Showing 33001 words to 36000 words out of 67070 words

Chapter 12 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt

03 Sep 2024

9256

kawai a kwana dasu, khaleesah Nice fa Nihal? Kiyi duk abinda zakiyi a inda ba'asan koke wacece ba, amma ni nan nasanki in and out so wannan abubuwan da kike duk nasan ma'anar su" Tsawa Hakeem ya dakawa Nihal, a zafafe ya ce "Barnan wurin Nuhal" Tsaye tayi tana kallonsa na kusan 5seconds sannan ta juya batare data yi magana ba da wuce ciki. 'Tayaya zanyi kuka, bazakiyi kuka ba Nihal take gayawa zucuyar ta, wlh bazakiyi kuka ba, Hakeem kuwa zai shigo hannunki idan yazo hannunki zaiyi babban bayani' Ta ayyana a ranta. Kitchen na part ɗinta ta shiga taje ta saka aka girka mata abinda zata ci ta dawo ɓangaren ta ta soma chat da ƴan gidansu.


Gaba ɗaya Hakeem ya rasa dalilin sa najin haushin Nihal akan abu kaɗan, amma shin anya daidai ne yanda yake mata? Ita tayi girkinta duk a cikin su babu wacce take masa girki kotake kula da sassan sa sai ita, shin meyasa yake mata haka? Miƙewa yayi tsam bayan ya idarda cin abincin ya shiga part ɗin Huddy. Tasha ado cikin baƙar doguwar riga ta mata kyau sosai. Gayar dashi tayi cikin shauƙi tare da faɗawa jikin sa "Baby yazo" Murmushi yayi ya sumbaci kuncinta "Kinyi kyau my dear, kinata shagwaɓani, idan bama tare ji nake kamar ni maraya ne" Wani banƙaro ƙirji tayi tana wani lanƙwasa


"Koda wane lokaci zanso mu kasance a tare, amma sam ni banason shiga haƙƙi, Honey kaga abinda kayiwa Nihal jiya sam wlh baka kyauta ba, ka ɗauki kwanan ta kaje ka kaiwa waccen Khaleesah, ka fahimci wani abu ba wani kare dayake binta kawai so takeyi ta riƙa shiga haƙƙin mu" Zama yayi akan jurar dake cikin ɗakin ys zaunar da ita akan cinyar sa "Allah ko Huddy yanzu ke dama kina jin mu? Ɗan lanƙwasa kanta tay "Duk abinda kukeyi ina jinku, yanzu ma daidai ne ta girka abincin ts bayan ka ƙwace mata kwana kuma sannan har girkin datayi haƙuri tazo tayi ka ƙwace ka baiwa Khaleesah, gaskia ni banason ka da rashin adalci saboda haka yanzu ƙarkaje wurinta danta rigada ta fusata amma da dare kayi ƙoƙarin shiga ka bata haƙuri kuma ka kwana mata gaskiya" Nisawa yay "Kinsan nima inataji ajikina cewar ba daidai bane, to bakiga yanda khaleesah ke zuwa bane a mugun firgice fa, saita giɗima ni wlh" Haushin yanda ƴake rawar jiki akan khaleesa taji sannan ta ce tana taɓe baki


"Ka daina biyewa makircin wata kana cin zalin wata, Allah ma bazai barka ba, datazo tana firgici ka haɗata da ƴan aiki mana ? Sa kwana mata amma ka ɗauki kwanan mace amarya ka baiwa wata haba mana Honey" Nisawa yayi "Na daina gaba ɗaya Baby na, zankuma mata kwana kinta biyu idan kin yarda" Tana murmushi ta ce "Ba komai ka biyata haƙƙinta, amma me yau ka ƙoshi ne bazaka sha madarsa ba? Hannun sa yakai ya shafesu "Indai za'a bani mezai hana insha ehm" Tana dariya ta ce to muje ɗaki mana" Tamkar raƙumi da akala haka ta caji zuwa bedroom duk hanyar da haske ke shigowa saida rufeshi sannan fa zare rigarta ya saura daga ita sai pant dama ko bra bata saka ba , Kamar kullum yauma rungumarshi tayi ta dinga feeding nashi tamkar wani jinjiri tana smfani da Nails na middle finger nata tana masa tafiyan tsutsa har ƙasan mararsa, anan suka lalace har bacci ya kwashe su.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels






Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************


****************
Tun ƙarfe huɗu na yamma Nihal take yawon gyaran part ɗin Hakeem, wanke wannan boxer wanke toilet kai komai sanda tayi masa. Lafiyayen tuwon semo miyan kuɓewa ɗanye ta masa yasha naman rago da kuma man shanu, sannan ta haɗa kunun Aya da ruwa ta jere akan dining ta nufi part ɗinta sai bagan sallan isha sannan ta dawo alokacin ta tarar Hakeem ya dawo danta lura da buɗe ƙofar babbar falon da kuma takalmin sa awurin. Ɗakin baccin sa ta wuce dayake tamkar wani shago fankacece anan ta tarar ya fito wanka da ruwan data haɗa masa! Da sauri ta tura masa trolley tare karɓan towel ɗin hannunda ta shiga rage masa ruwan jikin sa, a hankali tana goge ruwan bayan kunnen sa ta ce "Barka da dare yaa Hakeem" Ɗan murmushi yay "Huddy ce tazo tamun gyara ko? Kallon sa tay tana mamakin rainin hankalin sa cikin takaici ta ce "Nina gyara" Murmushi Ya kuma yi "Haba nace kamar ƙamshin part ɗinki wurn keyi" Bata kulashi ba sai mai data tsiyayaa hannun ta ta murza ta soma shafa masa a fuska, shidai yayi sororo yana kallon ta, ita kuwa dukda nauyin sa datake ji hakan bai hanata tunawa da huɗubar Ƙanwar maman taba Mama dija, Haka ta shiga shafa masa man ƙirjinsa. Sanda hannunta mai laushi ya isa akan ƙirjinsa zuwa nonuwan sa lumshe ido ya yi sannan ya ɗaura hannun sa akan nata ya riƙe a wurin, kawar da kanta tayi shi ɗinma dayaga zai bada kanshi saiya janye hannun sa ya ce, "Inaji ai man ya isa haka ko" Juyawa tay batare da tace dashi komai ba ta shiga haɗa kayan, shi kuwa ya ɗakko kayan baccin sa ya shiga changing room yana lumshe ido har lokacin yanayin yanda ta shafa masa mai yana masa yawo, dama haka ake akewa miji kodai ita kaɗai ce take ji dashi haka, komai idan ya taso zai yi saita tayashi, gaisuwarta ma da banne data sauran. Falo suka nufa cin abinci suna fitowa ta hango khaleesah akan dining a zaune, bata ce masa komai ba,.suka je suka zauna Khaleesah ta wani matso kusa dashi tana karairaya "Dama zuwa nayi in gaya maka, zan kwana a part ɗin Nihal saboda ina tsoron wannan karen ya dawo" Ɗagowa yayi ya kalle ta amma bai ce mata komai ba, Nihal ta ce tana kallon ta "Nima ina tsoron karen nan dake kaɗai ya raina agidan nan yazo ya cijeki ƙawata. Ki tafi abunki ki shirya kizo part ɗin nawa ki kwana" Harara ta wurga mata sannan ta ce "Yaa Hakeem kaji" Cokalin dake hannun sa ya ajiye sannan ya ɗago ya kalle ta "Ba kince zaki kwana tare damu ba? Kije ki kimtso mana kizo mu kwana" Juyawa tayi tana wani mazaya ƙugun dayake a cike da ɗuwawu, Murmushi Nihal tay sannan ta zauna taci tuwon ta sosai shima Hakeem Haka, suna idarwa suka zauna falon kallon, basufi mintuna goma da zama ba bamaiwa wani magana saiga Khaleesa ta dawo da wata mara mutuncin dress gaba ɗaya da shap na gabanta da kuma nipples nata a tsaitsaye ga wani turare mai hawan kai, wanda nan da nan ya cika wurin ya sanyawa Nihal tashin zuciya, ita kuwa kai tsaye kusa da Hakeem ta zauna, tana wani hamma da miƙa "Yaa Hakeem yauma bacci nake ji sosai" Kallonta yayi yana lumshe idon sa, wannan turaren sha'awa yake saka masa da zaran ya shaƙa harya soma fahimtar hakan. Nihal dai batace masa komai ba sai zaman kallon ikon Allah. Kafin suyi wani nisa da komau Huddy ma ta fito kai tsaye kusa da Nihal taje ta riƙo hannun ta ta miƙar da ita tsaye suka kalli juna "Ki tafi part ɗinki Nihal, zanzo na sameki yanzu kinji" Bata gane komai dan idonta a rufe yake da yanda taga Hakeem nata bin Khaleesah da kallo... Wucewa tayi ita ko Huddy taja hannun Hakeem dake mata ƙoƙarin turjiya har cikin ɗakin sa dake part ɗinta. Hannu bibbiyu ta sanya ta waigo da fuskar Hakeem yana kallon ta sannan ta ce "Man ur out of controll, wane irin sakarai kakeso ka zama nifa laɓel nake muku kunacin zalin yarin yar nan kaida khaleesah, waikai baka fahimtar khaleesah batazo gidan nan danta barmu mu zauna bane?" Dafa kanshi yay, "Ki taimakeni kawai i really need to be with a woman now, help me out or lemme go to her" Riƙe baki tay "Meyake damunka ne haka?


