Showing 225001 words to 228000 words out of 411050 words

Chapter 76 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

8069

be of  9hours and 11minutes. We will be flying at an altitude of  feet/meters 5612 miles .

At this time, make sure your seat backs and tray tables are in their full upright position and that your seat belt is correctly fastened. Also, your portable electronic devices must be set to ‘airplane’ mode until an announcement is made upon arrival. Thank you.”

Ta sake maimaitawa cikin yaren faransanci .

( Mesdames et messieurs, voici Rose Jackson et moi, votre agent de bord. Au nom du capitaine Mike Abraham et de l'ensemble de l'équipage, accueillez le vol sans escale de Turkish Airlines entre Niamey Niger Republic et Washington DC, États-Unis d'Amérique.

Notre temps de vol sera de 9 heures et 11 minutes. Nous volerons à une altitude de 5612 milles.

À ce stade, assurez-vous que vos dossiers de siège et vos plateaux sont dans leur position verticale maximale et que votre ceinture de sécurité est correctement bouclée. De plus, vos appareils électroniques portables doivent être en mode "avion" jusqu'à ce qu'une annonce soit faite à l'arrivée. Je vous remercie.")

Girgizan da jirgin ya ɗauka shi yasa ba shiri Falmata ta sake ɗora ɗayan hannun ta akan na Youssouf tana ƙanƙame sa  hannayen su suka cure guri guda , kamar yadda zuciyoyin kowannen su ke ƙoƙarin jawo kusanci a tsakani .

Idanun sa a kafe kan fuskar ta dake bayyana tsoro ɓaro-ɓaro .

Cikin ikon Allah jirgin ya samu dai-daituwa a sararin subahana ya shilla da gudun gaske cikin tafiyar gaibu bisa iska a tsakanin sama da ƙasa .

Nigeria

Tafiyar kwana ɗaya da yini biyu ta sada Hajja da birnin Maiduguri , da la'asar sakaliya motar da ta kawota ta dakata a ƙofar gidan Prof .

Kai tsaye ta sauƙa ta shiga gidan , tarɓa ta musamman ita da direban suka samu daga sabbin ƴan aikin gidan guda biyu tare da Rahima da daman duk ansan da zuwan su .

Bayan magarib ta nemi iznin zuwa gaishe da prof da  zuwan su a ɗazu suka tadda shi tare da baƙi , hakan ya sa basu samu ganin sa ba sai yanzu .

Bayan doguwar gaisuwa tare da godiyar da akayi musayar su tsakanin  Prof da Hajja , taƙaitatciyar hira suka yi wanda duk rabin ta akan Al'amuran da suka shafi taɓarɓarewar tsaro ne tsakanin Niger ɗin da Nigeria da har kawo yau Ƴan tawayen Boko Haram basu saduda sun bar yin kisan mimmiƙe tare da ɓarnannaki tsakanin ƙanana da ma manyan garuruwan Niger da Nigeria ba .

Sannan kuma har kawo yau gwamanatin ƙasar Nigeria ta gagara kawo ƙarshen hare-haren ƴan kungiyar duk kuwa da cewa cikin ƙasar tushe da MAFARIN kafuwar ƙungiyar da ta jefa Dubunnan rayukan Al'umma cikin HARGITSIN RAYUWA yake .

Shin yaushe ne kome zai kawo ƙarshe ? Yaushe ne abubuwa zasu koma dai-dai ? Yaushe ne za'a ƙira ƙungiyar Boko Haram da shuɗaɗɗan lamari da ya zama tarihi ?  Allah Shine Mafi sani .

Hajja ta miƙe ta ƙarasa gaban Prof tana miƙa masa envelop ɗin dake ɗauke da hoton Mama ,

Alhaji ga hoton Amaryar taka ta Niger ka ga yadda ta girma duk da ƙarancin lafiyar ta amma ta miƙe .

Miƙa hannu yayi ya karɓa yana dariya , dai-dai da shigowar Doctor Hamza wanda ya dawo daga Masallaci .

To toh Masha Allah , Babu kome ai kowacce cuta Allah yayi maganinta , sai dai idan har sanin ɗan Adam bai kai ga gano maganin ba .

