Showing 108001 words to 111000 words out of 411050 words

Chapter 37 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

8129

a cikin birnin maiduguri daɗi da kwanciyar hankali , zasu ci su sha kuma su adana ƴan kuɗaɗen su , babu ƙyara babu tsangwama ,

Ka'in da na'in yakaka ta kama aikatau ɗin ta ta riƙe kullum a chan take yini tana aiki chan take cin abincin rana , sai yamma lis take komawa gida , tayi wankan ta fes a banɗakin wurin aikin ta , a hanya zata ɗan saya musu ƴan kayan gwari da ake yayin su lokacin , karas ,lemo ,cashut da sauran su ,

Falmata kuwa har ta gane hanya daga wurin barar ta zuwa ƴar rumfar kwanan su , dan haka ta daina jiran yakaka ta zo ta mayar ta , daga ta ji kasuwa ta fara alamun watsewa sai ita ma ta tafi bakin rumfar ta jira zuwan yakaka , a hankali har suka fara sabo da jama'ar kewayen wurin ,

Yau an tashi garin a ɗan hargitse sakamakon kwana da aka yi ana ɗauki ba daɗi da ƴan tawayen boko haram da suke neman shigowa garin ta karfi ta wani yanki , sai dai basu samu nasara ba dakarun soji sun tarwatsa su wanda hakan ya jaa dayawa daga cikin su sun fantsama cikin gari da hakan kuma yake babbar barazana ga rayukan al'umma .

  Saboda ɗaukar mataki sai soji suka fantsama cikin gari , tare da sanya dokar hana zirga-zirgan motoci akan manyan titunan garin , kasuwar kan ta yau ba'a buɗe ta ba duk inda ka bi motocin soji ne suke kai kawo ,

Jugum-jugum falmata da yakaka suka yi , su sam basa ƙaunar wannan jiniyar ta motar sojoji , tsinka musu zuciya take ta tada musu hankula kamar yadda ya faru a yanzu tun safe sun gaza ko cin abinci sai faman wuri-wuri suke , ko ƙwaƙwarar magana sun gagara yi da junan su , illa hannun su da yake cikin na juna , lokaci zuwa lokaci yakaka tana ɗan leƙawa ta tsaƙanin labulen rumfar su tana ganin yadda garin yake shal tamkar an share .

Sun kwashe tsawon lokaci a haka , har zuwa lokacin da suka ji an kamo wasu gungun mutane an wuce da su ana ta dukan su ,

Basa fahimtar maganganun da suke tashi a wurin illa dai suna jin ana yawan ambaton kalmar boko haram , boko haram , boko haram !

Yakaka ta so leƙawa ta ga ko su waye ,? Amma sai ta ji falmata ta sake damƙe mata hannu , ƙasa ƙasa ta ji tace
    Yakaka kar ki leƙa , tsoro nake ji , zuciya ta bugawa take , yakaka mu yi addu'a kar su gan mu su kashe mu .

Wucewar mutanen bai fi da mintoci biyar ba suka ji ƙarar fashewar bam da matuƙar ƙarfi har sai da rumfar da suke ciki ta girgiza ,

Harbe harben bindigogi ya biyo bayan tashin bam ɗin tare da guje -guje har ta gaban rumfar su suke jin takun gudun mutane tare da wucewar harsashi ,"

Iyakacin ruɗani tare da tashin hankali sun shiga kuka suke yi suna tsaye charko charko cikin rumfar ,"

Suna nan tsaye falmata ta ji wani ƙaƙƙarfan abu ya bugi kafaɗar ta ya wuce wanda sai da ya sa tayi baya da karfi ta bugu da jikin kofar shagon kafin ta silale ƙasa , cikin wani irin azabar raɗaɗi da take ji yana gauraya illahirin jikin ta takamaimai bata san ina ne yake mata ciwo ba ,

a razane yakaka ta jiyo jin yadda hannun falmata ya kufce daga cikin nata , abun da tayi arba da shi ya sa zuciyar ta ta tsaya da bugawa , bata san lokacin da ta zube a ƙasa ba tare da tallafo falmata wacce jini ke malala daga jikin ta , idanun ta suna rufuwa su buɗu da kan su , jikin ta kuwa babu inda baya rawa ,.'

  Falmataaa

ta kira sunan ta da wata irin murya tamkar ba tata ba , wani irin ihu ta kurma lokacin da ta fahimci abun da ya faru ,.......!

   Masha Allah ina gaida masoyan littafin mafari a duk inda suke !

