Showing 141001 words to 144000 words out of 155577 words

Chapter 48 - BUDURWAR MIJINA BOOK COMPLETE BY Sadnaf.doc

Sadnaf   

07 Nov 2025

2735

nema Masa aurenta"

Ammi kuwa ganin ya dage yasa tace ba damuwa.

Washegari kuwa ya dau hanyar katsina ya samu tarba Mai kyau awajen Sameerah a karantar da ya Mata kamar dai tana da nutsuwa bai bar garin ba sai da yaga Iyayen Sameerah ya fada musu bukatar sa ga mamakinsa mahaifinta albarka Yasa musu yace ba damuwa wata dayan yayi dama badan an fasa auren ba da tuni tana dakinta ba wani Abu da zai tsayar dasu na Game da siyayan auren.

Mahfuz har zai tambayeshi mai yasa aka fasa wancan auren ya fasa.

Ya ajiye musu kyautar kudi tare da musu sallama

Sameerah ta rakashi har wajen motarsa sukayi sallama sai wani sunne Kai take,sai yaji Kamar wanan kunyar nata ara tayi,yafa tuna a grp din daya ganta,sai Kuma ya yakice tunanin haka ya kirgo dubu goma ya bata ya Kara d'auke kunnensa daga tambayar da ta Masa akan Ina Maman mimi baisan mai yasa take tambayarsa ba.

A takaice a satin aka Kai kudin auren mahfuz har da kudin sadaki katsina yayan mahfuz yaso ayi bincike kafin a Kai Mahfuz ya azalzale su da shi dai yayi bincikensa.

Lefe kuwa kudin ya turawa Sameerah shi dai burinsa lokaci yayi a daura mishi aure da ita bawai Yana Jin wani kaunarta ba tana dai burgeshi ne kila idan sunyi Auren ta samu gurbi a zuciyarsa duk da yasan abune mai wuya a samu mai ture lubna a ransa ba ranar da zai fito ya fadi bai tuna ta ba.

Text din da ta turo Masa ya zubawa Ido Yana Jin wani iri a zuciyarsa.

"Nasan bazaka tab'a canzawa ba Mahfuz ko sau daya banyi nadamar rabuwa da Kai ba dan Kai din ba mijin aure bane Ina tausaya wa yarana Ina tausayin mimi sabida bazan so ta girbi abinda ka shuka ba Kai a yanzu zina ta zame maka ado,na dauka rabuwar mu zai saka ka shiryu Ashe bazaka tab'a shiryuwa ba karuwan ma yanzu har gida kake Kai su ba wani auren da kayi mahfuz zanzo na karbi yata dan bazan so ka lalata min tarbiyarta ba....
MG'S SKINCARE

In kid'a ya chanza rawarma semutaru asauyata,
Wani Kaya se amalende
Haka Wani Hadi na musamman se MG'S,

Ina ma'abota amfanida kayan MG'S SKINCARE?

To bana fa tafi bara munqarawa kayanmu inganci muncire muntsefe munkawo maku qayatattun kayan gyaranjiki da Baki taba amfanida irinshiba a wannan qarnin,

Wani irin salo na gishirin kyan daukar magana zakiyi duk kikayi amfanida hadinmu b cika bakiba,ko yayan Hutu basa nuna maki tsadar fataba,duk a 11k fa kachal=?L?
Beauty kit:11k
Student package:7k
Soap:3k
Bridal kit 18k

Kicire kokonto ki warwaro Lalita kidebi Kaya n kerewa SAA

Chat:08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call:08064532391

Available in Kano and Kaduna

We also have beautiful yet luxury and unique frames for your apartments chat or call 07046881166

Serious buyers only please,

Inamasu bukukuwa=?
?
Kugarzaya @inteesar cakes nd more kuyi order small chops domin bakinku irinsu
Cupcake,fishroll,samosa,spring rolls dama duk kayan kwalam da makulashe kunemata 07067210195
Cika alkawari shine takenmu>??
Thank you


*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 5????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? 00 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi*


*Page 51*


Ya goge text din daga wayarsa Yana Jin tsananin b'acin rai,har shi Lubna zatace batayi nadamar rabuwarsu ba,yasan ba wajen Wanda zata ji labarin sai a wajen mmn Iman dama ya zargi hakan zai iya faruwa tunda har tagan shi mmn Iman ta dade tana hada masa munafirci ya d'auka matuniyar arziki ce ashe dai haka halinta yake sai yaji unguwar duk ta fice masa a rai ya zama dole ma ya bar unguwar nan.

