Showing 21001 words to 24000 words out of 155577 words

Chapter 8 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

2783

canza Mata Pampers goyata zanyi na Shiga kitchen

Hira Muka dan Kara tabawa kad'an kafin ya kashe wayar na goya mimi na fito nayi kitchen banga ummi a palon ba nasan tana cikin d'akin kila hutawa take tunda Lagos ba nan ba duk da banga alamar gajiya a tare da ita ba kila jirgi suka hau dan su Abdul din nada rufin asiri.

Ina cikin kitchen din na jiyo muryar Mmn iman tana kwankwasa k'ofa.

Ajiye muciyar hannuna nayi naje na bud'e Mata k'ofar ta shigo da ledoji a hannunta ko bata fadamin ba nasan na menene kayan gyara ta kawo min dana bata sautinsa dan so nake na tsantsame kafin na samu tsarki.

"Ke Kaya masu zafi ta kawo wlh sai kinyo ciko"

Gefenta na zauna na fara duba kayan a daidai lokacin da ummi ta fito daga d'akin motsinta yasa muka dago muna kallonta nace "kinfito kenan da zan shigo nace ban sani ba ko baccin gajiya kike"

Murmushi tayi a daidai lokacin da ta karaso wajenmu ta zauna a kasan kafet tana "Aa idona biyu ai ba wani gajiya da nayi tunda jirgi muka biyo Ina wuni"

Ta gaida mmn iman ta amsa cikin sakin fuska tana "kice bakuwa kikayi"?

"Eee wlh tun daga Lagos tazo"

Na bawa mmn Iman amsa na cigaba da duba jarkokin tsumin data shigo dasu da dan bokitin da aka dafa min ciccibi a ciki.

Kice Abban Mimi zai Sha Dadi na kashewa mmn Iman Ido data dafe baki tana "lah bakida kunya fa agaban bakuwar kike badala ko dai matar aure ce"?

Sunkuyar da kai tayi da muka hada ido da ita dan ni banma San kallona take ba

Murmushi nayi Ina "ba matar Aure bace wlh Mai dan nayi wanan hirar a gabanta ai Yan matan suma yanzu sun San komai"


Na karashe Ina dariya a daidai lokacin da nake dandana wani zuma Nan ma na sake hada Ido da ita ta sunkuyar da Kai da sauri

Mmn Iman tace "nidai mallama ki bani cikon kudin dana ranta Miki"

"Har nawa Kika ranta min"?

"Dubu bakwai na cika Miki wlh"

"Kai dubu ashirin na baki fa"

"Kwarai kuwa ai kayanta masu kyau ne da tsada wlh tamkar budurwa Zaki koma duk Inda Kika saka kafarki bbn mimi na biye dake"

Washe baki nayi Ina "Zan baki kudinki idan na Kai shi duniyar can kila na baki fiye da Dubu bakwai din"


Tafawa muka yi da ita ta mik'e tana "naji ma kamar abincin da kika Dora na kauri bari naje Nima na dora nawa girkin na biye miki ba abinda zan zanyi.

Tayi hanyar waje nayi mata godiya tare da kwashe kayan da dan bokitin cicicibin nayi hanyar kitchen dan a kitchen nake ajiyar irin kayan nan sabida wani zubin mahfuz akwai dube dube,Ina zuwa bakin k'ofa naji muryar ummi tana "Aunty ba abinda zan kama miki a kitchen din"?

"Lah tuwone kawai zanyi ba abu Mai yawa ba inada Miya dama ngd ki saki jikinki dan Allah Nan ma gidane ki kunna tv kiyi kallo"

Ina daga kitchen din nake Mata maganar na fara k'ok'arin tuka tuwon.

Muryarta da naji a bakin k'ofa yasa na juya

"Bari na Kama miki wani Abu aunty ki kawo na tuka miki"

"Kai haba wlh ki barshi"

Dak'yar.na samu ta koma Palon na tuke tuwon na kwashe.

Na Kara gyara ciccibin da aka kawomin na dumama na juyo a plate na dauki tsumi daya da na zuba a fridge din kitchen na nufi palon.


Tana zaune wanan Karin a saman kujera tana latsa wayarta har yanzu da hijabinta a jikinta har kasa.

"Wai bakya Jin zafine ki cire hijabin naki ki Sha iska Mana dagani sai ke a gidan fa kin k'i sakin jikinki"

Murmushi tayi bata ce komai ba na kwantar da mimi akan kujera na zauna a kasan kafet na mik'ar da kafafuna sabida naji dadin cin cicibin.

