Showing 60001 words to 63000 words out of 155577 words

Chapter 21 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

2778

Kuma wajen aiki zasuyi chatrn dinsu,da yamma ko kafin yaje gida sai ya biya ta gidansu Hadeeza,har wani kib'a yayi dan a tsakanin lubna da Hadeeza baisan wacce tafi kaunar faranta masa rai ba, girkin rana haka Hadeeza ke aika masa dashi,ko gajiya batayi idan kuwa yaje gidansu sai sunyi wani irin mahaukacin romance da yake ganin a wajenta kadai yake Jin dadin romance dan sakin jikinta takeyi sosai sabanin lubna da ko kiss Mai tsayi bata jurewa baisan dalili ba abinda yafi so a rayuwarsa yanzu sau uku Hadeeza na masa zai so ace lubna itama ta iya din banda Yana Kai zuciyarsa nesa da ya sake neman Hadeeza dan dai kawai a gidansu ne, duk da zasuyi iya yin komai batare da an Kama su ba dan mai gidan da matar gidan daddare suke dawowa yaran kuwa ko kusa da wajen da suke zance basa zuwa.

A yanzu yake ganin wautar da yayi a baya da ya bari lubna har ta dago yana tare da Hadeeza,lokaci zuwa lokaci Hadeeza kanyi mishi maganar aure, Wanda a yanzu shi kansa sabon da tayi Masa da wasu Abubuwan bazai iya jure rashin su ba, badai zai iya hada san da yake yiwa Lubna da Hadeeza ba amma Yana Jin Hadeeza a ransa da a yanzu Kuma yaji zai iya auren nata,duk da yakan ji jikinsa yayi sanyi da auren nata idan ya tuna rsntsuwar da lubna keyi akan indai Hadeeza zai Auro mata macen da ta gama sanin sirrinta duk san da take masa a ranar zata rabu dashi, gefe guda Kuma ga Ammi dake matsa masa da zancen auren Hadeeza Wanda yasan hidima da Hadeeza take da Ammi yasa take so ya auro Hadeeza, Yana so dai a samu Kamar shekara tukunna idan ma zai bijiro da zancen auren Hadeeza sai ya bijiro da zancen aurenta inyaso sai ya kama kafa da Aunty nurse idan lubna ta nemi bijire Masa.


Wata hudu kenan komai na tafiyar masa yanda yakeso suna zaune kalau da Lubnar da yake fatan mutuwa ta rabasu dan tabbas yasan zaa Dade a mata baa samu mace irinta ba bata bashi mamaki ba sai da yake mata zancen ya samu kudin da yake so ya siyi mota Dubu dari biyu yake nema yanzu ya cika ya siyi motar Yana ganin Abdul zai yiwa magana ya ranta masa kudi.

Murmushi kawai ta Masa tana "Yanzu dai iya Dubu dari biyun kake nema idan ka cika zaka siyi motar"?

Gyada mata kai yayi cikin tsokana yana "ko zaki cika min ne hajiya"?

Murmushi tayi ta mik'e ta Shiga daki ba dadewa sai gata ta fito da wani bakin leda a hannunta ta zauna a gefensa ta bude ledar kudin bandir daya na Dubu guda daya sai na dari biyar guda biyu sai dubu dubu da bai san ko nawa bane"

Cikin dan mamaki yace mata "Ina kika samo kudin nan"?

"Dazu nan Mummy ta Aiko zainab ta kawo min wai na ringa juyawa Ina Sana'a bata San zaman hakan da nake ya Kamata Kai ma na ringa tallafa ma da wani abu ita dai tana so na zauna lafiya dakai shine nake jira idan ka dawo sai na nuna maka mu shawarta muji wane irin Sanaa zanyi toh amma tunda har kana neman cikon kudin siyan mota bari na ranta ma idan ka samu sai ka bani idan yaso sai nacewa mummy nayi order kaya nan da wata uku zasu iso,kila kafin lokacin ko Dubu darine ka samu sai ka bani"

Girgiza kai ya hau yi Yana "aaa bazan karbi kudinki ba kija jarin mama dai ta rigani baki kudin jarin ne dan dama so nake na fara siyan motar kafin na nemi kudi na baki kiringa Sanaa amma tunda ta rigani Angode Allah ya saka Mata da alheri"

