Showing 24001 words to 27000 words out of 67070 words

Chapter 9 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt

03 Sep 2024

9250

tsaye yakai hannun sa awurin sunan ta "Huddy na" kira ya wurga mata inda nan take ringing biyu ta ɗaga kiran tare dayin sallama, runtse idansa yaƴi wuri ɗaya sannan a hankali ya ƙanƙame soft pillow ɗinsa ya furta cikin murya mai sanyi, "Huddy na" wani sanyi ne ya mamaye ta ta nutse acikin katifar datake kwance akai ta lumshe idanta sannan ta ce, "Man i tot i lost u for ever, Alhamdulillah ka dawo rayuwa ta a yanzu, Alhamdulillah for everything" Murmushi yay tamkar tana gabanshi "Baby i missed you so very much, na miki laifi kinata kirana a waya ban ɗauka ba, Huddy so ake a rabani dake ina da gatana a duniya anaso a auramun mata har biyu kuma wallahi duk bana sonsu! Dafe ƙirji tayi tare da miƙewa zaune, muryanta yana rawa ta ce, "Baby ban gane ba" Kwantar da murya yay cikin shauƙi da tausayin da suke ba shi ya ce, "Baby dear please calm down, yanzu kina ina? Inaso zanzo sokoto na ganki gobe" Cikin mutuwar jiki ta ce,