Vote
Share
Comments [10/3, 2:42 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )


umm'muaz

22




Da gudu ta tako ta fito daga ƴar rumfar , yanayin da ta ga falmata a ciki ya mantar da ita duk wani halin fargaba da tsoron soji da suke ciki ,

Tana kuka ta nufi bakin titin inda ta hango gungun soji da wasu mutane farar hula suna tsaye , tun kafin ta karaso gudun da ta taho da shi ya ɗau hankalin su ,tare da ihun da take faman yi

Tana ƙarasowa ta zube a gaban su ba tare da ta ji tsoron bakin bindigar da ta ga sojojin suna gyarawa ba tare da saita ta da ita ,"

    Da rishin kuka take cewa kun harbi ƙanwa ta , zata mutu , kun kashe min ƙanwa ta me tayi muku ? Mu ba boko haram bane , meyasa zaku harbe ta wayyo Allah ƙanwa ta ,"

Wasu daga cikin su sun fahimci abun da tace dan haka wani daga cikin su fararen hula ya ɗan matso kusa da ita ,
    Ina ƙanwar taki take ?

Waiwayawa tayi tana nuno masa ƴar rumfar da suke ciki , tsabar kuka da ruɗanin da take ciki har numfashin ta sarƙewa yake yi ,

Su biyu suka nufi rumfar
   Yakaka ta take musu baya

Nan take suka fahimci bullet ne ya samu falmata a kafaɗa cikin rashin sani ,"

Da gudu gudu suka koma wajen sojojin tare da neman taimakon su akan a kai yarinyar asibitin kurkusa , ba tare da gaddama ba soja ɗaya ya amince zai jaa su a motar su ta soji .

Dan haka suka ciccibo falmata wacce ta riga ta suma suka ɗora ta bayan hilux ɗin sojin tare da yakaka wacce idan banda sambatun kiran sunan falmata babu abun da take gaba ɗaƴa ta ƙanƙame falmatan a jikin ta .

Da isar su babban asibitin gwamnatin jaha ( general hospital ) wanda bashi da wani tazara mai yawa da bakin kasuwar , aka shige da falmata bangaren bada taimakon gaggawa ( Accident and emergency)  nan suka tarar da mutane dayawa da suke cikin hali makamancin na falmatan wanda tarzomar jiya ta ritsa da su birjik , wasu sun ji munanan raunika , wasu babu hannu , wasu ba ƙafa , likitocin da suke kan aiki sai kai kawo suke , da alama sun gaji likis ga har zuwa yanzu akwai waɗanda ko kai ga fara basu taimako ba'a yi ba ,

Nan suka ajiye falmata akan dandaryar siminti bakin kofar domin duk gadajen da suke cikin ɗakin a cike suke ,

Bayan sojan ya shiga ciki yayi musu bayani , likitocin suka ce a ajiye ta kawai zasu zo kan ta domin aiki ya musu yawa , ko kuma idan likitocin safe sun zo su duba su tun da sun ce harsashin a kafaɗa ya same ta da sauki akan waɗanda bam ya tashi da su ,

Tsayuwar da bata fi ta rabin awa ba mutanen da suka kawo su suka yi , suka matso kusa da yakaka wacce har zuwa lokacin idanun ta zubar hawaye suke har sun kumbura ,
     Yarinya mu zamu tafi , domin muna da aiyuka a gaban mu , su kuma likitocin nan ƴan walakanci ne basu da niyyar zuwa su duba ta , ki cigaba da jiran su , sannan ki dunga leƙawa kina damun su akan su zo su duba ta , idan kuwa ba haka ba har jinin jikin ta sai ya ƙare ta mutu anan indai likitocin nan ne babu abun da ya dame su , mu mun tafi ,

ga wannan ki rike a hannun ki ko zasu ce ki sayo wani magani ,suka miƙa mata dubu ɗaya suka kaɗa kan su suka yi ficewar su ba tare da sun sake kallon inda falmata take yashe a ƙasa ba ,"

Wani sabon kuka ta sake fashewa da shi tana tattaɓa fuskar falmata wacce tayi sanyi ƙalau ,"
    Falmata na dan Allah kar ki bar ni , Falmata dan Allah ki tashi ,'
  Kamar mahaukaciya ta yunƙura ta tashi ta bazama ta faɗa cikin ɗakin da ake duba marasa lafiyan ,"
   Tana shiga nurses ɗin da suke taya likitocin aiki suka yi mata chaa ,"
   Mata meye hakan ? Baki ga aiki muke ba zaki zo kan mu da ihu ? Ki koma daga waje ki jira a fito da marar lafiyan ku , ba'a shigowa nan idan ba mu muka kira mutum ba fita-fita dallah ,"

  Kuka ta fashe da shi
   falmata na zata mutu dan Allah likita ki zo muje ki duba ta jini sai zuba yake daga jikin ta jinin ta zai ƙare ta mutu idan ta mutu bani da kowa ,"