Ban taba ci ba na dauka dadi ne dashi ai Ina kaiwa bakina naji daci daci na kwabe fuska Muka hada Ido da ita dama tunda zu Ina Jin idonta a kaina

Dak'yar na hadiye Ina "Kai kinji daci kuwa da kina da Aure da kinci kinji"

Murmushi ta sake yi wani zubin Ina da surutu na hau zuba "Kinsan mace sai da gyara idan baka dage kayi gyaran nan ba sai namiji ya fara k'ok'arin hango ta waje kuma idan mace ta haihu Salam take komawa dole sai ta zuba gyara sosai zata koma yanda take sai kinyi Aure zaki gane haka,Amma dai kin kusa shiga daga ciki ko"?

"Eee"

Washe baki nayi Ina "Masha Allah ansa Rana.kenan kice Muna da zuwa Lagos Shan biki dama ban taba zuwa ba Kinga ta silarki sai naje"

"Insha Allahu"

"Saura wata nawa"?

"Saura wata uku"

Masha Allah Allah ya nuna mana shima acan Lagos din yake"?

"Eee acan yake"

"Saurayine ko Mai Mata,kiyi hakuri Kinga Ina ta zuba miki tambayoyi"

"Lah ba komai wlh Mai Mata ne"

"Kash amma banji Miki Dadi ba auren mijin wata ai bashida wani dadi,ki more aure shine ki samu santalellen saurayi ki aura ku Sha soyayyar ku,kai amma na tausayawa wacce zakije ki tarar nasan tana nan zuciyarta kamar tayi bindiga kishiya ba dadi sam Allahu ya tsare mu da ita ya nisanci mazajen mu da tsinannun Yan matan Nan dake makale wa mazajen mutane,kiyi hakuri fa karki ce da ke nake wlh nima Ina da wata shegiya da ta makalewa mijina sai da nayi da gaske suka rabu matar saurayinki Allah ya bata hakuri da juriya kema dan Allah karki cutar da ita"

"Aunty ai har yan matan baa san ransu suke auren mai Mata ba sai dan kawai ya tsago a kaddararsu nima saurayi naso aura Allah baiyi ba toh ya zakayi da kaddara"

"Hakane Kam mudai Allah ya rabamu da mumunan kaddara"

Ji nayi nama kasa cin ciccibin hararowa nake ni zaa kawo yarinya irin ummi,satar kallonta nayi Muka hada Ido,ta sakar min murmushi ta sunkuyar da Kai Ni kuwa ban d'auke idona ba na zuba Mata Ido,doguwa ce mai zagayyen fuskan hancinta nada tsayi gashin girarta yakusa hadewa waje daya,tana da dan.manyan ido,da karamin baki,bata fiye duhu ba bata fiye haske ba,duk da banga kalar jikin nata ba,daga zaunen da take Ina iya hango tudun kirjinta indai ba ciko tayi ba tana da na fulani manya kiris ya rage ta shiga sahun masu kib'a indai kishiyar tata ba mai balain zafi bace lailai wanan zatayi saurin kwace shi,badan tace an sa Mata rana ba da gidanmu Zan kaita wlh bazan bari ma mahfuz ya ganta ba na ayyana a raina.

Kiraye kirayen sallah magriba yayi daidai da tsayuwar machine d'in mahfuz a k'ofar gida.

"Aikuwa ga maigidan ya dawo"

Mik'ewa tayi da sauri nace "A Ina zakije ki koma ki zauna idan ya shigo ku gaisa"


Komawa tayi ta zauna a kasan kafet ta sunkuyar da kanta sai Wasa take da zoben hannunta inasan yanda take da dan kunya.

Shigowar mahfuz da sallama yasa na m'ike Ina "oyoyo Abban Mimi"

Na karbe ledojin daya shigo dasu Ina ta mamakin ko dai kudi ya samu haka da yawa wanan uban leda haka.

Wajen da Mimi ke kwance ya nufa bai ko kalli b'arin da ummi take ba ya d'auki mimi a daidai lokacin da ummi ta Masa sannu da zuwa sai a lokacin ya kalleta ya amsa ya d'auke idonsa daga kallonta a daidai lokacin da ta mik'e ta nufi daya d'akin sai dana tabbatar da ta shige ciki nace "itace wacce Abdul ya kawo bakuwar tamu"

"Naganta takura Mana kawai yakeso yazo yayi dan rainin hankali"

Kasa yayi da murya ya matso kusa dani yana "Wai kina nufin a wancan d'akin zata zauna"?