"Wani turare ne da khaleesah, duk idan ta saka sainakejin sha'awa yanamun yawa" Ƙirjinta ne ya doka, tana shirin magana khaleesah tazo ta soma bubbuga ƙofar da ƙarfi ,dama ta sakawa ƙofar key dan haka tayi banza da ita, toilet taja Hannun Hakeem ta wanke masa fuskar sa sosai sannan suka dawo ɗakin suka zauna, shiru kusan 30mns sannan ta ce dashi "Ka kabi ta wannan hanyar kaje gun Nihal matarka ce, khaleesah kuma ka ɗauki mataki akanta kokuma wlh in gayawa Ummi" Baice komai ba ya miƙe saboda ya samu nutsuwa tunda ruwa ya taɓa jikin sa. Yana fita fa part ɗinta ta zaro wayarta ta kira Aunty Hali dubu


"Anty na gaya miki banida damuwa da Nihal, bata isheni kishi ba basason juna, makamina ce agidan nan ta hanyarta zankai ga mallake Ummin sa, amma khaleesa tafimu shiga bokaye, yanzu dake wannan kwallin idan na shafa hakeem damun haɗa ido komai yana gayamun shine ya gayamun wai idan yaji ƙamshin turaren dake jikinta sha'awa take taso masa" Nisawa Anty tae "Ohh Hali dubu! Wannan khaleesah anyi hatsabibiya, kawai kin gane bara gobe zanje, kedai yanzu ki shishigewa Nihal, ki manne mata akan komai zamuyi bata kashi muda Khaleesah" "Yauwa Aunty na dubu da babu kamar ta, zan kimtsa na kwanta" Haka sukayi sallama. Shi kuwa a part ɗin Nihal koda yaje ta sanya suturun bacci marasa nuna tsiraici sosai, zama yayi kusa da ita sannan ya riƙo hannun ta "Am sorry my sister" Kallon sa tayi da idonta dasukayi ja jajir sannan ta kasa ɓoye ƙwallanta ta ce muryanta yana rawa "Hakeem ko zaka barni naje gun momy dan Allah, kwana goma zanyi na dawo wlh, nan gidan na gaji da zama" Haka kawai sai yaji tausayin ta ya rungumeta gaba ɗaya "Kiyi Haƙuri zan zama mai kirki agareki, zan ɗauki mataki akan duk wanda keson ya shiga tsakanina da ke amma karkice zaki je gun momy kinji" Kuka ne ya ƙwace nata gaba ɗaya ta shiga rerawa baji ba gani, kasa ce mata komai Hakeen yayi kawai ya lumshe idonsa yana jijijjigata a hankali har bacci ya kwashe ta a hannun sa. Kwantar da ita yayi shima ya rage fitilar ɗakin ya kwanta tare dayi mata addu'oi har bacci ya suresa shima.