    Kalaman ta suka doki kunnuwan sa yayi tsai daga aikin ɗinkewa wani mutum mummunan rauni da yake yi ,"
    Tabbas ita ce , ita ce da kullum damuwar ta yake ga falmata ƙanwar ta ita ce da kullum hawayen ta yake zuba akan ƙanwar ta falmata , bata da wani abu mafi muhimmanci da ya wuce ƙanwar ta falmata , ita ce wacce ya kwashi watanni yana neman ta har ya zo ya haƙura ,

   Cikin nutsuwa ya waiwayo yana duban inda take lokacin da nurse ɗin ta sanya wata security guard da take tsaye daga bakin kofa , tayi waje da ita domin tana son bata musu aiki ,"
    Security guard ɗin ta cukuikuyo hijabin ta tana tura ta waje ,
   Ita kuma tana sake ƙara karfin kukan ta tare da neman su taimaka mata ƙanwar ta kar ta mutu ,"

Hey jumai let her come in .

Suka tsinkayi muryar babban likitan su da yake duty , ya bada umarni

A tare suka waiwaya da yakaka wacce jin muryar sa ya sa ta waiwayo da fatan son kasancewar shi ne da gaske a wurin ai kuwa tayi arba da shi jikin sa sanye da korayen kaya ,'ɗan siririn farin gilashin da yake ɗore saman karan hancin sa bai isa ya sa ta gaza gane shi ba ,"

Da ƙarfi ta fizge jikin ta daga riƙon da security tayi mata , ta tako da gudun gaske ta ƙurɗo ta tsakanin gadajen marasa lafiya tana zuwa ta kamo hannun sa da yake cikin safar hannu ta duba marasa lafiya ta shiga jaan sa tana cewa
    Dakta ƙanwata falmata ai ka san ta ko ? Ita ce harsashin bindiga ya same ta , ta suma kamar ta mutu jini yana ta zuba a jikin ta , dan Allah ka zo muje ka duba ta ,kar ta mutu dan Allah ka taimaka min !

  A hankali ya zame hannun sa daga riƙon da tayi masa , ya maida duban sa ga nurses ɗin da suke tsaye

   Ku sa a shigo da ita !

Doctor bamu da gadon da zamu ajiye ta ,"
    Yana mai komawa bakin aikin sa yace
     A nemo gado a ɗaura ta akai yanzu zan duba ta ,'

   Biyu daga cikin nurses ɗin suka fita tare da security guard ɗin , yayin da ɗaya ta aunawa yakaka harara ,
   Ai Sai ki fita mata , domin ba'a tsayuwa anan ,'

   Ba tare da ya juyo ba yace

Sister kalsum ki bar ta ta tsaya anan , yanzu za'a shigo da ƙanwar ta ,!

Tashin hankalin da ya hango a fuskar ta ya taɓa masa zuciya sosai ,"yana jin  tausayin ta mai ƙarfi yana taso masa , ita kullum a cikin kuka da wahala take !

Mokaɗe baki nurse kalsum tayi ,
   Cikin ran ta tana son sani alaƙar dactor hamza da wannan kucincinannar yarinyar ƙazama !

Cikin mintoci goma sai ga falmata an turo ta a gadon marasa lafiya an shigo da ita ," da hakan ya zo dai-dai da kammala aikin da yake yi ,
   Ya tako ya zo gaban gadon falmatan ya duba ta tare da yin aune aune , nan ya fahimci ta zubda jini dayawa da ya sa dole sai anyi mata ƙarin jini , bayan an cire harsashin da yake cikin jikin ta
   Dan haka yayi umarni a kare gadon falmatan a kuma sauya mata kaya zuwa na tiyata," sannan ya juyo da ganin sa ga yakaka , cikin tausasa murya tare da sigar lallashi yace ,
      Ki nutsu ki daina kuka haka kin ji ko ? Ki samu wuri ki zauna a waje ,ki sayi ruwa ki sha ,insha Allah babu abun da zai samu ƙanwar ki , ɗan rauni kaɗan ta ji kuma yanzu zan cire mata harsashin na ɗinke mata wajen na sa magani zuwa anjima zata farka kuyi magana kin ji ko ?
   Gƴaɗa kai tayi tana duban fuskar sa
 cikin son samun tabbaci ta ce
" Ka ce zata samu sauki har ta tashi anjima koh ?
    Sosai kuwa insha Allah
ya bata ansa yana mai duban ƙwarar idanun ta da tsabar kuka ya sauya musu launi ,"
    da jan ƙafa ta fice tana waiwayan inda falmatan take ,
   Shi kuma ya juya ya ɗau wata ƴar takadda yayi rubuce rubucen sa ya kira ɗaya daga cikin ma'aikatan da suke tura gadajen marasa lafiya/kujerar marar lafiya , ɗauko file da sauran su , ya miƙa masa takkadar bayan yayi Signature ya buga Stamp .
      Ka je blood bank ka kai musu , ka tsaya ka ƙarbo jinin ka kawo .
    Toh sir
  Cikin gwanancewa ya fara aiki ga falmata !

