Showing 36001 words to 39000 words out of 155577 words

Chapter 13 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

2786

maganarsa ma Kara samin zafin zuciya yake mummy sai mika Masa Mimi take yak'i karba ya cigaba da roko a daidai lokacin da Ammi ta karaso cikin masifa tana
"Bani ita nan Nima bazan so Yar dabba ta shayar da ita ba,ga Yar jamaa can a kwance bansani ba ko ta kasheta har zaa ringa wani rokonta ta shayar ita tana ki Zan nemi Mai shayar da ita.

Ta karbi mimi daga hannun Mummy na watsa mata wani mugun kallo, adaidai lokacin da mai napep yaja Muka fara tafiya,na kifa kaina akan cinyata na fara rera kukan rabuwa da yata,zuciyata wani irin zafi yake min mummy bubuga bayana kawai take har muka Isa gida ita ta bawa Mai napep din kudin,Ina Shiga gida,dakin da nayi yanmatanci na shige na kwanta a kasan tiles dan koina na jikina zafi yake min.

Mummy ta shigo itama d'akin ta cire hijabinta ta karaso wajen da nake kwance tana "Lubna mai afkuwa ta riga da ta afku ba yanda zakiyi cuta ya riga da ya cutar dake,kuka bashine mafita a gareki ba karki dorawa kanki hawan jini,sanan Mimi banga dalilin da zai sa kice bazaki shayar da ita ba haba lubna mai laifinta shikenan dan mahaifinta yaci amanarki sai ki k'i shayar da ita yarinya bata san Hawa ba bata san sauka ba.

"Mummy har gida ya kawomin budurwarsa mummy ya kwanta da ita a cikin gidana,na ringa hidima da ita,yace na ringa tambayar ta abinda take so adafa mummy wane irin cin mutunci ne wanan da wulakanci,ya kawomin budurwarsa har gida ta ganemin sirrina,mummy mahfuz bai tab'a min siyayya ba,sai gashi daga kawo budurwar sa yayo cefane,mumy na ringa murna na zama Yar gayu har ke sai da na bawa labari"

"Ya isa haka lubna tunawa da maimaita wa bacin rai zai cigaba da saka ki kiyi hakuri ki bar kuka haka karki jawa kanki matsala,amma gaskiya zan karbo miki Mimi dan kema bacin rai yasa kike ganin kamar bazaki iya shayar da ita ba amma nasan tsakanin uwa da ya wlh yau bazaki iya bacci ba"

"Mummy idan na karbi mimi na shayar da ita nayiwa mahfuz gata,bazai san girman laifin da yamin ba duk da ba abinda zai saka na tab'a koma masa na tsanesa mummy Allah ya Isa tsakanina dashi bazan tab'a yafe mishi ba"

"Ya isa haka lubna yanzu duk abinda zakiyi ko ki fada a cikin bacin rai ne ki bari.ki samu nutsuwa Ina zuwa"

Ta mik'e tayi waje na maida idona na rufe inajin nono na na dadaurewa tausayin Mimi ya rufeni kila tana can tana kuka.

Mummy bata jima da fita ba ta dawo ta tayar dani tsaye tana muje kiyi wanka Lubna kiyi alwala kizo kiyi sallah dan bakiyi sallah asuba ba,idan kin iddar ki Sha tea na baki.magani kisha ki samu nutsuwa.

Koda na Shiga bandakin haka nayi zamana sai wacce ta tab'a Kama mijinta da cin amanarta zata fahimci kwatan abinda nakeji a raina,duk da a ganina babu macen da mijinta yayi wa mummunar cin Amanar da mahfuz yamin,a yanzu na fahimci ni kadai nake san mahfuz mahfuz bai tab'a kaunata ba,duk Mai kaunarka bazai ma irin wanan zaluncin ba, Hadeeza kuwa har na koma ga Allah Ina Kai kukana wajen Allah akanta.

