Showing 111001 words to 114000 words out of 155577 words

Chapter 38 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

6049

ji bakya gani burinki muyi ta tashin hankali dake,na baki hakuri na miki kuka kashe kaina kikeso nayi,nima mutum ne Kamar kowa shaidan zai iya galaba a kaina a yanzu Kuma nace miki na daina abinda nakeyi kin ki yarda ya kikeso na miki a yau Ina murna kin dawo Zan samu kwanciyar hankali sai gashi daga an tura Miki hoto kin yarda kina furta kalmar na sake ki tunda muka rabu Hadeeza ta sakoni a gaba har sai da ta ringa nuna min zata kula min sharri a wajenki sabida Kar tayi haka na aika gidansu Allah daya taimakeni kafin auren asirinta ya Tonu,bakin cikin naki aurenta yasa ta dage bazata tab'a barina na samu farinciki ba Kuma idan har dan ke naki aurenta itama bazata tab'a yarda na sameki ba sai tayi duk abinda zatayi ta raba mu duk abinan kin kasa ganewa idan har Ina tare da ita dole Zaki gane bansan Mai yasa idonki ya rufe ba haba bari Kuma kigani"


Yayi gaban mudubi Kamar zai kifa ya dauko wayarsa Yana wani irin hucci ni sai na ma kasa motsi balle nayi magana.

Bansan wa ya kira ba naji dai ya saka a handsfree sai da yayi ta ringing har ta kusa katsewa naji muryar Hadeeza ta ratso wayar da dariya tana "Masoyina sako ya iso kenan shiyasa ka kirani mahfuz kana Wasa dani ko wlh baka ga komai ba yanda ka sakani bakin ciki ka saka bana iya bacci wlh sai na jefa ka cikin bakin ciki,yau ka maida lubna gidanka amma wlh bazan tab'a bari ku samu kwanciyar hankali ba wanan kad'an kenan da ga cikin balain da zan ta hada ma akwai babba da zan maka da dole ka dawo ka aureni"

"Hadeeza duk abinan da kikeyi wlh karamin mugun tsanarki kike ke baki Isa ki sakani bakin ciki ba kinyi kad'an Kuma baki isa ki rabani da lubna ba insha Allahu mutuwa ce zata rabamu ke din jahila ce dakikiya sai aka ce miki dan kin bada pant da jan baki har dasu tsinken gwaji da hotuna da kika turo zai saka lubna ta Yarda dake har ki hana mu zaman lafiya haha lailai ke din jahila ce dan ita lubna ba dakikiya bace ba duk Wanda yaga abinda kikayi yasan ke din bakisan abinda kike ba wanan tsohon yayi ne tunda har a kasan hoto kince sai kin cusa mata bakin ciki ki nemo wata hanyar Kuma ko mata sun Kare a duniya Hadeeza bazan taba aurenki ba kije ki nemi dan bariki irinki ki aura"

"Haka kace ko"?

Tsaki yaja ya kashe wayar duk sai naji kunya da na????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
damar abinda nayi nama kasa motsi balle na bud'e baki yana gama wayar ya dago da rinannun idonsa ya zuba min Yana "ganin damanki ne a yanzu ki yarda ganin damanki ne Kuma kice karya nakeyi hada baki mukayi da ita"

Daga haka yayi wajen kofa ya bude k'ofar ya fice daga d'akin tare da banko k'ofar da k'arfi