Kudin ta dora.masa a cinya bayan ta ciri dubu dubu da bai san nawa bane tana "Kudina ai kudinka ne mahfuz tunda har bukatar kudin ya taso ka karba wlh wanan Dubu ashirin ne da ta Saba Mana kyautarsa shi kawai zan dauka nima Zan so ka siyi motar nima na faso gari duk Inda zamuje sai na danne motar kawai"

Kara mayar mata da kudin yayi ta hade rai tana "Wlh sai ka karba ya zaayi ga kudi a wajena kace zaka wani tafi Kiran Abdul nidai gashi nan na baka Nan da wata uku ko Dubu darine sai ka bani dubu Darin kuma na bar maka"

Ido kawai ya zuba mata wani irin Santa da kaunarta na ratsa shi,kasan ransa Kuma Yana Jin kamar baya Mata adalci,yafi kashewa Hadeeza kudi akan ta dan ko jiya sai daya bawa Hadeeza Dubu goma ita kuwa iya kudin cafenan yake ajiye mata ya zama dole shima ya dage wajen kyautata mata inama zai iya rabuwa da Hadeeza yayi rayuwa da ita kadai bazai yafewa kansa ba idan har ta Kara kamashi da laifin cin amanarta sau tari idan ta kyautata Masa yasha yunkurin yaga ya rabu da Hadeeza amma suna haduwa da Hadeeza kuma shikenan.

Jawota yayi ya rungumeta ya hau mata godiya

Ita kuwa sai kyalkyale dariya take tana "duk abinda zan maka ban Fadi ba"


Washegari kuwa da sassafe ya fice dan shima kansa doki ya ringayi gari ya waye yaje ya dauko motarsa dan tun a jiya ya tura na cikin acct dinsa cikon da lubna ta basa zai kai.

Har aka sallama masa motar da takardu bakinsa kasa rufuwa yayi mallakar mota na cikin manyan burikansa.

Koda yaje wajen aiki haka aka ringa Masa Allah ya Sanya alheri,sai da ya nutsu ya kira lubna akan ya karbo motar ihu ta saka tana "Wlh ni Zan fara dannawa"


Dariya ya sa Yana "karki damu ana tashi zanzo gida ki shirya muje mu nunawa Mama daga nan sai muje wajen Ammi itama ta saka Mana albarka.

Yana jin tsantsar farin ciki a muryarta har tana ta matsu ya dawo taga motar

Ahaka sukayi sallama kafin ya kira Hadeeza da dama bai fada mata zai siyi mota ba so yake ya bata mamaki sai dai ko daya kirata 2 miscal bata d'auka ba hakane yasa ya ajiye wayarsa ya fara aikinsa bai Kara waiwaiyar wayarsa ba sai wajen daya anan yaga miscal din Hadeeza wajen goma yasan wajen biyu zata Aiko masa da abincin haka kawai yakeso yau yaje ya bata mamakin.

Koda ya iddar da Sallah wajen Hadeeza ya nufa sai da yaje k'ofar gidansu ya kirata a waya tana dauka yace "Ina waje"

Ya katse wayar Bata wani jima ba ta fito sai da ta gama waige waige kafin ta kallo motarsa dake fake dan nesa da gidan.


Wani irin gwallo Ido tayi cikin sauri ta iso wajen motar ta hau tsalle kirjinta na tsalle Ido kawai ya zuba mata tana tsallen har ta bud'e motar ta shigo tana "Dan Allah mafarki nake ko gaske mahfuz wanan motarka ce"?

Gira kawai.ya daga mata dan da alama bata saka bra ba dan dogon hijabine a jikinta har kasa kamshin turaren ta har ya kashe Masa jiki hakan ya tilasta masa dora kansa a steering motar Yana kallon kirjin ta ta cikin hijabinta Yana daga Mata gira ta fado jikinsa kafin ta ankara ta hade bakinsu ta mishi kiss.

K'arfi da yaji Hadeeza ke neman susutar dashi tana cire bakinta tace "shikenan tunda ka siyi motar sai Kuma Aurenmu ko"?

