Showing 99001 words to 102000 words out of 411050 words
Chapter 34 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
? , a hankali ta kai agogon hancin ta ta sunsuna gami da rufe idanun ta , shi ma'abocin ƙamshi ne kome da ya dangance shi ƙamshi yake hatta kuɗaɗen da ya bata ƙamshin sa suke ," a hankali laɓɓan ta suka motsa cikin yaren ta tace,"Bature kam silum ," ( baturen baƙaƙen fata ,)
Motsin da ta ji yana nufo ɗakin ya sa tayi saurin ajiye agogon a gefen kuɗin ta fara jera kayan ta bisan su ,"
******************
Iya adadin nisan da yake yi da yarinyar iya adadin daɗuwar rikicin da yake ji cikin zuciyar sa tare da gangar jikin sa baki ɗaya ji yayi masifar da yake zaton ta ƙare tana sake taso masa ,'
Addu'o'i ya shiga yi iri-iri idan ya kama wannan ya gama ya kamo wancen ,
Ga mamakin sa kamar sake ƙaruwa lamarin yake domin zuwa yanzu karfi da yaji yake jin ana son sarrafa gangar jikin sa ya juya kan motar ya koma wurin ta , kamar yadda zuciyar sa ta riga tayi tsalla ta koma gare ta , "
Karfin addu'ar da yake yi ita ta duƙushe tasirin ko ma menene , har ya samu ya kawo inda suka yi masauki a bakin dajin ,
Bai kula kowa ba duk kuwa da gaisuwar ban girman da suke yi masa ta hanyar ƙamewa su sara masa ,
Kai tsaye ya shiga bayin sa ya ɗauro alwala , ya dawo cikin tantin sa ya sauke farillar sallar asubha da take kan sa ,
Yana idarwa baiyi ƙasa a guiwa ba ya ɗauko alqur'anin sa ya buɗe murya cikin nutsuwa ya fara tilawa ,
A hankali nutsuwa tare da amincin da suke tare da alqur'ani suka fara ratsa shi tare da yin tasiri ga wannan yanayin da yake tunzura shi ,'
Jingina kan sa yayi da jikin karfen tantin nasa lokacin da yaji wani irin bacci mai nawi yana son fusgar sa ,'
Ƙiran wayar sa shi yasa shi buɗe idon sa daga son yin bacci da yake ,'
Ami Tafeêdah
Shine sunan da ya bayyana à fuskar wayar !
Da rashin kuzari biyamuradi ya amsawa tafeedah sallamar sa, bayan nan suka ɗora da tambayar lafiyar juna ," ?
Ɗan ouwa da dama kou ? meke damun ka ? lalle cikin yanayin ka akwai damouwa yi gaogawar sanar da ni ?
Shiru youssouf yayi , yasan tafeedah yayi masa farin sani , yana kuma iya karantar kowanne irin yanayi yake ciki ," to amma baya jin zai iya faɗa masa damuwar sa, toh yace me wai ?? Ya sake dulmiyewa cikin alfasha bayan wanda tafeedan ya san yana aikatawa, ya ƙara da wata ??
Ɗan ouwa bani jin daɗin jiki na ne kawai , ciwon kai na damu na ,!
Babu kome ka ɗaure abokina idan har ka cigaba da ƙaurace mata a hankali ahankali duk wasu yanayi masu wuya da kake shiga idan baka sha ba zaka ji ka daina jin yanayin , sannan ka sake dagewa da addu'a .
Uhum
ita ce kawai kalmar da youssouf ya furta
Da ace tafeedah ya san abun da ya aikata da babu abun da zai hana abotar su ta samu tangarɗa
Nagode ! Cewar youssouf
Daga haka suka ɗan yi hira sama-sama , ganin youssouf ɗin bai tare da nutsuwar sa sosai ya sa suka yi sallama tare da sake ƙara masa ƙarfin guiwar gujewa burkutu !