"Emana da a Ina kakeso ta zauna"?

"Lallai bakida hankali,ga dakinmu ga d'akin da take ciki kinsan kuwa duk motsin da akayi a daki ana jiyowa"

"Kai jamaa toh Ina kakeso na kaita"?

"D'akin tsakar gida amma zamanta anan ai da takura gaskiya"

"Haba Mahfuz d'akin tsakar gida sai kace namiji taya zan sauketa a tsakar gida sai nake ganin kamar hakan bai dace ba ko Abdul ne yazo gidanan yaga na ajiyeta a tsakar gida zaiji ba dadi wlh"

"Wlh ba abinda ya shafeni nida gidana baza'a a zo a takura min ba a d'akin tsakar gida zata zauna na gama magana"

Ya fara k'ok'arin mik'ewa yanda ya had'e rai.yasa ban Kara magana ba na fara bude ledojin daya shigo dasu,gwanwanin Madara ne dasu bournvita har dasu cornflakes, siyayya sosai har dasu kifin gwangwani da balangu bredi mai yanka yanka mamaki yasa nace "A ina ka samo kudi haka mahfuz"

"Wlh wani kudi yau aka raba Mana shine nayo Mana siyayya"

Tunda na aure shi bai tab'a yo Mana irin wanan siyayyan ba, shiyasa mamaki rufeni farinciki Kuma ya gaza b'oyuwa a fuskata,dan dama ni mayyar cornflakes ce dan sacet nake siyowa
"Yeee nima na faso gari mun zama yan gayu Kai wanan bakuwar ta zo da goshi"

Bai kulani ba ya nufi daki Yana bari yaje yayi alwala

Cikin farinciki na kwashi kayan na Kai kitchen na hau jerawa a dan glass din dake kitchen din har dasu bama ya siyo Mana na kuwa ji dadi sosai.

Sai da na gama jerawa na dauki balangun na juye a plate na dibar wa ummi na saka mata tuwo mulmule biyu da Miya na dauki karamin exotic na hada a faranti gabad'aya na Kai Mata har daki a kwance na tarar da ita da alama daga wanka ta fito dan jikinta da lema ta saka karamin t shirt da bakin dogon skirt,sai da gabana ya Fadi dana ga surarta take na karbi shawarar mahfuz na in maidata d'akin tsakar gida tab.

Tana ganina ta rarumo hijabi tasa ta tareni tare da karbar farantin hannuna tana "Sannu Aunty"

"Yauwa nace Mata cikin murmushi Ina ga abincin ki nan idan kin gama ci zanzo na Kai ki d'akin can Kamar sai kinfi sakewa acan"

"Toh Aunty ngd da dawainiya"

"Lah ba komai na sakar mata murmushi na fito daga d'akin.

Na Shiga nawa mimi ce kawai a kwance da alama mahfuz ya fita massallaci.

Wanka na Shiga dan tuni na watsar da wankan jego na koma normal wanka.

Ina fitowa daga bandaki yayi daidai da shigowar mahfuz bai d'auke idonsa akaina ba ya zuba min Ido

Nida kayana nasan hali, ya matsu yaga Ina sallah

"Mallama Wai har yanzu shiru nafara gajiya fa"

"Tab kwana ashirin kawai da haihuwa sai nayi arbain fa"

"Wlh baki isa ba tab so kike na mutu kenan ya zauna a gefen gado,na gama shafe shafena na saka kayan shan iska.

Ina sai kayi sallah zamuci abinci ko na zubo yanzu"?

Bari ayi sallah Isha Kar nazo na kasa tafiya massallaci.

"Tom mu tafi Palo mu zauna"

Na dauki Mimi nayi gaba ya biyoni a baya.

A Palo muka zauna Muna kallo muna tab'a hira Yana latsa wayarsa hankalinsa dai Yana Kan wayar gabad'aya.