Gyada Mata Kai yayi dan ji yayi maganar na neman Masa wuya

"Wlh ni Zan fara danna motar nan"

"Bari na Shiga gida na Saka kaya daga wanka na fito sai ka ajiyeni a saloon"

Da sauri ya ruko hannunta dan har ga Allah Yana so idan zai fara d'aukar wata a motarsa ya zama lubna ce farko

"Sauri nake Hadeeza zuwa nayi dama na nuna miki Ina da aiki da yawa yanzu zan koma idan na tashi zan biyo"

"Aaa wlh sai ka rage min hanya"

Tayi caraf ta cire mukullin motar ta fice daga motar har ga Allah ba haka yaso ba yaso Lubna ya fara d'auka amma sai gashi Hadeeza na neman b'ata mishi plan dinsa.

Bata fi minti goma da shiga ba sai gata ta fito cikin Riga da skirt sun balain matseta Yana ma iya hango tudun kirjinta ta mayafi da ta yafa hannunta rike da kula da alama na abincin da zata aika Masa ne tunda yazo shine ta fito dashi idonsa a kure a kanta har ta bud'e motar ta shigo tare da bashi mukullin tana " muje"

"Nifa bana san wanan shigar da kike na riga da skit idan har kika saka bayyana surar jikinki yake Kuma kinsan banaso"

"Zan daina sawa"

Kamar Kar su rabu daya kaita saloon din koda ya sauketa sai da ya biya kudin kitson anan take fada Masa har gyaran jiki zaa Mata duk wata takeyi dole yaji Yana San ya ringa Jin Yana San kasancewa da ita.

Koda ya koma office sai da yaci abincin kafin ya sake Kiran Lubna da bugu daya ta dauka tana "Anya zan iya jiranka ka dawo bazan zo na sameka ba wlh na matsu naga motar"

"Kai Kai haba karki damu yau da wuri Zan dawo kedai ki shirya kawai ba sai kin wahalar da kanki yin girkin dare ba"

Hira suka tayi tana zayyana mai inda zai kaita da mota har tana ta fadawa ma Aunty nurse zasu zo ta Kuma kira Ammi bata d'auka ba

Ce mata yayi Kila Ammi bata kusa ne bari ya kirata.

Yana katse wayar ya kurawa wayar Ido,Yana tunanin da gangan ma Ammi taki d'aukar wayar lubna sau uku kenan lubna na ce masa ta kirata bata dauka ba tsoron sa ma suje tayi Masa maganar Hadeeza agaban lubna Anya zaije ma kuwa gidan nasu,?yanzu Kuma idan yace Kar suje sai lubna ta zargi wani abun

A haka yayi ta sake sake a ransa Yana aikinsa karfe hud'u Hadeeza ta kirashi akan ta gama yazo ya maida ta gida,Yana ce Mata bazai samu zuwa mayar da ita ba ta saka mishi shagwaba akan dole ya dau mukullinsa dan dama ya riga da ya gama da office din gida yake San Zuwa.

Tunda ya d'auko Hadeeza daga saloon din yake Jin wani irin fitinannen kamshin na tashi a jikinta da hannu daya yake tuki ta rik'e Masa daya hannun nasa tana yawo da hannun a jikinta,

Koda ya kaita gida ji yayi kamar ya bita ciki su danyi Romance sai dai yasan idan ya Shiga zai iya dadewa bayaso kuma lubna tayi ta jiransa.

Da jajjayen idonsa yake kallon Hadeeza da fuskarta yayi kyau sabida kitson da aka mata ta zaro harshen ta waje ta kada masa tare da kanne Masa Ido daya, baisan Mai yasa Hadeeza ke san taga tana susuta shi ba,hannun nasa ma sai Wasa take da harshenta a tafin hannunsa sai kwace hannunsa yayi yana "Dan Allah ki daina daga min hankali Hadeeza"

"Yanzu tunda kayi mota gaskiya ya Kamata ka ringa ware mana Lokaci da zamu na fita mahfuz mu dan zaga gari mu Sha iska"

"Ki bari sai zuwa next week haka dan wanan satin gabadaya zan zaga dangi nayi zumunci akwai wayanda da yawa bana iya zuwa wajensu wlh a machine amma tunda yanzu nayi mota zanje"

"Tom shikenan Allah ya kaimu zaka kirani idan na ka koma gida"

"Gobe idan na fito Zan kiraki yanzu idan naje gida zamu fita da lubna"

Take ta hade rai

Lafiya kuwa

"Ni dai Allah ya nuna min ranar da Zan samu yancin nan mahfuz nima ka aureni mu daina wanan kumbiya kumbiya din"


"Karki damu lokaci na zuwa"

Hmm ai shikenan sai goben kenan

Ta bude kofar motar ya ruko hannunta Yana "bazaki min good bye kiss ba"?

