Showing 30001 words to 33000 words out of 155577 words

Chapter 11 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

2780

janta da kasa nayi hanyar palona da ita,bayan na dauki wukana

Bata da k'arfi jini ko ta Ina a jikinta ko hannunta bata iya dagawa.

Da gashin dokinta najata har bandakin daya d'akin na saka mukulli na kulle.

A seat din bandakin na zauna Ina maida numfashi kirjina suya kawai yake min.

Ita Kuma tana kwance a kasa bakinta yayi suntum jini kawai take zubarwa.

A daidai lokacin da Mahfuz ya duro tsakar gidan a haukace Ina jinsa ya bude kofar gida mijin mmn Iman da mmn Iman din Suka shigo da wasu da bansan muryarsu ba

Mahfuz sai zabga sallati yake Yana "ta kashe Yar mutane Hamisu kaga jini ko ta Ina innalillahi wa Inna ilaihi rajiun basa d'akin.

Suka shigo palon a haukace.

Ido kawai na zubawa Ummi da sleeping dress dinta ya baci da jini rigarta ta dage tayi sama pant dinta ya fito nononta kuwa suna nan a zube.

Tuna yanda na gansu da kamshin turaren da take a jiya daddare da naje Kai Mata abinci har daki nake kaiwa budurwa mijina abinci na cije lebbena a fili na furta "Har cikin gida ya kawomin budurwarsa nake bauta Mata.

Kamar an cinna min fetur a kirji haka naji nayi wani irin kara na dira kanta na rufeta da mugun duka ihunta yasa naji su mahfuz sun fado dakin.

"Lubna karki kashe ta lubna ki bud'e min k'ofar nan idan wani Abu ya samu yarinya nan na rantse da Allah sai na dau mumunan mataki akanki lubna"

"Mahfuz zata kasheni idona kaina ku kawomin agaji wlh Ina dab da mutuwa na Shiga uku wayyo kaina"

"Lubna ki bud'e k'ofar nan Hamisu kaga zata kasheta LUBNA na rantse da Allah na nemo.mai balla k'ofar nan na shigo sai na Miki jina jina"

Na tsaya cak da bugun da nake Mata "Mahfuzzzzzz kutumar bura ubanka Allah ya tsine maka albarka Allah yasa ka dawwama a wutar jahanama Mahfuzzzzzz kasheta zanyi inyaso ka mutu ka bita"


Nace a haukace Ina daga Kan ummi Ina bugawa da kasa tana ihun Kiran sunan mafuz,mahfuz ya jijjiga k'ofar a haukace Yana Hadeeza innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Lubna"

Tunda zu nake Jin kukan mimi tana hannun mmn Iman dake kuka da sallati.

"Kaga tunda k'ofar bazata Ballu ba ka Kira mahaifiyrta tazo ko zata bud'e"


"Tundazu na kirata tana hanya har da mahaifiyata"

Ya fada cikin rawar murya Yana cigaba da jijiga k'ofar.

Hadeezar daya kirata dashi yasa na tsaya cak na kurawa ummi da bakinta da hancinta ke zubar jini kirjinta na sama da kasa Ina saman kanta a zaune"

Dagata nayi na dauko wukar dana wurgar sai sheki yake tana ganina da wuka ta mike zaune da alama ta manta uban ciwon dake jikinta

"Mahfuz kayimin rai ta dauko wuka innalillahi wa Inna ilaihi rajiun mahfuz shikenan tawa ta Kare wlh gata da wuka a hannu Aunty na Miki laifi Dan girman Allah ki yafemin duk abinda kikeso zan Miki wlh Tallahi Zan rabu da mahfuz har abada ko a hanya na ganshi wlh gudu zanyi,wayyoo Allahna Mahfuzzzzzz ta fada da karfi adaidai lokacin dana dora wukar a wuyanta na zauna a gabanta.

