Showing 126001 words to 129000 words out of 155577 words

Chapter 43 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

6050

Shige station din lokacin takwas da minti goma Koda muka je mahfuz inina ya tsaya yayi ya kasa magana sai da na fara magana ya karbe tare da tsara musu duk yanda na fada masa ya Kara da a taimaka masa a kamota a mata gargadi Kar ta watsa videos din, ganin bayasan yace nima tana min barazana yasa na karkace nace musu ta turo har gida anyimin duka dan haka abi min hakkina kullum sai tace sai ta kasheni ta waya

Mahfuz dai bace komai ba Suka gama d'aukar statement dinmu Suka tambayi mahfuz a inda zaa iya samun Hadeeza yanzu.

Ya fada musu tace tana hotel sunyi ma zasu hadu karfe tara.

Ganin a motar mu muka zo yasa suka bamu mata biyu Yan sanda da namiji guda daya,muna tafe suna bin motar mu a baya har muka iso rayyan hotel din ina cikin motar a zaune motar yan sandan Kuma na nesa damu, Yan sandan ne Suka tsarawa Mahfuz ya shiga ya fito musu da Hadeeza.

Hakan yasa Mahfuz yayi cikin hotel din Yana Kiran Hadeeza a waya.

Ni Kuma na fito daga motar na nufi wajen da Yan sanda sukayi parking Mata Yan sandan duk sun fito daga motar namijin ne a mazauni driver

Wajen wacce tafi sakin fuskar naje nayi kasa da murya Ina su taimaka min su ci min uban Hadeeza su rama min dukan da tamin ko nawane Zan Basu"

Washe baki naga tayi ta matsa kusa da dayar inaga dai fada mata tayi hakan yasa ta matso kusa dani tana "cash zan Basu ko transfer"

Nace ba kudi jikina zan musu transfer fatana su ci min uban Hadeeza kawai shine burina.

A wajensu na tsaya dan banaso ma Hadeeza idan ta fito tagani.
Sai da muka kusa minti goma Sha biyar a tsaye kafin na hango mahfuz ya fito jere da Hadeeza

Ta saka bakar doguwar riga sam bata hango mu ba.

Daga nesa dai kamar masifa take sai tafa hannuwa take, adaidai lokacin da mata Yan sandan Suka tambayeni ko itace tare da mahfuz nace musu ee

Basuyi wata wata ba Suka nufi wajensu na bisu a baya zuciyata na suya da ganin ma Hadeeza da mahfuz din a tsaye yanzu fa sun san junansu ko na hau tambayar kaina yanda Mahfuz yake kwanciya dani haka ya kwanta da Hadeeza"

Sai da muka kusa Isa wajensu ta ankara da yan sandan naji kamar na dake tsalle na shaketa a daidai lokacin da ta kalli mahfuz idonta warwaje tana "Ni ka kirawa Yan sanda mahfuz"?

"Tunda kin ki rabuwa dani cikin sauki inaga hukuma ne zasu iya sawa ki rabu dani cikin sauki"

"Ni zaka yaudara"?

Madam shut up karki Kara magana duk abinda kikace anan zamuyi amfani dashi a kotu

Cewar gajeriyar Yar sandan da ta kamo hannun Hadeeza da hawaye ya hau zubo mata ta kalli mahfuz ta kalleni doguwar kuwa ta karbe wayar Hadeeza tana ta wuce su tafi

Ni kuwa wani irin kallon tsana nake mata Ina Jin dama su bani dama na harbeta kawai na huta.

Keyarta suka tisa har motarsu mu kuwa muka hau namu motar Muna binsu a baya.

Mahfuz na "Wlh tunanin kai karar Hadeeza bai tab'a zuwar min ba sai da kika kawo shawarar mu kai ta kila da duk haka bata faru ba"


"Mtsss naja dogon tsaki dan so nake na gama da babin Hadeeza tukunna kafin na jiyo kansa.

Muna isa station muka Shiga gabad'aya aka karanto mata karar da muka shigar akanta.