"Kaje lubna ta maka"

Ta fusge hannunta ta fice daga motar mahfuz yasa dariya dan yasan kishine ya motsa Mata.

Sai da ya ga shigewarta gida ya tafi.

A cikin kwalliyar purple din shadda ya samu lubna ta kashe dauri ture kaga tsiya tayi balain kyau har wani kib'a yaga tayi ta ajiye kumatu ta Sha Jan bakin da ke kara sakata kyau sai baza kamshi take Mimi ma ta Mata kwalliya.

Tsalle kawai ta ringayi kamar yarinya ta ringa zagaye motar sai dariya yake Mata.

Dak'yar ta bari yayi wanka shima ya shirya cikin kananan Kaya,Kiran sallah magriba yasa ya tafi massallaci dan yayi sallah ita kuwa lubna dama hutun sallah take.

Koda ya dawo daga massallaci a jikin motar ya sameta a tsaye bakinta yak'i rufuwa.


Sosai yake Jin dadin yanda ya ganta cikin farinciki Yana tuki ta fara musu hotuna tana musu video.

Kafin su isa gidansu lubna ya tsaya a wani karamin super market ya danyi siyayya da zai kaiwa Aunty nurse,duk da yaga itama lubna ta siyi wasu Abubuwan da kudinta baisani ba ko itama so take ta kai wani abun.

Kyakyawa tarba Suka samu daga wajen Aunty nurse ga lafiyayen abincin da ta musu sai da suka ci suka koshi.

Wajen takwas suka Mata sallama tayi ta musu adduoi anan shima ya Mata godiyar jarin da ta bawa Lubna,Yana Jin lubna na fada mata tayi order kayan kitchen Anty nurse kuwa ta ringa mata fadan kayan order ma duk damfara ce.

Shi dai motarsa ya shige sukayi danyi maganganunsu.

Zainab ta rakota har bakin mota Suka dau hanyar gidansu haka kawai yaji gabansa na faduwa yaso.ma ya fasa zuwa lubna ta dage akan suje gani yake kamar Ammi zata Masa maganar lubna.

Har Suka iso gidansu lubna kawai ke Masa hira sai da suka iso yagane siyayyan da tayi Ammi tayiwa sai yaji kunya ma ta Kama shi dan baifi Dubu biyar ya kashe ya siyi kayan shayin daya kaiwa aunty nurse ba amma ita kuwa ta kashe ya kusa Dubu goma ko fi.

A tsakar gida suka Samu Ammi a zaune akan tabarma Shemau na can gefe tana latsa wayarta,Ammi kuma da radio a gefen ta.

Mahfuz da hasken dake tsakar gidan yaga yanda Ammi ta hade rai ta amsa sallamar da sukayi ciki ciki.

Ya saci kallon lubna da har lokacin faraa bai gushe a fuskarta ba ta mik'awa shemau mimi


Lubna

Har kasa na duka na na gaida Ammi amma ga mamakina ko kallon Inda nake batayi ba balle ta amsa sai mahfuz da ta hau yi wa magana tana "Dazu baka ga kirana bane"?

"Wlh bangani ba Ammi"

"Taya zaka gani tunda kana tare da ishashiya matar da ka fifita akan kowa ai dole kace baka gani ba"

Tunda na dawo gidan mahfuz sai yau nazo gidan take na sha jinin jikina na tuna na dan yiwa Ammi rashin kunya a cikin zuciya amma da zata min adalci ai zata ga laifi Mahfuz yamin

Satar kallon mahfuz nayi da fuskarsa kawai ta nuna baiji dadin abinda Ammi tamin ba

Ammi na san cigaba da magana ya katse ta yana "Haba Ammi Mai yasa kike hakane wlh banga kiranki ba"


"Bazan mamaki dan kayimin rashin kunya ba Mahfuz zama da madokin kanwa ai,har nayi mamaki zaka iya Buda baki ma ka zageni ai a wajenta ka koya"

"Ammi yanzu laifine dan munzo gaisheki Zaki Mana irin wanan tarbar mota nazo nuna miki fa ki sa Mana albarka"

Tuni hawaye ya hau zubomin dan Ina da saurin kuka dama nasan Ammi Kamar ba kaunata take ba sai gashi kamar jira take nayi kuskure, hawaye kawai nake bakina ya min nauyi balle na bud'e na bata hakuri.