Idan ya samu nutsuwa Bayan auren shi da Sameerah ginin zai fara yi ya saka wanan gidan a kasuwa.

Sameerah ya Kira a waya dan ya ya hucce Haushin text din da lubna ta Masa.


Lubna

A ranar da na cika wata uku a gida sai da naci kuka nagode wa Allah abin Kamar Wasa babu igiyar Auren Mahfuz a kaina,a daren nayi tashin dare na roki Allah zabin sa a gareni dan bansan Kuma wane shafin kaddarar ne ya budemin ba, a yanzu Kuma da na fita daga idda sai naji na damu bansan dalili ba kalmar bazawara na tsananin b'atamin rai, duk ranar da mijin mummy zaizo idan naga yanda mummy take dan gyare gyaren gida su kunshi da haddaden girki da nake tayata duk sai naji wani iri a raina Zawarci bashida dadi sai dai idan Allah ya kaddara ma,daddare haka zanyi zuru a daki nikadai nayita juye juye har na tafi tunanin rayuwar Aurena daga lokacin da kuma na Tuno Hadeeza da mahfuz a ranar haka abin zai ta fadomin ina b'acin rai karshenta sai na sha magani zan iya bacci abin ya hademin da rashin Mimi,marainiya nake jina sosai har.nakan ji dama nasani ban kalli videon nan ba da kila yanzu Ina gidana da yarana banji a raina nadamar abinda nayi nake ba sai nake ganin kamar rabuwar tamu ta fimin alheri,dan da ace Saminu Sameerah gayu bata Kira mahfuz ba da zan iya yarda yayi nadama amma Kiran nan da tayi yasa gabad'aya naji ba abinda zai saka Mahfuz ya tab'a canzawa ya rabu da Hadeeza ne ya sake d'auko wata domin da ace ba halinsa bane iya irin abinda Hadeeza tayi masa ya Kamata ya tsorata da mace sai nake tunanin kila ya dade ma da Sameerah gayun kila ma idan ya Dade a waje Yana wajenta suna watsewa.

Sati daya da kamalla idda ta na fara zuwa school of nursing da mummy ta samo min dan Dr mijinta yamin hanya,har ga Allah fitar da na fara sai yake min dadi dan bana Jin dadin zaman gidan da nake Sam, Ateeka ita take kularmin da daddy,da ace Ina da wajen da zan zauna banda gidan mummy da na zauna dan bana sakewa a gidan idan har mijin mummy na Nan.

Abinda ya fara damuna bai wuce Koda na fara zuwa makarantar ba abinda nake iya ganewa ko.na tsinana idan ana koyarwar ma sai na tafi tunani na rasa.mai yake damuna.

Iya k'ok'arina inayi dan na maida hankali amma abin yaci tura haka dai nake zuwa,na kasa sakewa da kowa ma ajin duk da wata Afrah na dan shishige min a karantar da nayi yiwa rabin.matan ajin suna da Aure rabi Kuma Yan matane sai na rasa sahun da zan saka kaina,na Riga da nasan banida aure Kuma nidin ba budurwa bace ba.

A seat din da nake zama na matan aurene idan har bamuda darasi haka zanji suna hirar Ma'aurata kowace na tofa albarkacin bakinta Wanda hakan sai yake zama Kamar fami a zuciyata da ace Ina da Aure da kila Nima Ina cikinsu Ina zuba"

A yau Ina dawowa daga makaranta na fito daga wanka kenan naga mmn Iman na kirana sharewa nayi ban dauka ba dan yarda daya ce yanzu Kuma ba abinda zatayi na iya sakin jiki da ita ta riga da tasan Aurena ya mutu daga lokacin da aka kwaso kayana daga gidan mahfuz sai gata washegari tana nuna tsananin damuwarta da rabuwar mu na nuna mata ba komai Allah ya kaddara aure ya kare a tsakanina da mahfuz duk yanda taso ta ji mai ya hadamu wanan karon muka rabu sai naki akan dolenta ta kyalleni.