Kamar ba jini a jikina na zube a kasa na dauko wayar tawa daya maka da kasa na duba naga screen din ta fashe amma ba abinda tayi na Kara Shiga watsapp na budo hotunan nayi zooming din hoton da tace a yau suka dauka,na duba zanen shaddar na ga sam ba iri daya bane da Wanda yasa yau lailai Hadeeza Yar iska ce jikina har rawa yake wajen yi mata magana na hau danna Mata zagi da naga ma hannuna rawa yake yak'i bani hadin kai sai na danna mata vn Ina "Shegiya karuwa jahila dakikiya kin dauka dan kin turomin wadanan hotunan zaki cusa min bakin ciki dan kinsa wani ya saka masa pant da jan baki a Aljihu zan yarda dake, Hadeeza kinyi kad'an ko da ubanki kike tsafi wlh baki Isa ki rabani da mijina ba yanda kika gani da mijina dole haka zaki barmu ba yanda zakiyi tsinnaniya mayya tunda har burinki kiga mun samu sabani ni Kuma zan baki mamaki wlh komai zakiyi ba abinda zai saka nayi fada da mijina dan kafin ya had'u dake ba ruwansa,mace da kunya aka santa amma ke kinyi hannun Riga da kunya ke din tsinnaniya ce kin koyawa mijina abinda ba haka ba to bari kiji na fada miki mijina yafi karfinki sai dai ki nemo dan iska irinki ki aura banza karya ballagaza ashawo karuwa da bata da aji ko kad'an ke zaki daura aure da bakin ciki bani ba tunda ni gani da masoyina soyayya kuwa yanzu zamu kafa sabuwa ke kuwa sai dai kiyita Jin labari kina hadiyar yawu tsinnaniyar da bata ramin kanta sai dai tayi ta wani jahila jaka"

Ina gama tura mata naga yayi deliver a k'ok'arin nayi blocking dinta ma naga ta hau online ya nuna min tick din blue na tura mata stickers din dakuwa har da zanyi blocking dinta na fasa dan inaso naga zata min reply ko bazata yi ba.

Na kashe data na mike duk Ina Jin ba dadin abinda nayiwa mahfuz na koma gefen gado na zauna nayi zuru Ina adduar Allah yasa ya dawo d'akin amma shiru nafi minti talatin a zaune banji motsinsa ba kuma sam banaso naje dakinsa ya d'auka wani abu haka na kwanta zuciyata duk ba dadi.

Baccina rabi da rabi sai tsinewa Hadeeza nake na Kuma ringa shan alwashin tura mata aniyarta duk wani bakin mahfuz da fushin da nake dashi sai na Nemi shi sama ko kasa na rasa bansani ba ko dan wayar da yayi da Hadeeza yaci mutuncinta bane ya faranta min rai.


Zan iya cewa banyi wani baccin kirki ba dan duk sai nake ganin zai dawo d'akin kasan raina Kuma Ina ta mamakin yanda ya dau fushi da zuciya tsakani da Allah ai uzuri ya Kamata yamin,tunda shine dai a hoton dole koma wacce tayi abinda nayi,tunda yayi wayar a gabana na gane sharri ne sai ya Kara fahimtar dani komai ya wuce amma shine ya tsiri fushi har da tafiya dakinsa ya kwanta.

Ina jinsa da asuba ya fita massallaci.

Nima tunda na iddar ban koma baccin ba haka na zauna Ina jiran shidda da rabi tayi na fita na dora breakfast wanda duk a jiyan da na dawo ban taba tunanin zan girkin ba kila idan nayi girkin ya sauko daga dokin zuciyar da ya hau.

Kafin na fita kitchen na sheka wanka nayi kwalliya da wani doguwar Rigar roba mai Kama jiki na fita Palo.

Kitchen din dama a Palo yake na dauka zan ganshi a palon sai dai haka nayita zirya daga Palo zuwa kitchen banga alamar zai fito ba har na gama soya dankalin na dafa ruwan tea dan komai akwai na bukata mummy ta siya mana,naga Kuma kamar mahfuz shima ya Kara Mana Koda na gama na ajiye kayan Karin a Palo banga alamar zai fito ba gashi nasan dole zai fita aiki yau tunda ba weekends bane,ba Kuma naso wai naje d'akin yayi tunanin shiri nake nema nafiso ya dawo ya rarrashe ni.

Kukan daddy dana jiyo a daki yasa na koma daki na dauko shi na dawo Palo na zauna na Kara kallon agogo naga bakwai ta wuce har da rabi.

Motsin fitowarsa naji daga dakinsa hakane yasa na zubawa daddy Ido Ina cigaba da shayar dashi.

