Showing 6001 words to 9000 words out of 155577 words

Chapter 3 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

2775

bi ba ya danna Mata blocking dan ko mai zata yi bayajin zai saurareta shi da Allah ya bashi finta ma Lubna Mai so da kaunarsa ba abinda ta rage shi dashi.

Ga mamakinsa Hadeeza haka ta cigaba da canza lambobi tana kiransa ko da zai gaya mata bak'ar magana hakan bazai saka ta fasa kiransa ba har ta kai message din safe daban na rana daban na dare daban.

Bai tab'a bari lubna tagani ba take yake gogewa dadin dayaji lubna bata mai bincike bata damu da taba masa wayarsa ba.

A haka ya samu shekara da Aurensu da Lubna watarana yaje wajen aiki awa biyu a tsakani sai ga Hadeeza a office dinsa.

Rabonsa da ita shekara biyar kenan taci kwaliyya ta Kuma yi kyau kamar ba ita ba ta canza akan sanin daya mata a baya ta Kara gogewa sai kamshin turare take.

Ledar da ta shigo dashi ta ajiye masa agabansa ta langabar da kai ta hau matsawar kwalla.

Mahfuz kuwa kau da kansa yayi yana "Hadeeza dan Allah mai kike nema a wajena"

"Ba abinda nake nema a wajenka so nake kawai komai ya wuce mu cigaba da soyayyar mu"

"Shekara daya da Aurena Hadeeza idan ba yaudararki kikeso nayi ba banida ra'ayin yin soyayya ko na Kara aure matata ta isheni rayuwa Dan Allah kije ki nemi wani"

Bai idda magana ba ta fara hawaye har da sheshek'a mahfuz ya shareta ya cigaba da danne danne a laptop din gabansa sunansa data Kira yasa ya dago ya kalleta

"Allah ya jarrabceni da kaunarka mahfuz bansan ya akayi na wayi gari cikin tsananin sanka ba amma tunda kace haka dan Allah Ina neman alfarma mu cigaba da zumunci ka zama abokina"

"Ana abota tsakanin namiji da mace ne Hadeeza cigaba da muamalla dake kamar dai muna soyayyar kenan Mai amfanin haka"

"Dan Allah Mahfuz iya alfarmar da zaka min kenan ko ba kullum ba muringa waya ko chatt har Allah ya yaye min"

Burinsa kawai ta tafi daga mata Kai kawai yayi yace jeki naji"

Washe baki tayi ta mike tana "Nagode mahfuz ga wanan ba yawa sai na kiraka anjima"


"Hadeeza karki kirani kinsan inada mata kidaina kirana anyhow"

"Bakada matsala"
tace tare da sakar.masa murmushi ta juya tana wani irin takun daya sa Mahfuz kasa d'auke idonsa akanta har ta fice.

Sai da ya gama abinda yake ya bude ledar da ta kawo turare ne.masu kamshi sai snacks da akayi wrapping a foil paper har zai mayar da snacks din ya gutsiri meatpie din yaji ya masa dadi a haka ya gyara Zama yaci iya Wanda zai iya ci dan ta hutashe shi siyan abincin Rana, lubna taso ta ringa aika Masa da abincin rana ya hanata dan baya san ya wahalar da ita.

Tunda ga lokacin Hadeeza da zage wajen zuwa office d'insa tun bai wani bata fuska ba har ya fara bata fuska duk zuwan da zatayi da kalar abinda zata kawo Masa, text kuwa haka take tura masa.

Bai tab'a d'aukar wayarsa ya kirata ba sai dai ita ta Kira shi.

Yau da gobe a hankali ya fara damuwa da lamuranta har idan bata zo wajen aikinsa ba bayajin dadi, yayi balain sabo da snacks masu Dadi da take kawo Masa.

