Showing 24001 words to 27000 words out of 155577 words

Chapter 9 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

2734

ciki ta zauna a dogon kujera tana kalle kalle nima na zauna a kujera mai kallonta Ina "kefa wani zubin kanki ba dadi Mai kike dubawa ne"

"Mai nake dubawa kuwa so nake na tabbatar da ba kowa a gidan kafin nayi magana duk da Naga fitar mahfuz da bakuwarki"

" Ba kowa dagani sai Mimi kin samo mai zafi kenan"?

Nace Ina maida hankalina gabadaya kanta dan Naga alamar da magana tazo Mai mahimmanci

"Eee da magana nazo Kam amma nariga da nasan halinki gajen hakuri baki iya bin komai a hankali ba"

Mik'ewa nayi da sauri na koma gefenta na zauna Ina "Mai ya faru mmn Iman bani labari"

"Wai ya kuke da bakuwar nan da tazo jiya"?


Yamutsa fuska nayi Ina "Wai Ummi"?

"Eee"

"Ba dangi iya babu na baba Ina Abokin Mahfuz Abdul da nake dan baki labarinsa Yana yawan yi Mana aike har kike cewa idan kina da kanwa da kin bashi"

"Eee na tuna shi"


"Toh yarinyar yayarsa ce suna zaune a Lagos tazo nan wani program ne na sati daya ko kwana goma yace ne jiya dai da kansa ya kawota,lafiya kuwa kike tambayeni"?

Ajiyar zuciya ta sauke tana "Ni yarinya Sam ban yarda da ita bane naga tana ta Abu kamar mara gaskiya,kinsan jiya nan Ina zaune wlh satar kallonta kawai nake ni a idona ma sai naga kamar kallon banza take miki kasa kasa"

Dariya na kwashe dashi Ina "Kai mmn Iman abin naki har da sharri yarinya da ko kallona bata iya yi ga kunya"

"Kefa dadina dake hauka wlh Ina miki maganar serious shi Abdul din duk wayanda ya sani anan ga gidansu mahfuz Mai yasa bazai kaita can ba sai nan, Taya zaa kawo Miki tsalleliyar budurwa irin wanan haba mana"

"Wani kusancin ai yafi wani mmn Iman shiyasa ya kawota nan Allah sarki kawata tsoro kike zaa kwace mun miji ko"

Na kyalkyale da dariya mmn Iman ta zuba tagumi tana kallona

"Kwantar da hankalinki ba Mai kwace min miji mahfuz Zan iya rantse Miki ba lailai yasan kamaninta ba dan ko kallonta bayayi,itama ba lailai tasan kamaninsa ba dan tana ganinsa take sunkuyar da Kai"

"Tom ai shikenan amma nidai ban yarda da ita ba wlh masu shiru shiru da saka hijabin nan wlh munafikai ne,a idona jiya ta Miki kallon banza ke Kuma ga saurin sakin jikin balai name kike wani janta da hira"

"Kai mmn Iman bakonka annabinka so kike na hade rai,nifa kinsan ban iya wulakanci ba"

Mmn Iman shiru tayi dan ba iya maganar da ya shigo da ita kenan ba,jiya taji mahfuz nata waya a k'ofar gidan ta har makalewa tayi a jikin kofa dan taji Mai yake cewa soyayya yake zubawa a waya da wata taso ta fadawa lubna ta saka mishi ido amma tuna haukar data Mata kwanaki yasa ta hakura"

Maganar lubna ya katse Mata tunanin da take

"Mmn Iman mun zama yan gayu fa jiya Kinga siyayyar da Mahfuz yayo Mana kuwa zomuje kitchen kigani"

Na jawo hannunta mukayi kitchen din Ina bata labarin abubuwan da mahfuz ya siyo Mana jiya.

A bakin kitchen ta tsaya na hau nuna Mata ta ringa gyada Kai dan ita dama mijinta na siyo mata nice dai bakuwa da aka siyomin a Karon farko.

"Aaa lailai kam kun zama Yan gayu kin huta da siyan kanana Yan sachet nidai ko dan bakuwar aka muku siyayya haka sabida Kar ta Raina ku"?

"Ko daya fa tazo dai a daidai ne wani kudi suka samu yayi Mana siyayyan,dazun Nan yake cemin ya bada kudin ragon layya,yau saura kwana biyar fa Mai da me ya Kamata muyi?