Yadda youssouf ya ga rana haka ya ga daren yau ," tsafi gaskiyar mai yin sa ne ,"
Da ita yake son kasancewa a yanayi irin na daren jiya , rashin samuwar hakan a gareshi ya haifar masa da masifaffan ciwon ciki da amai bayan masifar da yake ji a ruhi da ƙwaƙwalwar sa , ji yake kamar ya zura da gudu yayi ta gudu har ya tadda ta , ko kuwa dai yayi fiffike ya sauka gare ta a cikin daren ,"
Shajaran majaran ya wayi garin a halin jikkata , da ya sanya tilas likitocin da suke abokanan aikin su suka shiga bashi taimakon gaggawa , ƙarin ruwa zuwa magunguna ,"
ba laifi lafiyar jikin sa a zahiri ta dai-daita amma shi kaɗai ya san halin da yake ciki a ruhin sa ,
Zuwa azahar ya ɗan ji karfin jikin sa , dan haka yayi wanka ya ɗau shiri , zuciyar sa ta gama samun galaba akan sa tare da taimakon shaiɗanin da yake tare da shi yana bibiyar sa tare da ingiza shi ,
Karfe biyar na yammaci tayi masa dot a ƙofar su yakaka ,'
Kan sa tsaye ya shiga gidan yana mai fatan cin karo da ita kawai su tafi , sai dai kuma inda gizo ke saƙar shine , shi fa bai wani tantance da kamannin yarinyar nan ba ," alhali kuma ya gama shawartar kan sa akan ya tsaya tare da ita kawai ta dunga biya masa buƙatar sa tun da shi ne mutum na farko da ya fara sanin ta ," shi kuma zai ɗauki duk wasu hidindimun ta har sai zuwa lokacin da ya fita a masifar da ya faɗa ,'
Da wannan tunanin ya sanya kai cikin rumfar madam saly , ya tadda babu mutane dayawa mafi yawa suna wurin chasun da ya gitta a yayin shigowa ,"
Wuri ya samu daga gefe ya zauna , zuciyar sa na fatan ganin ta kamar yadda yake yawata idanun sa akan ƴan matan da ke kai kawo ta gaban sa , baki ɗaya bai ga fuskar ta ba acikin su ,
Ina take ?
Ya san fara ce tas , bayan haka babu abun da zai ɗorar na daga suffar ta ,'
Yagana ce ta ratso ta cikin rumfar cikin shirin tafiya gida, yakaka biye da ita da nufin yi mata rakiya ta dawo ta ƙarasa aiyukan da take kaiwa har dare tana yin su daga wannan zuwa wancen !
Tana sanyo kai ta ji ƙamshin sa ,' tabbas wannan ƙamshin "bature kam silum " ne , a take bugun zuciyar ta ya sauya tare da wata kewar sa mai tsanani da ta taso mata
Ina yake ! Tambayar zuciyar ta
Tun da suka bullo ya gan su , a take zuciyar sa ta shaida ta tabbas ita ce abar kwaɗayin sa ita ya zo nema ,!
Hankalin ta ya rabu biyu ɗaya yana ga hirar da yagana ke yi mata ɗaya yana ga son gano inda yake , dan haka bata samu nasarar ganin sa ba har suka zo giftawa ta gefen sa ,"
Ganin zata wuce shi ya sa shi miƙa hannu ya kamo hannun ta ,"
Da sauri ta juyo domin ganin waye ne ,"duk da cewa an saba yi mata haka ,"
Idanun su suka sarƙe cikin na juna kowannen su ya gaza ɗauke idanun sa , a yayin da suke fassara kallon da suke yiwa juna a zuciyoyin su ,"
Kallon da yakaka ke bin biyamuradi kallo ne na nayi kewar ka , na kuma yi farin cikin sake ganin ka ,
Yayin da take fassara kallon da biyamuradi yake jifan ta da shi a nufin.!
Gani na dawo ki sake taimaka min .,'
Zan taimaka maka ta ƙudurce cikin ran ta ,!