A irin wanan yanayin ta daina aiko Masa da text din da ta sabar.masa dashi,ta bar zuwa office d'insa haka.kawai.yaji ya damu tun Yana ganin zai iya daurewa har yaga bazai iya ba aranar da aka samu sati daya baiji daga wajenta ba ya kirata a waya sai daya mata.miscall ya kusa goma Kafin ta daga murya can kasa da Sunan bata da lafiya shiyasa yaji shiru Nan kuwa karya takeyi so take ta gwada shi taga ko ya damu da ita.

Ana tashi daga wajen aikin ya kirata ta mishi kwatancen gidan da suka koma bai Sha wahala ba dan ba wani nisa tsakanin gidan nasu da wajen aikinsa.

Sai gashi har da kayan dubiya.

Har dan karamin palon gidan aka masa iso da alama ba kowa a gidan sai kannenta da suka kasance yaran kanin mahaifinta.

A kwance ya sameta a doguwar kujera ta Sha kitson attach da tayi parking,sai riga yar kanti armless da taje mata har kasa duk da batayi kwalliya ba bata yafa komai ba tayi wa mahfuz kyau.

Nanarkewa kawai take tana shagwaba Kamar bazai tafi ba lubna dake ta kiransa a waya yasa ya Mik'e ya Mata sallama ya ajiye Mata kayan dubiya ya fito.

Wani ikon Allah Koda ya dawo gida suna Hira da lubna Yana tuno Hadeeza da yanda ta ringa Masa shagwaba tunda ga wanan lokacin ya dawo da Hadeeza rayuwarsa ta samu matsayi a zuciyarsa dan ta Kai yanzu har breakfast take Masa idan zai wuce ya karba da Rana ma abincin take aika Masa.

Dak'yar yake yakice cin abincin dare a wajenta gudun kar Lubna ta zarge shi.

Zuwa yanzu baya iya kwana biyu bai ga Hadeeza ba duk da ba abinda Lubnarsa ta rage shi dashi wanan kenan.

LUBNA

Jan kunshi mai kunshina ta rangada min a hannu da kafa.

Tana ciremin na sallameta ta tafi na hada Abubuwan da nake dan gyaran jiki dashi na hada na mulka a jikina dashi sabida fatata ta Kara laushi.

Iya kokarina zanyi dan na dawo da hankalin Mahfuz kaina bazai yu wata Yar iska can ta kwace min shi ba,nima sai a yanzu naga wautata da na hau fushi da shi,waya sani ma ko kwana ma yayi jiya yana waya da yar iskar SR.

Sai da na goge ko'ina na jikina na Shiga wanka har wani iska naji Yana Kara Shigana.

Mahfuz na san shinkafa da wake da salad hakane yasa na dafa shinkafa da wake na hada masa zobo sai da na gama na koma d'akina Ina duba kayan da Zan saka yau nayi Masa kwalliya yasan har yanzu da saurana ciki ne kawai yasa bana kwalliya duk kayana sun min kad'an dak'yar na samu wani kamfala da nayi wa dinkin bubu mai kalar dorawa da bak'i ya shigeni ya kuwa min kyau dan na cika kayan bansa breziya ba dan mahfuz bai fiye San na saka breziya ba, Hoda da Jan baki na shafa Nima kaina nasan nayi kyau na mulka jikina da turare na fito daga d'akin na koma Palo na zauna.

Wayata na dauko na kira shi a waya Yana fara ringing ya dauka na sauke ajiyar zuciya da naji muryarsa

"Matata ta kaina kin sauko kenan"?

"Hmm dama ni ba fushi nayi ba kishin mijina kawai nake aka nuna nayi laifi"

"Mijinki nakine ke kadai bai Kamata ki dagawa kanki hankali ba"

"Tom mijina ya Kamata ka dawo yanzu matarka nasan ganinka"

"Mai Kika ajiyemin"?

"Kaima kasani"

nace Ina sakin murmushi kamar Ina gabansa

Murmushi yayi yace gashi nan ya kashe wayarsa yana kashe wayar Kiran Hadeeza na shigowa wayarsa.