**************
Ɓangaren ta koma bayan sunyi sallah, a nemi breakfsat chips and eggs, da dabara tace masa ya zauna anan falonta ta masa girki da kanta ta kawo, haka kuwa akayi taje tana shiryawa saiga khaleesah, suka tsaya suna kallon juna, tsaki khaleesah tae Nihal ta matso kusa da ita cikin masifa ta ce "Kinsan Allah Khaleesah, this will be the firts and the last time dazan baki warning akan zuwa nan part ɗin ranar girki na, kinga dai bana shiga sabgarki ko to ki fita a nawa sabgar, banza mai masifar son mazan tsiya" Cikin mamaki Khaleesah ta ce "Nice banza?" Tsaki kwai Nihal tay ta juya abinta ita kuwa ta shiga danna mata ashar ko kallon inda take batayi ba.
Hakeem Namiji ne mai tsananin sha'awa, yana cikin jerin mazajen da sam sex bata gundirarsu dan haka acikin matayen sa babu wacce bayason kasancewa tare da ita, Nihal ce zaɓin iyaƴen sa kuma ya rasa ta inda zai gabatar mata da buƙatar sa! Yanda yake kallon ta har ta zauna ya sanya ta tsargu, tana yamutsa fuska ta ce "Ya akayi ne naga kanata kallona" Dankalin data ajiye ya buɗe sannan ya ce "Yanda akayi kika tsaneni nake mamaki,ada kinfi kowa sona, yanzu gaba ɗaya ko kishina bakyayi kina kallon sauran abokanan zamanki sunamun abinda nakeso amma banda ke" Murmushi tay mai nuni da cewar yama bata dariya sannan ta ce, "Yaa Sadaukee nifa tausayin kanmu nakeji nida kai, su momy sun kawoni anan sun ajiye da sunan matarka amma baka sona bakuma na sonka, dazamuyi wata dabara daba yanda zasuyi mu sawwakawa juna wannan jarababben auren" Nan da nan ransa ya sosu cikin takaici ya ce "Aurena dakikayi shine ƙaddara Nihal? Kawar da kanta gefe tay "Ko acikin labarun hikayoyin dasuka gabaci namu kai ka taɓa ganin amarya irina? Bazan maka ƙarya ba aguna wannan auren ƙaddara ne, kuma wlh dazaka sakeni a yau danafi kowa murna" Saukar hannun sa kawai taji a kuncin ta saida taga wasu matasan tausarari, da sauri ta riƙe wurin tana kallon sa "Allah ya isana tunda ban maka komai ba kake duka na" Hannu ya saka ya ɗalli bakinta, nan da nan ta soma turjiya a ƙasa duk ta tarwatsa kayan dake wurin har ruwan shayin masu zafi dake wurin suka zubar mata a ƙafa! Da sauri takai hannu ta murza wurin saiga fatar ta saɓule sai sabon ihu, da ƙyar tayi shiru ta soma sauraren sa


"Haba Nihal, shekarunki ashirin da ɗaya kina wannan haukan meye haka? Kukan ta ta ƙarawa sauti, mesa zaka tsaneni, mena maka niba mace bace kawai saika ajiyeni a kusa da mata kayi muzgunamun, tunda baka sona ka rabu dani mana! Rungumar ta yayi "Haba Nihal waini yaushe nace bana sonki, shine zaki ƙona ƙafarki"


"Kaine ka dakeni, kanacin zalina ban maka komai ba, baka tausayina ko kaɗan, ka tausayamun mana nima macece, dan Allah ka sake ni" Runtse idonsa yay cikin takaici "Calm down mana, kiyi shiru tayaya zan sakeki, yaya zaki riƙa magana irin haka ke bakya ganine ina matuƙar sonki Nihal, idan bansoki ba wa kikeso naso a duniya" Bata saurara ba ta ce "ƙarya kakemun kafison waccen shegiyar Khaleesat ɗin muguwa, na tsane ta wlh" Zaunar da ita yayi akan kujera ya shiga fifita ƙafar yana mata sannu "Nihal Mesane kikeson rikitani, ni bansan menakeji a raina game dake ba amma kome nene nasan mai nauyi ne sosai, yaya zaki ƙona kanki irin haka, tashi muje asibiti" Ƙwace ƙafar ta tayi da sauri "Ba inda zanje wanke ƙuna suke, kaɗanne zan kula da abuna, tunda dukana kake saina gayawa Ummi" Miƙewa yayi ya ƙureta da ido, kome Nihal.ke nufi da tsiro da sabon hali irin wannan, yasanta da surutu sanda take ƙarama, ya bar Nigeria yana dawowa karatu ya tarar tayi hankali sai wani girman kai datake fama dashi, ana soma shirin haɗasu aure ta shiga gaba dashi gaba ɗaya inzaiyi awa biyar a wurinta bata tanka maganar sa, yanzu kuma meye haka?" Ganin zata tsaya yi masa musu ya sanya gaba ɗaya ya ɗagata zuwa waje sai wutsilniya take da ƙafanta.


