Showing 357001 words to 360000 words out of 411050 words

Chapter 120 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

8095

ta shiga ta fara kai kawo cike da tunanin kan mataki na gaba da zata ɗauka wajen cigaba da tsare Falmata dan kada a samu wani lamari ya gifta da asirin ta zai shiga hatsarin tonuwa

A ɗan firgice ta waiga jin motsin shigowa ɗakin Hafsatouwa ce ta ƙaraso gaban ta da sassarfa bayan ta rufe ƙofar .

"Hafsatouwa sirrina yana cikin haɗari ya zama dole ki shirya ki tafi Zuru wajen mai jar-tawada ki amso min wani gagarumin aikin da zai kurumtar , ya makantar idan ya kama ya gurguntar da duk wasu da zasu iya kawo min tsaiko kan ƙudiri na ne ma duk ayi .

" a min aikin da zai shafe tunanin ita kan ta yarinyar nan da ta san sirrin na sannan a mantar da duk wasu makusanta nata daga tunanin ta har sai lokacin da na gaji dan kaina da hukunta ta na sake ta , ke Hansatouwa ina so na zama ni nice , kowa kuma ya zama ba kowa ba , ina nufin kowa da kowa na cikin masarautar Maradi su dawo ƙasan iko na a baɗini da fatan kin gane ?

Cike da jin tsoron yanayin da take hango uwargiyar ta a ciki hafsatouwa ta shiga gyaɗa kan ta .

"Oumarnin ki abun bi ne ranki shidaɗe uwargijiya ta mai girma .

"Da kyau to ya ya kin yi abunda nace kiyi ?

"Ranki ya daɗe tuni nayi .

"Kin ji motsin ta ko kaɗan daga inda take ?

" ba wata alama dake nuni da cewa akwai rayayyen mahaluki a bigiren da alama yarinyar bata da taurin kai .

"Idan ta yi haka ta sauƙaƙawa kan ta riskar wasu daga cikin tarin horon da nake mata tanadin su .

"Kina iya tafiya yanzu , idan buƙatar son ganin ki ya zo zan aika a min ƙiran ki .

" To ranki ya daɗe godiya nake .

Gaf da Azahar bayan hankulan mafi yawan mutanen gida ya tafi ga haramar sallah Hajiya Mama ta kashe jiki ta nufi tsohon sashin babar ta kuma Uwargidan Sarki Azizou Baskore "Hajiya Uwa .

Da tun bayan rasuwar ta sama da shekaru goma sha takwas babu wanda ya sake zama a sashin ya zama tamkar kufai , sai fa Hajiya Mama da jifa-jifa take zuwa sashin tana yin wasu abubuwan da ta ce raya sashin take yi da yake a matsayin na uwa a gare ta wanda kuma a baɗini daga Allah sai ita sai kuma tsirarun mutanen da tayi haɗakar ƙulla sirrukan ta da su , suka san ainashin abunda take aikata a sashin a duk ƙarshen kowanne wata .

Bayan ta gama nazarin wajen ta tabbatar babu wani mahaluki a wajen da zai iya jin abunda za ta yi ta sanya ɗan makulli ta buɗe ƙofar falon bayan ta ɗau wata leda da take yashe daga kusa da ƙofar .

Kan ta tsaye ta shiga falon ta tura ƙofar ta rufe tana mayar da ganin ta kan Falmata wacce take takure daga can gefe cikin datti da ƙurar da ta maye gurbin shimfiɗar ɗakin ya zama duk inda ka ɗora ganin ka datti ne da tankaɗaɗɗiyar ƙasa kamar an kwaso an zuba ba'a ko iya ganin ainashin dandaryar ɗakin .

A hankali Falmata ta ɗago kan ta dake tsakanin cinyoyin ta da ta haɗa su ta takure ba'a ce mai ciki bace .

Taku tayi ta ƙarasa gaban Falmata tashin sautin ta ya biyo bayan ledar da ta wurgawa Falmata

" wataƙila kina jin yunwa ki ɗau abinci ki ci ya rage naki ki cinye shi duk ko kuma ki rage dan anjima .