Bayaso ya d'auka tace Masa yazo tunda har ya samu lubna ta sauko da kanta Kamata yayi shima ya faranta Mata.

Kashe wayarsa yayi gabad'aya dan yasan Kira zatayi tayi


Ana kiraye kirayen sallah magriba naji tsayuwar machine d'in mahfuz ido na zubawa kofar har ya shigo idonsa kyam a kaina Nima idon na zuba Masa ina dan sakin murmushi dan har dan sakin baki yayi nasan mai hakan ke nufi

"Iyye wai duk wanan kwalliyar ni akayiwa Kinga yanda kikayi kyau kuwa aikuwa ya Kamata na biya kudin kwalliyar nan daga haka ya nufo wajen da nake baiyi wata wata ba ya daukeni dak'yar Yana nishin nayi nauyi


Nasan Mai yake nufi ce Masa nake ya bari muyi sallah fir yak'i har sai da muka samu nutsuwa da juna na gamsu da mahfuz nawane ni kadai ba wata Yar iska da ta Isa ta rabani dashi sannu a hankali zan rabashi da wata SR.

Tare muka yi wanka muka yi sallah mu kaci abinci tamkar lokacin da nake amarya.

A kan cinyarsa bacci ya d'aukeni Yana ta shafa min kaina Ina jinsa ya d'aukeni dak'yar ya je ya kwantar dani a d'aki bacci mai dadi da nutsuwa yayi awon gaba dani.

MAHFUZ

Daga sakin munsharin da lubna keyi yasan bacci yayi awon gaba da ita,baisan Mai yasa hankalinsa ya rabu gida biyu ba so yake kawai ya Kira Hadeeza ya riga ya Saba sai sunyi waya ko video call yaji muryarta ta masa shagwaba a hankali ya zare jikinsa daga jikin lubna cikin sand'a ya fito daga d'akin ya fito daga palon ya fita can waje gudun ma Kar lubna ta Kara kamashi.

Akan dakalin gidan ya zauna ya fara Kiran Hadeeza da tak'i daga wayarsa hankalinsa yayi balain tashi hakane yasa ya dage da kiranta.


LUBNA

karar bud'e k'ofar palona yasa na bud'e idona dan banida nauyin bacci ko kad'an


Mikewa nayi a hankali na zauna da naga mahfuz baya d'akin.

Haka kawai gabana ya Yanke ya fadi Allah yasa ba Kara Kama mahfuz zanyi Yana waya ba.

Daga idona nayi na kalli agogon d'akin 12:20am.

Saukowa nayi daga Kan gadon haka kawai naji zuciyata na rayamin Mahfuz na palo Yana waya da Yar iskar yarinya Nan da bansan adadin tsinuwar da na mata ba.

Kishin daya rufe min ido yasa na fito daga d'akin da sauri sai dai Koda na fito baya palon hakane yasa nayi wajen tsakar gidan dan k'ofar palon a bud'e yake haka ma k'ofar gidan dagani sai sleeping dress na nufi wajen k'ofar a hankali kirjina na bugawa,zuciyata Raya min kawai take na koma Kar naji abinda zai daga min hankali daya zuciyar tawa da bakin kishi na ingizani da gwara na ganewa idona mai mahfuz keyi waje.

"Dan Allah kiyi hakuri haba mana na fada miki bada gangan na kashe wayar ba abinda ya sauka a kunne na kenan....

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke=????=????=????maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi=??>?)?
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum=?L?hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatarc'?
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki=?+?
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy >??ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa>??
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go>?)?
Then @mgs skincare gat you covered =د?
Now is time to glow=?
?
Pamper ur skin>ص?
Shine like bride=?p? @&
Glow>???
@&?

=د? tested nd trusted>??
Guarantee


Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166*BUDURWAR MIJINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F.*

*PAID BOOK*

*PAGE 4*

Runtse idona kawai nayi jikina na rawa badan nayi da gaske ba ba abinda zai hanani faduwa.