Sai ni kedai ke zuba surutuna har aka Kira sallah Isha ya fita massallaci bai dawo gidan ba sai wajen tara daga zuwa massallaci abincin ma da na jera Mana ya hucce tuni na cika nayi fam zuciyata ta fara rayamin kodai zance yaje take naji hankalina ya tashi,Ina tsoron tsinaniyar yarinya nan Mai nacin tsiya ce ta dawo rayuwar mijina wayata na d'auko dan na kirashi sai gashi ya shigo,da carbinsa a hannu da jalabiyar sa.

"Daga zuwa massallaci abban Mimi"?

Ina k'ofar gida wlh da Hamisu muke ta hira da kin leko zaki ganmu ai

Sai a lokacin hankalina ya kwanta

Muna cikin cin abincin Muka ji motsin bud'e k'ofar d'akin sai ga ummi ta fito da dogon hijabinta har kasa mahfuz ko kad'an bai dago ba Ina k'ok'arin Magana tace "Aunty dama bacci nakeji shine nace ko Zaki nunamin d'akin"?

Mik'ewa nayi Ina sude hannuna nace "e???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ee zomuje nama dauka kinyi baccin ne wlh'

Nayi gaba tana bina a baya har muka fice daga palon,dama d'akin duk da baa kwana a ciki Ina yawan gyarawa Ina Kuma turarawa sai dai ba bandaki a ciki, bandakin a tsakar gida yake idan nayi baki da bandakin tsakar gidan suke amfani ,Yan uwa ke Shiga bandakin cikin daki.

Muna Shiga d'akin nace "dafatan d'akin ya Miki"?

Kai sosai ma wlh yayi aunty ngd Allah yasaka da alheri"

"Lah ba komai ai an Zama daya sai dai nace sai dasafe kenan"

"Toh aunty sai da safe a shafa min Kan Mimi"

Da murmushi na amsa Mata na fito daga d'akin.

Sai da muka gama cin abincin na kwashe komai na Kai kitchen na dawo na tarar da mahfuz na latse latse a wayarsa.

Nima wayata na d'auko na hau latsawa Ina chatting Ina kallo kafin goma naji bacci ya fara k'ok'arin daukana.
Hakane yasa na kashe data na kalli mahfuz daya danke wayar sa da hannu biyu nace "Tom nidai bacci nakeji zanje na kwanta"

"Kije kiyi kwanciyar ki dan ni ba bacci nake ji ba ko na biki daki ciwon maran zaki sani a banza nidai na fara gajiya fa tam"

"Kazo muje mu kwanta na maka tausa wlh Zan maka dabaru"

"Naki fa kibar ni na cigaba da hira da abokina"

Ya hasko min fuskar wayarsa Inda naga sunan Abdul din da Abokina

"Ai shikenan sai ka shigo"

Bai bani amsa ba Ina shiga ciki na canza kayan jikina zuwa na bacci Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani bansan lokacin da ya shigo ba.

Washegari da wuri na tashi dan na hada breakfast dan mahfuz da wuri yake fita.

Ina cikin soya dankali naji sallamar ummi.

Na amsa Mata daga kitchen ina mamakin me ya sa ta tashi da wuri haka.

Har kitchen tazo ta sameni muka gaisa da ita Ina satar kallonta Ina San yanda take shigar hijabi har kasa da alama tana da kamun Kai

"Aunty Ina tsintsiya nayi shara"?

"Ummi dan Allah koma kiyi kwanciyarki dan kawai ki tayani aiki Kika taso"

"Dan Allah karki hanani tun jiya nakeso na tayaki kina hanani" karfe Tara zanje wajen da zamuyi program din shiyasa na tashi da wuri"

Duk yanda naso hanata ki tayi akan dole na nuna Mata wajen da tsintsiya yake ta d'auko ta fara share palon.

Har tsakar gidan naji tana sharewa.

Sai da ta gama ta Kara shigowa da bokitin mopping da abin mopping din tana cikin mopping mahfuz ya fito daga d'aki cikin shigar suit sai kamshin turare yake.

Adaidai lokacin da Nima na fito da farantin abincin karyawarsa.

Gaisuwar ummi ya amsa ba yabo ba fallasa ya tambayeta ya bakunta ta sunkuyar da Kai tana murmushi nidai idona nakanta atoh karta sake ta kallarmin miji ganin na ajiye farantin a gabansa yasa ta ajiye abin mopping din tana "idan ya gama na dawo na karasa"

Hankalinta na Kara gani,dan naga tana nesa nesa da mijina haka nakeso shima mijina ya iya tsare gida.

"Mai kike murmushi ke kadai"?