"Mai kuwa zamuyi daya wuce ayi yanka mu soya ban karya ba mallama zubo Mana dankalin muci"

Ta koma Palon na juyo dankalin a plate da kwai flask din tea din na Palo da bredi Muka fara ci

"Kiringa Jan class dinki lubna ki daina sakar wa wanan bakuwar taki fuska kina zuba a gabanta haba jiya kin bani haushi wlh banda kin dage da a shawarce kin yiwa mahfuz magana ta koma gidansu wlh tunda akwai Yan mata acan itama sai tafi sakewa"

Mmn Iman nifa haka nake wlh ba sakin baki ne dani ba,ni ban iya wulakanci ba Sam,idan taga bana Mata magana ko bana Mata hira ai sai taga dan tazo gidana cin arzikine kinsan Kuma haka ba dadi"


"Hakane Kuma toh ki ringa ragewa"

Insha Allahu Koda muka ci abinci hirar muka cigaba da yi ta tayani yiwa Mimi wanka kafin ta tafi.

Tana tafiya Nima nayi wanka Yau kwalliya da soyaya nake ji dan dazu mahfuz yamin kyau.

Kwalliya naci da sabuwar atamfa a irin dinkin da mummy tamin dark purple ce da zanen yellow ta balain yimin kyau,ni kaina na kasa d'auke idona daga Kan mudubin.

Shayar wa da nake yasa kirjina ya ciciko ya fito har ta saman rigar dinkin yamun das a ciki,banida burin daya wuce mahfuz yaga kwalliyar nan.

Mimi itama purple din kayan kanti na saka Mata wayata na dauko na kira mahfuz a waya bugu daya ya d'auka

Yana "Madam yanzu nake Shirin kiranki naji lafiyarku"

Wal nayi ido kamar yana gabana nace "idan ba abinda kake yi ka kunna data muyi video call"

"Angama"

Ya katse wayar Ina kunna data kiransa na shigowa

Ina dagawa na sakar Masa murmushi tare da bankaro kirjina

Ido ya zuba min sai daya dade baiyi magana ba kafin yace "hmm kin kirani ne dan kawai ki tsokane ni ko?, zan kamaki ne ai"

Yace Yana tauna lebbe na Masa gwallo "Ina bakace nayi kyau ba"?

"Sai na dawo zakisan kinyi kyau ko bakiyi kyau ba ke kadai ce a gidan"?


"Eee wlh ni kadai ce ummi bata dawo ba so nake ma yanzu na tashi na dora abincin rana sabida ita amma idan tani ne cornflaskes Zan Sha"

Tab'e baki yayi bai ce komai ba nace "Ko na dafa har da Kai na Aiko maka dashi"?

"No ba sai kinyi dani ba karki wahalar da kanki abincin ranar ma karki wahalar da kanki wani dafa Mata idan ta dawo kice ta Shiga kitchen din ta dafa abinda take so da kanta ba yanda zaayi wata gardiya tazo ta samin mata wahala"

Abu kad'an ke Sakani dariya gardiyar da yace yasa nayi ta dariya har cikina na neman kullewa ganin zai kashe wayar nace "bakuwa ce fa bai dace nasa ta aiki ba"

"Kika dafa Mata Abu ban yafe ba kibari ta dawo tayi kayanta ke ai Yar aiki ma aka kawo miki har girkin Daren ma ki bata tayi"

"Lalalala Haram wata tayiwa mijina girki ni zan ma girki da kaina"

"Dariya yasa Yana to ayi mana mai dadi Zan aiko da kayan ciki anjima a dan yi Mana ferfesu"

"Waw abban Mahfuz kudi Wai ka samu haka kasan kuwa inata shaawar ferfesun kayan cikin nan bana so na maka maganar ne bansani ba ko bakada kudi"

"Da kin gayamin ai tunda na Sunan soyewa akayi karki damu Zan aiko anjima bari nayi wani aiki ya sakar min kiss ta wayar nima na mayar Masa ya katse wayar.

Bai sabar mun da haka ba hakane yasa na kasance cikin tsananin farinciki Ina adduar Allah ya Kara buda Masa inasan irin rayuwar nan dama ne bansamu ba.

Naso nayi girkin amma sabida mahfuz ya hana ni na hakura idan ta dawo nace ta girka abinda take so din.