Falmata da fuskar ta ta kumbura saboda kuka ta buɗe bakin ta da take ji ya mata nawi muryar ta bata fita sosai tace "Sallah nake so nayi ki nuna min wajen da zan yi Alwala .

Wani kallon banza Hajiya Mama ta mata kafin ta ƙuta , sai da ta mula sannan tace " ga rairayi nan kina zaune a cikin sa ki buga ƙasa kiyi taimama .

Bata jira ba ta cigaba da cewa " ina sake jaddada miki muddin kina son tsira da rayuwar ki to ki kiyaye abunda zai sa a san kina nan , idan kuwa kin ƙi ji .?

Da zubowar sabbin hawaye Falmata tace "Hajiya Dan Allah ki tausaya min , ki ji tsoron Allah mahalicci da yake kallo tare da jin kowa da kome , ban yi miki kome ba .....

"Ke .

Hajiya Mama ta daka mata tsawar da ya sa Falmata yin shiru " kina son karya doka ta ne ?

Da sauri Falmata ta girgiza kai .

"Tashi , tashi nace ko ?

Da kyar Falmata ta miƙe saboda ƙafar ta da ta ji ciwo a jiya ga yunwa da ƙishirwa , sun sa har jiri take ji bayan ciwo mai tsanani da kan ta yake yi , ta ɗingisa dakyar ta bi bayan Hajiya Mama wacce tayi gaba zuwa wata ƙofa ran ta cike da fatan "Allah yasa afuwa zata mata ta fitar da ita daga wannan wajen .

Da kallo ta bi ɗakin da su shiga wanda ba kome a cikin sa bayan tulin ƙura da yanar-gizon da ya zarta na falon sai fa wani karmamin gadon katako da duk gara ta cinye shi shi ɗaya ƙwal a ɗakin.

"Anan za ki cigaba da zama , ga banɗaki nan a ciki amma bani da tabbacin rasa macizai da kunamu a ciki sai ki kula wajen amfani da shi idan ba haka ba kin ga sun hutar da ni daga kashe ki.

Daga haka Hajiya mama ta juya da kusan tare suka juya da Falmata wacce ta zube a ƙasa tana wani irin kuka ta riƙe ƙafar Hajiya Mama tana shisshiƙa kamar ran ta zai fita tace "Hajiya Dan Allah , Allah .....

Hanɓare ta Hajiya Mama tayi ta taka da sauri kafin Falmata ta yunkura ta fita ta rufo ƙofar ta murɗa ɗan makulli .




Tare suke da page 51b
[4/15, 10:16 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( hargitsin Rayuwa )


Umm"muaz


51b



Duk yadda Maimartaba yake tunanin za'a yi samu wata alama da zai nuna ina Falmata take anyi amma babu nasara har aka kwana aka yini babu wani bayani takamaimai na inda take .

Zuwa lokacin kuwa Biyamuradi Youssouf gaba ɗaya ya gama birkice musu ya kuma matsa lamba kan son zuwa Niamey wajem Maimounatou dan ta faɗi inda ta kai Falmata.

A ƙarshe ba yadda maimartaba ya iya ganin yadda ɗan nasa ya zama yasa ya masa umarnin tafiya bayan ya masa nasiha akan haƙuri da mallakar zuciyar a duk lokacin da rai ya ɓaci sannan ya gargaɗe shi da gujewa ɗaukar mataki cikin fushi .

Ƙarfe goma na ranar jirgi ya ɗaga da shi da Bilal da zai masa rakiya zuwa Niamey .

Bayan tafiyar Youssouf Hajiya Mama ta ƙira Hafsatouwa ta umarce da cewa gobe da sassafe ta kama hanyar Zurun Jahar kebbin Nigeria bayan ta danƙa mata isassun kuɗin da zasu ishe ta .

Duk da cewa Falmata baƙuwa ce a masarauta Maraɗi amma hakan bai hana masarautar ta zama cikin alhini ba kasantuwar ta riga ta zama wani ɓangare na gidan , ko'ina ka ratsa za ka ji bayun gidan suna batun ɓacewar Gimbiya Fatima da cikin jikin ta .