Ƙwarai maganar ka dutse Alhaji .
    Cewar Hajja .

ya zaro hoton yana gyara zaman gilashin idanun sa , bayan sun haɗa baki wajen amsa sallamar Doctor Hamza ,

ka ga Babban Likita , Likita bokan turai , ƙarshen ƙwaƙƙwafi da bincike sai likita , lalle tafiyata bana me sa'a ce tunda naci karo da kai , shekaru fiye da biyar rabona da na ganka .

Murmushi yayi yana zama daga gefen ƙafafun Prof .

Hajja sannun ki da zuwa , da fatan kin  samu isowa lafiya ?

Lafiya ƙalau Likita ,yaya bayan rabuwa ? Ya iyalin naka ?

Duk kowa lafiya hajja .

To Alhamdulillah .

Masha Allah wannan Amarya tawa ai tafi kama da ƴaƴan nasara , ga dukkanin Alamu tana da wayo .

Prof ya furta haka yana mayar da hotunan cikin envelop ɗin .

Wayo kuwa na sosai Alhaji ai Mama sai godiyar Allah ba shakka tana da kaifin ƙwaƙwalwa da saurin ɗaukar abu

Allah shi rayata , ya bata lafiya , yayi Albarka cikin rayuwarta ita da sauran yaran musulmai baki ɗaya !

Ameen Ameen Alhaji

Hajja ta amsa tana sanya hannuwanta biyu ta karɓi envelop ɗin da yake maida mata , ta miƙe tana yi musu bankwana tare da barin falon ta koma cikin gida .

Baba , wacce yarinya ce hajja ta kawo maka hoton ta ?

Doctor Hamza ya tambayi Prof .

Ya buɗe baki da zummar bashi amsa shigowar ɗaya daga cikin dattijan unguwar da suke cin abincin dare tare da Prof ya katse musu hirar .

Abuja

Yakaka ce a zaune kan hannun kujerar falon Malama Maryam gabanta kuwa babbar jakar kaya ce da take shaƙare taf da kaya , daga gefen ƙafafunta ma wata ƴar matsakaiciyar jakar ce .

tana shirye tsaf cikin dogon hijabinta da yake har kusa da idon sawun ta , fuskar ta fayau babu ko kwalli , ramar da tayi ta fito sosai akan fuskar ta da idanunta da suka ɗan zurma ciki .

daga gefe a cikin falon Lubna ce a zaune tayi jugum tana kallon Yakaka wacce idanun ta ke kallon ƙasa , tayi shiru tamkar ba sune masu yin dararraki ba muddin suna waje guda .

Malama Maryam ce ta fito itama shirye take , ta kai dubanta ga Yakaka tana jin yadda tausayin ta ke sake narkar da ranta tabbas Yakaka tana buƙatar majiɓanci cikin Rayuwar ta .

Yakaka tashi mu tafi , lubna taya ta ɗauko kayan ku kai cikin mota Abban ku yana jiran mu , kar mu rasa motar farko ko ta biyu , saboda mu samu isa da wuri tafiya daga Abuja zuwa Maiduguri da tazara gara muyi sammako . 

Jikin Lubna babu kuzari ta miƙe tana gyara zaman hijabin jikinta ta sunkuya ta ɗau ƙaramar jakar tare da kama gefen babbar ta taya Yakaka riƙewa ,

Sun zo tsakar gida Lubna ta jaa ta tsaya da hakan ya sa Yakaka waigowa .

idanunta cike taf da ƙwalla tace

Sahiba irin rabuwar da zamuyi kenan babu bankwana ? Shekaru biyar ba kwana biyar bane Sahiba ban so ba zaki tafi tare da maɗaukakiyar damuwa .

ɗan guntun murmushi Yakaka tayi ,
Sahiba kin san har abada kina cikin mutanen da bazan iya mantawa da su ba cikin rayuwata , cikin kowanne irin hali na tsinci kaina , nima zanyi kewar ki Lubna , ta ƙarasa zancen siririyar ƙwallar da bata shirya zubowar ta ba na sauƙa bisa ƙuncin ta .

Idan kika tafi a yanzu waye zata maye min gurbin ki ? Waye zata zama babbar ƙawata a bikina ? Da ke muka tsara kome Yakaka .