***************
Khaleesah a rikice ta shirya ta fita, kai tsaye wurin Hanifer taje bata ma nemi izinin Hakeem na fita ba, da motar Hanifer suka nufi wurin boka, dama sabon boka ne za'a haɗata dashi.


Mom Nu'aiym.
07084161619
9/17/21, 10:51 PM - Buhainat: HM


23.


Kallon ta yayi yanda ta ƙwamushe masa riga tanata zabga ihu, ana ɗaye ƙunar tamkar ana ƙwaye mata ranta, yanda take murzarshi. Gaba ɗaya shi kuwa yanayin mulkar datakewa jikinsa ya sakar masa kasala ga tausayinta yanaji, ƙunar bama wata babba bace amma dukta gama tara musu jama'a a wurin daƙyar suka gama sukayi dressing aka rufe wurin, shi ta dafa suka je mota tamkar ƙaramar yarinya aka take kuka "Momy wayyo ƙafana, momy" Shidai yayi zaune driver na tuƙasu tana masa taɓara a gaban driver har suka isa gida. A falonta ya ajiye ta sai kuka takeyi masa, ya ɓallo magani ya tsoyayo ruwa ya miƙa mata, nan da nan hankalin ta ya tashi da mamaki yake kallon ta "Wai meye haka ne? Saikace na baki kunamu ki haɗiya maganine fa agabanki likita ya bayar" Ja baya ta soma yi, ko kallon magani mayi tsigar jikina tashi yake, kayiwa Allah ka rabu dani bazan iya haɗiyar saba" Komawa yay ya zauna


"Idan bazaki sha magani ba ko allura zamu koma a miki" Langwaɓar da kanta tay "Haba Yaa Sadauki, waime na maka ne ka tsaneni? Allura bayan duk wannan azabar da nasha, ga yunwa ko karyawa banyi ba fa" Dafe kansa yayi "Me kikeso kici yanzu a dafa miki"


"Su dafan indomie da ƙwai yunwar zata kasheni" Dafa kansa yayi sannan ya nufi waje inda bai dawo ɗakin ba saida aka dafo da ƙwai sannan. Miƙa mata yayi sannan yaja mata ƙaramin centre table gabanta ƴa karɓa ya ɗaura mata akai sannan ya nemi wuri ya zauna, maƙe kafaɗa tay "Ni ka bani da kanka" Wani yawu ya haɗiya danya soma ƙosawa "Ke baki iya cin abinci bane ba? Kawar da kanta ta yi "Fisabilillahi mutum bashida lafiya, idan dai har bazaka bani da kanka ba yau yunwar ta kasheni" Tsaki ya ja sannan ya miƙe tsaye cikin nuna rashin kulawa "Kar Allah yasa ki ƙara cin abinci,ko duka jikinki kika ƙona iyakar iskancin da zakiyi kenan, nayi abinda zan iya ya rage naki yanzu kuma" Yana kaiwa nan yabar falon ita kuwa ta zauna ta dinga kuka taƙi kula abincin, wannan Halayyar tun a gida an hanawa Nihal yinshi amma bataji, yau inta ɗauki fushi da abinci sai tayi azumin kwana 2 daga ruwa sai ruwa.



****************
Malamin mai kamada malamin addini kallon khaleesah yayi sosai ya lashi harshen sa sannan ya ce, "Hajiya aikin dakika zo dashi mai sauƙi ne kuma mai wahala ne, amma idan kin sauƙaƙawa kanki wahalar zaki daɗe sosai kina damawa a hannun mijinki, zaki zama wacce tafi kowa fice acikin matan sa daga ƙarshe ma zaki iya korar sauran matan kekiyita murɗa kambun" Murmushi tay cikin jin daɗi


"Indai akan in taka wani matsayi ne a rayuwa Malam meye bazan yiba? Ni fatana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login