"Tunda aka sanar cewar kana raye na tarkato nazo Abuja gidan anty Hali dubu, nayita ƙiran wayar baka ɗagawa man, najejje neman a Villa ban isa in shiga ba ya zanyi? Da sauri ya miƙe zaune cikin zaƙuwa "Beb u could have text me ai, sena san kina gari am coming to see you right away" Tsalle ta daka ta ajiye kiran, a gurguje tayi wanka ta shiga feshe feshe,.fuskar nan raɗau da makeup tamkar wata tsohuwar karuwa! Kwallin tsafin data karɓo danshi kawai ta saka take hasken manya manya idanuwan na ya ƙara bayyana. Huddy kyakkyawar gaske ce tamkar ka sace ta ga gudu, gata fara ƙal saikace haihuwar larabawa saidai nonuwa ne da ita jarkan jarkan amma ba ɗuwawu, yanda kukasan an wurga allo a jaka haka hudaisa take a baya. Wannan dalilin ne ya sanya koda wane lokaci acikin cikon ɗuwawu take da heeps na ƙarya, idanda zaku ganta a riga da zani intayi cikon nan zakuce wsnnan ita ta ƙera kanta! Tasha ado fiyeda tunanin mai tunani, sanda ya iso ya sanar yana mota da gudu ta sauka. Saida tazo yake iya hangota sannan ta sauya akalar takunta zuwa catwalk. Koke nace ƴar uwar Huddy kika ganta a wannan lokacin saita burgeki. Kwantar da kansa yayi ajikin backrest na sit ɗin motar ya lumshe idon sa yana mai ƙare mata kallo, tsarki ya tabbatarwa ubangijin daya ƙagi wannan baiwar Allah, yanason kyau arayuwa a ranshi ya ce 'kalli idon dan Allah" Murfin motar ta ɓalle ta shiga ta zauna, duk tasiri da ƙarfin da turarukan sa suke dashi saida nata ya bar masa dukan ƙirji, kai tsaye faɗawa tayi jikin sa cikeda shauƙi shi ɗinma a yau hugging nata yayi kafin ya ce, "My baby is all grown up now, me kikeci ne kika zaɓa ɓulɓul anya ma tukunna kinyi missing ɗina kuwa?" Janye jikinta tayi daga nasa sannan ta narke fuska wane zatayi kuka "Nayi missing naka sosai Man, i tot i lost ma, ko abinci ban fara ciba saida naji sanarwar kans raye na ganka a tv kana magana" Hannun ta ya riƙo yana murmushi "Am sorry, da farko na zata zan iya haƙura dake amma gaba ɗaya sainaga ina neman zaucewa shine na lalubo ki da gudu, wannan zuwan ma na neman alfarma ne" Ha ɗaɗdun idanuwan ta ta zube masa tana mai lumshe su "Man me kake nema aguna? Koma wane alfarma ne ina mai tabbatar maka ka samu tunkan ka faɗa" Serious face a ɗaura akan tashi "Da gaske?" ya furta yana mata wani kallo daya kusan kashe ta a zaune, wani irin sha'awar Hakeem takeji tamkar ta far masa takeji! Cikin shagwaɓa ta ce "To da wasa? Murmushi ya yi "So nake ki taimaka ki aureni Huda, so nake kiyi haƙuri da yanda ƙaddara tazo mana ki zauna acikin mataye biyun dasuka zama zaɓin iyaye agareni" Murmushi tayi mai ciwo dukda tarigada ta gama amincewa kanta da ƙafarsu zasu bar mata gidan imma anyi auren "Man koda zanzo ƙwarƙwara bayan kayi mata huɗu wlh indai zan rayu dakai.ba matsala, wannan buri nane in rayu dakai koda akwai ko babu, bare akan mata" Wani daɗi yaji ya mamaye ruhin sa gaba ɗaya nan suka shiga hira ta masoya, wayar dake ringing ta daƙƙo daga gefen murfin motar data ajiƴe ta ta ɗaga kiran bayan ta kammala ta ajiye wayar. Kallon wayar yayi "Baby meye haka? Meya samƴ screen na wayar? Kallon wayar itama tayi "Lafiyan sa ƙalau meka gani? Hannu yakai ya ɗauki wayan ya duba "Babu latest nashi ne? Murmushi tayi "Akwai mana last 2 weeks yafita" Riverse gear ya saka ya juya ya hau titi daidai "Muje kin girmi wannan, waima tunda kikazo kinje yawo kuwa? "Murmushi kawai tayi bata bashi amsa ba" Ɗan kallon ta yayi a dame "Menene Beb?" yatsun hannun ta tashiga ja "Kawai inajin kishin kane, idan fa ka aure wasu matan, kai mijin sune ko? Dariya yayi ya ce, "ƙuruciyar nan tana nan wai baby? Mijin sune mana" Ɓata fuska tayi "An you will be kissing and hugging them, bama wannan ba U'll be doing all sort of things with them ko? Da mamaki ya kalle ta "Meye wani sort of things" Cinno baki tayi waje "Abinda akeyi a haifi yara mana" Dariya kawai yayi "Yarinyar nan.ta girma, ke bakyaso nayi hakan dasu ne? Ya furta yana kallon ta "Banaso gaskiya, that thing suppose to me mine and mine alone" Mamakin sa ne ya ƙaru "What?" Rufe fuskarta tay da tafukan hannayen ta sannan ta ce "Anty Halidubu take gayamun yanda ake zama da miji, so banshirya sharing ba, tunda baka sonsu kawai ka auresu amma karka taɓa su" Dariya yay "Tunda baby bataso nime ya kaini? Kece zaɓina kuma kin isheni" Wani far tayi da ido ta ɗauke kanta ɗaya ɓarin. Shiru sukayi har zuwa lokacin da suka isa Maiƙaya mall. Fitowar su a mota yayi daidai da fitowar Nihal da mahaifiyar ta daga cikin mall ɗin kallon juna suka tsayayi shida Nihal na kusan 30seconds, shine ya fara wayancewa ya matsa kusa da momy ya durkusa ya gayar da ita, ta amsa da fara'a a fuskarta, Nihal a cen ƙasan maƙoshin ta ta ce "Hakeem ina wuni" Miƙewa yayi suka ƙara kallon juna sannan ya ce, "Nihal kina lafiya" Bata bashi amsa ba ta mayar da dubanta zuwaga Huddy wacce ta saka cingum a bakin ta tana ta faman taunawa ta ɗauke kai daga dubansu, ga alama yanayin kallon da Hakeem yakewa Nihal ya ɓata ranta. Mommy tsayawa kallon ta tayi daga sama har ƙasa ga iyayen fake nails anyi fixing, ga gashin doki an zubo har gadon baya hatta idonta lashes ne, tabbas fara ce amma a kallon farko zaka fahimci tana ƙarawa da mai, Jinjina kanta tayi sannan ta ce dashi,