Ba alamar tsoro a idonta ga mamakina sai ta musanta duk zargin da ake mata ta Kara da ba wani video data ce zata watsa sharri muke mata ita bama tasani ba


Mahfuz ya fusata ya dauko wayarsa ya matsa kusa da dan sandan Yana ga videos din nan ga Kuma maganar da takeyi akasa,


Tana k'ok'arin Magana mace Yar sandan ta kwada mata mari tana "da alama kanki na rawa dole mu koya miki hankali har mu zaki rainawa hankali"

Basu kara bata damar magana ba sukayi cell da ita

Mahfuz Yana ganin an shige da ita yace "Nidai ku taimaka min ku tilasta mata ta goge videos dinan shuuma ce wlh ku Kuma yimin tsakani da ita"

Gargadi kawai nakeso ayi mata idan har duk ta goge videos din kun ja mata kunne akan ko a hanya tagani Kar ta sake ma tamin magana burina dama shine ta rabu dani gabad'aya"


Ce masa sukayi Kar ya damu yaje kawai gobe ya dawo dan ya zama dole su ta kwana.


Nidai sai da nasan yanda na ja gajeriyar Yar sandan gefe na tura mata Dubu biyar akan ta cimun uban Hadeeza.



Koda muka baro station gida muka koma da isar mu na Shiga gidan mmn Iman na karbo daddy duk yanda taso taji Inda naje ban fada mata ba akan dole ta rabu dani.

A Palo na tarar da mahfuz ban kalli Inda yake ba na shige d'akina na zauna a gefen gado daddy na dora a cinyata dan na shayar dashi,Ina ciro abincinsa mahfuz ya dago labulen d'akin Muka hada ido fuskata a mugun hade nace "Mahfuz ka fitar mun a daki Kar ka d'auka wai sabida kai nayi abinda nayi wlh tallahi sabida yarana ne kaji na rantse ma ka fitar min daga d'akina banaso na budu idona na ganka"



"Lubna abinda ya faru ya riga da ya wuce dan Allah kiyi hakuri"

"Ka fitaaaaa"

Da sauri ya saki labulen yayi waje sabida ihun da na saka.

A ranar wuni nayi a dakina ban ko fito waje ba ko yunwa banji ba zuciyata cike da bakin ciki,duk abinda mahfuz yamin tundaga lokacin da nake da ciki da yake waya da Hadeeza zuwa lokacin da ya kawomin Hadeeza gida har minjibir da ya kaita ya hau dawomin daki daki, Ina jin zuciyata namin nauyi da bakar tsanar mahfuz da dazu cikin tashin hankali naga videos din da Hadeeza ta tura masa, take na Tuno tace ta sake turamin wasu.

A haukace na dauko wayata dan naga videon duk da nasan ba abinda hakan zai haddasa min sai tashin hankali amma zuciyata ta ringa ingizani da na duba watsapp naga video da ta turomin.

Sakwani na gama shigowa naga ta turomin video mai nauyi wajen mb 30 minti kuma wajen goma.

Tun kafin ya gama buduwa na hau zubar kwalla nayi matukar nadamar bud'e videon da Hadeeza ta Tiromin dan ashe dazu banga komai ba,naga tashin hankalin da ba kowa ne zai iya jure yaga mijinsa tsirara iya surfa wata har da ihunsa bata yanke jiki ta Fadi ba,Wai Wai Wai nakeji hoto nagani zuciyata ta kusa bugawa na kusa zaucewa balle a yanzu da nake ganin videon su turmi da tabarya dan ko a gidana dana kamasu ba turmi da tabarya na gansu ba a rungume suke da juna da sai da nayi da kyar na daina tuno yanda na gansu.

Wayar subucewa yayi a hannuna na hau hakki Ina jin numfashi na min wahalar shak'a "wayyo baby kinfi lubna dadi"

Kawai ke amsa kuwa a kunne na.

Sosai naji d'akin na juyamin video nan na minti goma na replaying a kwakwalwata.

Tabbas Hadeeza tamin register a kwakwalwarta da bana Jin zai gogu nayi matukar nadama kallon videon nan.