Ban baro bandakin ba sai da mummy tazo ta fito dani, sallah ma inayi Ina kuka har na iddar kaina kamar baa jikina yake ba sabida tsananin ciwo,hanuna ma sai zugi yake min duk yanda naso na sha shayin da mummy ta hadamin kasawa nayi dan bana Jin komai nikam akaina,ni ji nayi ma duniyar ta ficemin a rai, no-no kuwa har zuba yake mimi ce kawai a Raina.

Mummy ganin na matsantawa kaina da kuka yasa ta min allura ba jima bacci yayi awon gaba dani"


Mahfuz

Hankalinsa ba karamin tashi yayi da tafiyar lubna ba Kamar ya dora hannu aka yayi ta zunduma ihu haka yaji,har sai da suka bace masa ya iya barin wajen Ammi kuwa bata saurare shi ba ta goya Mimi ta tare Napep,a wajen d'auko Hadeeza da ta dade da sumewa ta hau durawa Mahfuz zagi akan yazo ya dauketa su kaita asibiti.

Sai a lokacin ya tuna da halin da Hadeeza take ciki,da taimakon Mai Napep Suka kinkimi Hadeeza Suka sakata a napep,ya hau gefen Mai Napep Ammi ta zauna a baya har Suka iso wani karamin asibitin private Ammi zagin lubna kawai take tana rantsuwar mahfuz ya gama aurenta.

Halin da suka ga Hadeeza a ciki yasa sukayi emergency da ita dan sun dauka hatsari tayi,ta Sha bak'ar wahala a wajen treatment dan har dinki sai da aka mata a inda gashi ya fita.

Sai ihu take Mahfuz kuwa haushinta kawai ya keji kamar ya Kara lakada Mata dukan,tunda ga lokacin da yaji lubna na fadar Abubuwan da yayi Mata,har dasu maganin da yake zuba Mata a lemo dan bacci ya d'auketa,har da kyautar da tayiwa Ammi sam bai taba tunanin bata da sirri ba,ko Mai zaa Mata bai dace ta tona musu asiri ba,ya rasa ya akayi lubna ta gano duk iya saninsa ya na balain taka tsantsan sabida Kar ta gano su,shi Kam dawowar Hadeeza rayuwarsa ba karamin masifa ta jefa shi ba,har a tsayen nan dayake kunyar kansa yake ji yasan Yan unguwar su da gulma zuwa yanzu kowa yasan abinda ya aikata,ba wacce ta haddasa Masa wanan tashin hankali sai Hadeeza yayi matukar nadamar biye mata daya sani gidansu ya dage mata ya kaita,bai tab'a sanin tana da wani manufa ba a zuwa gidansa da tace zatayi,a yanzu duk da ta tona musu asiri da kanta ya yarda cewa dama da makirci a lamarinta so take dama ta raba su,idan akace Masa Lubna tana da zafi da zuciya haka karyatawa zaiyi dan lubna macece Mai saukin kai bai san haka take ba,da ace baya nan ya dawo ya tarar da tayiwa Hadeeza haka bazai tab'a yarda ita ta iyawa Hadeeza wanan dukan ba,dan Hadeeza ta fita kib'a da tsayi bai san har ya akayi lubna ta mata irin wanan dukan ba,a tsaye kawai yake a asibitin amma zuciyarsa na wajen Lubna da Mimi data bar Masa dake kananan kuka a bayan Ammi na jijjigata.

"Kai jeka Nemo Madara a damawa yarinya Nan tundazu take kananan kuka"

"Ammi dan Allah muje ki tayani bawa lubna hakuri da mahaifiyarta"

"Bakada hankali ni zanje na bata hakuri yarinya data gama zuba min rashin kunya har dasu zagi,ko ba'a gabanka tacemin kwadayaya ba,har dan ubanka kaje ka bata labarin an bani turmin zani"

"Wlh bani na fada Mata ba Hadeeza ce ta fada Mata duk wanan tashin hankalin ita ta jawomin"

"Wai dagaske yarinya ce wanan"?