Har yagana tayi ɗan nisa ta waiwaya bata ga yakaka ba dan haka ta dawo da baya
nan ta tadda ta suna kallon juna da wani mutum da bata kai ga sanin sa ba , da ido ta bi hannayen su da yake manne ,!
Dafa kafaɗar yakakan tayi ganin irin shagalar da tayi ,bata san ma ta zo wurin ba
Da sauri yakaka ta zame hannun ta daga cikin na biyamurdi ," Ina zuwa ,' tace da shi !
A bakin kofar shigowa ainahin gidan ta dogare
yagana zan koma daga nan kin ga ana jira na !
Da ido yagana take bin ta cikin ranta tana mamakin farin ciki tare da murnar da yakaka take yi wanda kafin fitowar su a ɗazu babu shi,'
A karo na huɗu ta sake tambayar ta
Wai yakaka sai tambayar ki nake kin share ni waye wannan ɗin ko ƴan uwan ku ne ?
Bature kam silum ne ,
Ɗan uwan mu ne
Daga haka ta juya da sauri har tana haɗawa da ɗan gudu ta koma ciki ,
Ta bar yagana da mamakin ta fal cikin rai ,
" bature kam silum' ta maimata sunan ,!
sashi guda na zuciyar ta yana shakkun ambaton sa da tayi da ɗan uwan ta , kai wannan daga gani ba yaren mu bane !
Da murmushi akan fuskar ta ta ƙaraso gaban sa ,
Ki kimtsa ki taho mu tafi ,kadda ki ɗau lokaci
Ya furta hakan yana mai ɗauke kan sa daga kallon ta ya mayar ga agogon hannun sa ,"
Kalmar kimtsawa tai mata tsauri wurin fahimta , amma da yake tana jin sa cikin zuciyar ta , sai ta kintata ta hasaso abun da yake nufi , dan haka ta shige ciki ,"
Ƙasa-ƙasa ya bi takun kafafu da kallo wanda yake halin sa ne kallon ƙasan ido ,"
nan ya hango dauɗa tare da taron kursashin da yake danƙare ƙasan kafafun ta . Cikin sauri ya ɗauke kan sa !
A gurguje ta shiga ta ɗibi ruwa tayo wanka , ta dawo ɗakin su larki ta hau shiri ," falmata wacce take zaune shiru kamar yadda yake al'adar ta ce killace kan ta wurin da babu kowa tayi shiru ,"
Motsin da taji an taɓa musu jakar kayan su , ya sa takai hannu tana kamo jakankunan nasu ,"
Waye anan ?
Yakaka wacce ɗoki ya sa bata ko yi sallama ba bare tayi wa falmatar magana , tace,
Nice fa falmata nah ,"
Aiyo yakaka na , to ai baki min magana bane ! Yau har kin gama aikin ne ?
Ban gama ba falmata ,
Mutumin shekaranjiya ne ya dawo yana so mu je na sake taimaka masa ,"
Zuruf falmata ta miƙe nima zan biki yakaka ,!
Tsam yakaka tayi ta bar ƙoƙarin sanya kayan ta da take yi ,
Ta taso ta zo ta kamo hannuwan falmata ,"
Falmata na kiyi hakuri ki zauna har naje na dawo , kin ga aikin da nake yi masa mai wahala ne baza ki iya ba , kuma yau bazan kwana ba , anjima kaɗan zan dawo kin ji ?
Da kyar ta shawo kan ta ta yadda zata jira ta tare da alƙawarin baza ta kwana ba zata dawo , da haka ta kammala shiryawa cikin wata atamfar cote d'ivoire ruwan zuma mai cizawa da aka yiwa ɗinkin riga da siket , duk cikin ire iren kayan da samy baby tayi mata kyautar su ne da basu sha jiki sosai ba ," wani turaren da samy baby ta bata lokacin da take menses ta ce ta dunga shafawa a jikin ta ,"shi ta ɗauko ta mutsittsika ,"
Fes tayi kyau ta ɗaura ɗankwalin ta shigen yadda ta ga samy baby na yi , bata sanya gyale ba domin bata da shi kuma ka'idar gidan madam saly ba'a yawo da mayafi .!