MAHFUZ da su mamn Iman suka saka ihu gabad'aya mahfuz cikin muryar kuka naji shi abakin k'ofa Yana "Dan Allah lubna karki kasheta dan Allah ni namiki laifi karki hukuntata ni na kawota gidanan dan Allah dan annabi ki rufamin asiri ki bud'e kimin duk abinda Kika.ga dama ki bud'e Mata k'ofar ta tafi na hadaki da girman Allah lubna dan kaunar dake tsakanina dake"

"Mahfuz "

"Naam Lubna"

"Kai Dan wutane Allah ya tsine maka albarka"

"Nasani lubna komai zakice naji ki bud'e k'ofar nan Dan Allah karki kasheta"

"Idan na kasheta nima sai a kasheni"

Na danna wukar kad'an a wuyanta ta saka ihu.

"Shikenan ta kasheta Hamisu"

LUBNA dan Allah ki bud'e k'ofar nan Mimi kuka take karki Zo kiyi abinda Zaki Zo kiyi nadama"

Naji muryar mmn Iman

Na d'auke wukar daga wuyan lubna da jikinta ke wani irin karkarwa har wajen da nake zaune fitsarinta ya gangaro kirjinta kamar ya fado sabida bugawa da yake.

Na Dora wukar a tafin hannuna a tsaye na fara juya wuk'ar,wuk'ar nada balain k'aifi take ya huda tsakiyar hannuna jini ya hau zuba ko a jikina banji zafin wukar kamar yanda nakejin zafi a zuciyata ba


Ido a suntume take kallona a tsorace tana kallon hannuna na sakar Mata murmushin da bansan dalilin dayasa na Mata shi ba nace "Ummi mai wanan a hannuna"?

"Wukane Aunty"

"Kasheki zanyi dashi Ummi"

"Dan Allah karki kasheni kimin rai wlh nayi nadamar abinda na miki"

"Daga Baya kenan"

Na maida wukar wuyanta na danna ta gwallo Ido "kimin rai karki kasheni"

Duk tambayar da na Miki ki bani amsa na rantse da girman Allah kina min karya Zan luma Miki wukar nan"

"Wlh zan gaya Miki gaskiya Aunty na rantse da Allah"

"Hadeeza Sunanki ko ummi naji saurayinki ya kiraki da Hadeeza"?

"Hadeeza sunana Aunty Hadeeza Idris sabo Ina zaune da kanin mahaifina a sharada iyayena suna zaune a gombe tun dana gama primary school na dawo wajen kanin mahaifina da Zama a wajensa na karasa makaranta Aunty"

Murmushi nayi danaga daga tambaya daya ta jera min amsa"

"Yaushe kuka hadu da mahfuz"?

"Shekara biyar kenan da saninsa aunty Yana Sona sosai"?

Cije lebbena nayi da k'arfi a hankali nake magana itama a hankali take bani amsa,mahfuz kuwa shirun da yaji yasa ya hau kwalla Mata Kira akan ko na kasheta ne hawaye ya zubo min wato lafiyar Hadeeza tafi Masa mahimmanci akan cin amanar daya min.

"Mai hana ki aurensa sai yanzu Kika dawo rayuwarsa da Kika tabbata yayi Aure"?

"A lokacin bashida komai Aunty ko machine bashi dashi Ina da manema da suka fishi rufin asiri hakane yasa nake ganin bazai iya rikeni ba na Masa kora da Hali sai ya hakura dani ni Kuma na cigaba da kula wani saurayina dana sa rai da aurensa ya yaudareni yaki Aurena bayan ya samu abinda yake so,a hankali duk masu Sona da aure suka fara guduwa duk Wanda yazo wajena ba dan Allah yake zuwa ba sai dan jikina,ni Kuma ganin na rasa Wanda Zan aura mahfuz ne bamuyi wani banzan muamalla dashi ba Kuma ya kaunaceni hakane yasa na yanke na nemo shi dan ya aureni Aunty"

Na girgiza Kai tare da Kara danna wukar a wuyanta "shine da kika dawo rayuwarsa Kika Sako shi gaba da Kira safe rana dare kike Masa girki Kuma kinsan Yana da Mata ko"?

"Nayi kuskure Aunty kiyi hakuri"

"Ya akayi kuka hada baki aka kawoki gidana da Abdul Ina iyayen naki suke suka barki Kika zo gidanan"?