"Bayan isha ka sameni gida Hakeem" Saida ya russuna sannan ya ce, "Inshaa Allah momy" Murmushi yayiwa Nihal ita ko tamau ta tanke fuskar nan abinda ya sagar masa da gwiwa sosai. Gaba yayi Huddy tazo ta wuce ta gabanta tana watsa mata wani mugun kallo. Wucewa sukayi kawai suka shiga motar su suka zauna driver yaja suka fara tafiya, waya momy ta zaro a jakar ta ta kira Ummi, "Hajiya ba'a samu bane? Gyaran murya tayi sannan ta fara magana "Dan Allah ki kira Hakeem kice ya sameki gida yanzu, nima ina kan hanya" Da mamaki ta ce, "Lafiya dai? "Inna ƙaraso zamuyi maganar" Ɓata fuska tayi sosai ya kalleta da kulawa "Huddy ya dai" A taƙaice ta ce, "Waccen mayyar ina ka sanu kuma meye na mayancewa wurin kallon ta" Murmushi gajere yayi sannan ya ce, "Wannan shine kawai? Dan Allah manta da ita kawai muje" hannun sa ta riƙo ganin yayi gaba yana gama faɗar haka "Magana nake maka fa" Ɗan shan mur yayi "Huddy meye haka? Dan Allah kinsanni bana maganar wani, kizo muje muyi abinda zamuyi mubar nan" Sanin halinsa yasa tayi shiru tabi bayan sa yanzun nan sai ya mata fushi.


Sanda Ummi ta masa waya hankalin sa ya tashi sosai, a gaggauce ya dire huddy gida ya wice Villa. Shigar sa Villa kai tsaye part ɗin momy ya nufa hankali a tashe, ganin yanayin fuskar Momyn Nihal kaɗai ya tabbatar masa yau halinta na masifa ya tashi. Kusa da ita yaje ya durkusa ya kuma gayar da ita, cikin tsare gida ta amsa ko sheɗawa baiyi ba ta ce,


"Zubar mana da mutunci zakayi a gari? Yaushe ka fara neman mata? Da sauri ya ɗago ya kalle ta,cikin damuwa Ya furta "Momy mata fa? Tsawa ta daka masa "Waccen yarinyar dana ganku tare kuna gararamba a gari wacece? Kana zubar mana da mutunci a gari, karasa wa zakayi yawo da ita sai ƙadangarun bariki" Cikin sanyin jiki ya ce,


"Momy Hudaisa ce fa, dana baku labarin inaso na aure yarinyar sokoto, hutu tazo wurin yayar ta dake aure anan" Miƙewa tsaye tayi cikin masifa "Lallai sadauki bakada hankali, yarinyar dazaka aura zan haɗu da ita kafaɗa na ya gogi nata bata gayar dani ba, kai kuma baka nuna mata muhimmanci na ba? Bayaga haka yarinya saikace ifirutuwa batada siffar mutanen kirki ko ɗaya kama daga suturun jikin ta har zuwa tarbiyar ta, wlh bari kaji indai ni Baraka na isa da kai wlh bazaka auri wannan gantalalliyar ba, nasan zakayi tunanin saboda inaso ka auri ƴar uwarka Nihal ne, to ka sani ur my son and so she is, banawa kowannen ku tunani da ban, dan haka daga rana irin ta yau na janye maka auren dake kanka na Nihal tunda baka so kuma bata so amma wlh karna kuma jin labarin wannan tsamurarriyar mainsifar angulu" Ummi dai batace komai ba, Hakeem tun yana ƙaramin sa a hannun Baraka ya tashi, sannan itace ta fara kawo shawarar tanaso ya auri Nihal, ada sosai suke shiri daga zancen haɗasu aure komai ya watse, idan har Baraka tayi hukunci akan ƴaƴa sam Ummi bata saka bakin ta, dan haka wannan ma bazata ce dasu komai ba. Ƙara zubewa Hskeem yaƴi ya shigaya akan tayi haƙuri yana son Huddy amma ina bata saurare shiba, daga ƙarshe ma korashi tayi akan ya bar mata wurin.


Mom Nu'aiym.
9/14/21, 3:33 PM - Buhainat: *CM*


18.


Ƙafan momy ta riƙe cikeda tashin hankali "Momyna Hakeem ne fa, dan Allah ki taimake ni karki rabani da Huddy, wlh kin mata fahimta ne kawai a baibai amma tanada nagarta, zan gaya mata ta daina saka gashin doki ta daina yin duk abinda bakyaso kinji momy?" Harara ta wurga masa "Abinda bana so ko abinda yake haramun ne? Yaya yarinya zata ganni taga ka kai gwiwoyinka a ƙasa ka gayar dani ta danna mun harara ta ɗauka kanta. Kaga Hakeem ka daina yaudarar kanka, na gaya maka daga kan Nihal ɗin har ita na janye maka auren su kaje khaleesa ta isheka, koba komai nasan batada rashin tarbiya, Nihal kuma baka sonta itama bata sonka na aure dai, so a bar maganar su" Nihal ce ta taso tazo kusa da momy dama wannan budirin dik da ake bata ce komai ba itada Ummi.