Ganin Kiran nata bana karewa bane yasa na d'auka bayan mun gaisa tace "Lubna wlh gwara da kika Rabu da mahfuz dan bazai tab'a canzawa ba kinsan wlh Allah jiya mun fita da Abban Iman mun siyo kaya sai na fito na tsaya a k'ofar gidanku ai sai gani kawai nayi wata ta fito daga gidanki da matsatsun Kaya mahfuz ya rakota Muna hada Ido dashi ya koma abin nasa ma Kara gaba yakeyi ashe Kun rabu ma karuwai kawai yake kaiwa gidan wlh kinyi abinda ya dace sam ba mijin Aure bane ba Allah ya baki Wanda yafi shi alheri amma me akeyi da namiji mazinaci"

Sai na kasa magana Ina Jin kirjina na min nauyi sai da ta sake magana nace "Mmn Iman ba abinda ya shafeni da raywuar da yakeyi ki daina wahalar da kanki ma kirana ki fadamin"

Ban bari ta sake magana ba na katse wayar na sulale kasa na kwanta,maganganun mmn Iman ya ringa dawo min tiryan tiryan a yanzu rayuwar da mahfuz ya koma yi kenan dauko karuwai ya Kai su gida ya Kuma zo ya rabani da Mimi,dama ya samu masu biya Masa bukatarsa ne shiyasa naga ko ta kaina bai Kara bi ba balle ya waiwaiyeni.

Hannuna na rawa na tura masa text Ina jiran tsautsayi yasa ya kirani na gaggasa masa magana nayita kallon wayata ko zaimin reply baiyi ba.

Sai naji na Kara tsanar mahfuz baiyi nadamar abinda ya aikata ba bai damu da rabuwar mu ba ya cigaba da Nemo karuwai ya kuwa zama dole ya dawo min da Mimi yaje can ya karata da karuwai dinsa.

Mahfuz ya Kara fita a kaina naji ko kadan banaso na Tuno sa duk wani abu danasan zai tuna min shi na toshe shi,na ringa yak'i da zuciya ta wajen tuno min da wani mahfuz,na ringa k'ok'arin maida hankalina wajen karatuna,ba laifi na Kuma fara dan ganewan,sai dai abinda ya bani mamaki bai wuce yanda maza suka fara biyoni har gida ba Ina Shiga zanji ance ana sallama dani, da ace sun san yanda na tsani Maza gabadaya da basuyi biyoni ba,taya ma suka gane banida aure Bayan nasan banyi shigar da zai alamanta musu banida aure ba idan zanje makaranta uniform nake sawa fararre idan zanje islamiya kuwa na magriba zuwa isha hijabina nake sawa har kasa,ga mamakina sai naga mummy ma murna take ana zuwa sallama dani,har tana Allah yasa aurene ya kawosu nayi Aurena na hucce takaicin mahfuz,zataso ma na riga mahfuz aure,Anya mummy tasan ciwon da da namiji ya dasa min a kirjina kuwa taya zan ma iya sauraran wani da namiji ko nan da shekara biyar ne ni Zan iya cewa bansan Dadin aure ba sai kalubalen Auren.

Ina ji Ina gani mummy ta tilasta min fita wajen wani Mai shegen nacin tsiya da ya ringa turowa nazo.

Banida yanda zanyi na fita Ina fita nace masa ni matar Aure ce bansan wane kala bane shi dan a cikin mota yake bansan ya fito ya biyoni ba sai ji nayi an ruko hannuna Ina juyawa na zabga masa mari na shige gida aguje jikina na rawa dama haka zawarcin yake.


Mahfuz

Lumshe idonsa yayi a lokacin da yaji marokan dake bakin massallaci na shelar an daura auren shi da Sameerah sam baiji wani farinciki ba hasali a tsayen da yake da Abdul Amininsa daya samu halartar daurin auren tunanin shekara hudu da suka wuce yake da aka daura auren shi da lubna da yake ji Kamar bushara aka Masa da gidan Aljanna har ya Shiga gidansu lubna sukayi hotuna idonsa na kan lubna da taki bari su hada Ido,daga gidansu wajen da suka Kama dan ayi waleema sukayi,anci an sha aka hau tsokanarsa ya bi Yar mutane a hankali,da iskanci kowa ke fada masa yanda zaiyi idan an Kai Masa ita,dak'yar ya bar cikinsu ya Kira lubna Yana ji Kamar ya fusgota daga cikin wayar sai yaga lokaci baya gudu kwata kwata ya matsu shidda tayi a d'auko masa ita,idan akace Masa a wanan lokacin akwai kaddarar da zata rabasu karyatawa zaiyi sai gashi a tsaye an sake daura masa Aure da Sameerah da baisan zata iya mayye masa gurbin lubna na ko akasin haka,baisan Kuma ya zaman nasu zai kasance ba,dama a rayuwa abinda kake tsarawa daban abinda Allah ya tsara ma daban,ko a mafarki akace zai tsallaka garin Kano yazo wani garin Aure karyatawa zaiyi.