"Yo dan ka siyi mota sai na hau tsalle ko me,ai ba abinda zaka min a yanzu naji Dadi sama da kayi Aure,dan Ina nan akan bakana wlh sai ka Kara Aure sai ka auri Mata ta rufin asiri da bazata tona maka asiri idan kayi ba daidai ba,matar da zata darajani tasan mutuncina,tunda har ka siyi mota ka fara shirye shiryen tura kudi gidansu ...

"Ammi dan Allah mai hakane"


Mahfuz ya katseta da sauri cikin tashin hankali sunan Hadeeza da take so ta kira

Ni kuwa kirjina wani irin bugawa ya ringayi na dago Ina kallonta"

"Ooo dan nace sai ka Kara aure ko rude haka toh wlh sai ka auri yarinya nan matuniyar arziki Yar albarka da tasan daraja uwarka idan ma tsoron fada Mata kake ni bari na fada Mata tama shirya Zama da kishiya yarinya nan tasan mutuncina tana darajani a haka tun kafin ma ka aurota kenan inaga ka aurota"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Lubna tashi mu tafi"

Jikina rawa kawai yake na zubawa mahfuz Ido da nake ganin rashin gaskiya karara a fuskarsa nace

"Mahfuz aure zakayi dama bansani ba"?......
MG'S SKINCARE

In akaji gangami labarin kidane,sun shahara sun tumbatsa sunkai sunwuce tunanin duk wani meson Adama dashi aharkar gyaranfata d walwalinta,

Yar uwa haske ko qyalqyale kikeso kiyi Abu yaci tura?
Kyan fuskarda ko yar uwarki mace kance dama dama kikeso?
Kokuma ke kuraje d tabbuna suka lahanta mki fuska har ake ganinki d wani idon n daban,
Nankarwace tayimiki zanen kura a kyakyawar fatarki?
Kokumade Mai kikashafa be amshekiba yasa duk kika koma ruwa biyu Nan fari Nan baqi?

To duk kuzo insha Allah kudai naku y qare gdan kukazo,

Munkawo shahararrun kayangyaran jiki
Sabulu,
Man shafawa,
Man fuska,
Scrub,
Cleanser,
Glow oil,
Dukdan qawarmaku d matsaltsalunku,

Da 11k kachal zatasa kihaske kizama kalar madara qirar models,

Set 11k
Sabulu 3k
Student package:7k
Munakuma bayarwa in pieces duk afarashin mesauki.kayanmu bbu fariya ko tutiya angwada andawo,ankumayi farinciki d hkan,Kuna iya samummu d wadannan numbobin,
WhatsApp,
08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call only
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Idanba wadannan numbobinba to gaskiya b mg's bane, available in Kaduna and Kano only, thanks for always trusting us,our returning customers we really do appreciate wadanda sukeda burin Siya munamaku fatan alkhairi ubangiji ybaku yenda zakuyi,Allah Kuma yqaro mna dukiya me amfani ta hanyar halalinmu.








*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi*


*Page 24*

MAHFUZ

Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba dayasan idan yazo da lubna zatayi wanan b'arin zancen da Sam bai soma zuwa da lubna ba
"Ba auren da zanyi lubna Ammi ke San tilasta min nayi Aure"


"Ba wani tilasta maka da nake dan kaima kana so ni bansan Mai yasa kake tsoron yarinya nan ba ni a yanzu nasan wlh baa haka aka barka ba tom auren Dije ba fashi"dan haka take kiran Hadeeza

"Tashi mu tafi Lubna"

Hawaye kawai nake na kalli mahfuz na kalli Ammi kiyayya karara nake hangowa a idon Ammi,bansan wacce dijen Ammi ke San bawa mahfuz ba

Murya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login