"Momy tayaya akan maganar auren sa da wata zakice afasa namu, bayan tun a jeji mukayi Gamo muka aminta zamu auri juna, dan Allah karki masa haka mun muku biyayya shima kuma ku masa adalci, aishi mijinta ne zai iya hanata ire iren wannan shigar kinji" Kallon Nihal kawai ya tsayayi itakuwa ko kallon sa batayi ba.


"Kai da gaske take kun yarda kun aminta zaku auri juna?" Momy ta tambaya tana kallon sa, nan ma Nihal tayi zaƙal ta sharɓe zancen "Mom ai wanda ya mutu akewa ƙarya, nina mishi alƙawarin zan barshi ya auri zaɓin sa, yanxu kuma in aka masa haka gaskiya ba ai masa adalci ba" Sauke numfashi Momy tayi


"Tunda kince haka shikenan, Amma gaskiya wannan yarinyar saika kula da tarbiyar ta" Baice komai ba ya kai zaune cikin nuna tsananin samun relief, itama Nihal haka. Ummi se a sannan tayi magana a hankali tana zube idanta akan Nihal


"Sakarƴar wane garice ke Dazaki yarda mijinki ya aureki da yarjejeniyar auren wata bayan ke, keda ya dace kiyi babban yaƙi ki raba kanki da zaman kashiya, ni ina nan tamkar zan tashi sama akan bana ƙaunar Sadaukee ya haɗaki da kowa amma ke shirme ne a kanki, idan kinsan bakya sonsa gayamun a fasa auren"ƙurawa Ummi ido tayi batako ƙiftawa, tabbas batason Hakeem amma tayaya zata kalli idon uwar haihuwar sa tace bata sonsa ? Wage baki tay "Mom ina sansa mana, dama shirme nake yanzu kuma na dawo hankali na, dukkanmu nida shi da kowa ƙaddara ce ta haɗamu saboda haka ni da ku dashi gaba ɗaya mu dauƙi wannan ƙaddarar muyi haƙuri da ita a yanda tazo" Kallon juna momy da Ummi sukayi nan take suka sakawa abin albarka sannan suka zauna zaman meeting da magana akan auren da Mr. President keta hura wuta acikin sati uku!


Gidan ake renovating kamar hauka, kai jama'a naira shegiya ce! Babban wargajejen parlor ne da girman sa zai ɗauke set ɗin kujeru shida kuma ko wanne zasuyi tazara da juna. Acikin wannan babban parlor ko ina an baza ƙofofi wanda gidan mai ɗauke da part huɗu kowane part ƙofarsa ta zuwa falon a haɗe take! Gidan yayi kyau ainun daidai gidan Ɗan shugaban ƙasa. Tsayawa fassara uwar dukiyar dake cikin gidan ma ɓatawa kai lokaci ne, Hakeem kullum bayan fargaba babu abinda yake.


**************
Gabatowar lokacin auren nan ba ƙaramin tayarwa Nihal hankali yake ba, yanzu ba ƙiyayyar datakewa Hakeem ko rasa zaid bane yake damun ta a'a, ita damuwar ta rashin koda kiran waya daga angon nata, haka zata rayu dashi? Idan har yau tun tana gidan su baya kulata intaje gidan sa fa? Batasan menene tsakanin sa da zuciyar ta ba a yanzu amma tabbas koma menene tasan cewar mai nauyi ne.


Khaleesa kuwa rashin yawan damuwa da ita da yake ba abu bane daya dame ta sam, to ina ruwan ta dashi tunda cen bayan kwana biyu yakan kirata kuma yaje gunta a garinsu so biyu, bayan nan yanda take ɗaɗɗaga kai kawai ya isa ya nuna maka cewar ba soyayyar mijin bane a gabanta mulkin take so!