Idan Allah ya yarda zan dawo Lubna , zan halarci bikin ki na ɗau Alƙawari , amma dole na tafi a yau shekaru biyar Falmata tayi cikin rashina ,

Hon ɗin da aka matsa da ƙarfi shi yasa suka fara taku cikin hanzari ba tare da sun sake musayar wata kalma ba a tsakanin su .

Ƙarfe takwas da rabi na safe motar da su Yakaka tare da Malama Maryam suka shiga domin tafiya Maiduguri ta ɗau hanya ɗoɗar .

Tafiya ce me nisa ta tsawon fiye da awanni takwas tsakanin Babban birnin tarayya Abuja da Birnin Maiduguri dan haka a saboda yawan tsaye-tsaye akan hanya daga jami'an kula da hanya da suke gudanar da bincike , ya sa dare ya fara shiga har ƙarfe shida na yammaci ta gota , wanda hakan kuma ya sa dole su yada zango a garin Damaturu saboda lokacin dokar hana zirga-zirgan motoci ya shiga ( curfew)  ala tilas suka kwana a tasha ,

Washegari da hantsi ƙarfe tara suka shiga garin Maiduguri , a idanun Yakaka babu wani sauyi da garin ya samu tsawon shekaru biyar ɗin ko kuwa dan hankalinta bashi kan duban yanayin garin ne ? Baki ɗaya ta ƙagauta ta ɗora idanunta akan ƙanwarta da ƴar ta .

Tsawon lokacin rabuwar ta da garin bai sa ta manta da sunan unguwar da ta bar Falmata ba , dan haka bayan sauƙar su a tasha kai tsaye ta shaidawa direban taxi da ya ɗaukesu da kayan su unguwar da zai kai su .

tafiyar mintoci 15 kachal ta sada su da unguwar , layi bayan layi ta kwatantawa direban har zuwa gaban gidan da a koyaushe yake yawan samun gyaran da yake sake fiddo kyaun tsarin ginin dai-dai da na zamani .

Bayan sun sauƙe kayan su a gefen hanya daga jikin katangar gidan Yakaka tace ga Malama Maryam

Ummi bari na shiga na nema mana iznin shiga da kayan mu .

To Yakaka .

taku ta fara yi tana jin yadda zuciyarta ke bugu da fargabar da ta rasa takamaimai dalilin samuwarta daga ƙasan ran ta ,

ta kawo kusa da ƙofar gidan aka buɗo Babbar ƙofar ya danno hancin motar sa yana ƙoƙarin fitowa ... !!!!

Assalamu Alaikum wa Rahamatullah ta'aala wa barkatuhu .

Yan uwa masu karatu Maza da Mata,  ina mika sakon gaisuwa ta tare da fatan Alkhairi a gareku.

Sannan ina mika godiya ta ga dukkanin daukacin Mutanen da suka samu damar kirana a waya da wadanda suka bar sakonni su na gaisuwa tare da addu'o'in samun waraka ga 'ya'ya na,  har ma da wadanda Allah bai basu dama ba,  kalmar nagode ai tayi kadan wajen bayyana muku jin dadina , sai dai nace Alherin Allah ya isar muku a duk inda ku ka yi bigire .

    

Ehen Uhum uhun-hun

Kai daga jin wannan guntattakin sautukan da suke tasowa daga kasan maƙoshi ka san da su nake,  o'e da o'e ko kuwa dai a takaice na ce ghost r-r-readers 😂

Ba kome , Ba kuma zance kome ba , amma ku saurari haɗuwar ku da ɗanliti , Ah to meye ? Ai shine zai rama min irin cin tuwo a ƙoƙon da kuke min 😢.

A cigaba,  eh nace a cigaba da labewa a bayan labule . 😂 😂

Nagode .[11/14, 11:01 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )




Umm'muaz

36





Doctor Hamza tare da wasu abokan aikin su,  da wasun su ke a zaune wasu na tsaye  daga cikin ofishin shugaban su kuma tsohon malamin wasu daga cikin su a zamanin karatu , Professor Talba Garkiɗa,

A zahiri a nutse yake ya bada hankalin sa da ƙululun idanun sa bisa kan Prof wanda ya dilmiye sosai cikin yin bayanai game da cutar da take damun matar dake cikin mawuyacin hali a ICU da jagorancin duba ta ke a hannun mutane huɗu daga cikin su .

