Showing 3001 words to 6000 words out of 67070 words
Chapter 2 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt
khaleesah! Me nake ji a garin nan tamkar ƙarar saukar ruwan harsashi bayaga haka kuma ga kukan mashina, karki gayamun rashin jin maganar Momy na shirin tona asiri na! Kan khaleesah ta samu bakin bata amsa suka jiyo ƙarar bundiga a kusa da roof na ɗakin dasuke ciki, Muryar wani yana cewa "A duba ɗakin da baƙin ƴan matan suke ciki a fiddo mun su, wacce tace dani ƙurungu sarkin kawuna zanwa ciki ta haifi irina dan uban ta" Ƙirjin sune ya doka suka kalli window ɗakin da suke ciki, dama gini ne na alfarma me irin manyan windows ɗinnan dake ita amaryar ai mahaifinta wanine a Nigeria, faɗawa kawai sukayi suka fita ta window suka nausawa jejin dake bayan gidan a guje..... Allah ya tsare su dan gaba ɗaya ɓarayin basu lula ta bayan gidan ba. Haka sukayita gudu wanda tun suna gane inda suke wulla ƙafafuwan su har suka soma kasawa suka gajiya. Neman itaciya sukayi suka zauna s gefen ta sunata faman mayar da numfarfashi a wahale, jikin su banda rawa babu abinda yakeyi sun maƙale wa juna tamkar zasu koma ajikin junan su tsabar storo, anan suka yada zango har sanda gari ya waye tatas! Nihal ce ta fara miƙewa tsaye tana ƙarewa wurin da suke kallo, ƙirjin ta ne yayi mugun dokawa tace tana kallon Khaleesah,
"Gaba ɗaƴa gonakin damukayi ta kutsowa banga ko ƙurar suba anan Khaleesah, so nake mu juya mu koma inda muka fito semu bar garin, na tabbatar zuwa yanzu sun gama duk abinda zasuyi a ƙauyen" Khaleesa dake numfashi da ƙyar dama Athsma ne da ita yace tana kallon ta
"Nihal wlh bazan koma ba, kidnappers ne koda rana operation suke yi, muyi nan gaba kaɗan na tabbatar zamu haɗu da wani ƙauye a gaba, inyaso semu nemi hanyar gari mu koma gida" Hawaye ne suka gangaro daga idanuwan Nihal masu tsananin zafi, tabbas ta kawo kanta a halaka, banda hula da doguwar rigar bacci da kuma safa baɓu abinda yake ajikinta ko ɗan kunne ɓata dashi, seko zobe wanda ya zamar mata dole zama dashi dan ta saba, Khaleesa ma kayan bacci ne ajikin ta riga da wando masu santsi amma sunada faɗi se hula da safa, sabida yanayi irin na damina akwai sanyi ya sanya suka saka kaya me yalwa irin haka, dukda dai rigar Nihar gajeran hannu ne da ita. Hannun ta takai ta share ƙwallan sannan ta ce
"Khaleesah Momyna" Itama Khaleesa kuka ta saka ta ce,
"Nima Momyna nakeso naje gunta" Rungume juna sukayi suka hau kukan kusan rabin awa sannan suka haƙura suka kama hanyar dazata ɓulle dasu suke ga!
*****************
Saukar ruwan saman da ake me ƙarfi ne ya farkar dashi daga dogon suman dayayi wanda a zabure ya farka da salatin annabi a bakin sa, dukda ana ruwa wurin akwai yalwar haske, kallon kansa yayi kafin yabi inda yake zaune da kallo, tabbas kujera ce kuma ta jirgi sedai wannan karon yashe a cikin korayen ciyayi! A hankali ya soma tuna abubuwan dasuka faru dashi daga sanda aka soma sanarwar jirgi yana cikin matsala, ana nufi kenan wannan yayi surviving? Addu'ar dayake ta yi a lokacin da jirgin ke shirin tarwatse wa da gaske kenan Allah ya amsa, to amma wannan wurin inane? Kuma meyasa duk acikin jirgin bega ko turɓar saukar wani awurin ba saishi, kodai lahirar kenan??? Miƙewa yaƴi ya ganshi a tsaye adaidai lokacin kuma ruwa ya tsagaita sosai a wurin koma ace ya ɗauke cak! Wurin ya ƙarewa kallo tabbas shi kaɗai ne to ina sauran? Shidai a matsayin sa na musulmi ya tabbatar mutuwa akwai zafi kuma beji wannan zafin ba dan haka kuwa be mutu ba, amma to wai duk ina sauran passengers sama da ɗari da hamsin da jirgin ya ɗakko? Yanayin shirun wurin da rashin motsin komai ya tabbatar masa cewar a jeji yake! Aljihun sa ya laluba ya janyo wayoyi ukun sa ya shiga dubawa ɗayar ma ruwa ya shiga jikinta sosai na aljihun bayan wandon sa ƙwaya biyu ne ba abinda ya semesu gaba ɗaya ko alamar network babu awurin, gauron numfashi ya sauke sannan a sukwane ya soma taku batare daya san inda zashi ba, duk kuwa takun dazeyi daya ƴana fahimtar dashi tabbas yana ƙara nitsawa ne a ƙurmin jeji maras gaba ko yamma?!! Hankalin sa fa ya tashi babu wacce ke faɗo masa sai Ummin sa daya laftawa ƙaryar zai je Lagos amma yaje sokoto kuma yana tunanin bashida wata mafita a wannan wurin, haƙƙin saɓawa iyaye kaɗai ya isa a wurgashi wutar jahannama! Taku yaji a bayan sa wanda ya sanyashi saurin waigawa sedai bega kowa ba, wannan ya sanya yace tabbas illusion ne kawai, dan abinda ya sanya yanaso yaji kenan wato ya samu abokin tafiya amma shishi kaɗai fargaba kawai zata turashi lahira! Wani takun yaji sosai akusa dashi wannan karon wanda ya sanya ya juyo da ƙarfi yana ambatar "A'uzubillahi mina shaiɗanirrajeem" Shiru kuma tamkar beji komai ba, ya kalli ƙasan wurin ba taku sai nashi sannan kuma babu alamun kowa, nannauyan ajiyar zuciya ya sauke ya soma addu'a a hankali kafin ya juya zuwa hanyar dayake ji tamkar itace zata kaishi gari duk da dai yanaji ajikin sa akwai babbar matsala dan kuwa gabs ɗaya ya kula wurin babu wani taku dayake nuna akwai ko dabba dake bi! Shin ina ya nufa?