Itace Mana Ammi

"Tabdijam itace Yar dabbar matarka ta canza mata kamanin haka lailia lubna ba matar da zaka zauna da ita bane ka gama aurenta dan watarana zaka iya kuskure Mata ta maka duka haka,inyazo da karar kwana kaga sai mutuwa ta jawomin asara kaima banda rashin hankali ya zaka Kai budurwarka gidanka ba dauraa muku Aure akayi da ita ba,Ina Iyayenta suka barta tazo ta zauna a gidanka"?

Tiryan tiryan mahfuz ya bata labarin tafiyar da marikanta sukayi,

Kaima kaso iskancin ai shiyasa baka kaita gidana ba ai ga irinta nan dama kaima ta jibgeka haka"

Mahfuz takaici ne ya hana shi magana dan Sam Ammi ta kasa gane halin da yake ciki.

Shi a yanzu ma baa nutse yake ba Ammi taki bashi hadin kai ganin Hadeeza ta samu bacci yasa ya cewa Ammi zaije ya dawo ta kawo mimin"

"Ina zaka kaita"?

Mmn Iman dinan Zan kaiwa ita kema ki huta idan na tashi dawowa sai mu taho tare"

Ya Mata karya dan gidansu lubna yake San Zuwa

"Nima gida zani ai ka kira Shemau tazo ta zauna da ita kafin ta farka".

Shi ya fara tafiya Ammi kuma zata jira kanwar mahfuz tazo asibitin kafin ta tafi tunda ba wani na Hadeeza da suka sani ballantana su nemesu.

Mimi a rungume a kirjinsa da tsananin tausayin jaririyar da ko wata batayi a duniya ba amma abinda yayi na Neman raba ta da mahaifiyarta.

Daa ce bai saka Abdul a cikin wanan abinda yayi ba da ba Mai yiwa Lubna magana ta saurare shi Kamar Abdul,yasan Abdul idan yaji abinda yayi ransa ba karamin b'aci zaiyi ba,Yana balain girmama lubna Yana ganin mutuncinta,sau tari idan Hira ta hadasu haka,yakan ce ya rike Lubna da hannu biyu dan irinta kadan ne a
al umma da basu da kwadayi da buri Kamar sauran Yan matan zamani.

Koda ya isa k'ofar gidansu lubna kasa shiga yayi yanajin kunyar mahaifiyar Lubna shima yasan bai kyauta ba.

Ganin Yana ta tsayuwa ga Mimi ta fara kananan kuka yasa yayi shahada ya Shiga har wani irin rama yayi sabida tashin hankali,ga bakinsa ya bushe Kamar Wanda ya dade bai Sha ruwa ba.

A bakin Palo ya tsaya ya Kara kwada sallama.

Yaji muryar mahaifiyar lubna ta amsa data buga tagumi a Palo tsananin tausayin lubna ya balain rufeta,cin Amana akwai ciwo da zafi, mahfuz ya matukar bata mamaki da Kai budurwa gidansa dan a fuska idan ka ganshi aka ce zaa saka Masa yatsa bazaka yarda zai iya ciza ba.

Ganin mahfuz ne yasa ta hade rai duk da kasan ranta taji dadin kawo mimin da yayi dan sam bazata bari lubna ta zalunci Yar da bata san hawa ba bata San sauka ba.

"Lafiya"?

Ta jefa masa tambaya tana binsa da mugun kallo

Mahfuz ya zube akan gwiwar sa hawaye ya fara taruwa a idonsa cikin rawar murya ya fara magana Yana "Mama nasan na muku ba daidai ba dan Allah dan annabi kuyi hakuri ku yafe min wlh sharrin zuciya ne Koda Wasa bantaba tunanin Kai Hadeeza gidana ba bansan Mai ya hau kaina ba"

"Tsakani da Allah baka kyauta wa Lubna ba kaci mutuncinta mahfuz ka wulakanta ta,taya zaka Kai budurwarka har gidanka ta zauna yanzu da ace ta kashe ta fa ko ta saka Mata guba a abinci yarinya Nan na zaune da Kai tsakani da Allah Mai ta maka data cancani haka daga wajenka"?

