Showing 141001 words to 144000 words out of 411050 words

Chapter 48 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

8127

da kalaman yaudara da wayo ta cikin amfani da makahon son da yakaka take yiwa Youssouf ,

har ta kai ga nasarar samun haɗin kan yakakan ta wani ɓangare ba tare da ita yakakar ta san haƙiƙanin meke cikin ran samy baby ba,

iyaka son youssouf tare da ƙwaɗayin son samun sa a matsayin miji ya sa ta fara amincewa da shawarar samy baby , ɓangaren zuciyar ta dake gargaɗin ta tare da tuno mata da so tare da tausayin dake tsakanin ta da falmata ya fara samun rauni , ! Soyayya tayi ƙarfi ta yadda ta fara rufe mata idanu !

Sannu sannu , yau da gobe zuciyar yakaka tare da taimakon huɗubar samy baby da ta shaiɗan , ta ƙeƙashe da son ganin cikar burin ta na mallakar youssouf a matsayin mijin ta , kamar yadda samy baby ta wanzu tana ƙara ƙwaɗaitar da ita ,

bata ko duban hidindumu tare da gatan da doctor hamza yake gwada masu ita da ƴar uwar ta musamman ma ita da komen ta yake mai matuƙar muhimmanci agare sa , ko sau ɗaya bai taɓa burge ta ba , Koyaushe ɗaukar sa take a matsayin me kirki me TAIMAKON SU,

hankalin ta a kullum daɗa tafiya yake ga youssouf wanda a yanzu hoton sa ya zama abun ɗebe kewar ta kullum dare har ma ta kan ɗan zanta da hoton idan dare yayi nisa wutar so kuma ta ruru iya ruruwa , sai ta fara sakin sambatun so ,

Sai dai tana ƙoƙari wurin boyewa musamman ga doctor hamza , wanda watarana a cikin ranaku ya kamata tana kici-kicin ɗaura agogon da youssouf ɗin ya bar mata a tsintsiyar hannun ta ,

ta shagala cikin bege sai murmusawa take har haƙoran ta na bayyana , sakamakon yadda idan ta ɗaura agogon yake zamewa daga hannun ta idan ta sauke hannun ,  sai tayi maza ta taro agogon ta chafe shi ta sake mayarwa cikin hannun ta , tana lailaya shi kamar tana ganin fuskar youssouf ɗin a jiki ,

Ya ɗauki lokaci dogare a bakin kofar yana kallon ta cikin shauƙin ƙauna , sosai tayi kyau a idanun sa tana sanye da atamfa buɗaɗɗiyar riga da zane, tayi ƴar madaidaiciyar ƙiba ta buɗu kaɗan , sai ɗaukar ido take

Hankalin sa ne ya koma kan agogon da take wasa da shi a hannun ta , yana iya hango girma tare da ƙƴallin agogon daga inda yake tsaye ," ya shaida agogon maza ne ," 

Takawa yayi ya ƙarasa cikin falon bata lura da zuwan sa ba , sai gani tayi hannun sa ya riga ɗayan hannun ta chafe agogon lokacin da yake silmiyowa daga tsintsiyar hannun ta ,"

Ɗaga agogon yayi yana ƙare masa kallo daga gani ba tambaya agogon mai matuƙar tsada ne , da samun irin sa sai a hannun goggagun attajirai ,"

Cikin taushin murya da nutsuwar da take mahaɗin cikar kamalar halittar sa yace ,"

    Agogon waye ?

Shiru tayi tare da sunkui da kai, tun usul ƙarya bata cikin halayyar su , basu ma san yadda ake yin ta ba idan ba yanzu da duniya take ƙoƙarin koya musu ba ,"

  Ganin sa ya janye daga kan agogon ya maida kan ta , tare da ɗan ƙara sautin muryar sa ,
   Wannan agogon na waye ne ??
A firgice ta ɗago kan ta jin kamar ya mata tsawa , matuƙa take shakkar sa tare da gwada yi masa biyayyah

Ba-ba-baba Agogon - agogon Baba ne !
  Ta harhaɗo kalaman da suka fito a baibai ,"  idanun ta na yin ƙwalƙwal .

