙira ta da wata irin muryar yana jijjigata a jikinsa ganin yadda idanunta suka yi sama , numfashin da take kokawar riƙewa kuma ya ƙarasa barin jikinta , dukkanin wasu jijiyoyin jikinta suka tsayawa aiki , kamar yadda zuciyarta ta tsaya chak daga barin bugawa na har abada .
Da gudu Yakaka ta ratsa tsakanin su ta kai hannu tana riƙo hannun Mama da yayi wani irin sanyi ƙalau ya sake ,
"Mama tashi mana , me ya same ki haka ? Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon .
Tace da kuka a muryar ta ,
"Mama ,
Falmata ma ta ƙira ta lokacin da ta ƙaraso gurin idanunta basa gani sosai Amma tabbas a yau tana iya hange gefen Fuskar Mama tar-tar , shafa kanta tayi da yake rungume a kirjin Babanta
"Mama meye ya same ki ? Ki tashi Mama , kin ga fa Mamar ki ta asali ta dawo zata rayu da ke , Mama baki ko mata magana ba , bata ji muryar ki ba shine kuma za ki zama haka ? Mama ki tashi ,
Ta ƙarasa maganar tana jijjiga su ita da Youssouf ,
Kafaɗar Youssouf Babban likitan ya dafa , yana cewa
" Innalillahi wa inna ilahi raji'oon , kuyi hakuri duk wani ciwo na safiyya ya warke , ta komawa ga Ubangijinta , dukkan wani mai rai mamaci ne kuyi haƙuri , kuyi haƙuri , kuyi addu'a
Baya yayi a hankali yana kaucewa ganin tashin hankalin da yake ƙwarar idanun su su ukun ,da suke kallon sa zuciyar sa cike da tsantsar tausayi , tabbas mutuwar abunda ka haifa akwai ciwo , ciwo kuwa mai raɗaɗin gaske , ɗaya bayan ɗaya likitocin suke ficewa daga ɗakin suka bar guda biyu kawai a tsaye ,
Jikin Youssouf babu inda baya rawa , ya zaro Mama daga ƙirjinsa yana kallon fuskar ta yadda kan ta ya tafi galau ,
Ya sa kukan da yake riƙewa fisge masa , sai ya fashe da kuka mai ƙarfi ya mayar da ita ƙirjin sa da yake wani irin bugu da matsewa tamkar ana daure masa jijiyoyin dake gudanar da jini ta cikin sa ,
amon kukansa ya sa Hajja shigowa ɗakin , cikin ranta tana aiyana inda ake gudu nan aka zo aka tsaya , Mama ta rasu ,
Tun-tuni ta ga Alamun mutuwa a tare da yarinyar tunda jikin ya birkice daman ranta yake kai-kawo , Allah sarki mutuwa bata a shekaru , bata barin ƙarami ta ɗau babba domin wai ta jinkirtawa girman sa , ita lokaci kawai take jira , ko ɗan da yake cikin mahaifiyar sa tana ɗauka ,
Falmata wacce hankalinta ya kasa amincewa da mutuwar Mama kamar yadda likita ya faɗa , ƙarasawa tayi ga Yakaka wacce ta zube guiwar ta biyu a ƙasa ta kifa tafukanta biyu akan fuskarta , kuka take marar sauti , illahirin jikinta rawa yake sai ta kai hannu ta dafa ta , a lokacin da Hajja ta nufi wajen Youssouf , da muryar dake bayyana tsoro da tashin hankalin da me ita yake ciki tace ,
"Yakaka , ki tashi , ki tashi ki karɓi Mama mu tafi , mu tafi da ita Yakaka , ko kin manta da Alƙawarin da muka mata tun tana ciki ? Cewa ni da ke zamu kula da ita Yakaka , zamu bata kariya yaya kuma kina gani Mama zata tafi ta bar mu , ?
Alhalin ...Ya.Yakaka ki tashi nace kin san fa mu uku ne kaɗai a duniya Dan Allah kar Mama ta mutu , Mama kar ki barni mana , yaya za ki min haka Mama ? Bayan nayi alƙawarin zaki warke Mama .