Kafin ma ya fito daga d'akin kamshin turarensa ya fara iso min ya fito daga d'akin ta gefen idona naga yayi Kamar zai fita ya Kuma nufo wajen da nake zaune ya sunkuyo naji kamshin turarensa na Neman kashe min jiki hakane yasa na dago na kalleshi na dauka tabani zaiyi sai naga kumatun daddy yaja Yana "My boy how was your night"?

Sai na kasa d'auke idona a kansa dan sai naga kamar bleaching ma yayi yayi wani fresh dashi gashi yaci gayu da kananan kaya ga wani gyaran fuska da yayi.

Abinda ya bani mamaki bai ko nuna yasan Ina wajen ba ya gama jagwalgwala kumatun daddy ya mike tsaye naga ya juya zaiyi hanyar waje

Nayi saurin cewa "Ga abincin karyawar ka fa tundazu na gama"

"Kai aikuwa azumi nake na tafi office sai na dawo"
Bai barni nayi magana ba ya fice da sauri

Mamaki ma ya kasheni a zaune har ni zai cewa Yana azumi na gama Shan wahalar girkin ni yayiwa laifi kuma yazo yana fushi sosai naji Raina ya b'aci naji ma haushinsa ya rufeni nidai nasan Mahfuz ba ma'abocin azumin litinin da alhmis bane balle nace azumin litinin da alhamis yake yau kuwa talata bansan azumin da akeyi ran talata ba salon kawai wulakanci dan ya samu ma na dawo mutumin da yake neman kwanciya na taka shi dan na dawo shine yanzu ya samu na dawo zai wulakantani naja dogon tsaki.

Haka nayita tsaki Ina maganar zuci ni kadai buga gidan da ake yasa na ajiye daddy nayi waje Ina mamakin Wanda yake bugawa da safen nan.

Ina bud'ewa naga mmn Iman ce da flask a hannu ga uban ciki ta sakar min murmushi na bata hanya ta shigo tana "Amarya amarya a lailai dole kiyi kyalli Allah yasa dai baa karya gado ba wanan d'aukar wanka haka ai ni na dauka yau ko wajen aikin ma bazai iya zuwa ba"


"Mmn iman muje kiji wulakanci da yamin"

Muna zama na hau bata labarin duk abinda ya faru jiya da yanda mukayi da Hadeeza har da Mahfuz da safen nan

"A gaskiya dole yayi fushi lubna baki kyauta ba kin Kai shi bango dole yayi fushi nifa na dade inaso na fada miki ki daina zagin miji babu kyau kalmomi marasa dadi da kike jifansa dashi sam basu Dace ba,ai a tunani na tunda har Hadeeza ta Sha alwashin hana ki zaman lafiya jiya da ta turo miki ya ci kigane makircinta a yanzu da kika dawo Kamata yayi ki daura damarar kwace mijinki a hannu kowace Yar iska ba iya Hadeeza ba haka ake fama da wasu Yan matan marasa tarbiya da basuda burin daya wuce su hargitsa ma'aurata kin min daidai na zagin da kika yiwa Yar iska yarinya shuuma ce wlh idonta na kanku karki sake ki bari ta sake cin galaba akanki"

"Haba mmn Iman a yanzu duk abinan da yamin na shanye na hakura na dawo dan naga hotonsa nayi fushi da pant sai ya tsiri fushi tsakani da Allah fa laifi yamin tunda sai da ya kirata a waya nasan sharri ta kula masa ai bai dace yayi fushi ba dariya yake so nayi da naga hotonsa da ita a rungume daga Wanda yake mata kiss sai Wanda ya cafo nonon ta wlh da shi yaga hotona Ina yiwa wani kiss saki uku zaimin real shine dai a hoton mmn Iman bazaki gane ba wlh Abinan ba Wanda zan iya mantawa bane Allah sai dai nayi adduar Allah ya mantar dani amma abin da wuya har ya wani cemin azumi yake bayan na gama Shan wuyan girki"

"Tunda Kika yarda Kika dawo dole ki manta komai ki shimfida sabon rayuwa dashi azumi Kuma dole yayi lubna tunda jiya kila ya balain sa rai wanan abu yazo ya faru dole ya dau azumi yau ya dade fa rabonsa da mace tsakani da Allah"