Agogon Baba ?

  Hamza da Falmata suka haɗa baki wurin tambayar ta !
wacce take ƙarasowa wajen da lalube daga cikin ɗakin saboda jin tashin muryar doctor hamza domin ta gaishe shi ,

Agogon Baba ? Yakaka ina agogon Baban mu ? Daman Baa yana da agogo  ,
      Falmata ta furta hakan cikin tsananin murna kasantuwar ta mai matuƙar ƙwalafacin iyayen ta , hakan ya sa ta ma manta da abun da ta fito yi ,"gaishe da doctor hamza ," ta himmantu wurin son a bata agogon ta riƙe , doctor hamza ne ya ɗaura mata agogon bisa hannun ta ,

bai sake cewa kome ba ya juya yana barin falon zuciyar sa cike da wasi-wasi akan kalaman da yakaka ta furta na dangana wannan tsadadden agogon ga mallakar mahaifin su ,

A sanyaye falmata ta ɗago kai daga barin shafa agogon da take yi ta saita idanun ta a inda take zaton yakaka na zaune ,
    Yakaka kika ce wannan agogon Baa ??
    Da ido yakaka ta kafe ta kamar tana son ta gyara mata sokuwar ƙaryar da tayi ," wanda ta hango rashin yarda da zancen nata ƙarara a idanun doctor hamza
   Miƙa hannu tayi ta zare agogon daga hannun falmata ,
   Falmata muje ɗaki na kwanta ki ɗan danna min kafafuna ciwo suke min ,

  Da sauri ta amsa da
  toh sannu yakaka

Tun daga ranar yakaka take koƙari wurin boyewa kowa duk wani abinda ya shafi soyayyar da take yiwa youssouf ciki kuwa har da Falmata ,

Da samy baby kaɗai take hirar sambatun soyayyar youssouf , wacce take daɗa ƙaimi wurin shiryawa yakaka gadar zare , tare da bugun cikin ta a koyaushe tana jin tsakanin ta da doctor hamza ,

irin kulawar tare da hidimar da yake yiwa yakaka yake sake bata tabbacin zaton ta gaskiya ne , doctor hamza son yakaka yake , soyayyar kuma mai tsanani ta aure ,

wanda a koyaushe idan ta tuno sofi da irin mahaukacin son da take yi masa da irin mummunan alwashin da ta sha a kan sa , sai taji abinda take kokarin yi da nufin raba tsakanin sa da yakaka dai-dai ne, a ganin ta taimakon yakakar zata yi , har ma tana danganta yunƙurin ta a matsayin CETON RAI ," 

Lokacin da yakaka ta shiga watan haihuwar ta hamza ke sanar da ita daga wannan satin zata daina zuwa makaranta , baza ta dunga zuwa ko'ina ba daga awu , sai dai ta fita motsa jiki da dare ,

Da farko ta shiga damuwa , da hukuncin da ya yanke na hana ta zuwa makaranta ganin cewa a makarantar take samun damar haɗuwa da samy baby duk lokacin da samy baby ta so ,"

Amma lokacin da ta sanar da samy baby sai ta ga bata wani damu ba , suka cigaba da hirar su da fiye da rabin hirar maimaici ne tare da tisawa akan yadda tsarin samy baby yake da yadda kome zai kasance , har zuwa gamuwar ta da muradin zuciyar ta kamar koyaushe yakaka ke ƙarasa hirar da sambatun yadda haɗuwar tasu zata kasance da youssouf da ɗokin zuwan ranar ,