Bana gani sosai ma Ina hada hanya na fita Palo da wayar a hannuna ban fita daga watsapp din ba a Palo na tarar dashi a zaune akan sallaya da carbi a hannunsa yana ja yanda ya gani yasa ya mik'e da sauri

Na tsaya a gabansa Ina "Kaganka mahfuz tsirara hannunka a kugun Hadeeza kana bugu Kamar ka samu matarka,ka tsallakeni Mahfuz ka tafi kayi tumbur ka rataya kafar ta a sama mahfuz,kace tafini dadi"

Na dartse lebbena da k'arfi jikina na wani irin rawa kirjina na sama da kasa

Mahfuz ya zube a Kan gwiwarsa "Lubna mai yasa kika kalli videon nan innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

"Tur da halinka mahfuz tir kasan ta fini Dadi Mai yasa baka aurota ba mai yasa ka dawo dani mahfuz dama abinda kayi kenan dubeka fa mahfuz zindir , mahfuz Kaine kaddarata, mahfuz abinan daka min Allah ya Isa ban yafe maka ba wlh bazan tab'a yafe ma ba"

Na juya jiri na dibana bansan ya akayi ba sai ji nayi ya fusge wayar daga hannuna ya dokata da kasa a haukace ya fara magana Kamar zaiyi kuka Yana "Waye ya aikeki kiga videon nan Lubna Mai yasa a rayuwarki kikesan tashin hankali nace Miki nayi nadamar abinda nayi na tuba bazan Kara kusantar zina ba so kike sai Kinga na Fadi na mutu tukunna hankalinki zai kwanta da ace zan iya maida hannun agogo baya da na mayar na goge wanan abin lubna ni kaina idan na tuna abinda nayi tsanar kaina nakeyi abinan ya dade da faruwa ya wuce Kuma bansan mai yasa kika dawo dashi yanzu ba haba lubna kimin adalci mana


"A yanzu a turo maka video nida Abdul abokinka zigidir muna abinda kayi da Hadeeza mahfuz ya zakaji a ranka zaka iya min adalci idan kagani"?

"Inaso kasan wani abu, na jure na farko na jure na biyu wanan din ba lailai na iya jurewa ba idan har bazan iya ba Aurena da Kai yazo karshe mahfuz..& ..


Tom mun kusa dai zuwa karshen insha Allahu
Ina mata y'an kwalisa ma'abuta gyaran jiki macce Mai gyara daban take ga zuciya mijinta muna da kayan mata da supplement na gyaran jiki kala muna hadin amare da uwargida Dana masu jego muna da set Mai hade da kaza Mai kwai 3 da cicicibe da kifi da galam 3 na tsime da Burkett din gumba 2 da garuruka da zuma wanna set na maccen da ta isa ne muna hadin shi 20k akwai karami set na 15k akwai na 10k akwai na 5k

Muna da magunguna masu jawo hankali maigida da kara martaba

Fanin supplement ma ba'a bar mmn mujaheed abaya ba tana da nagyaran fata da kara haske akwai na gyaran brst na gyaran hip na kiba
Kamar su Lady capsule 4500
Sugar wanita 3500
Glutathione 3500
Vitamin e 3k
Gluta white 3500
Royal jelly 3500
Apetamin 3k
Frozen collagen 3500
Da sauran su insha Allah duk Wani supplement Zaki same su ga mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa

Y'ar uwa kiyi bayani abaki dai2 da type dinki indai sanyi ki Hana Miki jindadin aure ku budewa GABA ku rashin niima to kedai yima mmn mujaheed bayani zata baki dai2 Dake

Mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa
08066726866

Kayan mu iya kudinka iya shagalin kane

*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi*


*Page 46*

Mahfuz
Bai iya mata magana ba ya bita da ido har ta shige daki,ya dafe kansa dayaji Yana neman rabewa gida biyu baisan ya lubna takeso yayi ba da ace yasan zai shiga irin wanan tashin hankalin da bai tab'a kusanta kansa da aikata zina ba,Jin dadin dan lokaci ya sa Yana neman zaucewa,Yana murna ya fara samun kwanciyar hankali suna zamansu lafiya da lubna Hadeeza ta kara dawo masa rayuwa har yanzu yana mamakin yanda akayi ta d'auki videos dinsu bai tab'a sanin Hadeeza tarko ta danna masa ba ba, da ace yasan zata masa haka da shima bai goge nata da guntun gatarinka ya tura Masa ba da shima ce mata zaiyi zai yada nata videos din,runtse idonsa yayi Yana tuno videos din da shima sam baisan yayi wanan sumbatun har Yana tafi Lubna dadi,baisan ya furta haka ba, Hadeeza ta cuce Shi bazai taba yafe mata idan lubna ta canza masa ba.

Ya zama dolensa yasa Yan sandan su matsa Hadeeza ta goge duk videos din har da wayanda yasan tayi ajiyarsu a wani wajen Dan iya lubna ce ta gani yaji kamar ya mutu sabida tashin hankali Ina ga an watsa mutane sun gani,a yanzu burinsa lubna ta sauko da wuri daga yanda bata danna masa Ashar ta masa hauka ba yasa ya danji sanyi a zuciyarsa kila bazatayi dogon fushi ba zata iya saukowa da wuri tunda ba wai sabon video bane ta Kuma San ya rabu da Hadeeza.

Ko waje a ranar bai leka ba, lubna Kuma na d'aki sau biyu Yana shiga tana korosa balle ya samu ya rarrasheta.

Tashin hankalinsa yanda Yana Palo yaringa Jin sheshekar kukanta hakin da takeyi yafi komai daga masa hankali ya rasa ya zaiyi haka ya zauna a bakin k'ofar dakinta daga shi har ita ba wanda ya nemi abinci.

Bacci baiga idonsa ba kamar dai yanda yasan lubna batayi bacci ba.

Sai addua yake Allah ya sauko masa da zuciyar lubna ya bata ikon manta abinda ta gani,dan yasan shima yayi wa kansa karya lubna bazata manta abinda tagani ba.

Sallah asuba ma a gida yayi dan gani yake idan ya fita massallaci kafin ya dawo wani masifar zai Kara faruwa dan duk abinda ke faruwa sai ya tafi massallaci ya dawo yake zuwa ya tarar da tashin hankali.

Washegari duk yanda yaso ya shawo Kan lubna tama saurareshi k'i tayi dan a karshe rantse masa tayi akan idan har ya Kara shigo mata d'aki sai ta hada kayanta ta tafi,hankalinsa ya tashi da yanda ta zabge lokaci guda Kamar wacce tayi amai da gudawa idonta ya Kara firfitowa waje wani irin zabura ma take idan ta ganshi, shi din ne bataso ta gani tace ko muryarsa bataso taji a tsaye daga bakin k'ofar yace ya batun komawa police station din tunda sunyi zasu koma washegari.

Lubna bata kulashi ba illa maida idonta da tayi ta rufe haka ya shirya ya nufi station din shi kadai kafin ya karasa ya kira Abdul a waya.

Ko da ya daga wayar kwashe komai yayi ya fada masa na abinda ya faru.

Abdul yayi shiru na tsawon mintuna kafin yace "Da ace ka sanar da ita da wuri da duk haka bata faru ba da ace kabi shawarata da duk baka tsinci kanka a cikin wanan kwamacalar ba, toh tunda ta riga da ta gani shikenan sai ka dage da Addu'a Allah ya daidaita ku dan wlh Mahfuz Nagaji da wanan case din naku da baya karewa daga wanan sai wanan naga k'ok'arinta ma da ta shige ma gaba kuka Kai Hadeeza station din abinda ya Kamata ace tuni munyi tunani yi kenan amma tunda har kaga bata tafi gida ba inaga zata sauko insha Allahu amma dai karka matsa mata ka dan bata space komai yayi sanyi a hankali idan ta fara saukowa sai ka Kara bata hakuri a yanzu zaka Kara samun kwanciyar hankali batare da kayi fargabar akwai abinda zai biyo baya ba tunda hukuma ta Shiga tsakaninka da Hadeeza"

Shawarari Abdul yayi ta basa har ya isa station din da zuwansa aka Kai shi office din Wanda yake in charge sai da ya duba statement din daya shigar yasa wani dan sanda ya Kira Masa Hadeeza.

