Showing 114001 words to 117000 words out of 155577 words

Chapter 39 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

6047

kunna ya tafi dakinsa dan yayi waya da Hadeeza na tuna maganar mummy "a lokacin da kike fushi da mijinki tamkar kina kusan tashi ne ga budurwarsa"

Labulen d'akin na daga a hankali dan ban rufe kofa ba dan kar na rufe kofa yak'i shigowa.

A doguwar kujera na hango shi a kwance daga shi sai gajeran wando ba komai a jikinsa ya zubawa tv ido,kamar dai mai tunani,na fi minti biyar a tsaye Ina kallonsa Ina Jin wani iri a jikina wato wajena ne dai bazai zo ba ya gwammaci ya kwanta yayi kallo Ashe duk munafirci.ne ma dayace yayi kewata.

Wani bakin cikn ya Kara rufeni na koma na kwanta


Wajen Sha biyu naji ya kashe kayan kallon nayi sauri na rufe idona Ina kyautata zaton zai shigo dakina.

Ga mamakina sai ji nayi ya banko k'ofar dakinsa.

Na tashi zaune da sauri na je na leka naga fitilar palon ma a kashe.

Haka na kulle k'ofar d'akina nima na kwanta kwanan bakin ciki nayi dak'yar bacci ya saceni.

Da asuba kuwa da nayi sallah ban ko fita ba dan banaso ma yaga fuskata.

Ina jin motsinsa a palo ko kadan banyi niyyar girki ba dan zan ma iya yi yace min azumi yake.

Ina kwance a Kan gado wajen karfe bakwai da rabi naji ya turo k'ofar dakin na hade fuskata.

Sallamar da yayi na amsa kasa kasa

Ya hawo gadon ya dauki daddy ya fara masa Wasa nidai ko kallonsa banyi ba ya gama jagwalgwala daddy ya ajiye shi ya sauka daga kan gadon Yana "ni zan fita sai na dawo"

"Ko kallonsa banyi ba dan na dauka hakan da nayi zai saka ya gane nayi fushi ga mamakina sai gani nayi yayi hanyar waje.

Sai tashin motarsa naji.

Jikina har rawa ya ringayi sabida b'acin rai bansan ma mai yasa na dawo gidan mahfuz ba bayan yasan wulakantani zaiyi.

Wayata na d'auko na Kira mummy tana dauka na fara "Mummy a gaskiya na gaji da wulakanci da mahfuz yake min bazan iya ba gwara kawai ya sauwake min"

"Mai ya faru shekanjiya Kika koma fa"?

Tiryan tiryan na kwashe komai na fada mata da silar fadarmu

Shiru naji mummy tayi nace "kinyi shiru"

"Takaicinki ne ya hanani magana yanzu lubna da yaranki biyu bazaki tab'a hankali ba ko dan Allah bakiji kunya ba toh da so kike ya cigaba da binki kina taka shi yanda kikeso? Wlh yamin daidai ya nuna shi din dan halak ne Allah yasa ya auro mai hankali wlh har gudunmawa zan bashi idan ya tashi auren tunda ke din shashaSha ce mara tunani Kuma wlh naga kafarki a gidanan sai naci mutuncinki karki bashi hakuri ki zauna jiran yazo ya baki hakuri"

Kit naji ta kashe wayar nabi wayar da kallo

Wani bakin ciki ya kasa rufeni mantawa nayi na kira mummy dan nasan bazata tab'a bin bayana ba

Abinda ya Kara Kona min rai da na Shiga gidan mmn Iman itama laifi ta Dora mun har tana "Mai a cikin bada hakuri da baza ki iya bashi ba wlh wanan halin naki zai saka sanki ya fice a zuciyar mahfuz haba lubna kamar bakida wayo tunda Kika dawo ai sai ki ajiye komai a yanzu da Kika ga yayi fushi idan ma hakurin wahala yake baki sai kiyi da jiki,kici kwaliya kije d'akin kiyi abinda Zaki ja hankalinsa har yayiabinda zaiyi daga Nan komai sai ya wuce bansan mai matsalarki ba wlh"

"Mmn Iman kin Manta Mai yamin taya Zan zama ni nake binsa ina bashi hakuri a lokacin da nake gida Kamar ya kwanta dan na dawo yanzu sai ya wulakantani bayan hotonsa karuwarsa ta turamin a matsayin sannu da zuwa shikenan ba zuciya a kirjina bazan fushi ba"

"Tom bansan mai Zan ce miki ba Kuma nidai idan Aljannar ki kike nema ki bashi hakurin a wuce wajen

Haka na baro gidan mmn Iman duk takaici ya cikani dan karfa karfa nake gani duk uban abinda yamin amma Kuma ni zan dawo na bashi hakuri.

