Showing 162001 words to 165000 words out of 411050 words

Chapter 55 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

8146

ma ita da ƙanwar ta bamu ji ba , wallahi ranka ya daɗe ba ni na kori yarinyar nan ba raina yana son ta ina ƙaunar ta ita da abun....

Marin da ya ɗauke ta da shi ya hana ta ƙarasa dogon labarin ƙanzon ƙuregen da ta kwaso ,"

  Ku musu duka ku kai su mota mu wuce da su barrack , idan sun ɗanɗani azaba zasu faɗi inda take , " cewar Yaoussouf

  Kamar jira suke suka fara ƙwallo da su nan take guri ya ruɗe da ihun matan banza da kururuwar ɗan liti da ya buɗe maƙogoro yana zurma ihu tamkar ana watandar tsokar jikin sa , ya buɗe muryar sa ta asalin garjejen namiji ,"

   Kora su suka fara yi waje da shirin tafiya da su barikin su na soji ,"

  Nan fa idanun Yagana ya fara raina fata wacce ta sha manyan bulalai huɗu ,
   Ita tasan aka kai ta wannan barikin sojin sai ɗan buzun ta ,"  ta tsoraci soja ba kaɗan ba domin ta ga irin yadda basu ɗauki kisa a bakin kome ba ,
     Bulalar belt ɗin da wani soja ya sake sauƙe mata a gadon baya yana tunkuɗa ta ita ta gigita ta ,"

  Wayyo Allah bayana , fatar bayana ta sulluɓe , dan Allah ku tsaya wallahi na san inda take zan kai ku , zan kai ku Dan Allsh kuyi haƙuri kar ku tafi da ni ,
    Matsowa gaban ta yayi ya bar chasa madam saly da ta riga ta fara galabaita da bulalar soji ,

    Kin ka ce kin san inda take ?  Tana ina ? Ki kai ni yanzu - yanzu idan kin ƙi zan harbe ki ,"

    Muryar ta tana sarƙewa tace

Nasan inda take kuma ma ai ƴar uwa ta ce zan kai ku yanzu , Dan Allah kar ku ji min ciwo kar ku tafi da ni ,wallahi nasan inda YaKaKa take ,"

Finciko ta yayi ya miƙar ta tsaye , muje ki kai ni
     Yace yana tunkuɗa ta gaba , kafafun ta ko takalmi babu ,

   Ku cigaba da tsare su , idan mun same ta zan sanar da ku ta téléphone sai ku ƙyale su idan bamu same ta ba zaku zo mouna da su barrack ,

Ɗaya daga cikin motar suka hau , Yagana da Youssouf da Tafeeda ,

  Ki gouda muna hanya," yace da ita

Ba'a yi wata tafiya mai nisa ba Yagana tace a tsaya ga gidan
    Tana yi musu nuni da gidan Amne ,
Su suka fara fitowa shi da Tafeda suka tasa ƙeyar yagana kai tsaye suka sanya kai cikin gidan .

    Amne tana kishingiɗe akan ƴar daddumar ta tana shan hantsi ta ga tsayuwar sojoji akan ta ,"
   Miƙewa tayi zaune tana kallon su a tsorace ,
   Wannan ce ta ɓoye su
Yagana tace haka tana nuna Amne da ɗan yatsan ta ,
   Da sauri ta miƙe tsaye ,
Ranku ya daɗe lafiya ?
  Wanne laifi nayi dan Allah ?

Yarinyar da kin ka boye zaki fiddo mana ita yanzu mu tahi da ita ,ƙanwa ta ce ,

   Wacce yarinyar ?
  YAKAKA
Yagana ta bata amsa tana matse ido

Zuciyar Amne ta buga da ƙarfi dan razana ƙwarai ta gane yakaka yarinyar da ta mutu wurin haihuwa , ƴan gudun hijirar da ɗan ta ya taimakawa yake riƙon su a gidan su , ganin jami'an tsaro suna neman ta yasa hantar cikin ta kaɗawa ,

anya baza su harbe ta ba idan ta gaya musu ai wacce suke nema ta mutu ?? Ko su tafi da ita barikin su na soji su wahalshe ta a banza , bata da mai karbo ta , ɗan ta yau-yau yayi tafiya , ya bar garin , dole tayi taka tsantsan kar ta ɗaure kan ta !