Baifi minti biyar da fita ba sai ga dan sandan ya dawo Hadeeza biye dashi a baya,gefen fuskarta ya dan kumbura wani mugun kallo tabi mahfuz dashi kafin ta samu waje ta zauna mahfuz shima ya ringa binta da mugun kallo duk tashin hankalin nan ita ta jefa shi a ciki.

Sai da dan sandan ya Kara karanto mata karar ta da aka shigar yace ta yarda ko har yanzu karyar ake mata tace ta yarda anan aka tambayeta inda ta ajiye videos din da hotuna tace Yana wayarta take aka bata umarni duk ta goge da taimakon dan sandan dake tsaye akanta da mahfuz ta goge duka videos din da hotuna har da hotunan da mahfuz baisan ta daukesu ba duk sai da ta goge Mahfuz ya koma ya zauna Yana fadawa dan sandan Hadeeza nada copy din videos din a wani wajen ta fada masa da bakinta,Koda aka tambayeta cewa tayi ita barazana tayi Masa iya videos din kenan a wayarta.

Gargadi aka yi mata Mai zafi bayan ta saka hannu akan duk ta yarda da hukuncin da zaa mata idan har video ya fita ko hoto, ta Kuma yi alkawari ta rabu da mahfuz har abada kamar yanda Mahfuz ya roki yan sandan su masa.

Hadeeza sai a lokacin tafashe da wani irin kuka tana kallon mahfuz da duk ta dora buri a akan aurensa ta Sha bak'ar wahala duk akansa taci bakar duka a hannun matarsa har yanzu tsakiyar kanta akwai wajen da ba gashi,sa rai da zai aureta yasa iyayen ta suka ringa murna zata samu tayi aure tana ji tana gani Mahfuz ya fasa aurenta Iyayenta suka yafeta a cikin yayansu akan dole sai ta kawo miji tayi aure zasu yafe Mata,tunda take bata tab'a nadamar bariki ba sai da mahfuz ya fara nuna mata kiyaya,daga lokacin data fara gane mahfuz ba lailai ya aureta ba ta fara k'ok'arin raba kafa dan ta samu koma waye ta aura dan ita Kanta a yanzu sai taji tana shaawar aure da taji labarin duka kanenta uku sunyi Aure suna gidajen mazajensu tanaso tayi aure ta haihu itama a shekarun baya idan akace mata zata wulakanta kanta haka tazo tana Neman miji Ido rufe karyatawa zatayi,dan a baya maza mugun rububinta suke har da masu kuka akanta,surar da Allah ya mata yasa maza da yawa sun kwadaitu da san aurenta manyan masu kudi a wanan lokacin,ita kuwa ganin Allah ya bata surar da maza ke so tak'i amfani da damarta ta bawa mutanen banza fuska suka hau kashe mata kudi suna moreta da haka duk na auren suka koma neman jikinta a tunanin ta idan ta gama tara kudi mai yawa sai ta samu miji tayi aurenta batasan dama sau daya yake zuwa wa mutum ba yau duk wayanda ma Suka nemetan duk sun daina yayinta sun juya mata baya kamar wacce akayi wa asirin bakin jini, mahfuz da batayi muamalla banza dashi ba ta makalewa dan tasan baisan halinta ba,Kuma ya kaunaceta a baya ta d'auka zata iya Jan hankalinsa ya aureta sai gashi a san ta mallakeshi ta sakar masa jikinta a gidansa ya nemeta ta d'auka hakan da tayi zai saka ya Kara kaunarta sabida ba karamin gyara take yiwa kanta ba tasan karyane namiji ya nemeta bai haukace a kanta ba sai gashi hakan ma kwokwanto ya dasawa mahfuz a kanta,baisan wane irin so yake yiwa Lubna ba ta d'auka zata iya rabasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login