Dak'yar na taushi zuciyata nayi jollof Ina gamawa na shige daki nayi kwanciyata

Wajen shidda ya dawo Ina Jin motsin fitarsa massallaci Koda ya dawo daga bakin k'ofa ya tsaya yace "Na dawo"

Kasa kasa nace sannu

Ya saki labulen ya koma Palo.

Har na idda sallah Isha Ina dan Jin motsinsa wani irin ciwon Mara nake Allah yasan a matse nake amma haka na daure na kwanta har Sha daya duk bana Jin dadin jikina


Dabarar da ta fadomin yasa na m'ike da sauri na cire kayan jikina na daura towel bayan na watsa ruwa a jikina na tsaya a daidai bakin k'ofar toilet na saki wani irin gigitacen Kara Ina tsalle


Aikuwa sai gashi a guje na saki towel din jikina da gangan Ina cigaba da tsalle......


Da gobe Zan Baku wlh dan na fita amma da Babu gwara ba dadi
Ina mata y'an kwalisa ma'abuta gyaran jiki macce Mai gyara daban take ga zuciya mijinta muna da kayan mata da supplement na gyaran jiki kala muna hadin amare da uwargida Dana masu jego muna da set Mai hade da kaza Mai kwai 3 da cicicibe da kifi da galam 3 na tsime da Burkett din gumba 2 da garuruka da zuma wanna set na maccen da ta isa ne muna hadin shi 20k akwai karami set na 15k akwai na 10k akwai na 5k

Muna da magunguna masu jawo hankali maigida da kara martaba

Fanin supplement ma ba'a bar mmn mujaheed abaya ba tana da nagyaran fata da kara haske akwai na gyaran brst na gyaran hip na kiba
Kamar su Lady capsule 4500
Sugar wanita 3500
Glutathione 3500
Vitamin e 3k
Gluta white 3500
Royal jelly 3500
Apetamin 3k
Frozen collagen 3500
Da sauran su insha Allah duk Wani supplement Zaki same su ga mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa

Y'ar uwa kiyi bayani abaki dai2 da type dinki indai sanyi ki Hana Miki jindadin aure ku budewa GABA ku rashin niima to kedai yima mmn mujaheed bayani zata baki dai2 Dake

Mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa
08066726866

Kayan mu iya kudinka iya shagalin kane

*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi*


*Page 42*

Mahfuz

Wajen lubna yayi da take ta tsalle a tsirara ya kau da kansa da sauri dan wani irin harbawa yaji yayi

"Menene"?
Yace Yana dube dube ba karamin dauriya yayi ba wajen yak'ar zuciyarsa dan Kar ya fusgota dan shi kadai yasan mai yake ji.


Tsalle na cigaba da yi Ina neman dakumo shi ga mamakina sai ja da baya yake Yana dube dube

"Wai mene Ina tambayar ki"?

"Bera ne ya zo yabi ta Kan kafata"

Dan fito na duba toh

Yace Yana wani kau da kai

A hankali na bar jikin k'ofar na sunkuya na dauki towel din dana Yar na daura

Ya shiga bandaki ya fito Yana
"Anya beran kika gani ta ina bera zai shigo gidanan bayan ba Ramin bera"?