Bacci bacci na fara ji na kwanta a doguwar kujera Mimi bata da rigima ko kad'an ba karamin abu ke sata kuka ba.

Baccina ya fara nisa naji an kwankwasa k'ofa na Mike na kalli agogo karfe daya da rabi.

Ina bud'ewa naga Ummi ce da fuskarta ke d'auke da murmushi nan da nan ya dishe ta daskare waje daya tana kallona ni na dauka ma wani abin ne na juya dama da haguna na dawo da kallona kanta Ina "Ummi lafiya kuwa"?

Nidai a idona sai naga kamar murmushin yake tayi idonta har ya canza kala

"Sannu da gida Aunty kinyi kyau"

"Anya kalau kike kuwa ummi na ganki wani iri ko duk gajiyar ce"?

Gyada min kai tayi a daidai lokacin da ta shigo tana "bana dan Jin dadi ne wlh"

"Allah sarki sannu inaga gajiya ce ki watsa ruwa ko zakiji dadin jikinki Kinga ma ban yi girki ba dan bansani ba ko Zan girka abinda bakya so nace bari ki dawo ki dafa abinda kikeso da kanki"

"Toh Aunty ngd bari na watsa ruwan"

Ta bude d'akin tsakar gidan ta shige.

Na koma Palo na zauna na kunna tv na kai tashar Bollywood Ina cikin kallon aka Kara buga kofa naje na bud'e almajirin mmn Iman ne da kula a hannunsa.

Karbe kular nayi nace ya mata godiya na koma ciki.

Ina bud'ewa naga danwake ne ya sha hadi har da dafaffen kwai gashi da manja tuni yawuna ya tsinke na je kitchen na wanko hannuna har Zan fara ci na ga dacewar yiwa ummi tayi kila tana cin Dan wake.

Labulen d'akin na daga da sallama tana waya kasa kasa shigowata yasa ta katse wayar da sauri,nidai a idona Kamar akwai abinda ke damunta duk sai naji ba dadi a yanda na ganta.

"Ummi dan wake aka aikomin dashi bansani ba ko kinaci nace bari na miki tayi"

"Wlh aunty ban fiye san dan wake ba ngd sosai

"Ummi kodai na kawo miki Panadol ki Sha ne"?

"Aaa wlh aunty gajiya ce kawai da yunwa yanzu zan fito na dafa ko indomie ne"

"Toh sai kin fito"

Na juya na koma palo na zauna na fara cin danwake Ina korawa da exotic din mahfuz ya siyo mana jiya saura kiris na cinye duka sabida dadin daya min.

Da sallama ta shigo palon na amsa Ina kallon doguwar rigar da ta saka Mai balain kyau yellow ta yafa mayafinsa.

"Bari na dafa indomie Aunty"

"Akwai komai mai kike bukata a kitchen din"

Ta amsa da toh ta shige na cigaba da kallona Ina hararo doguwar rigarta a jikina yamin kyau inama Ina da kudi na siyi irinsa Ina Kuma mamakin Inda ta ajiye hijabin nata,ko saka hijabin dama na bakunta ne.

Ta dan jima a Kitchen din kafin ta fito da plate a hannunta sai pure water da ta d'auko da daya hannun har zata wuce nace "kiyi zamanki anan Mana kici kya shige daki ke kadai ki zauna"

Murmushi tayi ta dawo ta zauna a kasan kafet ta tankwashe kafafunta ta dago tana "Aunty kizo muci"

"Kai cikina a cike yake wlh"

Na saci kallon indomie da ke ta zuba kamshin sardine lailai da alama ummi Yar hutu ce da mahfuz bai siyo kifin ba da kila sai dai ta siyo kifin da kudinta,a Raina na ayyana kila ta d'auka haka muke da kayan a ajiye.

Tana cin abinci lokaci lokaci muna hada Ido sai muyi wa juna murmushi,bakina ma nauyi yamin a San na dau shawarar mmn Iman Kar na ringa zuba kamar yanda tace amma so nake kawai muyi Hirar.

Sai data gama cinye indomie ta kai plate din kitchen ta dawo ta zauna.

A daidai lokacin da wayata ta fara ringing ganin mahfuz ne yasa na d'auka cikin murmushi Ina "Abban mimina"

"Madam na aiko yanzu zaa kawo kayan cikin"

"Tom sai an kawo ya aikin"

"Alhamdulillah Ina mimina"?

"gata idonta biyu kaci abinci"?