"Ɓangaren Huddy kuwa soyayyace ta asali ake dandaƙawa itada Hakeem, wanda har ya zamana sukan raba dare atare, babbar damuwar ta ayanxu baifi ita kaɗaice ƴar talakawa ba acikinsu, bayaga haka kayan ɗaki yana neman yi mata karan tsaye, mahaufin ta dama sheksrunsa kusan 7 yana kwance yafa fama da ciwon shanyewar ɓarin jiki!. Tayaya zata rayu da waɗannan shaiɗanun da ruɓaɓɓun kkayan ɗaki? Takaici iya takaici ys ishe ta.


Hakeem yana kwance asaman gadon sa ya runtse idansa abubuwa sun masa yawa, baisan ta ina zai fara da waɗannan matayen uku ba, yasan yana yiwa Huddy son da koda kansa baya yiwa shi, khaleesah kuwa baya sonta sam, haka kuma ba wai ƙinta yake ba, kawai mahaifin ta ya tsana fiye da komai a rayuwa, ya tsani maƙaryaci, ya tsani munafuki, mayaudari kuma makwaɗaici. Amma Nihal fa? Zarya takeyi a tsakanin zuciyar sa da ruhinsa, ya tabbatar cewar gangar jikinsa da ruhinsa sun aminta da nagartarta amma zuciyar sa ce take hango masa Huddy aduk sanda yake tsara rayuwar sa tajin daɗi da mace! Meyasa baya yiwa Nihal adalci bayaji koda a waya ya kirata sama da so uku tun faruwar abinda ya faru shida momy. A hankali ya buɗe idonsa a lumshe sannan ya zari wayar sa ya kira lambar ta. Tana zaune tana dudduba kayayyakin da aka kawo domin shirin dinner ɗinta, a hankali ta zari wayarta tare da barin cikin mutane kafin takai ga ɗaga wayar kiran ya yanke call ɗin ya yanke. Tana shirin komawa ya kuma kira wannan karon a hanzar ce ta ɗaga tare da faɗin "Assalamu Alaikum" jin sautin muryarta ya sanya ya nutsa sosai acikin katifar dake kan gadon tare da lumshe idansa, "Amin wa Alaikissalam, Nihal" Yanda ya kira sunanta saita da ɗan rikice cikin dabircewa ta ce,


"Nihal kina lafiya?" A taƙaice ta ce,


"Lafiya na ƙalau" Shiru dukkansu sukayi na some seconds sannan ya kuma ce wa, "Akwai abinda kike buƙata ne? Cikin jin zafin tambayar sa ta ce "Kamar ya?" Shi ɗinma haushi sosai ta bashi ya ajiye wayar tare da hanging up 'Yarinyar nan gaba ɗaya girman kanta yana ban haushi da ita, taje dan kanta' Ya ayyana a ranshi kasai.


*******************
Gaba ɗaya a haɗe akayi shagalin bikin nan a garin abuja, sannan kuma a Villa akayi ɗaurin auren dukka uku sha'ani na auren ƴaƴan manya. Babu wacce ta zama koma baya a kayan ɗaki, amma dau duk a ciki babu kamar Nihal wacce take cikin tsananin zullumi da baƙin ciki akan auren mutumin da gaba ɗaya bai damu da ita ba!
A babban falon daya zama mahaɗar shigar me gida kowane sassa daga cikin gidan aka tarasu Hakeem kowa ya watse an barshi da mace uku duk aciki babu wacce zaice yau itace uwargida, abu ɗaya ya sani auren Nihal aka fara ɗaurawa sannan na Huddy kafin na khaleesa, amma ya rasa ta ina zai fara, kallon su yake da ɗaɗɗaya ko wacce ta caɓa ado ido fiki fiki amma banda Nihal ga alama ma kuka take, nannauyan ajiyan zuciya tausayin ta ya sauke itada bataso danshi ya samu cikar burinsa sannan a hankali ya furta,


"Amm ina fatan ko wacce tasan cewar zaman haƙuri zatayi da ƴar uwar ta, ko wacce da dalilin zuwanta gidan nan, kuma ko wacce anan ƙaddarar ta ce aure anan, Allah ya rigada ya tsara cewar ku ɗinnan dukka matane kuma zan aureku a atare, babu wanda ya isa ya tsallake tsarin rayuwar Allah akan sa, saboda haka ku xauna lafiya, ku sani ni mutum ne mara son hayani ya ko kaɗan, bayan haka kuma banason ƙarya abinda zakayi in tsaneka shine ƙarya. Kwana bibbiyu zankeyi a ɗakin ko wacce ammafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login