Tamkar a handsfree ya saka haka nake jiyo maganar ta Cikin shagwaba da kuka

"Dan kaga Ina sanka da kaunarka kake wulakantani mahfuz mai yasa kake min haka"?

"Wlh ba haka bane haba sweetyna ya za'ayi na wulakantaki ban isa ba cajina ne ya d'auke Kuma wani uzuri ya tasomin naje gidanmu ban baro can bama sai goma na dare wlh "

"Wlh ban yarda ba kace matarka dai ta kwace wayarka ta kashe ta hana ka zuwa wajena na dade da sanin tsoranta kakeji ka sa na sha wahalar dafa maka abinci har konewa nayi a hannu"

"Ya salam dan Allah kiyi hakuri wlh ba da gangan naki zuwa ba ki hakura Mana karki sa na kasa bacci"
"Um um bazan hakura ba sai ka goyani Kuma wlh sai ka biyo gobe kacinye abincin Nan shine kawai zan hakura"

Dariya mahfuz ya kyalkyake dashi Yana "Angama sarauniyar mata idan na fara goyaki sai kin gaji gobe weekend bana fitowa da wuri wajen 10 zanzo a dumama min abincina,kinyi kitso da kunshin"?

"Emana har kwalliya nayi fa da sabon Kaya kak'i zuwa"

"Haha karki damu gobe idan nazo zan ma biya kudin kunshi da kitso amaryata kifita wajen haske na kiraki video call"


Iya abinda na iya jure ji kenan zuciyata kamar ta fado sabida tsananin bakin ciki mutumin daya gama tumurmusheni san ransa da tsohon cikina shine yanzu ya baroni a daki yake zuba soyayya da wata.

Wutar kishi kawai ke ruruwa a raina Ina Jin kamar na rufe kofar na kulle ya kwana a waje ko yaje wajenta ya kwana da bakin ciki da takaici ace kina iya k'ok'arinki akan ki kyautatawa namiji amma shi ba take yake ba zuciyarsa na wani wajen.

So nake na bar gurin amma.kafafuna sunki bani hadin kai,haka na zubawa mijina Ido,dake ta murmushi kamar an Masa bushara da gidan Aljanna har Mai nayi Masa haka,dame na rage shi da zai min irin wannan sakayyar bana ma iya gani sosai sabida hawayen daya cikemin idona.

Nasihar mahaifiyata kawai ke dawo min kaina da kyar na iya danne abinda nake ji da shaidan daya ke ingizani akan na kulle k'ofar ya kwana a waje ko naje na cakumu wuyan rigarsa na dadana Masa ashar.

Dak'yar na koma ciki Ina Shiga daki na kwanta naja bargo har saman kaina hawaye na cigaba da zubarmin zuciyata na suya,daga yanda Mahfuz ke magana da yarinya nan ba karamin so yake Mata ba har baya iya bacci idan baiji muryarta ba, wato shiyasa yanzu bai damu da yaci abincina ba? wacece yarinya nan,da take San kwace min miji,.har tana Masa shagwaba da sai ya goyata,tunani na tafi mai zurfi naga ko dai akwai ta inda na gaza har wnan yarinya ta dauke masa hankali Ina matarsa ta sunna ya baroni a daki ya fita waje dan kawai yayi waya da ita,tsafta, girki mai dadi, uwa uba iya gado,daga samun cikina na zama raguwa,Ina da kunya amma sabida kawai na faranta masa, duk da ni ba jarababiya bace har nemamsa nake da kaina,dan naji matan da suke neman miji da kansu daban suke a wajen mazajensu.

Ganin ya dade bai shigo ba yasa na daga kaina na kalli agogo karfe biyu saura minti goma,wasu matan na can rungume a kirjin mazajensu ni gani a kwance nikadai mijina na waje Yana Shan soyayya.