"Aa banci ba sai na dawo zanci abincin Mai numfashi da Mara numfashi tunda har Kika tsokano ni"

"Lalala badani ba ban shirya yiwa Mimi kanwa ba"

"Zaki shiryeni ki tanadeni mallama"

Ya katse wayar na sauke wayar Ina dariya na kallo wajen da ummi ke zaune naga ta zuba min Ido muna hada Ido ta d'auke da sauri.

Bance Mata komai ba na ajiye wayar nima Ina satar kallonta tana ta cizar yatsarta.


Tuna ban gama Shan tsumin da mmn Iman ta kawomin ba yasa na m'ike naje kitchen na d'auko na dawo na zauna na bud'e ta dago ta kalleni ta sakar min murmushi Nima na sakar Mata na Kai gorar bakina.

Wani daci naji ya gauraye min baki na furzar da tsumin da sauri Ina "Subhanallahi"

"Lafiya kuwa Aunty"?

Ban iya bata amsa ba na cigaba da goge bakina dan daci sosai.

Sai da na gama nace "wlh daci ne da tsumin nan sosai ke kinji dacinsa"

Bata ce komai ba tamin murmushi na fara mita Ina bari na gama aikina na Shiga gidan mmn Iman na fada Mata.

Ba'a fi minti goma ba sai ga Wanda mahfuz ya aiko ya kawo kayan cikin.

Ummi ce ta bud'e masa kofa ta Kuma karbo ta kawomin nace ta Kai kitchen karfe hudu zan shiga kitchen,Koda ta Kai banga ta fito ba sai buruntun ta kawai na ringaji a kitchen banaso nabi bayanta ta d'auka ko yarda ne banyi da ita ba hakane yasa na cigaba da Zama amma hankalina na kanta.

Bayan Yan mintina sai gashi ta fito tana "tayaki dorawa nayi Aunty na dauraya kwanun da naci abinci dashi

"Allah sarki na kuwa gode ummi"

Har a raina naji dadi bata da san jiki Sam.

Koda na Mik'e dan na Shiga kitchen din tashi tayi ta bini Ina tayi zamanta ba sai ta tayani ba amma ta dage sai ta tayani a dole na kyalleta muka yi fried rice na hada coslow.

Ga ferfesun kayan cikin shima yayi dadi sosai.

Sai da muka gyara kitchen din.

Muka fito tayi tsakar gidan ni Kuma na fara hada ruwan da zanyi wa mimi wankan yamma.

Tun jiya kamar jinin ya d'auke duk da Wasa yake min inaga anjima nayi wankan tsarkin amma ban shirya daukan wani cikin ba banaso mahfuz ya tabani har sai nayi tsarin iyali.

Ban Kara Jin motsinta ba har nima nayi wankar yau shigar kananan Kaya nake ji.

Hakane yasa nasaka Riga da wando maroun yayi balain min kyau banida wani tsayin gashi sai cika na gyara gashin nayi parking na Kara gyara ko'ina na turara jikina da turare na kame a Palo.

Kamar zan leka ummin Kuma na fasa dan bana so na Kuma ringa shige Mata tunda nice matar gidan.

Gab da magriba mahfuz ya dawo.

Sai daya shigo har palon naje na rungume shi dak'yar na kwace bakina daga nasa nayi baya yayo kaina Yana "Baki Isa bafa Ina zaune Kika tsokano ni"

Dariya na ringa yi sabida zagaye kujerun Palon mukayi tayi,dana ga ya kusa kamani na fita waje da gudu a daidai lokacin daya damkoni jikinsa Yana "Wa na Kama"

Karar faduwar bokitin da muka ji yasa mukayi firgigit muka kallo wajen da muka ji karar Ummi ce a tsaye ta sunkuyar da Kai jikinta na dan rawa da alama ruwa zata Kai bandakin rigar dazu ce dai a jikinta bata cire ba.

Mahfuz cikani yayi da sauri ya koma ciki.
Na nufi wajen ummi Ina "garin yaya bokitin ya Fadi"

Bata dago ba tace "wlh subuce min yayi"

"Gashi rigar taki kuwa ta jike"

"Ee dama wanka zanyi Bari na canzo ta dago ta kalleni.

Yanda take kallona daga sama har kasa yasa nace "Yadai"

"Kinyi kyau sosai Aunty"
Cikin murmushi nace "Kina san fasa min Kai ummi jeki yi wankanki bari nayi sallah Nima.