"Aunty kanin mahaifina da matarsa da yayansa Hajji suka je ba kowa a gidan suka ce na koma wajen iyayena kafin su dawo"

Sai tayi shiru tana b'arin baki
Na watsa mata wani mugun kallo na danna wukar a wuyanta

Wlh tallahi kina min karya ko Kika nemi Raina min hankali aikaki lahira zanyi Hadeeza kinsan Zan aikata ko, zuciyata a bushe take dake da mahfuz kasheku ba wahala zaiyi.min ba Ina jinki"

"Aunty dan Allah kiyi hakuri karki kasheni idan na fada miki gaskiya "

"Ina jinki"

"Bana san abinda zai rabani da mahfuz ko na second daya,wani irin kaunarsa Allah ya jarrabceni dashi idan bangan shi a Rana ba kamar nayi hauka haka nakeji bazan iya komawa gombe wajen iyayena ba nasan yamin nisa sosai Kuma ba lailai yazo wajena ba hakane yasa daya zo cikin shagwaba da marairaicewa nace Masa iyayena ma sun tafi aikin Hajj banida Inda Zan zauna tsoro nakeji sai yace naje wajen Yan uwana mana na can gombe,shine nace Masa ni iyayena kadai ne a gombe Yan uwanmu suna kauye rabona da kauyen Kuma tun Ina yarinya,sai yace min yanzu Mai nake so ayi,sai nace mai zai hana na zauna a gidansa kafin su dawo tunda bazasu wuce sati biyu ba.

Tayi shiru

"Ina jinki"

Lubna ki bud'e k'ofar nan ga Ammi ta iso.

Naji muryar Mahfuz

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun mai Zan gani haka Mahfuz wanan jinin daga Ina"
Muryar Ammi ya doki dodon kunnena

Kamar zaiyi kuka yace "Ammi Yar uwarsu Abdul ce tazo gidanan ta zauna dan Iyayenta sun tafi Hajj daga tafiya massallaci shine lubna ta kulle gidan take ta dirmarta ta dage sai ta kasheta"

Tunda asuba muke Abu daya Ammi,

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun mahfuz Ashe Yar dabba ka aura bansani ba shikenan mace bazata Zo maka gida ba kenan a lailia yarinya nan ba Yar arziki bace Sam ba matar da zaka zauna da ita bane dole ka rabu da ita kafin na wayi gari ta kasheka tamin asara"

"Ammi wlh ba gaskiya ya fada miki ba budurwarsa ya kawo Mata har cikin gida haba Ammi wanan wane irin wulakanci ne da cin Amana har cikin gida a kawo maka mace tsakani da Allah"

Naji muryar mmn Iman cikin kuka

"A tsawace mahfuz yace "ni nace miki budurwa ta ce dama ke kike zugata Hamisu wlh matarka ce ta hada min fitinar nan"

Idona dana lumshe Ina sauraransu na bud'e a hankali na zuba akan Hadeeza data Dora hannunta aka,ko'ina na jikinta jinine ni nasan ba karamin rauni na Mata ba bakinta yayi suntum goshinta da kumatunta,ba yanda ma zaka Mata kallo daya ka ganeta.

"Ina jinki kinyi shiru ko na dan yanka ki ne ki tabbata ba Wasa nake Miki ba na karta mata wukar a Kan nononta ta saki ihu dayasa duk sukayo bakin k'ofar mahfuz Yana "Lubna lubna karki kashe yar mutane dan Allah ki bude kofar nan Lubna ki rufamin asiri dan girman Allah ba budurwa ta bace kanwar Abdul ce"

Na saki murmushi inaga baisan nagansu ba ko Yana tunanin zarginsa nake ko mmn Iman ce ta fadamin duk hirar da muke a bandakin baji yake ba

"MAHFUZ"

"Naam Lubnata mmn mimi Allah ya huci zuciyarki"

"Naci Kan uwarka shege Mara tarbiyya dan Akuya dan wuta wlh na fito idona idonka"

"La haillaha illallahu Muhammad rasullilahi sallahu Alaihi wasalam, mahfuz Kai Yar iskar yarinya nan ta dannawa zagi haka har dasu kaina a ciki tab wlh ka gama aurenta a yau sai ka saketa"

Idan na biye musu bazan ji abinda nakeso naji ba hakane yasa na gyara wukar hannuna na dan yanketa dan har gurin ya fara jini tana ganin Ina gyara wuka ta hau ihu

"Mahfuz yanzu bazaka iya taimaka min ba kana kallo zata kasheni mahfuz ta yankeni mahfuz"

"Ina jinki kafin na luma Miki wukar nan a cikin ki Dan kutumar ubanki nace a tsawace a gigice ta cigaba da magana

Mahfuz tashi yayi tsaye yana Ashe bakida hankali Hadeeza yanzu gidana kikeso na Kai ki ki zauna kuut toh nacewa lubna Mai Ina laifin ma kice na kaiki gidanmu tunda Ammi ta sanki"

"Ooo Ammi ta sanki"?