Mahaifin su Hamza babban mutum ne ba abu mai sauƙi bane a tozarta shi musamman ma da ta san basu yi wani  mummunan laifi ba , tana da yaƙinin idan ta sada su da shi kome zai zo da sauƙi , shi zai iya musu bayani su fahimta ,

     Ni ba nice mariƙiyar su ba riƙon kwana ɗaya jal nayi musu , a halin yanzu suna gidan mariƙin su , zan iya kai ku gidan na dawo ?

  Ta ƙare jawabin ta da sigar tambaya ,?
   Ki gouda mana gidan , idan har kin san gaskiya kin ka faɗi ,"

  Gaskiya ne wallahi , muje na kai ku ,

Babu Ɓata lokaci Amne ta kai su har Unguwar su Doctor Hamza ta nuna musu gidan daga nesa ,

Kuna iya komawa muhallin ku Tafeeda yace da su, Youssouf zai yi magana , ya masa alama da yayi shiru ,"

    Gudu-Gudu Yagana ta tare mai napep ta shiga ,
sansanin ƴan gudun hijira zaka kai ni ,"
tace da shi tana waiwayen bayan ta ,
    Ta ɗan madubin gaban napep ɗin ya dube ta , wanne daga cikin sansanin ƴan gudun hijirar zan kai ki ??
   Na hanyar bulunkutu tace da shi ,
Cikin ran ta tana kitsima gara ta koma sansanin ƴan gudun hijirar inda samun ta zai yi wahala , zata ɓace a cikin dubunnan ƴan gudun hijira ƴan uwan ta domin ta san ta yarda ta bari  wannan sojan ya san da haɗin bakin ta aka gudu da Yakaka har wani garin da ita kan ta ma baza ta ce ga sunan garin ba , bata da hanyar saduwa da samy baby , toh fa tasan ba abunda zai hana shi harbe ta har lahira ya kashe ta !

   Tattaki suka fara suna nufar gidan da kowanne cikin su ke yiwa kallon sani ,
    Kusan a tare suka ce da juna wannan ai gidan da munka zou biki kwanakin baya ,"
      Babu shakka shine Yarima Youssouf ya amsa ,

Maigadin gidan ne ya tare su , cikin ladabi ya gaishe ya ɗora da tambayar su ina suka nufa ?
  Suka shaida masa gurin maigidan suka zo ," nan ya shaida musu zai shiga ya sanar da shi zuwan su , har youssouf zai yi magana , Tafeeda ya sake dakatar da shi , bayan wucewar sa yace da shi ,"
    Ɗan ouwa mu bi kome a sannu , kar muyi garaje .
  Bai ce da shi kome ba , suna tsaye maigadin ya fito yayi musu iznin shiga gidan ƙarƙashin jagorancin sa ,"

Har cikin falon yayi musu jagora , prof yana zaune suka shigo bayan sun sunce ƙwafta-ƙwafatan takalman su daga waje ,
   Da kallon rashin sani yake bin su bayan sun gama taƙaitatciyar gaisuwar da ta shiga tsakanin su ,"
    Samari daga ina kuke ? Ban shaida fuskokin ku ba !
    Ɗan jim suka yi suna tattaro nutsuwar su , kafin Tafeeda da shine ya tsara kome yace
   Baba munzo neman watta ɗiya da anka ce kana riƙo sunan ta Yakaka , " wannan mijin ta ne ,
   Ya ƙarasa zancen yana nuna youssouf
    Ɗan jim prof yayi, wacece yakaka ? Ko dai yarinya ƴar gudun hijira ? ,'