Bayan gama hirar su , sai samy baby ta ciro ƙaramar wayar ta , ta kamo hannun yakaka ta danƙa mata ,"
    Zamu cigaba da tattaunawa akan waya yaks , saboda kin ga bana son mutanen gidan su san da alaƙar mu domin kar a zarge ni har a bibiye ni bayan kammaluwar kome , ki tabbatar babu kowa a wurin a duk lokacin da zamu yi waya , ki dunga min flashing idan kina son magana da ni , sannan kuma daga mun gama magana ki dunga kashe wayar , kar ki bari kowa ya san da wayar ,

Idan chaji ya kusa ƙarewa ki sanar da ni , ni zan san hanyar da zan yi na karɓi wayar nayi mata chaji ,"

Abu na ƙarshe shine kar ki manta da tsarin mu ko cikin dare kika ji ciwon haihuwa na zama mutum na farko da zaki fara sanarwa kafin kowa , kin san dai shirin mu zai fara ne daga haihuwar ki ,  ai kin gane ko ?

  Naji anty samy kuma bazan manta duk tsarin da kika shirya min ba , nagode sosai da taimakon da kike min a kullum tunda muka haɗu , Allah ya saka miki da Alheri ,!

Murmushi mai wuyar fassara samy baby tayi,
    Ameen yaks ,

Tun bayan da doctor hamza ya sawa yakaka dokar hana fita unguwa , ya zama kullum da dare tare suke fita ita da Rahima , da misalin karfe 8pm , su ɗan yi tattaki su zagaya unguwar zuwa 9pm sai su dawo gida ,

Ƙwarai yakaka take jin daɗin fitar tasu saboda yadda a kwanakin take jin nawin cikin kafafun ta duk sun ɗan kumbura , ga kwonkwason yana mata tsuku idan ta daɗe ,"

Tare suka fito da Rahima daga sashin su , Rahimar tana ta mitar Yakaka ta katse mata kallon TV da take ta dame ta akan tazo su fita ta raka ta motsa jiki ,"
     Yakaka ni fa yau baza mu yi wani nisa ba , zamu dawo kin ga dai garin da sanyi ma , ga duk hazo ya rufe sama , ni ba dan kin nace ba ma wallahi yau baza mu fita motsa jikin nan ba duk ƙura ta bi ta shigewa mutum hanci ta sa mura ,"

  Gyara zaman burmemen hijabin ta yakaka tayi tana murmushin jin daɗi domin tun basu yi nisa ba ma ta fara jin kafafun ta na warwarewa ,"
     Ni kuwa Rahima daɗin yanayin ma nake ji , kiyi haƙuri kin san ba laifi na bane yaya dakta ne ya ce kar na dunga fashin fita motsa jikin ,"

   Doctor hamza ne ya shigo ta ƙaramar ƙofar gidan jikin sa sanye da ƙananan kaya ya rufe bakin sa da hancin sa da abun tare ƙura ,"Mask ,"

Idon sa ya sauke a ƙan su lokacin da suke ƙarasowa ,"
     Gaishe shi suka yi ya amsa musu ya ɗora da
    Za'a je motsa jiki ko ?
Da sauri Rahima ta tari numfashin sa , big bro daman an bar zuwa motsa jikin nan yau sai gobe , ji fa garin duk hazo wallah ,"
       Rahima dan Allah kiyi haƙuri muje yakaka ta ce , tana marairaicewa ,"
      Cuno baki Rahimar tayi taƙi cewa kome , "
     Murmushi hamza yayi ,
   Koma ciki abin ki Rahima yau an ɗaga miki ƙafa sai gobe ,
     Da sauri Rahimar tayi juya tana dariyar murna , dan kar yace ta dawo ma har da ɗan gudun ta , ta ƙarasa shigewa sashin su , "

   Ganin sa ya mayar kan Yakaka , wacce ta sunkui da kai tana wasa da hannun ta ,"
      Noori
  Ya ƙira ta
   Na'am
  Tace tana ɗago kan ta ta dube shi kafin ta sake sunkui da kan ," ba wani sanin ma'anar sunan tayi ba , ita dai tasan yakan ƙira ta da kalmar a irin lokuta haka da suke su biyu kaɗai !

         Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yace mata ,
  Bismillah mu tafi ,' ya buɗe mata ƴar ƙaramar ƙofar
  Tare da shi zan tafi ?
Ta tambayi kan ta lokacin da take sanya ƙafafun ta da ta cusa wasu ƴan takalman roba na mata ," kumburin da ƙafar ta ta tayi ya sa takalman suka ɗan kama kafar ,"

    Ta ina-da-ina kuke bi idan kuka fito ?
      Ta nan muke bi tace da shi da ƴar siririyar murya ,"
    To yau ba nan zamu bi ba , zo mu bi ta nan , ya ce mata haka yana nuna mata hanyar da tayi baya wacce take da rangwamen mutane da hayaniya ,"
   Ba musu ta bishi ,
  Suka fara tafiya sannu ,sannu ,  rabin hankalin sa baki ɗaya na ga inda take sanya kafafun ta , "
    Ɗan takaitatcen shiru ne ya biyo bayan fara tafiyar ta su ,"
   Kafin Hamza ya lalubo hirar da yake ganin zata fi armashi ga yakaka ,"
    Noori , ya ƙira ta ,"
    Wanne suna kike tunanin zamu sawa baby ?
     Yana hango lallausan murmushin da ya bayyana a fuskar ta da taimakon hasken fitulun bakin hanya, kafin ta ɗan sunkui da kan ta ,"

    Nima ban sani ba yaya dakta , kawai duk wanda ka zaɓar mata ,"
 
  Ɗan murmushi yayi kafin yace ai uwa ita ce mafi soyuwa ta zaɓarwa ƴaƴan ta suna ,
    Ni mata ta duk ita zata dunga zaɓarwa yaran mu suna , dan haka mu fara da wannan babyn , ki tuno suna mai kyau da asali a addini da za'a sa mata , "
  Kasaƙe tayi ita a dole tana son tuno da sunan ,!
     Mama ?
tace masa da sigar tambaya ,"
    Mama! 
shima ya maimaita yana kallon kwarar idanun ta ,"
    Eh
tace da shi tana sunkui da kai ,"

Toh kin samar mata da laƙabi ," ya furta hakan yana mai yi mata murmushin da ke bayyana sautin sa ,

    Ita ma ƴar dariya tayi , tana jin yadda farin ciki ke mamaye mata rai , kafi ta ɗan cije baki a hankali tace na gaji ,
    Yawata idanun sa yayi , nan ya hsngo wani ɗan tudun da aka yi da siminti a bakin hanya , domin zama ,
     Muje ki zauna a chan yace da ita ,
Ƙarasawa suka yi ta zauna shi kuma ya tsaya daga gefe ," , ƙura ta taso tare da ƙasa ba shiri suka kare fuskokin su ,"
    Sai bayan da ta lafa ya mayar kallon sa kan ta ," mask ɗin fuskar sa ya sanya hannu ya ƙunce , " a hankali ya miƙa mata ,"
          Karɓi noori , ki saka ƙura tayi yawa ," kar ya cutar da ke ,"
      Da hannu biyu ta karɓa , ta fara juya mask ɗin a hannu bata san yadda ake sawa ba ,"
       Fahimtar hakan da yayi , yasa yace mata yana mai kwatantawa da hannun sa,
    Haka zaki sa ,
  Sake juyawa shi tayi ta fara ƙoƙarin ɗaura shi ba dai-dai ba ,"
   Bani ki ga
  Ya zare mask ɗin daga hannun ta , 
Zagayawa yayi ta bayan ta ya daidaita mask ɗin a fuskar ta tare da ɗaura mata shi , dai-dai kan hamcin ta zuwa haɓar ta ,"