Kuka ne ya ci ƙarfin ta har tana shiɗewa numfashinta ya fara yin sama-sama
Da sauri Yakaka ta rungumeta kukan ta yana daɗuwa ta riƙe fuskar ta ,
"Falmata kiyi addu'a , kice innalillahi wa inna ilahi raji'oon , mu da Mama duk Allah ne ya yimu , ya bamu rai da muke rayuwa da shi , kuma shine ya hallicci mutuwa ya sa ta zama mai zare rayukan mu idan lokacin da ya kayyade mana na rabuwar mu da ruhin mu yayi , da ni da ke da Baban ta duk Allah ya fi mu sonta kiyi mata Addu'a Falmata ,
Da ƙarfi Falmata ta rungume Yakaka wacce ƙarfin hali ne kawai take yi domin kadda Falmata tayi rauni dayawa ,ita abunda take ji bata taɓa jin makamancin sa ba wani abu take ji mai ɗaci yana kai kawo a tsakanin zuciya da maƙogoron ta , gaba ɗaya ranta cike yake da duhu da take iya ganin duhun har ga idanunta ,
Hajja tana ƙarasawa ga Youssouf ta shiga bada baki da tunasarwar da ake yiwa wanda aka yiwa mutuwa , itama sharar hawaye take zuciyarta cike da tausayin su , tana kimanta irin zogin da zuciyoyinsu ke ciki kan mutuwar ɗiyar su ,
Sun ɗau mintoci kusan goma a haka cikin halin ɗimuwar jin zafin mutuwa kafin likitocin biyu su nemi da ya basu Mama zasu zare duk na'urorin su da suka riga suka jona mata ,
Bai dube su ba kamar yadda bai ce kome ba illa bakin sa da tun-tuni yake motsawa da alamun addu'a yake yiwa ƴar sa ,
Shi da kan sa ya raba jikinta da duk wasu na'urorin su ba tare da ya ajiye gawar ta ba ya jaa farin mayafin su na asibitin ya rufe fuskarta zuwa jikinta da shi , bayan ya shafe fuskarta da tafin hannun sa .
Cigaba yayi da zama a wajen yana riƙe da ita tamkar wanda ya samu ɗaukewar tunani .
Ganin haka ya sa likitocin da suka rage su biyu suka fita , Hajja ta ƙarasa wajen su Yakaka tana ba su baki , da har yanzu basu bar kuka ba .
Turo ƙofar aka yi Tafeeda ya shigo tare da shi dattijo ne wanda yana sanya ƙafa a ɗakin ƙamshinsa ya gauraye ɗakin da ya sa Youssouf ɗago kansa suka haɗa ido ,
Maimartaba Sarkin Maraɗi Abdoul-azizou Baskore , ya taka ya ƙarasa gaban gadon da Youssouf yake zaune riƙe da Gawar ƴar sa ,
"Youssoufa ,
Ya ƙira sunan sa .
Ɗago da kansa yayi a karo na biyu , laɓɓan bakin sa na karkarwa da kyar ya fisgo kalmomin da a tun farkon samuwar Mama yake tsoron Furta su ga Maimartaba a tsa-tsan idanun sa , a yau neman tsoron ya yi ya rasa a lokacin da Mama ta ƙare ta zama Babu .
" Baaba , ɗiyata ce , wannan Mama ce , ɗiyata ce , ta rasu , Mama ta rasu ta barni Baaba .
Kuka ya sake fashewa da shi idanun sa na zubar hawayen da suke ɗiga akan gawar Mama ,
Maimartaba sai ya zare gilashin idanun sa , da bayyanuwar sabon yanayi akan fuskar sa saɓanin wanda ya shigo da shi ,
Yayi tsumu ! yana kallon Youssouf da yake cigaba da kuka marar sauti , zuciyarsa ce ta rau-rawa saboda dalilai biyu da suka haɗe mar a lokaci guda .
a hankali ya kai hannu ya dafa ƙafaɗar Youssouf ɗin, cike da tausasawa a muryar sa mai ƙwarjini yace ,
"Youssoufa kayi haƙuri dukkanin mai rai Mamaci yake , Rayukan mu kuma ababen aro ne a gare mu da babu shakka masu komawa ne ga Ubangijin da ya bamu aron su a domin mu bauta masa , Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani , a cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da yake daidai , Sam, kada ka yarda ka ɗauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata saɓo , Idan ka kiyaye wannan, zai zamar maka kamar magani mai kyau, ya warkar da raunukanka, ya kuma sawwaƙe maka azabar da kake ciki ,
"Miƙata ga Tafeeda ka taso mu tafi ga yi mata sutura zuwa miƙata ga kabarinta ,Allah ya jiƙanta , Allah shi sa ta zama dalilin samun afouwar Ubangiji a gareka .
Kalaman Maimartaba sunyi tasiri ga duhuntatciyar zuciyar sa mai ciwo , dan haka sai ya sasssuta riƙon da yayi wa gawar Mama , ya miƙata ga Tafeeda zuciyar sa na tuno masa rana ta farko da ya fara karɓar ta da tafukansa , ya rungumeta a ƙirjinsa , sai ga shi a yau ya zareta daga jikinsa da hannunsa , zarewa irin ta har Abada , ji yayi tamkar bazai iya ba , tamkar wani sashi na ransa ne ya bar jikinsa .
A hankali Tafeeda ya samu damar zareta daga jikinsa , wanda shima tasa zuciyar tayi laushi tausayin Youssouf ɗin ya cika zuciyar sa tare da ƙarin tsoron Allah , da ya tuna irin ƙauna da tsantsar son da Youssouf yake yiwa wannan ɗiyar , da har ta kai ya zaɓe ta