Yaya kamannin ta yake ? Kuma a wanne yanayi take ,"
   Doguwa ce fara , tana da tsago a fuskar ta , sannan , sannan kuma tana ɗauke da juna biyu ,  
   Youssouf ya ambata

Kaine mijin ta ?  Prof yace da shi fuskar sa na nuna jimami ,"
  Ni ne baba
  Ya amsa
  , cikin zuciyar sa yana fatan tambayoyin su tsaya iyaka nan , tare da zaƙuwa da son a ƙira masa ita ya gan ta , Allah sarki ashe ma ƴar hijira ce ,
   Tunanin sa ya tsaya chak lokacin da yaji prof yace
    Yaro ina baka haƙuri tare da tunasar da kai akan cewa duk wani mai rai mamaci ne , yarinya yakaka ƴar gudun hijira ta rasu a wajen haihuwa bayan riƙon su da muka yi a gidan nan tsawon watanni bakwai , ta rasu ta bar ɗiyar da ta haifa tare da ƙanwar ta da muke riƙon su tare ...

Ji yayi wani irin yanayi mai kaifi yana ratsa zuciyar sa wanda ya zarce kaifin tsoro ko firgita , tsintar kan sa yayi a hali na shuɗewar tunani na wucin gadi , jikin sa a take ya ɗauki rawa , da wannan yanayin ya watsa idanun sa kan Baba prof ,"
   Yarinya yakaka ta mutu ? Ta mutu a wajen haihuwar abunda ke cikin ta ? Ta mutu bamu gana na nemi yafiyar ta ba ?  Ta mutu ban gyara kuskuren da nasa muka aikata tare ba ? Ta mutu Alhalin ban nuna mata godiya  ta akan irin taimakon da ita take tunanin ta mun ba ? Meyasa ta Mutu ta bar min nawi mai girma bissa kaina ni kaɗai ?
   Tafeeda ne ya riƙo shi ganin yadda yake surutai kusan bai cikin hayyacin sa , tabbas shi da kan sa ya ji mutuwar  yarinyar , kome kuma ya kunce masa , zuciyar sa kuma ta raurawa ,

Kayi hakuri yaro mutuwa na kan kowa bari na ƙira a kawo maka ɗiyar ka , ƙanwar ta ma ta zo ku gaisa ,"

  Waya yayi cikin gidan akan a zo da Falmata da baby mama ,"

Ya maida hankalin sa kan su Youssouf da tafeeda yana nazartar su , akwai tambayoyi dayawa da yake son yi musu ba wai dan bai yarda da su ba , sai dan a farkon kawo yarinyar gidan Hamza ya sanar da shi mijin yarinyar ya mutu boko haram sun kashe shi , sai kuma ga shi yanzu ya ga jami'in tsaro a matsayin mijin ta ko daman ɓata yayi ba mutuwa ba tsawon wannan lokacin ?

Shigowar Falmata riƙe da mama tare da rahima , shi yasa biyamuradi Youssouf ɗago kan sa ,"
    Idanun sa so suke su ga ɗiyar , so yake ya samu rangwame ta hanyar fahimtar bashi da alaƙa da ɗiyar da aka samar ta hanyar banza wacce zuwan ta yayi sanadin mutuwar mahaifiyar ta me tarin rashin galihu , bai so lamuran sa su sake munana ,

   Sai dai wani yanayi da ya tsinka jinin jikin sa lokacin da hasken fuskar ƴar jaririyar da ya ɓanɓare daga hannun falmata ba tare da ya jira sun ƙarasa shigowa falon ba yayi tattaki da sassarfa ya taro su ,

    Yanayin mai ƙarfi ne da bai taɓa jin kwatankwacin sa ba da ɗai duniya ,

Jin sa yayi a wani yanayi wanda ya so ya saɓawa wanda yake cikin sa kafin ɗora idon sa akan ƴar da yaji ya gaza gane wacce matsaya yayi mata a halin da yake ciki ,