"Mama sharrin shaidan ne dan Allah ki tayani bata hakuri"

"Toh banida ta cewa mahfuz tunda nake da yarinya nan ban taba ganin tayi fushi haka ba,har ta iya cewa bazata shayar da yarta ba sabida ta hada jini da Kai kaga kuwa ai ba karamin fushi tayi ba dan haka ka nisance ta yanzu har ta sauko a Karan kanta idan taga zata dawo gidanka sai ta dawo idan taga bazata iya ba bazan Mata dole ba,dan Inda aka sanka aka san darajar ka Nan kake zuwa,a abinan da ya faru Ina kwokwantan San da kace kana yiwa Lubna,wacce kake so ita ka Kai gidanka Kama kasa hakuri a daura muku aure da ita,dan haka yanzu bazan iya Mata Dole ba duk shawarar da ta yanke Zan goya Mata baya,sanan a gaskiya mahaifiyarka bata kaunar lubna agaban idona ta ringa zagin ta tana kiranta Yar dabba ga mari ga tsunka jaka tasan Kaine kayi laifi amma take goyan bayanka ni yata ba gajiya nayi da ita ba idan bakwa Santa Ni Ina kaunar abata.

"Mama wlh Ina kaunar lubna sharrin shaidan ne"

"Dan Allah Zan iya ganinta"?

"Aaa bacci take dan allura nayi Mata"

"Dan Allah mama ga Mimi ta taimaka min ta shayar da ita Allah ya hucci zuciyarku ya mike ya shiga palon ya ajiye mimi da bacci ya d'auketa rabonta da nono tun Daren jiya.

Mahaifiyar Lubna bata ce masa komai ba ya ajiye mimi ya kara bata hakuri akan zaije ya dawo.

Yana fita tayi sauri ta d'auki mimi tayi dakin da lubna ke kwance.

Duk maganar da mummy da mahfuz suke Ina jinsu.
Idona biyu a yanzu sai naji Kuma bazan iya fushi na ki shayar da ita ba,amma auren mahfuz kam nagama yaje ya auri hadeezar sa daya fifita ta a kaina.

Koda mummy ta bani Mimi karbarta nayi.


Hadeeza

Da kuka ta farka tana Jin koina na jikinta a daure fuskarta ma Kamar baa jikinta ba bata tab'a tunanin lubna nada k'arfi haka ba,bata San yanda akayi har ta ganosu ba,Koda bata kalli mudubi ba tasan lubna ta mata lahani ta canza Mata kamani, abinda mahfuz zai Mata kawai taji Dadi shine ya saki lubna ya Kuma aureta da gaggawa sai a yanzu ta ringa data sani da a lokuta da dama da zuciyarta ke Raya Mata taje ta cakawa lubna wuka Bata aiwatar da haka ba,ta balain tsanarta da sai da tayi da gaske take iya dannewa har take kiranta Aunty,amma shine ta mata iirn wanna dukan ta kumbura Mata jiki ta d'auka idan ta farka zata ga mahfuz a gefenta hannunta cikin nasa,sai gashi bata gansa a asibitin ba wata daban ta gani da bata Santa ba ga bakinta ya kumbure bazata iya magana ba.

Tana a kwance har dare ya fara yi ba mahfuz ba dalilinsa Inda ranta ya fara b'aci da ace zata iya motsa jikinta ta Yi magana da ta tambayi yarinya Nan Mai Dan Kama da mahfuz,Taya lubna zata kusa aikata lahira mahfuz ya kawota asibiti ya direta bai zauna a wajenta ba.

Mamaki bai Kara Kamata ba sai da dare yayi aka aiko da abinci mahfuz baizo ba,burinta Bai wuce ya shigo ya bata hakuri ya nuna mata takardar sakin lubna ba.


Mahfuz

Kasa zuwa gidansa yayi sabida gani yake kowa yasan abinda yayi Koda yabar gidansu lubna gidansu ya tafi.

Sai da ya yayi sallah ya dan ci abinci ya lalubo lambar Abdul shi kadai zai iya taimaka Masa a wanan lokacin.....
Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba>??

Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai>??? @&?duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba

Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki

Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu

Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted

Soap price:3k
Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free

Maiso kindly message 08062991549
Call 08064532391

Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai=?O?

Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta=?O?adade anayi sai gsky>?-?>??

Mg's skincare


*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 ZUWA 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaida biya zuwa ga lambar 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min sharing idan bansanki ba bana ganinki Allah Yana kallonki na barki dashi*

*Bm*

*Na Sadnaf*

*Page 15*

Bugu daya ya d'auka Yana "Kasan kuwa yanzu nake Shirin kiranka inata Kiran Lubna dan na hadata da Aisha su gaisa bata d'auka ba halan bata kusane"?

"Hmmm Abdul Ina cikin matsala"

"Subhanallahi wani abune ya faru"?

"Abdul idan na fada ma nasan zaka ji haushina amma.kasa kanka a matsayina ko kaina zaka iya kwafsawa"

Mahfuz kasa ma bashi labarin yayi ya cigaba da kame kame sai daya ga Abdul zai kashe wayar ya bashi labarin abinda ya faru ya Kara da "Bansan Mai ya hau kaina ba banyi tunani ba Sam,wlh Hadeeza kanainayeni tayi,na kasa yakice mata gashi yanzu lubna tayi fushi tunda nake da ita wlh ban taba ganin ta yi irin Wanan fushin ba"

"Allah ya Isa tsakanina da Kai Mahfuz baka kyauta min ba yanzu dama yarinya nan budurwa ka ce Taya zaka aikata irin wanan danyen aikin,daka tashi abinka hada dani, wlh Azeem da nasan budurwarka ce ko kallonka bazanyi ba yanzu wane kallo kake San lubna ta ringa min kasa kanka.a matsayin ta yanzu ta kawo maka Saurayi gida ka ringa.kuma hidima da saurayin zaka ji Dadi,ka cutar da ita,wlh ka zalinceta"

"Wai dan Allah Abdul ka barni naji da daya Mana yanzu na kiraka dan.na samu kwanciya hankali da mafita Kai Kuma sai Kara maganganu kake"

"Toh Mai kakeso nace maka a lokacin da zaka yi abinka kayi shawara dani, wlh Ina Jin labarai naka ya banbanta idan ma holewar zakayi da ita ka kaita hotel mana why zaka kaita gidanka tsakani da Allah kace bazan maka.magana ba yanzu ka jawomin bakin jini a gurinta kenan,yanzu zata dauka da hadin bakina aka kaita gidanka a gaskiya banji dadin abinda kamin ba

Yace cikin tsananin b'acin rai kafin mahfuz yayi magana ya kashe wayarsa

Mahfuz yabi wayar da kallo,shi kansa Abdul din bai tab'a jinsa cikin bacin rai kamar haka ba,sake kiransa yayi,bai d'auka ba.

Haka yayi ta Kira a karshe yaji ya kashe wayar.

Mahfuz haka ya rike wayarsa Yana tunanin mafita Abdul kadai yake tunanin zai iya rokon lubna ta sauko sai gashi yak'i sauraransa.

Ammi Kuma yasan ko zai mutu ya dawo bazata saurare shi ba,karshe dai sai yayyensa sun Shiga maganar nan dole su zasu shige Masa gaba wajen shawo Kan lubna.

Zurfin da yayi a tunani yasa Sam bai san dare yayi ba sai muryar Ammi yaji a kansa tana "Wai uban me kake a daki tundazu baka koma asibitin ba"?

"Bana Jin dadi Ammi nima ban wuce a kwantar dani ba bazan iya komawa asibiti ba"

"Sabida ka rabu da Yar dabba Yar gwal ko"? shine zaka kwanta rashin lafiya,Kaine ka dauki yarinya Nan ka Kai gidanka matarka ta kusa kasheta badan Allah yasa tana da tsawon rayuwa ba,shine dan wulakanci zaka barta da shemau kawai a asibiti,idan ma dan ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login