Sai dai a baɗini cikin hankalin sa sam babu nutsuwa , babu jin daɗi bare kwanciyar hankali a tun jiya da ya amsa ƙiran prof .

Nisawa yayi yana sake jin yadda zuciyar sa ke ƙara ƙuntata , wai shikenan domin Ubangiji Allah yayi umarni 'ya'ya su bi iyayen su sai kuma su iyayen suyi amfani da wannan dama wajen cusgunawa 'ya'yan su ?

Ah cusgunawa mana , idan ba dai Baba ya so sanya shi a tsaka me wuya tare da damal-mala masa ginin tsarin rayuwar da ya riga ya tsarawa kan sa ba wanne dalili ne zai sa shi ya ɓaɓ-ɓako masa da maganar ƙarin aure ?? Wai fa ƙarin aure ? Shi lamarin ma har kawo yanzu mamaki yake bashi , yana tantamar anya ma kunnuwan sa sun ji zancen a dai-dai ?

Idan ya tuno da yadda kalaman suka fito daki-daki tare da sake jaddadawa akan babu shakka umarni yake ba shi har ma kuma ya riga ya sama masa matar , sai ya ji wani mololon baƙin ciki ya tokare shi , shi fa ba yaro bane yanzu.

Shi kenan haka zai yi rayuwar sa tare da mata har biyu da ba zaɓin sa ba a matsayin matan sa ? Safiyya da kan ta ba zaɓin sa ba ce , aure ne mai kama da na dole aka liƙa masa shi kuma ya sa hannu dole ya amsa daɗi da ƙarawa lokacin yana a tsakiya da jin takaicin ɗiya mace , domin haka yasa shi gaza musantawa .

Yanzu kuma da yake ɗan lallabawa da Safiyyan da daɗi ba daɗi suna zaman su tana faran ta masa dai-dai gwargwado shine kuma za'a sake bijiro masa da wani auren ? To a dalili da me ? Shi a tsarin rayuwar sa babu saki ba kuma gurbin mata biyu .

Mace ɗaya tal ta ishe shi ,shiyasa ma ya bada kai yana lallabawa da wacce ta zama ƙaddarar sa ,  rabon sa duk kuwa da cewa ba zaɓin sa bace .

to yayi yaya da mata biyu ? Jera su zai yi yana kallo ? Ko kuwa a wuya zai rataya su yana yawo da su suna reto ?  Ɗan tsaki ya saki a hankali .

Lokacin da ya fahimci professor Garkiɗa ya kammala jawabin sa ba tare da shi ya fahimci kome ba , alhalin kuma musamman yayi tattaki ya zo domin ya saurari koyarwar duk da cewa kusan abunda ya riga ya sani ne zai sake sanar da su , to amma shi ai maye ne akan neman ilmi kome ƙanƙantar sa , hakan ya sa shi yin zarra a cikin abokan aikin sa masu matsayin karatu irin nasa ,

Ai ga irin ta nan tun kafin a je ko'ina ya fara sururucewa akan tunanin rayuwa da mata biyu , anya kuwa zai iya ?

Miƙewa yayi yana jin takaicin rashin saurarar koyarwar da prof yayi musu .

Bayan fitowar su daga ofishin suka tsaya shi da abokin aikin sa suna tattaunawa .

Mata biyu ne suka doso wajen hannuwan su riƙe da kayayyaki ,  kondunan zuba abinci da wasu tarkace ,

Karaf idanun sa suka sauka akan matar rannan ,

Tun a ɗan nesa yake nacewa kallon kamannin ta da ke kamanceceniya sosai da na Khaalty Rahima , ba su da wata maraba , sai tsabar tsufa da wani irin duhu da wannan tayi marar kyaun gani,

tabbas ko da khaalty Rahima na raye bai ci ba ace tayi wannan tsufan, dududu shekaru biyar zuwa shidda ta ba shi ,

Bai farga ba suka gota shi , da sauri ya bi bayan su ba tare da yayi sallama da Abokin sa ba
   Yana son sanin wacece ita , ?