  Bayan awa ɗaya ya kammala ya ɗaura mata jinin da aka kawo leda ɗaya bayan yayi mata allurai ,
    Sai da ya sake jaddadawa nurses ɗin da suka karɓi aiki akan su kula da ita Ƙanwar sa ce ,  bayan yayi bankwana da likitan da ya ƙarbe shi a bakin aiki ya shigar masa da duk wasu bayanai akan marasa lafiyan da ya duba ciki har da falmata da ya roƙi Alfarma a lura da ita da kyau , abokin aikin nasa ya amsa da zai kula da ita sosai .
       Cikin takun da yake nuna tsabar gajiyar da yayi ya fito daga ɗakin , yana goge ruwan hannuwan sa da ya wanke da farin ƙyalle .
       Tana hango fitowar shi ta miƙe daga inda take durƙushe a jikin bango ta nufo shi ,"
        Cikin nazari ya tsaida idanun sa akan ta tana tahowa yana son tabbatar da zargin sa akan alamomin masu juna biyu da yake gani tare da ita alhalin shi a budurwa ya san ta .

Dakta ta farka ? Tana magana ? Jinin ya daina zuba daga jikin ta ? Ko na shiga na gan ta ??
      Bin fuskar ta da tayi jazur da kallo yake yana ganin yadda fatar bakin ta ta bushe idanun ta suka kumbura,

Bai amsa mata tambayoyin ba ,  yace mata

   Zo muje !

Ta bishi a baya tana waiwayen ɗakin da falmata take ciki , so take tayi gaddamar bin sa sai dai ta kasa ,

A bakin wani ɗan shagon da ake sayar da kayan sanyi da kayan fulawa irin su Biscuits, cake , meat pie , donut da sauran su , suka tsaya

   Duban sa ya mayar kan fuskar ta cikin kulawa yace me zaki ci marar nawi sosai ? Zaki sha Hollondia yogurt  ? Ko juice kika fi so ? Cake zaki ci koh meat pie ?

  Wani jirkitatcen kallo ta yi masa , falmata tana cikin yanayi irin wannan har shi yana tunanin zata iya cin wani abu ? Ai ita ko ruwa baza ta iya sha ba idan ba ta ga farkawar falmata cikin ƙoshin lafiya ba .

  Sunkui da kan ta tayi daga kallon fuskar sa ,' cikin siririyar murya tace
    Bana cin kome bana jin yunwa , dakta dan Allah ya jikin falmata ? Ta samu sauki , ka kai ni na gan ta dan Allah ,
    Bai amsa mata ba sai ya maida ganin sa kan mai shagon da yake tsaye  ta cikin ɗan shagon sa yana kallon su .

    Bamu hollondia yogurt babbar roba ɗaya da Chii exotics babba ɗaya , meat pie guda uku , tare da ruwan roba guda ɗaya .

    Suna tsaye ya haɗa a leda ya miko musu , dakta hamza ya karɓa gami da miƙa kuɗi aka bashi chanjin sa ,

A takaice yace mata
  Mu tafi ! Yana mai yin gaba
  Cikin ƙosawa ta bi shi a baya .

Wurin da motar sa take ajiye a wajen tsayuwa na musamman ya ƙarasa , gami da buɗe motar ya shiga
  Ita ma yayi mata umarni da ta shiga bayan ya buɗe mata ɗayan bangaren ,"
  Ta shiga ta zauna gami da mayar da kan ta jikin murfin motar ta kwantar tana jin wani irin yanayi marar daɗi yana taso mata , sam ita bata son takurar da yake yi mata a koyaushe idan suka haɗu ,!

   Ledar da kayan da ya sayo suke ciki ya ɗora mata akan cinyar ta .
    Bana son musu ko doguwar magana ki cinye kuma ki shanye duk abinda yake cikin ledar nan , ƙanwar ki na mata aiki na bata magunguna yanzu haka bacci take daga ta tashi zaki ganta insha Allah baza ta ɗauki lokaci mai tsawo ba zata warke, idan har kun zauna an bata kulawar da ta dace baku gudu ba !

Sanyin kayan da suke bisa cinyar ta suka haɗu da jin daɗin cewar falmata tana raye an yi mata aiki har ma tana bacci suka tayar mata da kishirwar da ta jima tana ji ,
   Ba tace kome ba , ta buɗe ledar gami da ɗaukar gorar ruwan ta kunce bakin ta kafa kai ta fara sha bayan ta muskuɗa ta juya tana fuskantar murfin motar ta bashi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login