Hajiya Umma da kan ta ta shiga damuwa musamman da ya zama Maimartaba yana ganin har da sakacin ta wajen ɓatan Falmata da har a jiya da dare ya tabbatar mata da hakan cikin fushi .

Hajja kuwa ƙurewar tashin hankali ta shiga tayi kuka har ta bawa aku lada ta haƙura ta rungumi charbi tana addu'ar Allah ya baiyana mata uwarɗakin ta a halin lafiya .



Niamey .


Lokacin da Youssouf ya isa Niamey daga airport kai tsaye babban ofishin 'yan sanda ya nufa inda har lokacin ake cigaba da tsare Mammadou da Maimounatou sakamakon rashin sanin halin da shi yake ciki da hakan ya kawo jinkirin miƙa su kotu a musu hukunci .

Bayan ya cike takardu aka masa iznin ganin su da Mammadou ya nemi ganawa a farko .

Lokacin da aka fito da Mammadou , Youssouf da yake zaune bai san lokacin da ya miƙe ba da sauri ya taka ya taro Mammadou da yake tangaɗi , ba tare da ya damu da tsami da warin da yake tashi daga jikin Mammadoun ba ya kama shi suka zauna .

Da wani irin yanayi a fuskar sa mai tsauri yace "Mammadou ƙaƙa ka zama hakka ? Shin baka da lafiya ne ? Ko kouwa horo ake maka ?

Mammadou da zuciyar sa ta cika taf da farin-cikin ganin Youssouf ya riƙo hannuwan sa duk biyu kafin ya fashe da matsanancin kuka cikin kukan yake cewa "Youssoufa kai min gafara , ka yafe min ɗan ouwana na tuba ka yafe min , nayi nadama marar amfani na kouma yi tir da muguwar uwa irin tawa tare da.....

Da sauri Youssouf ya katse shi yana cewa "Mammadou kar ka tsawaita zance domin ba shi da wani amfani dan kouwa ba zai yi gyara cikin abun da ya wouce ba kouma zouwa ma nayi mu tai gida tare nan ba wajen yin zance bane Mammadou .

Cikin wani irin sauti Mammadou yace "da gaske Youssoufa zowa kayi ka tafi da ni gida ?

Miƙewa Youssouf yayi yana zube hannuwan sa cikin aljihu ya fara taku yana barin wajen ƙarƙashin rakiyar idanun Mammadou da ya bi shi da kallo sai da ya kai ƙofar ficewa daga wajen bai jiyo ba yace "ƙwarai yau kake kwana a gida Mammadou .

Daga haka ya fita yana jin yadda tattaurar zuciyar sa ke son tasowa ta hana shi duk wani afuwa da sassauci da yayi niyyar yi ga ɗan uwan nasa .

Ya juya baya ga ƙofar shigowa lokacin da aka taso ƙeyar Maimounatou ta shigo inda yake idanun ta da suka shige ciki ta ware tana kallon sa a take ta shaida ko wanene a gaban ta , sannan 'yar murna da ta fara safko mata jin cewa an zo ganin ta ta koma ciki fargaba mai girma ya mamaye ta da yasa har wasu siraran gumi suka fara tsiyaya ta cikin rigar ta .

cikin raggon taku ta nufi inda yake sai dai kafin ta ƙarasa ya juyo baki ɗayan sa yayi tsaye ƙem a gaban ta da juyowar sa tayi hanzarin sauƙe idanun ta ƙasa tana jin wani yanayi da ta gagara tantance a wanne matsayi zata ajiye shi "kunya ce ? "Nadama ce ? Ko kuwa tsoro ne ?

Bata ankara ba ta gan shi daf da ita kamar an tunkuɗo shi hannuwan sa zube cikin aljihun wondon sa da sautin sa mai amo da ya sake kaurarara yace "Madame, êtes-vous surprises ?

Wani murmushin yaƙe Maimounatou tayi da ya taho da ɗoyin da bakin ta ke yi , ta ɗago kan ta ta saci kallon sa kafin ta wani karya kai gefe ɗaya cikin muryar da ta saba hilatar sa da shi wacce yau ta sake matsewa tace "Pas vraiment, tu ne m'as pas surpris, je sais que tu reviendras vers moi.
Hannun ta ta miƙa da nufin taɓa shi ya jaa baya da sauri yana kokuwa da ɓacin ran sa da idanun sa da suka yi jaa ya mata wani kallon gargaɗi da ya kaɗa mata ciki .