   Kallon ta yake tamkar yana son ganin abun da ke lulluɓe cikin fatar jikin ta , kallon da yake mata ya sa duk wata suffa tata jeruwa cikin tunanin sa tana juyawa tare da girma mataki-mataki har zuwa lokacin da kammanin ta da mahaifiyar sa suka gama fitowa tsaf , tamkar kobo da kobo ,
     Bai san lokacin da idanun sa suka samar da ruwan hawaye ba sai kawai ganin ɗigar su yayi akan fuskar ta , wanda ya nutsar da idanun sa kai babu shakka yana iya kallon ƙofofin gashin jikin ta ,
   Sauƙar ruwa a fuskar ta ya sanya ta buɗe idanun ta a hankali ta wara su akan sa , fes !  da shi ma ya sake ware nasa idanun tare da ɗage duk girar sa biyu abun da ya kan yi idan yana cikin yanayi na shauƙi ,

Yamutse fuskar ta tayi cikin salon su na rikicin jaririyar zata yi kuka ,
   
  Da sauri ya ɗago ta zuwa dai-dai fuskar sa ya sanya kan karan hancin sa yana goge mata ƙwallar sa dake kan kumatun ta da yake zaton ita zata sa ta kuka ,
   Ai kuwa tamkar ya kunna ta sai kuwa ta sa kuka ,
   Kukan ta ya zo dai-dai da fashewa da kukan falmata wacce da kyar Rahima ta banbare hannun ta daga cukumar da tayi wa rigar Youssouf , cewa take wanene anan ?
Rahima waye ya kwace min baby ?
Ka bani ita dan Allah ka bani ita kar ka sa ta kuka ?  Kai waye , ? Rahima kika ce min Baba ne yake ƙiran mu ,? To waye ne ya karɓe min Yakaka na ?

  Muryar prof ta sa ta ɗan samu nutsuwa har ta sassauta riƙon da ta yiwa youssouf , rahima ta samu nasarar janye hannun ta ,

  Amma kukan yarinyar da take jin sa kamar ɗigar narkakkiyar dalma ya sa ta kasa tsayar da kukan ta , "
   
    Ganin kukan ta yayi yawa ya sa Tafeeda tasowa ya dafa kafaɗun Youssouf , yana kallon fuskar sa , muryar sa babu ƙarfi sakamakon halin da ya ga Youssouf ɗin ya shiga tunda ya ɗaura idanun sa kan ƴar , yana nufin ɓullowar wani gagarumin lamari Masarautar Maradi .

Ɗan ouwa bada ɗiyar nan ga mariƙiyar ta , ga ta sai kuka take , !

Dauke idanun sa yayi da kyar daga fuskar ƴar ya mayar kan Tafeeda , da wata muryar da bata da amo yace ,"

  Ɗiya tawa ce Tafeeda , wagga Ɗiya jini na ce , Ɗiya ta ce , A yau ni Uba ne , Uba ne ga wagga ɗiya da tsautsayi tare da kaddarar zuwan ta duniya ya sa kome ya faru kamar yadda ya faru ,"

  Ɗan satar kallon prof , Tafeeda yayi yaga yadda hankalin sa baki ɗaya ke kan su , amma kasancewa falon me girma ne da ƴar tazara a tsakanin su ,
   Wallah ka lura Ɗan ouwa idan ba hakka ba kana iya ɓata mouna kome ,

Hannun sa ya kai da nufin karɓe ƴar daga hannun sa , wata irin zamiya Youssouf ɗin yayi ya janye ƴar jaririyar sosai zuwa cikin jikin sa ,"