"Hmm ba wani ya dade Kika sani ma ko Yana rage zafin Raina min hankali kawai zaiyi"

"Aaa fa lubna kiringa kyautata Masa zato ki cire zarginsa a ranki kema fa kinyi kewarsa nasan kema a matse kike idan ya dawo ki bashi hakuri kawai ku kashe wa juna kishi kema ga idonki nan fal jarraba"

"Kai mmn Iman wlh ba wani nan magunguna kuka dirka min ai kuka barni da ciwon mara"

"Toh idan ya dawo dai ki bashi hakuri"

"Tabdijam wlh bazan bada wani hakuri ba ni yaka mata ya bawa hakuri"

"Kaga Yar baiwa ke miji na Baki hakuri ma ni nawa mukayi fada dole dai ni zan bada hakurin nan wlh idan Kuma nayi fushi ana kashe arna mun shirya kenan"

"Tab aikuwa nidai bazan bada wani hakuri ba"

"Idan shaawa ya kusa kasheki Kya bashi ai dan naga kamar dai yayi fushin dagaske da bai tab'a yi ba"

Tabe baki nayi Ina tunanin idan ya dawo dai dolensa ya sauko

Hirar da mukayi tayi ya debe min kewa sosai sai wajen daya ta koma gida ba wani aikin da zanyi sai yamma idan zan masa girkin buda baki hakane yasa ina sallar azahar nabi lafiyar gado.

Ban tashi ba sai wajen la'asar nayi wanka na sake yiwa daddy shima naci kwaliyya da wani shadda ta maroun da ya sha stone work har kasa nasan duk fushinsa wuyanta yayi tozali dani.

Abinci kala biyu na masa na bud'e baki biyar da rabi na gama komai na turara ko ina na zauna a Palo na kunna tv Ina kallo

Karfe shidda daidai naji dirin motarsa ba jimawa sai gashi ya shigo palon da sallama na amsa ganin bai kalli Inda nake ba yasa na maida sannu da zuwan da nayi niyyar Masa ya shigo har tsakiyar palon ya ajiye ledojin da ya shigo dasu ya nufi wajen da na kwantar da daddy yana "My boy na dawo"

Yaron da ko wata biyu baiyi ba wai Wasa yake mai Ina satar kallonsa Ina Jin Raina na b'aci da rashin mutunci da yake so yamin

Ganin yayi hanyar dakinsa dan an ma kusa Kiran sallah magriba na daure nace "Ga abincin buda bakin ka nan"

"Ok Tom ngd Allah ya bada lada"

Bai ko kalleni ba balle yaga adon da nayi ya shige dakinsa naji wani abu ya tsayamin a makoshi lailai ma mahfuz uban me na masa da zaiyi fushi dani.

Zuciyata fal da bakin ciki ya sake fitowa da alama wanka yayi ya dauro alwala ya bude ledar daya shigo da ita ya dauki dabino yayi waje.

Nima dakina na shige Ina ta masifa a zuciyata Kamar idan ya dawo na tare shi na Masa magana wani zuciyar nawa na Hanani.


Ina idarwa na koma palo dan so nake naga idan har baici abincina ba wlh bazan sake masa girki ba

Ban dade da Zama ba ya dawo ya nufi kitchen ya dauko plate naga ya bud'e leda ya fito da kankana da lemo nidai Ido na zuba masa sai da ya gama Shan fruit ya jawo flasks din ya zuba abincin kad'an ya tsakura ya ci kad'an ya mike yayi hanyar d'aki ko kallona baiyi ba a fusace na bi bayansa dan nazo wuya.

A tsorace ya juyo dayaga yanda na banko k'ofar cikin hucci nace "Wai Mai kake nufi dani ne kasan baka bukatar dawowa ta Sabida me kasa na dawo"?...