Da baya-baya ya dangana da kan kujerar da take gaban ɗan teburin da yake cikin ɗakin ya zauna yana harɗe ƙafafun sa ɗayan kan ɗaya yace.

" idan kin ka yi tounanin kina da watta sauran dama guda da ta rage miki a gareni kin yaudari kan ki yau ba rana ce ta wassa ba don haka Arrêtez de jouer avec votre propre cœur et de vous dupe.

Wani murmushin ta sake yi kafin ta yi ɗan taku kaɗan tana juya baya ga barin fuskantar sa cikin ƙarfin hali tace " Bana neman watta dama dagga gare ka a yanzou sabbada kuwa duk watta dama na riga na same ta har ma......

Tsawar da ya yi haɗi da buga teburin gaban sa shi yasa ta juyowa a firgice , a tsaye ta gan shi fuskar sa da ta duba a lokacin ji tayi marar ta ta cika fam.

Ya matso daf da ita yana nuna ta da yatsan sa ya ce "kadda ki min wassa , ni damisa ne da ban juri wasa ba ban ɗauki wargin mazaje ba a fagen daga na sanya bakin bindiga na fasa ƙoƙon kan su na sa ƙafafu na taka cikin su kar kiyi zaton zan miki sassauci ,

hannun sa ɗaya da yake cikin aljihun sa ya zaro da yake riƙe da ƙaramar bindiga , yayi taku kaɗan zuwa baya kafin ya cigaba da cewa "zan iya tarwatsa kan ki da harsashi bayan na tattaka ki muddin kin ka cigaba da min fi'ili .

Kafin ya mayar da numfashi Maimounatou ta zube akan guiwowin ta ta haɗa tafukan ta biyo tana sakin wani mitsi-tsin kuka mai tafe da sautin tsoran da ruhin ta ke ciki tace jikin ta na ƙyarma tace ,

" Dan Allah kayi haƙuri kar ka kashe ni , wallahi sharrin shaiɗan ne ya sa na aikata abun da na maka ka yafe min .

Wani guntun murmushi Yayi kafin tace
"Ashe kina tsoron Mutuwa ? Ni kuma kin ka nemi kashe ni ? Babu yafiya a tsakanina da ke ko afuwa ba zan iya miki ba muddin baki sanar dani dalilin da yasa kin ka nemi raina ba?

Da sauri Maimounatou tace "wallahi zan faɗi dalili .

Komawa yayi ya zauna yana ƙoƙarin sassauta fushin zuciyar sa yace "Vous avez seulement 30 minutes.

Kamar an kunna radio Maimounatou ta shiga ba shi labari tiryan-tiryan tana yi tana kallon sa tana karya wuya da sharar hawaye .

Bai katse ta ba har sai da ta kai ƙarshe

Kan sa a ƙasa yace "menene gaskiyar cewa da kika yi Mammadou ya kawo gubar da kin ka ciyar da ni ?

Girgiza kai tayi cikin ƙaramar murya tace .

"ba shi bane ni na aiki Gnala ta sayo min . sannan cikin kuka ta cigaba da cewa

"Amma wallahi nayi nadama iyakar nadama dan Allah ka min afouwa ka sake bani dama na gyara kuskurena wallahi wannan karon da dukkanin zuciya ta zan zauna da kai zan tallafi soyayyar da kake '.....

Ɗago da kan sa da yake sunkuiye yayi yana ɗan buga tafin hannun sa akan teburin gaban sa yayi wani murmushi mai ciwo .
"Soyayya ? Yanzu kina zaton har kawo yanzu akwai sauran ɗigon na alamar son ki a raina ? Bayan duk abun ƙi da kin ka wanzu wurin aikata shi a gareni..