"Beran na gani mana nace ma nazo fitowa yabi takan kafata"

Na nufi gefen gado na zauna nayi wawan zama dan har yanzu banga ya wani kalleni ba Wanda hakan ya matukar sosa min zuciya ko da Kaya a jikina iya cinya ta idan mahfuz yagani sai naga sha'awa ta a idonsa sai gani tsirara amma yayi kamar bai ga komai ba

Ina kallonsa ya gama dube dubensa yace

"Tsorata kawai kikayi ba bera a bandakin Nan"

Yace Yana cigaba da leka bandakin

Ya rufo k'ofar bandakin Yana "ki kwanta kiyi baccinki ba komai a bandakin sai da safe"

Duk abinan bai ko kalli Inda nake zaune ba ya sa Kai ya fice nabi shi da kallo Ina jin zuciyata na min wani irin nauyi da bakin ciki,yanzu har ni mahfuz zai tattara ya watsar ko kallo ban ishe shi ba tunda na aure shi bai tab'a min haka ba duk fadan kuwa da zamuyi baya iya fushi da jikina sai gashi bayan tsawon lokacin da muka dauka da bama tare na dawo a madadin naga Yana rawar kafa a kaina sai gashi ko kallo ban ishe shi ba

Ban iya bacci ba sabida bakin ciki da tunani ganin har Sha daya da rabi bacci yak'i zuwar min yasa na dauki wayata na kunna data sai da na Shiga Facebook sama sama naga mahfuz ma na online Kamar na masa magana na share shi na fito daga Facebook na hau watsapp dan tunda na dawo ma ban wani maida hankali na hau ba.

Messages na gama shigowa na ga lambar da Hadeeza tamin magana dashi ta min reply din message din zagin da na mata da sauri na bud'e Ina tunanin hucce bakin cikin da mahfuz ya cusa min a kanta dan yau har kakaninta sai na zaga, zagin da tamin yafi shafi guda,har da cemin mahfuz yace Mata ban iya komai ba ba abinda na sani maneji yakeyi dani, zagi da cin mutunci mai tsayi tamin Wanda ban iya karasa karantawa ba sabida bakin cikin da naji ya rufeni,duk abinda tace na riga da nasan sharri ne tunda ta rantse Sai ta doramin hawan jini Wanda akeyin abin dan shi ma yanzu ban ishe shi kallo ba har da image ta tiromin ko ban bud'e ba nasan hoton da zan gani ya daga min hankaline banyi wata wata ba na danna mata blocking bacin rai yasa na kashe data na cilar da wayar gefe.

Kamar dai kullum dak'yar nayi bacci dan sanyin Ac dake ratsani na balain tayar mun da shaawa ko kadan banji wai zan iya wani bin mahfuz dakinsa ba balle na bashi hakuri,ko da can ma shi yake nemana bani ba,duk da ya nuna min Yana mugun so yaga yau da kaina na nuna bukata ta gare shi bana yi dan banaso ya d'auka ni jarababiya ce sai da naga Hadeeza na neman kwace shi ma na fara daurewa Ina nuna Masa bukata na.

Mahfuz.

Yana barin d'akin lubna ya dafe mararsa da yaji Yana Masa azabar ciwo tunda yake bai tab'a Jin tsananin sha'awa Kamar yanda yake ji ba yanzu,rabonsa dai da mace tun da suka je minjibir da hadeeeza kusan wata Tara kenan,lubna kuwa ya riga da yasan dan tana ganin Yana matukar Jin kishinta yasa take wulakanta shi shine har da zubewa akan gwiwarsa akan ta bashi hakkinsa a karshe daga ganin hoto Kamar Mara tunani ta hau zaginsa ya tsani shugaban makaryatan da take kiransa,lubna ta balain Raina shi Koda yasan ya mata ba daidai ba bai cancanci irin wulakanci da take masa ba tana jansa a kasa kamar yaronta ya d'auka da ya kira Hadeeza taji yanda sukayi ya zuciya ya bar dakin zata biyoshi ta bashi hakuri,sai gashi ko ta kansa bata bi ba duk da yasan da karfinsa tanadi na musamman yayi a ranar da zata dawo dan wani mugun hadin kayan shayi yayi da zai saka yaji ko gajiya baiyi ba dan burinsa duk ya fanshe watani da yayi ba mace,sai gashi tsinaniyar Hadeeza ta wargaza masa shiri itama lubna Mai karamin tunani ta biye Mata.