Na jefa mata tambaya

"Eee Aunty naje gidan na gaisheta Har turmin zani na Kai Mata da kudi da mayafi"

"Ina jinki"

Yana gama fadar haka ya juya zai bar palon shine na tafi da gudu na rungume shi ta baya na fasa kuka ta fada kamar Mai rada cikin tsoro.
"Ke karuwa ce ko"?

"Eee aunty wlh ni karuwa ce"

Na gyada mata kai

"Ina jinki"

Mun dade tsaye ahaka kafin ya juyo dani naki raba jikina da nashi Yana k'ok'arin janyeni na hade bakinmu"ta Kara fada a hankali

Ina jinki

A ranar muka fara kiss Aunty dan Allah kiyi hakuri sharrrin shaidan ne.

Ina jinki
Shi ya janye bakinsa da alama jikinsa a mace yake ya koma ya zauna.

Na zauna a gabansa na kwantar da kaina akan cinyarsa na fara kukan shagwaba dan nasan tanan nake saurin shawo kansa.

"Hadeeza Taya Zan kaiki gidana lubna bata Gane ba kinsan kishin lubna kuwa"?

Na Kara kamkame kafarsa nace "Haba mahfuz Kamar ba namiji ba wlh tsaf Zan zauna har na baro gidan bazata tab'a ganewa ba"

"Tayaya"?

Ya jefomin tambaya

"Ina abokinka Abdul da kuke yawan waya kana bani labarinsa shi zaka roka ya kaini gidan a matsayin Yar uwarsa tunda naga idan ya kiraka Yana yawan tambayarta"

"Tab wlh Abdul bazai tab'a yarda nayiwa lubna haka ba"

"Ai bazaka ce masa ni budurwarka bace kace mutunci muke da juna yayana abokinka ne"

"Abdul duk yasan abokaina Hadeeza"

"Tunda baa nan yake ba yanzu ba lailia ya gama sanin abokanan ka ba haba Mahfuz kamar bakasan yanda zaka tsara shi ba"

Nace cikin shagwaba
"Kai wanan abin da hatsari fa Hadeeza lubna nada sa ido zata iya ganewa"

"Wlh bazata gane ba ai bazaka nuna kasani ba hade rai zaka ringayi"

Dak'yar na tilasta masa ya Kira Abdul yasa a handsfree ya fada Masa abinda yake so ya Masa,tunda jibi zai shigo kano,ashar ya fara luka wa mahfuz Yana ya gaya masa gaskiya kodai budurwarsa ce ita yarinya bata da Yan uwa"

Idan ya kauce mahfuz sai ya taro shi ahaka Ina shafa shi Yana waya har muka samu Abdul ya yarda dak'yar"

Ta karashe tare da dora hannunta akanta dake zubar jini, na cije lebbena Ina kallonta a gaskiya yarinya nan ta wuce tunanina.

"Ina jinki"

Yanda akayi nazo gidanan kenan Aunty.

Janye wukar nayi daga wuyanta,na dora wukar a hannuna ji nake kirjina kamar ya fashe.

"Dan Allah dan annabi Aunty kimin rai wlh bazan sake ba na rabu da mahfuz har abada idan har Kika Kara ganina dashi duk abinda Kika ga dama kimin"

Shirun da nayi tunanin yanda Suka Raina min hankali na ringayi na cije lebbena komai na dawomin kaina har na luma wukar a tsakiyar hannuna bansani ba jini kawai ke zuba a hannuna na dago idona daya rine kamar jini na zuba Mata jikinta sai karkarwa yake ta hade hannayenta alamar roko.