Hannunsa dayaji an rik'e yasa ya dawo daga tunanin daya tafi.

Suka Shiga gidansu Sameerah akayi gaishe gaishe kamar wancan lokacin aurensa da lubna sam ya kasa Jin farinciki ballantana ya iya sakin fuskarsa sosai sai yake da yakeyi,ba laifi Sameerah tayi kyau sai yake hango fuskar lubna a nata fuskar.

Basu baro garin ba sai da Sameerah.

Da isowarsu aka wuce da Sameerah gidansu mahfuz.

Mahfuz Kuma ya wuce gidansa da Abdul da isarsu Mahfuz ya cire hularsa ya kalli Abdul Yana "Ko ya Lubna zataji idan taji labarin daurin Aurena"

"Mai zataji kuwa dadi zataji tunda Bata kaunarka ba wani Abu da zataji tunda da tana kaunarka ai bazata rabu dakai ba"

"Abdul Ina kaunar lubna duk abinda tamin na kasa ganin bakinta Banda wanan larurar tawa wlh da banyi gaggawan aure ba may be a year ko after zamu iya daidaita wa"

Mik'ewa Abdul yayi Yana "Nikam bansan Kuma Mai zance maka ba idan kasan kana kaunar nata ai da ka cigaba da azumin naka kana bibiyarta a haka har ku sake daidaita wa idan wani abu ya sake faruwa sai ta Kara tattara kayanta kabi bayanta"


Mahfuz baice komai ba dan yasan magana ya gasa Masa,akan dole yaja bakinsa ya tsuke ya fara tunanin yakice komai a ransa yajira lokacin da zaa kawo Sameera ya sauke mata duk abinda yakeji,a yau yafi kowane lokaci matsuwa

Yana fatan ya sameta yanda yakeso zahirinta ya Zama haka ma yake a badininta,karfe hud'u ya kwankwadi maganin Karin kuzari, ya bar gidan dan so yake idan ya tashi dawowa yazo ya tarar an kawo ta.

Bai kuwa koma gidan ba sai bayan Isha da ledojinsa a hannu.

Shi kansa bazai iya fassara mai yake ji ba farinciki ko akasin haka amma sai da yayi yaki da zuciyarsa wajen tuna masa da Daren farkonsa da lubna da a tarihin rayuwarsa bazai manta ba dan daga shi har itan sun Sha bak'ar wahala.

Yanda yakeji bayajin zai iya bin Sameerah a hankali.

Wani irin kamshi ya doki hancinsa a lokacin da ya Shiga d'akin lubna da ya zama na Sameera a yanzu dan a ciki aka Mata jere sai dan fenti da gyara daya Kara canja gidan.

Sai ya cire komai daga ransa asan ya mori Daren yanda ya Kamata.

Ya ajiye ledojin hannunsa ya zauna a gefen Sameerah dake zaune a gefen gadon mayafinta a lullube har baka hango fuskarta.

Yana yaye mayafin ta sakar masa murmushi sai yaga ta masa kyau a Karo na farko daya fara tabata ya rungumeta tare da sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

Dumin jikinta da kamshin jikinta ya Kara daga masa hankali dak'yar ya iya sakinta ya jawo ledar bata wahalar dashi ba Kamar lokacin lubna da sai da suka kusa awa Tama ki dagowa balle taga kazar,sai yake ganin kamar Sameera a waye take.

Suna gama cin kazar ta mik'e ta Shiga bandaki shima ya tafi nashi d'akin dan yayi wanka ya shirya samun nustuwa.

A gaggauce yayi wanka ya daura alwala ya koma dakinta.
Ya sameta a gaban mudubi Tana fesa turare.