Sallama ya dunga rangaɗa musu har baki biyu babu wacce ta juyo a tsakanin su sai da yayi ta uku ,

Ɗayar kakkaurar matar baƙa gajera ta juyo ,
" Au nan ne  ? Da mu ne ? Ca nake a iska nake ji ,

"Sannu Mama Da abokiyar tafiyar ki na ke son yin magana ,

ya furta haka yana nuna bayan ta da ta ɗan yi gaba batare da ta tsaya ba tana cigaba da tafiyar ta , takawa yayi ya bita ganin tana shirin shan wata kwana .

"Hajiya sannu ,
" sannu Hajiya ,"

Shiru ya ji tayi ,
Dan haka ya ɗaga taku ya sha gaban ta ,

Da sauri ta ɗago kan ta , ta kai duban ta kan shi ,

Kallon-kallo suka yi , jakar kayan da yake hannun ta ya sulluɓe ƙasa ,

Lokacin da ta wara idanun ta dake nuni ƙarara da halin ruɗanin da zuciyar ta ke ciki  ,

   Motsa baki tayi da sautin ya gagara fitowa  , sai kuma tayi saurin kauda kai .

,"Khaalty Rahima ??

Yace da wani irin maɗaukakin sauti , da ya zarce da wata ƴar dariya da ke nuna tsantsar farin-cikin da ya kawo masa ,

Hannuwan sa biyu duk ya kai ya kamo nata hannuwan dake cikin hijabi ya riƙe ,

" Malam lafiya kuwa ?
Matar da take abokiyar tafiyar ta ta furta haka lokacin da take ƙarasowa tana bin su da kallon mamaki da manyan idanun ta .

Bai kula ta ba ya jijjiga hannun ta dake cikin nasa ,

,"Khaalty Rahima tahadah 'iilaya rja'a ,
   Ya furta hakan yana sake kallon ta da ta sunkui da kai tayi ƙiƙam kamar bata jin sa , bai yi aune ba ta warce hannun da ƙarfi , ta sunkuya tana tattara kayan hannun ta .

Durƙuso yayi yana taya ta kwashewa ,tare da leƙa fuskar ta yana son sake ganin ta .

"Khaalty Rahima"

ya sake ƙira da wata irin murya , fuskar sa na nuna tsantsar damuwar da ta maye gurbin farin cikin sa .

"Yau ga ikon Allah Malam kurma ce fa kake ta faman yi mata magana , '

Tare suka miƙe da ita , da wani yanayi na firgici ya juya yana kallon matar .

"Kurma ?

"Eh kurma ce mana , hala ka san ta a wani waje ? Mamar Bulama da yawan gidajen masu kuɗi take ,  Ai manyan gidaje ɗaya-ɗaya ne a cikin garin nan da bata yi aiki ba , har gidan inn-in wannan mashahurin attajirin mai tashen kuɗi na bala'i da masifa , bani sunan sa ma ? Ga shi da suna mema sunan na sa ??,'

," kika ce kurma ce ? Mamar Bulama ? Wacece ita ? Ba gaskiya bane wannan ƙanwar Mama ta ce .

Juyowa yayi , sai dai ko alamar ta bai gani ba a wajen ,

" ina take ?,"

",Tayi tafiyar ta , ai kaga halin ta na miskilancin da yake sa ake tisa ƙeyar ta a kore ta daga gidajen da tayi aiki , miskilanci da faɗin rai na tsiya , to Allah na tuba kana talaka faƙiri mai neman na sawa a bakin salati ina kai ina faɗin rai ? Wa kuma zaka gwadawa ya ɗauka?  Gidaje daban-daban huɗu muka yi aiki tare , biyu akan halin ta aka ƙore ta biyu akan wannan ifiritun ɗaya-ɗayan ɗan nata Bulama haba me ake da batsal-tsalewa irin ta Bulama ya ɗan yayen biri ? .

Bai ƙarasa sauraron matar da take tsakiyar yi masa bayani har bakin ta na kumfa ba yayi wucewar sa ya bi sawun ta ,

  Cikin ran sa yana faɗin

",haba me ake da ɗan banzan surutu marar ma'ana ?

Duba ta yayi har ɗakin da ya san marar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login