Na saki murmushi takaici "Ashe sabida zuwanki gidanan mahfuz yayi siyayya ranar da kika zo nake murna mun zama Yan gayu mijina ya samu kudi na dage da Masa addua ke Kika fada Masa ya siyo"?

Ina magana hawaye na zubomin

Na maida wukar wuyanta ta fara magana cikin sauri

Eee Aunty ana washegari zanzo duk na fada Masa Abubuwan da nake so nace Masa idan Zan samu nafiso na ringa girki da kaina Ina balain san ferfesun kayan ciki hakane yasa ya siyo washegari"

Gyada Kai nayi nace "Da kyau"

Kuma a zuciyarki bakiji wani Abu ba, Ina mace Yar uwarki kika zo har gidana kike juya mijina kike shimifida mulki Hadeeza

Sharri shaidan ne

Ban bari ta idda fada ba na rufeta da mugun. Duka ta saka ihu su mahfuz suka hau kirana naji muryar Mummy mahaifiyata muryata da naji yasa na fashe da mugun kuka na bar bugun Hadeeza

"Bud'e min k'ofar nan Lubna bud'e min yanzu Nan"

Wukar na dauka dan ban gama da Hadeeza ba na jawo hannunta da balain k'arfi na Dora wukar na danna wukar ya yanketa tasa ihu duk wayanda suke d'akin suka rude da ihu dan Hadeeza ihu take tana yankani take mahfuz innalillahi wa Inna ilaihi ta kasheni wlh"

"Na rantse da Allah sai ka saki yarinya Nan a yau wlh ka gama aurenta ko karuwai ka jera a gidanan ya Kamata ta maka irin Wanan cin mutunci ta Tara Mana jamaa a gida da waje"
Naji muryar Ammi

Hadeeza Bata bar ihu ba tsawan Dana daka Mata yasa tayi shiru tana neman shidewa.

"Yaushe Mahfuz ya fara zuwa dakinki"?

"Washegarin Dana Zo gidanan Aunty"

"Sau nawa ya kusanceki?


"Dan Allah kimin rai"

"Wlh tallahi Zan luma Miki wukan Nan"

Hannu ta hau yarfawa nikuwa na dauki wukar na dora a kirjinta da sauri tace "Sau biyune Aunty wlh sau biyune"

Wukar hannuna ya subuce daga hannuna

Na dade banyi magana ba bama na fahimtar abinda ake cewa a waje ina dai Jin muryar mahaifiyata da ta saka kuka tana Kiran sunana ga kukanta ga na mimi ga jijjiga kofa kamar za'a b'alla.

"Ashe ke budurwar mijina ce na ringa Miki girki aka yo siyayya aka kawo sabida ke,tunda nake dashi bai tab'a siyo abu musamman dan ni ba ni da nake matarsa ta sunna kenan,amma ke da kike budurwarsa yayo Miki uban siyayya Ina zaune daku dan Allah Ashe kallon shasha kuke min Hadeeza a cikin gidana Kika kwanta da mijina Hadeeza"

Na runtse idona jikina na rawa

Ganin Hadeeza in tuna Abubuwan da suka min na iya sawa na dauki wukar na caka mata shaidan nata ingizani bazan tab'a kissan Kai ba mahfuz bai cancani na kashe wata a kansa ba.

Na Mik'e tsaye na kalli Hadeeza nace "Allahu ya sakamin abinda Kika min bazan tab'a yafe Miki ba na saka mukulli na bud'e k'ofar na fita da wukar a hannuna Ina fitowa idona ya sauka akan Mahfuz na yi kansa aguje da wukar hannuna ya juya aguje yayi waje......


Wanan novel din na kudine biya 500 Via 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko recharge card din mtn ko na Airtel har yanzu akwai discount zuwa gobe insha Allahu

Maza Yan albarka ku biya na harhada na tafi hajjin nan ku samu lada>??>??>??>??
[6/11, 8:47 PM] Mmn Abiyat: Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba>??

Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai>??? @&?duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba

Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki

Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu

Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted

Soap price:3k
Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free

Maiso kindly message 08062991549
Call 08064532391

Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai=?O?

Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta=?O?adade anayi sai gsky>?-?>??

Mg's skincare



*Wanan littafin na kudine biya 500 zuwa 2029764071 first bank ko katin mtn ko Airtel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login