Tambayar da mahfuz ya jefomun kenan

"Wlh yarinya nan nada hankali mahfuz da gani ta samu tarbiyya sosai duk da a Lagos take zaune"

Tab'e baki yayi bai ce min komai ba Nima ban Kara magana ba har ya gama cin abincinsa
Ya Mike zai tafi na tafi dan na raka shi munje bakin k'ofa ya juyo Yana "Na manta ban fada Miki ba Abdul jiya yace na fada Miki wanan yarinyar ba komai ta iya ci ba ya roki arzikin a ringa tambayarta abinda zata ci ko a barta ta dafa abinda takeso dakanta wlh badan kin dage ba da sai na Masa rashin mutunci nida gidana azo ana min iko"

"Allah sarki wlh ba damuwa ai kana ganinta kasan Yar hutu ce ba irinmu da duk abinda muka samu ci zamuyi ba Tom ba damuwa ai tunda ba laifi muna da Abubuwan Yan gayu yanzu a gidan idan ma cornflask take so ta ringa Sha gashi nan"

"Ku kuka sani"

Yace a daidai lokacin da ya ida fitar da machine dinsa ya tayar ya tafi Ina daga masa hannu.

Ina komawa ciki na karasa mopping din na turara koina kafin na koma d'akin Ummi dan na tambayeta mai zata ci.

Kwalliya na tarar tanayi a lokacin da na Shiga tana ganina ta saki murmushi tana "so nake na shirya kar nayi latti"

"Kina nufin bazaki karya ba Zaki tafi nidai na soya dankali da kwai sai kayan shayi bansani ba kinaci ko bakya ci idan bakya ci sai a sama Miki wani abu dan Abdul yace Wai ba komai kike ci ba"

"Eee wlh aunty duk wani abu Mai maiko ban fiye ci ba da safe nafiso nasha corn flask haka ko bakin tea"

"Toh shikenan ki gama shiryawan akwai cornflask sai ki hada ki Sha"

Godiya tamin na sakar mata murmushi na fito.

Ban Dade da fitowa ba sai gata ta shigo da dogon hijabinta har kasa da farin glass.

Tana Zama na dauko mata kofi da cokali da tuni na ajiye Mata Madara da cornflask din

Cikin nutsuwa ta hada ta Sha sai satar kallona take narasa Mai yasa take San satar kallona.

Tana gama Sha ta mik'e da Yar Jakarta tana "Bari naje kar makara sai na dawo"

A dawo lafiya" ta fice daga gidan ni Kuma na koma daki.

Ina kwanciya mamn Iman ta hau bugun kofa tana kwallamin Kira

Ko mai take nema a wajena da sassafe haka oho na mike nayi hanyar waje........



Karku manta a gobe zamu gama free pages insha Allahu ku biya 500 ta 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko ta Nan 0000551222 taj bank nafisa Nuhu ko katin mtn a turo da shaidar biya ta layin nan 08033719070 yanzu zamu shiga cikin labarin budurwar mijina karki sake a barki a baya


KAYAN MATA

Assalamualaikum kina mace hadaddiya komi kincika ama kinada nakasu tawurin dadadawa miji?

Shin kinkai kin isa kina gogayya d sauran mata Amma tafannin ozaroom mishkila tasamu?

Shin sanyi y addabeki tayanda Baki iya gamsarda miji kullum kina makalemai yana kauda Ido?

Shin minene matsalar?
Kinshiga ko Ina kinnemi magani bawani chanji?

Tosaurara yar uwata aminiyar arziki, ubangiji yakawo mikini har inda kike,kizo kiji qawata,

Inada maganin sanyi me fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki,

Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, >?p? kikerewa sa'o'i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga,

Munada tsumi nau'i nau'i
Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu
Akway ruwan jaraba
Ruwan Dadi
Hadin minannas
Hadin dafa kaza(manta uwa)
Hadin yar gaban goshi,
Turarukan mallaka.

Duk a farashi mesauqi.
[6/9, 8:43 PM] Mmn Abiyat: *BUDURWAR MIJINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F.*

*PAID BOOK*

*LAST FREE PAGE*

*PAGE 10*

Ina bud'e kofa na yamutsa fuska Ina "Shi bawa bazaa barsa ya huta ba"

"Eee baza'a barki ki huta ba wuce muje"

Dariya nasa dan muna Yar Wasa da mmn Iman sosai muna Shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login