A tashe haka ya kwana ga azabar ciwon mara maganin ma daya sha bai wani Masa aiki ba ganin ba sauki sai wajen Allah yasa ya yanke d'aukar azumi washegari ko zai samu sauki.

Hakan kuwa akayi ya tashi da azumi,bai ma taba tunanin zai ganta a Palo har tayi girki ba ga mamakinsa cikin kwaliya ya sameta a palon har da girkinta.

Baisani ba ko dan ya tashi da azumine baiji komai ba daya ganta ballantana ta daga masa hankali Yana so ya nuna Mata shi din namiji ne Yana Kuma gaba da ita hakane yasa ya yanke shareta har sai tazo dakinsa da kanta.

Ya dauka idan ya dawo idan lokacin bacci yayi zata biyoshi dakinsa ko kwanciya ma ta nuna zatayi a d'akin yasan ta nuna yana da wani matsayi a wajenta sai dai ga mamakinsa da masifar ta ta shigo d'akin tana mai yake nufi da ita.

Yanzu yasan shi kadai yake haukansa akanta bashida wani mutunci a idonta wanan abu ya matukar Kona masa rai haka yasa ya sha alwashin sai dai ta kawo kanta tazo su sulhunta amma ko shaawa zata kashe shi bazai nemeta ba.

Azuminsa ya cigaba da yi Yana samun salama daddare ne idan yaci ya koshi yake kusan mutuwa sabida shaawa ya rasa yanda zaiyi,ko kusa baya so yabi wata hanyar duk da har ya kan raya a zuciyarsa akan ko zuwa zaiyi ya rage zafi koma a wajen waye dan yanda ya rabu da Hadeeza bayaso ya dawo da ita rayuwarsa amma yasan da Yana kiranta ko a Ina yake zuwa zatayi ta same shi,ruwan ne.ma bayaso ya koma.


Ganin Lubna na tsalle a tsirara ya tayar mai da hankali Koda ya Shiga d'akin jikinsa ya kama da k'arfi ya rasa hanyar da zai bi ya fitar sau biyu Yana zuwa bakin k'ofar dakin lubna Yana komawa daki dan gani yake kamar marar tasa fashewa zatayi.

Ta karfin tsiya ya daure ya koma d'akin sai daya yi ta kwarawa kansa ruwa sanyi ya danji dama dama Bayan ya Sha maganin dake lafar Masa da ciwon maran.

Sanin bacci ba daukarsa zaiyi da wuri ba yasa ya dauki wayarsa ya kunna data sabida Hadeeza ya goge watsap akan wayarsa duk da daidaikun rana ne bata tura masa text,a duniya yanzu ba wacce ya tsana sabida ita, dan rashin mutunci taje tayiwa ummi a fadar Ammi har dungure Mata Kai ta ringayi dan ba kowa a gidan.


Zagi kuwa kamar saarta ta dage sai Ammi ya biyata kudinta da ta kashe Mata,Ammi kuwa sai kwashe mata albarka take tana gwara da mahfuz bai aureta ba Ashe bata da tarbiya dama Yar iska ce wanan ya fusata Hadeeza ta kinkimi dan madaidaicin plazma da aka sa mata a daki ta tafi itama tana zagin Ammi


Yana office Ammi ta kirashi tana kuka sai da yaje take bashi labarin diban albarkan da Hadeeza tazo ta Mata.

Bai tab'a tunanin rashin mutunci Hadeeza ya Kai haka ba cikin kuka Ammi tace ko a hanya yaga Hadeeza ya kulata bata yafe ba hakane yasa ya goge watsapp din gabad'aya dan ta nan tafi Masa magana da layika iri iri,sabida ita Kuma bazai ta canja waya ba, Facebook ya koma hawa dan yayi blocking dinta ta can.


Akan Facebook yaga wani grp wai "Mace gidan Dadi"

Har zai wuce yayi joining anan ya ringa ganin yanda ake posting Yan Mata tsalla tsalla da kamar su sukayi kansu Rabin hotunan kuwa duk sun bayyana tsiraicinsu.

A ranar a hotuna ya lalace yana kallo yana jin dadi.