Yau dai nayi muku na yau da gobe

Yauwa duk wacce/Wanda ya hada min documents din novel dina Allah ya Isa ban yafe ba Allah yabi min hakkina iya satar ma a karanta baiyi ba sai an hada min documents Tom wlh ban yafe ba
MG'S SKINCARE

Laifin Dadi qarewarshi,fanfanfan inji Yara,da yarda d Kuma amincin Allah munkawo qarshen promo namu Alhamdulillah munga ruwan jamaa annuna mna qauna,muna godiya maras adadi,Allah yaqaro arziki ninki b ninki,

Tau Bafa waimun tsayabane,yenzuma akasoma inbamu Baku kunyi kyauba me akayi?

Akwaysufa kayan gyaranjiki hajiyata,

Beauty kit 11k
Soap 3k
Student package 7k

Chat:08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call:08062991549

Available in Kaduna and Kano,

We always serve you the bestd'?


*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi*


*Page 41*



Bangane ba mai ya faru Kuma"?


Mahfuz yace Kamar irin bai gane ma mai nake nufi ba

Wani bakin ciki ne ya a Kara rufeni cikin masifa nace "Kasan mai nake nufi sarai taya daga dawowata gidanka zaka fara Jana a kasa kana wulakantani na kwashi awa uku Ina maka girki ka wani ci kad'an ka tashi kasan dama baka bukatar dawowa ta gidanka sabida me ka matsamin na dawo"?

Kansa ya dafe yana "Lubna dan Allah banida karfin fada yanzu ki barni ruwan da na sha ya tsirgamin,taya zan iya cin abinci mai yawa bayan azumi nayi zuwa anjima ai zan Kara ko, komai naki na fada ne wai ke bakisan zaman lafiya kenan"?


Hankalinsa kwance yake min magana

Tsananin bakin ciki ya hanani ma magana na zuba masa Ido Ina kallonsa shi kuwa ya zauna a gefen gado ya dauko wayarsa dake gefen side drawer ya fara latsawa ya bawa banza ajiyata.

"Dole ka wulakantani tunda na dawo gidanka amma inaso kasan ba dole bane zaman idan dai kaga bazaka iya ba sai ka sakeni"

"Allah ya kyauta"

Shine kawai abinda ya furta bai ko dago ma ya kalleni ba

Sosai naji na muzanta har ni mahfuz ya watsar yake wulakani daga dawowa jiya jiyan nan

Na juya a fusace na bar d'akin ban tsaya ma a Palo ba na dauki daddy nayi d'akina

Kamar na fashe dan bakin ciki

Lailai ma mahfuz zan bashi mamaki dan ya samu ma na sauko na dawo gidansa shine zai nemi Jana a kasa toh kuwa zan bashi mamaki har sai ya zo da kansa ya bani hakuri,halan ya manta girman laifin da yamin,a jiya na dawo a jiya tsinaniyar budurwarsa ta turamin hotunan shi da budurwarsa wanda da k'arfi nake yakice hoton a idona duk yana tare dani ya ringa zuwa wajenta Yana watsewa da ita a motarsa dan na nuna fushinsa shine zai fini zuciya har Yama ki kallona.

Tsaki nayita jerawa a kai kai dan har a yanzu Kamata yayi ya bani hakuri bawai ya fini fushi ba.

Koda na iddar da Sallah isha wanka kawai nayi na saka kayan bacci nayi kwanciyata dan nasan idan dai yaga dagaske nayi fushi nasan zai biyoni har d'aki.

Kasa ma bacci nayi nadai ji motsinsa a falo har ma naji yo karar tv.

Har yanzu ma mamakinsa nake,dan na dauka yanda yace yana kewata duk abinda zan masa bazai yi fushi ba zaiyi duk abinda zaiyi dan ya samu kaina,na kankame jikina Ina Jin sanyin dake ratsani har cikin kashina da hakan ya kara sakani Jin kasala da ace nasan abinda zaiyimin kenan da ban yarda na sha magungunan da mummy tayi ta dirka min ba.

Tun Ina zuba ido akan zai shigo naji shiru har Sha dayan dare na mike cikin sand'a dan har lokacin tv a kunne yake sai naji zuciyata na rayamin waya sani ma ko tv kawai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login