Na juya na shige palon na barta a tsaye tana kallona

Nima ko bata fadamin ba nasan nayi kyau inaso ace min nayi kyau Dadi nakeji, idan har mace Yar uwata zata ce nayi kyau inaga mijina.

Ina shiga d'akin mahfuz ya fito daga bandaki ya canza kayan jikinsa zuwa jallabiya ruwan kasa Mai zip a gaba.

Ya dau carbinsa yayi waje.

Bai dawo cikin gidan ba sai da aka iddar da Sallah Isha

Yana shigowa na jera Mana abinci a tsakiyar kafet na zubawa ummi na dora Mata akan karamin farantin na d'auka na Kai Mata har daki.

Koda na Shiga akan katifa na ganta a zaune ta saka wani vest ja Rabin na fulaninta a waje sai dogon wando.

Da murmushi na ajiye abincin Ina "gashi nan"

"Tace ngd Aunty"

Nayi waje Ina fatan ba abinda zai sake fito da ita,dan sam.bangane Mata ba jiya wuni tayi tana saka hijabi yau Kuma ba hijabin dan ma naga.mahfuz ko kallonta bayayi abinda ya kwantar min da hankali kenan"

Koda na koma Palo hankali kwance muka ci abincin mu muna tab'a hira Inda nake ce Masa jibi zanje kitson sallah da kunshi sabida bazan iya bin layi ba,yace Allah ya kaimu ya bani kudin.

Karfe goma naji na fara Jin bacci nikam bansan Mai yasa yanzu nake da saurin Jin bacci ba.

Ina mik'ewa shima ya mik'e ya d'aukar min Mimi muka Shige daki.

Ban bari yayi komai ba sai dabaru da na Masa Nima yamin muka samu nutsuwa dan ce Masa nayi ya bari nayi allura tukunna.

A tare mukayi wanka na dauka zai kwanta ne yacemin Palo zaije yayi kallon ball baya Jin bacci.

Sama sama ma naji shi dan baccin ne a kaina sosai.

Bansan lokacin daya shigo ba.

Washegari ma ummi ce ta tayani sharan tayi mopping Ni Kuma na hada mana breakfast mahfuz yaci ya tafi.

Itama Tara nayi ta fice na shiga gidan mmn Iman muka yi ta hira anan nake fada mata a cikin tsumin da ta kawomin akwai mai balain daci,tace tana ganin ba tsumin na Sha ba dan duk tsumin ba mai daci ko kad'an nayita mamaki tace na gwada sauran ragowar naji ko da daci sai da na koma gida na dauko mata ta dandana tayi ta mamaki tana ta sha irinsa ba daci ko daya,ban bar gidanta ba sai karfe biyu na koma gida a daidai lokacin. Da ummi ta dawo wanan karon ma ita ta Shiga kitchen ta samawa kanta abu taci.

Ta tayani wanke wanke,girkin yau ma ta dage min ita zatayi yanda ta dage yasa na kyalleta tayi girkin.

Yau dai ita take Jin hirar hakane yasa nima na biyeta dan nikam inaso naga muna Hira.

Yau ma bata saka hijabin ba Kamar na tambayeta na Kuma share.

Sai cewa take na iya wanka zata Zo wajena d'aukar course idan auren ya kusa muna burgeta nida mahfuz

Tuni na washe baki nace insha Allahu duk zan bata sirrin zamantakewa na aure,na bata labarin irin soyayya da muka zuba da mahfuz kafin muyi aure,kamar zan bata.labarin tsinaniyar yarinya nan data makalewa mijina da irin hawan jinin da ta so doramin na Kuma fasa.

Itama ta bani labarin yanda saurayinta ke Santa akanta har fada yake da matarsa.

Anan na nuna mata rashin Jin dadina akan bai dace saurayinta yayi haka ba dan itama zai iya mata haka idan ya aureta idan giyar so na kwasar sa yanzu ta ringa Dora shi akan hanya.

Godiya tamin wajen shidda ta mike ta tafi d'akin nima na dau mimi dan yau bamuyi wanka da wuri ba.

Haka kawai sai na fara gaskata mmn Iman akan bata yarda da ummi ba,dan sau biyu Ina Kamata kamar hararata take idan taga na ganta sai ta wayance da sosa Ido,yau bansan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login