A haka ya shiga profile din wata Sameerah gayu dan ba karya ta wanku ta ci sunanta gayun ya tura mata friend request kafin ma ya sauka yaga tayi accepting.

Kamar Wasa sai gashi suna chatting har ya sake bukatar wasu hotunan nata dan ya tabbatar da mace yake chat ba namiji bane yake amfani da sunan mata dan yayi yaudara.

Ya ga ta watso mai hotunan ta da yawa,take yaji shi cikin nishadi suka hau hira da ita a hirarsu ya gane Yar katsina ce,hira kawai da yayi da Sameerah gayu ya rage masa kadaici basuyi wa juna sallama ba sai wajen biyun dare.

Washegari kamar kullum da azuminsa ya tashi.

Koda ya shirya fita bai ga lubna a palon ba hakane yasa ya Shiga dakinta agaban wadrobe dinta ya hangota tana saka bra ya saci kallonta ya nufi wajen da daddy ke kwance ya wayance Yana yiwa daddy Wasa Yana satar kallon ta har ta gama saka bra din ta saka riga burinsa yaga ta iso wajen gadon ta gaishe shi ta bashi matsayin sa na mijinta shi Kuma iya haka idan tayi zaiji dadi sai gashi ta jingina da wadrobe din fuskarta a hade tana Wasa da farcenta hakane yasa ya girgiza kai Yana matukar mamakin halin lubna.

Ce mata yayi ya fita sai ya dawo.

Kasa kasa yajiyo tace a dawo lafiya ya sa kai ya fice daga gidan.

Koda ya isa office sai da ya rage aikace aikacensa Sameerah gayu ta fado masa hakane yasa ya hau Facebook ya kuwa ci saa tana online suna gaisawa yace bani lambarki zan kiraki mu gaisa

Ba jimawa sai gashi ta turo masa wani lambar etisalat special number.

D'aukar lambar yayi ya kirata a karamar wayarsa.

Bugu biyu yaji siririn murya ya ratso wayar,Kamar Wasa sai gashi sun kusa awa daya suna hira a waya kamar irin ta San shi dinan,a cikin hirar da suke yake fada mata shi mazaunin Kano ne Yana da Mata da Yara biyu,idan bazata damu ba Yana so ta Zama kawarsa

Dariya ta saka tana ita batasan ana kawance tsakanin namiji da mace ba da haka Suka cigaba da hira.


Lubna.

Ina ji Ina gani Mahfuz ya maidani hoto kallon arziki ban ishe shi ba Koda yawo zanyi tsirara girki dai idan nayi zai ci,idan Ina daki zai shigo yayi ta Wasa da daddy amma ba abinda yake hadani dashi,wanan shareni da yake Yana matukar Kona min rai,Ina Kara Jin haushinsa ga masifar shaawa da nake fama dashi Wanda a lokacin da nake gida ba abinda ya dameni ba abinda yake daga min hankali sai gashi mahfuz ya kawoni gida ya maidani namiji dan uwansa a yanzu Kuma sai naji aurensa ya sake ficemin a rai,dan banyi tsamanin karamin abu wai zai saka ya tsiri fushi dani haka ba abinda bai tab'a min ba har ace sati na uku na tafi wata da dawowa mahfuz ban ishe shi kallo ba yasan baya kaunata mai yasa ya dawo dani har na yarda na dawo Bayan wulakanci da yamin da cin Amana amma Wai ni zai wulakanta.

Mummy sai dai tayi hakuri a yau wlh sai ya bani takarda ta tunda baya murdina.

A yau ko girkin banyi ba nayi zamana a palo da takarda da biro a hannuna dan nafisan Yana shigowa na bashi ya sakeni kawai na bar masa gidan dan banga amfanina a gidan ba.


Yau bai shigo gidan ba sai da aka iddar da Sallah magriba Ina Jin motsin sa a Palo dan nima Ina nawa d'akin Ina sallah.

Zumbur na Mik'e da birona da takarda nayi Palo.

A tsakiyar palo naganshi a zaune ya baje yana Shan fruit Ina fitowa.muka hada ido ya maida kansa ya cigaba da Shan kankanan dake hannunsa

A fusace nayi wajen da yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login