Sai idonsa ya sauka akan kirjinta da nonon ke kwance da gani dai ya zube nonon kamar ta shayar bai dasawa kansa tunanin komai ba ya sa a ransa Mata hallitarsu ba daya bace amma lubna tafi Hadeeza da Sameerah kyaun nono.

Ya umarceta da ta saka Hijabi suyi sallah rakaa biyu.

Tayi yanda yace din.

Bai ja wani lokaci mai tsayi ba ya mik'e ya rike hannun Sameerah sukayi Kan gadon.

Jikinsa rawa kawai yake ya kashe fitilar d'akin burinsa kawai ya samu nutsuwa.

Hadin Kan da ta bashi a romance ya kawo duk wayewa ce kila sai da yaje wajen samun nutsuwar sai yaji Kamar dai ba haka.ya Kamata ya jita ba.

Bawai ya Shiga zuruf ba amma Kamar dai ba wanan shine karonta na farko ba daya samu nutsuwa ya mike ya zauna tare da zuba mata Ido.....
MG'S SKINCARE

In kid'a ya chanza rawarma semutaru asauyata,
Wani Kaya se amalende
Haka Wani Hadi na musamman se MG'S,

Ina ma'abota amfanida kayan MG'S SKINCARE?

To bana fa tafi bara munqarawa kayanmu inganci muncire muntsefe munkawo maku qayatattun kayan gyaranjiki da Baki taba amfanida irinshiba a wannan qarnin,

Wani irin salo na gishirin kyan daukar magana zakiyi duk kikayi amfanida hadinmu b cika bakiba,ko yayan Hutu basa nuna maki tsadar fataba,duk a 11k fa kachal=?L?
Beauty kit:11k
Student package:7k
Soap:3k
Bridal kit 18k

Kicire kokonto ki warwaro Lalita kidebi Kaya n kerewa SAA

Chat:08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call:08064532391

Available in Kano and Kaduna

We also have beautiful yet luxury and unique frames for your apartments chat or call 07046881166

Serious buyers only please,

Inamasu bukukuwa=?
?
Kugarzaya @inteesar cakes nd more kuyi order small chops domin bakinku irinsu
Cupcake,fishroll,samosa,spring rolls dama duk kayan kwalam da makulashe kunemata 07067210195
Cika alkawari shine takenmu>??
Thank you


*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min SHARING bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi*


*Page 52*

Sai ta rufe fuskarta alamar kunya, Mahfuz yaji wani abu ya tsaya Masa a zuciya kunyar me kenan yasan mata biyu Lubna har sati baya iya shigarta baya mantawa har dasu Vaseline duk dan ya samu Shiga ta sauki,lubna a wahale shima ya sha wahalar har Suka samu wata uku da Aure da lubna bata iya sakin jikinta ya shiga haka zatayi ta kankame jikinta tana tureshi, Hadeeza kuwa ita dama yasan ba budurwa ya sameta ba tunda tace fyade a ka mata Wanda daga baya yasan duk karya ne,Sameerah kuwa har tafi ma Hadeeza bud'ewa.

Ya hadiyi yawu dan yajika makoshinsa yaringa tausar zuciyarsa dan Kar ya gaura mata Mari dan bayasan bugunta ya d'auka zai samu nutsuwa yanda yakeso ya d'auka zai sameta a budurwa sai gashi ya sameta a cikakiyar macen da tayi sabo ma dan ko lubna da tayi haihuwa biyu tafi Sameerah matsewa a yanda yaji.

"Sameerah ya najiki haka"?

Yace kamar an fusgo maganar daga bakinsa
Sai ta jawo bargon ta Kara rufe kirjinta tare da yamutsa fuska tana "Kamarya fa"?

"Sameerah kin tab'a Aure ne ko haihuwa kikayi najiki a bude haka Sameerah na aureki ne a matsayin budurwa ba bazawara ba,ko fyade aka miki sau daya dai ba yanda zaayi ki bud'e haka"

Sai ta mike zaune hannunta dafe da bargon a kirjinta ta sha Ghana weaving kananu

"Mahfuz past dina bashida kyau banaso na fada ma komai dan hakan ba abinda zai jawo sai b'acin rai a baya nayi rashin ji amma yanzu na daina"

And baki zabi ki gayamin ba sai da na aureki Sameerah"?

"Idan na fada maka bazaka aureni ba mahfuz ba Wanda zai ce bashida wani boyayyen hali mara kyau na fada ma iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login