Huci yayi yana danne ƙiyayyar ta da yake ji mai karfi tana naso a cikin ran sa daga lokacin da ta ambaci sunan Ghaddafi Yacouba Dango a matsayin mutumin da ta nemi kashe shi a kan sa bayan irin ha'intar sa da tayi ta dunga yaudarar sa da sunan soyayya har ya aure ta bayan sun gama tanbaɗewar su da wannan riƙaƙƙen ɗan ta'addan haƙiƙa Maimounatou guba ce ba domin yana yaƙar zuciyar sa da babu abunda zai hana ya harbe ta a lokacin .

Ya tsaya faɗa mata matsayin da take kai a wajen sa a yanzu tamkar ɓata lokaci ne ko kuwa bata wani matsayi na daban da ya wuce wanda takai kai yanzu a wajen sa dan haka ya mayar da ganin sa gefe daga kan fuskar ta da alokacin yake ganin ta da muni fiye da duk wani mummunan abu da ya taɓa cin karo da shi a tsawon rayuwar sa .

"Ina kin ka sa a ka kai Matata ?

A dabar-barce Maimounatou tace wacce matar ka ?

Taku ɗaya yayi ya miƙa hannu ya figo ta tayi zaman 'yan dabaro a gaban sa ya shaƙe wuyan ta kafin ya danna mata bakin bandiga akan ta wata irin razananniyar tsawa ya daka mata yana sake maimaita tambayar ta.

" Ina ki ka kai Fatima-zahra Mata ta nace ? Ki faɗa min ko na fasa kan ki .

Baki ɗayan jikin ta ɓari yake ta kasa magana saboda maƙogoron ta da ya shaƙe ya sa ta fara jin ƙamshin mutuwa .

Ta kai mintuna biyu a haka a shaƙe a hannun sa , sai da yayi da gaske tukun ya iya haƙura ya sassauta shaƙar da ya mata ya ingiza ta ta faɗi .

Kan sa ya sake sauƙewa ƙasa yana huci bai ɗago ba yace " za ki faɗa min ko kuwa na kashe ki ?

Tana wani irin kuka Maimounatou tace "wallahi Allah ɗaya kenan bani da watta masaniya kan ɓatan ta .

Cikin tsawa yace "to waye zai sace ta? Waye maƙiyi na da ya wucce ke ? Ina da wani Maƙiyi bayan ki ? Za....

"Wallahi kana da Maƙiyiyar da ta wucce ni wacce ita tayi sanadin faruwa duk wassu abubuwa marasa kyau da sun ka samu rayuwar ka .

"Wacece itta ?

Ya tambaye ta a daƙile

Da sauri ta amsa masa da "Hajiya Mama.

Yamutsa fuska yayi kamar yana son tuna inda ya taɓa jin sunan .

Ganin haka ya sa Maimounatou cigaba da cewa " Baka da wata maƙiyiyar da ta wuve Hajiya Saratu , Matar Mahaifin ku Mahaifiyar Mammadou Hajiya Mama.

"Ita ta wanzu tsawon shekaru tana bin ka da sharri da ita da Tsohuwar Matar kakan ku Hajiya Uwa su biyun sune suka fara lalata rayuwar ka ta hanyar yi maka mummunan sihiri,

" su suka sa ka zama mashayin giya "giyar burkutu , su suka sa kayi zina da yarinya Amina wacce take 'yar uwa ga ɗaya daga cikin matan da za ka aura,

Su suka yi ma Asiri tun kana ɗan shekaru biyar bai fara aiki ba sai da ka shekara goma sha takwas , ranar da ka cika shekaru goma sha takwas a ranar ka fara shan barasa, ranar da ka cika shekara talatin a ranar ka fara yin zina a kuma ranar ...''

Ɗago ta Youssouf yayi ya haɗa ta da jikin bango gaba ɗaya jikin sa tsuma yake cikin ɗimauta yake cewa "ƙarya kike yi , ke maƙaryaciya ce maha'inciya munafuka ki faɗa min gaskiyar aina duk kika samu wannan bayanin ? .

Idanun Maimounatou sun fito waje amma bata haƙura da magana ba ta cigaba da cewa " kuma Hajiya Mama bata daina sabunta aikin asirin ba ko bayan mutuwar Hajiya uwa babban burin su ka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login