Baka ganin kuka take ?? Ka bari na lallashe ta ,

  Haɗiye firgicin sa Tafeeda yayi , ka bada ita Yarima uwar goyon ta zata mata lallashi , akwai abubuwa dayawa a gaban mu ,
   Ina uwargoyon ta ?
Yace yana mayar da duban sa kan su Falmata da duk budurin da tayi na cukume sa da kalmomin ta duk bai ji su ba , ruɗanin da yake ciki ya toshe masa kunnuwa daga barin jin hayaniyar ta ,
    Da ɗan yatsa Rahima ta nuna masa Falmata wacce tayi shaɓe-shaɓe da hawaye sai ajiyar zuci take ,
  Ga ta nan ,
Matsowa yayi , ya miƙa mata ƴar
   Karɓe ta , ki kula da ita kar ki bari kome ya cutar da ita , kar ki bari tayi kuka ban lamunta ba ,"
   Hannun ta miƙa saitin inda take jin hucin sa , ta karɓi ɗiyar tana jin wani sanyi na ratsa zuciyar ta yana kore tunanin da zuciyar ta ke son kawo mata akan kamar ta taɓa jin amon murya kwatankwacin wannan ,!

Da kallo Rahima ta bi shi , kamar shine ? Kamar fa shine na jikin hoton cikin kayanYakaka , babu shakka ma shine ,"

   Ku koma ciki Rahima , prof yace ga su ,"
   Toh ,
suka ce suna kama hanyar barin falon ,"
    Youssouf zai magantu , Tafeeda yayi saurin yunƙurowa yana faɗin ,
  Mun gode Mun gode Baba , Allah ya saka da Alheri ya bada ladan Taimakon da kayi mana , yanzu zamu koma saboda a bakin aiki muke amma muna dawowa cikin kwanaki biyu masu zouwa da yardar Allah ,"

Ameen toh babu kome Allah ya nuna mana kwanaki biyu masu zuwa Allah ya ƙara muku haƙurin jure rashi, idan kun sake dawowa zamu yi magana ,..

Youssouf zai yi magana ,
  Tafeeda ya sake katse shi yana jan hannun sa
   Ɗan ouwa tashi mu tafi ,
Jaan hannun sa yayi suka fito daga gidan suna fitowa Youssouf ya zare hannun sa daga na Tafeedah ,
A tare suka haɗa baki wajen tambayar junan su ,!

Ɗan ouwa meye haka kake shirin yi ?

Kana nufin nan zan tafi na bar ƊIYA TA ?
   Hannun mutanen da ban san su ba ?

Kallon baka da hankali Tafeedah ya yi mass kafin ya fara taku ya nufi wajen motar su , ',kazo muje muyi magana a tsanaki ,
   Ran sa bai so ba ya faɗa motar ya shiga Tafeeda ya fara ƙoƙarin tada motar lokacin da yake magana da sojojin nan akan su bar su madam saly an samo inda yarinya take ,"  ya sauƙe wayar yana hawa kan titi ,

Da fitar su Prof ya ɗaga waya ya ƙira Doctor Hamza bayan sun gaisa , yace
     Yanzu mijin yarinyar nan ƴar gudun hijira mai rasuwa ya bar nan gabana tare da ɗan uwan sa , ka ga ikon Allah ashe shi bai mutu ba , ya zo ya ga gan ta tare da ƴar sa yana...
   Wani mummunan cin birki da Doctor hamza yayi wanda hatta prof sai da yaji ,
  Subahananlahi , Hamza ban hana ka ɗaukar waya alhalin kana tuƙi ba ? Da fatan dai baka yi haɗari ba ? kana jina ?

   Muryar sa ƙasa ƙasa ya amsa bayan ya ɗauke kan motar zuwa gefen hanya bakin daji ya tsaya ,

Ina ji Baba , a bashi ƴar sa tare da ƙanwar matar sa ya tafi da su kar su sake dawowa Baba ,"

   Jimm prof yayi ,
Kafin yace
Toh babu kome idan sun nemi hakan ai sai a basu daman ai hakan ya kamata , ka dunga kula hamza ka daina ɗaukar waya alhalin kana tuƙin mota , kana ina ne yanzu ?
   Ina jigawa Baba , insha Allah zan kula baba , ka min addu'a baba , zamu yi magana idan na isa .
  Toh Allah ya tsare hanya daga ka isa ka sanar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login