Motsin rufe k'ofar Palo yasa na d'ad'a Jan bargon kaina.

Ina jinsa ya shigo cikin sand'a har da lekani kafin ya kwanta a gefena a hankali ko minti goma baiyi da kwanciya ba naji Yana sakin munshari.

Haka na kwanta zuciyata kamar tayi bindiga har aka Kira sallah na Mik'e naje na daura alwala na tada Sallah.

Har na iddar bai tashi daga bacci ba ta Ina zai tashi ya kwana Yana waya.

Ko ganinsa bana so nayi hakane yasa na koma Palo, so nake na taushi zuciyata na daure Kar na nuna Masa komai a fuska nabi shawarar mahaifiyata dan tunda na taso duk shawarar da ta bani idan har nabi Ina ganin haske.

Yanda nakejin jikina nasan ko tsinke bazan iya dagawa ba nama wahalar da kaina dafa Masa abinci shi da zaije wajen budurwarsa yaci dumame.

Haka nayi kwanciya ta a dogon kujera wajen tara sai gashi ya fito Palo Yana "Uwar biyu shine yau baki tasheni nayi Sallah ba ko wlh bansan ya akayi na makara haka ba,A'a lubna lafiya kuwa ya Naga idonki a kumbure ko bakida lafiya"?

Duk maganar da yake ban daga kaina na kalleshi ba,ban tabbatar idan na Budi baki dan na masa magana ba magana zan gaya Masa ba hakane yasa ban magana ba na ja bakina na tsuke Kai kawai na gyada masa da Sunan banida lafiyar"

Kamar gaske ya nufoni da sauri ya zauna tare da jawoni jikinsa Yana tattab'a jikina.

Na janye na koma na kwanta sam bana San ganinsa duk abinan da yake na munafircine Yana da wacce yake so da kauna.

"Jiya Kuma kalau kika kwanta fa,Allah dai ya saukemin ke lafiya sannu kinji"

Yace tare da manna min kiss a goshi,nidai lumshe idona nayi, ba'a zagin miji amma na danna masa Ashar a zuciyata.

"Bari na dan gyara gidan mai zakici na dafa miki"?

Ganin ban bashi amsa ba yasa ya kara yimin sannu ya fita waje nabishi da mugun harara inajin Kamar na jawo shi na rufe shi da duka,sabida me zai nuna min kulawa alhalin Yana da wacce yake so da idan baiji muryarta ba baya iya bacci,a yanzu Kuma banida burin daya wuce na san wacce yarinya ce wanan da har ta d'auke masa hankali.

Bai dade ba ya dawo da leda a hannunsa daga kamshin nasan kosai ya siyo Ina balain san kosai da kunu,Yana cikin abincin dana fiso na karya dashi da safe kitchen ya wuce dama muna da garin kunu,da alama shi yake damawa.

Yanda yake nuna damuwarsa a kaina yasa wani bakin cikin Kara turnikeni duk abinan da yake min da wata a zuciyarsa.

Motsinsa da naji yasa nayi saurin maida idona na rufe Ina jinsa ya ajiye kofin daya damo kunun a ciki ya ajiye Yana "Lubna tashi ki karya kinji ga magungunan ki nan sai ki sha.

Ya jawo kafafuna kasa.

"Bana Jin cin komai"

"Ki daure mana kinsan baaso mace Mai ciki ta ringa wasa da abinci ko dan abin cikinta"

yace Yana kawo kosai bakina na d'auke kaina Ina "zanci anjima"

Tilasta min ya ringa yi naci nasan nacinsa akan dole nasaka hannu na fara cin kosai na karbe kofin a hannunsa dan bana San munafircin wani bani a baki.

Dadin daya min yasa na zage naci kosai baifi biyar ba na bari, na Sha maganguna na, ya dauki flasks din ya Kai kitchen,ya fito da tsintsiya ta share palon har da mopping mahfuz ba dai baya ba wajen aikin gida idan dai Yana nan, wanke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login