Wannan karon a tsaye ta tarad da shi ya saka hannun sa ɗaya cikin aljihun wandan sa , da alama tsumayen ta yake cikin ƙaguwa ,"
Babu laifi a idon sa tayi kyau , duk da cewa shi ba wannan bane ya dame sa ,
Sai dai tana matsowa kusa da shi ya ji wani ƙamshi marar daɗi a hancin sa yana tashi daga jikin ta , sam ƙamshin bai masa ba ,!
Juyawa yayi ya fara taku ba tare da yace da ita ƙala ba ,"
Zungui-zungui ta bishi a baya ,
Duk yadda yaso ya Daurewa ƙamshin turaren dake tashi a jikin ta ya kasa , sosai yake jin wani yanayi marar daɗi a cikin ƙamshin , shi mutum ne mai tsananin tsafta da ƙyanƙyami sam bai son wani abu da yake da alaƙa da ƙazanta ,"
Dan haka lokacin da suka daidaita akan titi ,ya ɗan juyo da ganin sa kan ta ,"
Ki gwouda mini hanyar les salons !
meye kuma Les salons, ? ita hausar sa gaba ɗaya wahalar fahimta take yi ma ta ,"
A takaice ta amsa
ban san wajen ba !
Wani wuri ya samu a gaba kamar super market ya tsaya shaguna birjik a wurin ,
Mayuka tare da sabulai zuwa turaruruka na mata , masu kyau da tsada ya jida ,
Ya koma banagare kayan sawa ,"shi ba wani sanin size ɗin ta ya yi ba dan haka ya ɗauki dogayen riguna baƙaƙe biyu ,
A wurin biyan kuɗin ya tambayi Cashier wurin salons , nan ya masa kwatance na wani shahararren wurin gyaran jiki da yin kwalliya , TaTa saloons da yake kan titin danboa .
Ya ajiye kayan a kujerar baya ya zo ya tada motar ba tare da yace da ita ƙala ba , ita ma kuma tayi shiru bata magana sai satar kallon sa ,
Tata salon babban wurin gyaran gashi , ƙafa da ƙumba , yin kwalliya da gyaran jiki , zuwa sayar da turarurrukan arabs masu kyau da ƙamshin sanyaya rai ,suna da gyalalluka na yayi masu matuƙar kyau da inganci .
Hajiya ruma mamallakiyar shagon mace ce mai karamci wacce ta san harkar kasuwa dan haka take girmama abokan cinikayyar ta , ( Allah ya ƙara ɗaukaka ƴar ƙanwa ta )
Sun ci sa'ar tarar da ita da kan ta , inda tayi musu tarɓar girma tare da ruwan gora da lemun gongoni ,"
nan youssouf yace ayi wa yakaka gyaran jiki tun daga salons zuwa pédicure , kai har wanka ma ayi mata ,! . Aka sa masa kuɗi ya biya .
Nan aka shiga da yakaka wani ɗan ɗakin da ya wadata da fitilun haske ,'
Suka fara aikin su , goge nan wanke chan , dirza nan shafa wannan goge wancen , har dai suka samar da yadda suke so a jikin yakaka , duk da cewa su da kan su sun yi mamakin irin dauɗar da take danƙare a kowanne lungu da sakon jikin yakaka ,
,misalin karfe takwas na dare suka fito da ita , tayi kyau ba kaɗan ba , ɗan nude makeup ɗin da suka mata ya sake fiddo da zallar manyan kyaun da take da shi , jikin ta sanye da ɗaya daga cikin dogayen rigunan da ya saya mata ,sun yi mata naɗi da gyalen rigar bayan sun tara mata gashin ta mai rangwamen duhu sai tsanananin laushi da tsawo a tsakiyar kan ta sun kama mata shi da roba ,"
, ita da kan ta jin kanta take kamar ba ita ba kamar an sauya ta , wani irin nishaɗi ne yake huda ta , ƙamshin da yake mamaye da sassan jikin ta yana bata wani irin farin ciki na musamman, tsafta tayi a rayuwa ," ita kuwa me bature kam silum zai biɗa a wajen ta da baza ta iya masa ba ? ai babu !