    Ya dawo ya tsaya , yana kallon fuskar ta , suna haɗa ido ta sunkui da kan ta tana jin wani irin yanayi marar ƙarfi chan a gefen ran ta ,"
  A hankali ta motsa laɓɓan ta
  Nagode ,!
Bai amsa mata ba illa zura hannun sa da yayi a aljihun sa tare da kai kallon sa sama yana ganin yadda garin yayi jaa hazo ya lulluɓe sararin samaniya ,

Wani irin so da shauƙi mai ƙarfi yana fusgar sa bai ƙi ba suyi ta kasancewa anan daga shi sai ita ,

    Shiru suka yi na ɗan wani lokaci kowa da abun da ke saƙawa cikin ran sa ,"  ya katse shirun da cewa
   Zamu ɗan ƙara gaba ne ko mu koma gida ?
      Mu koma gida yaya dakta , da rahima bama nisan haka ,"
  Ok
  Yace da ita .

Suka kamo hanyar komawa gida suna tafe kakkarfar iskar juyin yanayi na shigowar Hunturu , na bugun su , rayukan su sun cika taf da mabanbanta tunaninnika ,!

*****

  Tun asubahin ranar juma'a Yakaka take jin ciwon baya da mara sai zirga-zirga take tsakanin banɗaki , ta gaza gane yanayin da take ji ,

   Misalin ƙarfe tara Rahima tayi shirin ta zata karbo result ɗin ta na SSCE ,
   Tayi musu sallama har tana tsokanar Yakaka ko zata raka ta ?
   Uhum tace tana yamutsa fuska saboda ji da take kamar ciwon na ƙaruwa ,
    Bayan fitar Rahima ya rage daga ita sai Falmata domin Hafsa ma tun bayan bikin Zainab ta tattara ta koma Hostel da zama baki ɗaya tana fuskantar jarabawar su ta ƙarshe ,

Doctor hamza kuma yayi kwanan asibiti , bai kai ga isowa gida ba ,

Karo na barkatai ta yunƙura da kyar ta tashi ta shiga banɗaki , sai dai a wannan karon ba tsugunno tayi ba wayar ta ta zaro daga cikin zanin ta ta kunna ta gami da fara neman layin samy baby tayi mata flashing ,

Tana addu'ar Allah ya sa ta tashi a bacci yanzu , domin wayar ma gaf take da kashe kan ta chajin ya kusan cimma ƙarshe ,

Ta kuwa yi sa'a  cikin ƙasa da mintuna biyu sai ga ƙiran samy baby ,"

Hello yaks ya Kike ?

Bani da lafiya anty samy bayana kamar zai ɓalle nake ji ,"

        Miƙewa samy baby tayi daga kwance ,"

    Yaks ko dai haihuwar ce ?

  Da ƙyar take magana saboda ciwon da take ji yana sake tsungulin ta ,"

   Inajin ita ce anty samy  daman haka haihuwar take da ciwo ??

  Gintse dariyar da take taho mata samy baby tayi , sannu yaks , ki tabbatar dai bamu samu kuskuren aiwatar da nufin mu ba , yanzu zan je harabar asibitin da kike awun na tsaya da mota ta , na jira zuwan ku kin ji ko ?
   to
tace tana sauƙe wayar daga kunnen ta ,"

  Falo ta dawo tana cigaba da murƙususu , tare da nishi ƙasa-ƙasa
    Tsai Falmata tayi daga barin tilawar Al-qur'anin da take yi cikin suratu,"Duhaa,'
    Da sauri ta miƙe tana laluben inda take jiyo nishin Yakaka ,"
  Yakaka ,Yakaka , Yakaka ,nydan3 ? Aiyii waaz3n ? Manan3 Yakaka , Aiyii ? 
    Buguwar da tayi da kujera ta faɗi shi yasa Yakaka wacce take durƙushe daga bayan kujerar rarrafawa ta fito , tazo ta kama hannun Falmatan , wacce bata kula da zafin da ɗan yatsan ta yake ba wanda ya fashe

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login