Da ido yake bin ta da kallo lokacin da suka fito , duk da cewa idanuwan sa sun saba ganin kyawawan mata daga bangarori daban daban na duniya , amma kwarai irin nata kyaun ya burge shi ," daga inda yake yana jin tashin ƙamshin ta ,"
Da hakan ya sa shi sakar mata murmushi da suka haɗo ido , a karo na farko da yakaka ta ga murmushin sa wanda yake ƙarawa fuskar sa haiba , nan take ta washe gajerun hakoran ta da suka sha wanki tana maida masa da martanin dariya , tsintar kan ta tayi da tambayar sa ,"
Nayi kyau ko ?
Murmushin bai gushe ba akan fuskar sa ya haɗa yatsun sa biyu babban da mabiyin sa ya mata alamu da kinyi kyau sosai !
Hannun sa ya miƙa mata ta ɗora nata akai ya ja ta suna mai ficewa a shagon
ma'aikatan shagon suka bisu da kallon sha'awar da suka basu ,"Cikin ran su suna aiyyanawa ma'aurata ne irin sabon auren nan har wata ƴar gaza gani daga cikin su ta tanka ," perfect couples"
Kwanakin da suka biyo bayan wannan ranar biyamuradi youssouf da yakaka zama suke irin na masoyan ma'aurata , babu wata rana da ta tsallake musu da basu kwana tare ba .
Yayin da biyamuradi yake fidda kuɗi yana mayar da yakaka irin macen da yake so , ƴar hutu ƴar gayu mai tsafta , tata salons ya zama wurin zuwan su , bai jin ƙyashin kashe mata kuɗi tare da bata farin kuɗin tsurar su domin ta biya wasu buƙatun , har ƴar ƙaramar waya ya saya mata , wanda yake amfani da ita wurin kiran ta idan ya zo ɗaukar ta ," a yanzu burkutu guzurin ta yakaka take yi masa , har ɗakin da suka mayar na kwanan su a garki Guesthouses ,
Yakaka kuwa sau da kafa take bin biyamuradi youssouf cikin dukkanin buƙatun da ya zo mata da shi bata iya kuya masa baya , tana bashin haɗin kai tare da juriyar ɗaukar bukatun nasa ,"
A yanzu aikin gidan madam saly ya ragu a kan ta , saboda yadda biyamuradi da ita kan ta yakakar suke sakarwa madam saly kuɗi , wacce a rana ta biyu da yakaka ta sake bin biyamuradi suka kwana alhalin bata gama mata aiyukan ta ba kusan raba dare tayi tana zagin yakakar tare da shan alwashin a gobe gobe zata kore su ,
Da hakan ya sa falmata kwana tana kuka ita ba kome yafi bata mata rai ba irin kalmar "ƙaramar karuwa sabuwar yar iska ," da madam saly ta danganta yakakar da shi ba ,"
cikin muryar kuka ta dunga maimaita kalmar
Yakaka na ba ƴar iska bace
Yakaka na ba ƴar iska bace
Ƙasa-ƙasa yadda madam saly bata jiyo ta ,' tsaf ta gama kintsa musu jakar kayan su tana jiran gari ya waye yakaka ta dawo su kama hanyar su,"
Sai dai abun da ya ɗaure mata kai washegari bayan dawowar yakaka gidan tayi ta kasa kunne ta ji hayaniyar madam saly tana zagin su tare da kora kamar yadda tayi rantsuwa , " sai taji tsit , sai ma jin