*****************
Lokacin da khaleesah da Nihal suka fahimci rana tana shirin faɗuwa basuga koda alamar kiyashi a tafiyar tasu ba sesuka fahimci cewar tabbas suna cikin tsaka mai wuya, idan suka ce su koma inda suka fito ma to bazasu gane hanya ba, sabida sunyi ta sakin hanya, duk inda sukaga kwana ɗauka suke hanyar gari ce sai subi ta kawai! Nihal data gama gajiya ta galabaita ga yunwa ga kishi ruwa ta kalli Khaleesa ta ce,
"Khaleesah ajali shine abinda ya fito damu daga gida gaba ɗaya, khaleesah idan da zamuga gari agaba toda tabbas babu garin dazamu gani babu gonaki a wannan yanayin na damina, amma ki dubafa sai daji muke tsallaka babu alamar gona ko ɗaya, bama wannan ba haba ɗaya babu alamun mutane kaiko dabbobi banaji sunabi wannan hanyar, ina mukace a haka zamu ta tafiya wlh mutuwa zamuyi" Kallon ta khaleesa tayi dan ita gaba ɗaya ma ta sare cikin tausayin kansu ta ce,
"Nihal muyi addu'a kawai, muci gaba da tafiya, in Allah yaso zamu kuɓuta" Nihal dai shiru kawai tayi tabi bayan ta amma sam bata samu nutsuwa ba.
Mom Nu'aiym ce.
Mai Buƙatar samun ci gaban littafin GAMO da kuma HUDA yayi ƙoƙarin ganin ya nememu ta wannan hanyar.
07084161619.
9/11/21, 6:59 AM - Buhainat: *GAMO!*
*NA: BILLY GALADANCHI*
3.
Ummi tana zaune sanarwar faɗuwar jirgi ya bayyana a faffaɗan TVn dake manne a parlor ɗinta, cikin hanzari ta miƙe tsaye tana ambatar sunan Allah wayarta da aketa kwaɗawa kira bata daga ba ta kalla cikin tashin hankali, ko wannan shine dalilin kiran? Da azama ta ɗaga kiran wayar tana sallama.
"Your Excelency Barka da wuni" Bata amsa gaisuwar ba ta ce,
"Jirgi daga sokoto zuwa Abuja akace yayi bundiga daga sama, babu mutum ɗaya daya rayu" Nisawa Commissioner of information yayi kafin ya ce,
"Wlh yau abinda muka tashi dashi kenan Ur Excelency, jirgin nan ya ɗakko sama da passengers 150, a zuwan ze zube wasu a abuja ya wuce da wasu lagos idan yaƴi juye, aciki akwai Ministan lafiya daya baro gida wato sokoto, akwai kuma kwamishinan jin daɗi na jihar kaduna, akwai mataimakin gwamnan jihar jigawa shikuwa yaje ɗaurin aure, Excelency gaba ɗaya gari ya rikice dan wasu ma yanzu muke samunmlabarin dasu aciki" "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" ta furta a giɗime
"Wannan labari ne mafi muni a yau, zan kira shi a waya yanzu" Nan da nan ta kirashi adole yace ze dawo a ranar.
****************
Yunwa ta gama sosai da matsalar su Nihal, gaba ɗaya sun rasa tudun dafawa, sunyi galabaita iya galabai ta har yamma basu kai ga wani gari ba. Neman wata bishiyar kuka sukayi mai kogo suka zauna a kusa da ita suna mayar da numfarfashi, seda aka daɗe sannan suka nemi cin ƴaƴan kukar ta hanyar tsinto wa su fasa su ɗakko ƙwame, haka suka zauna zaman shan ƙwame babu ruwan sha har saida azabar tsotso ya goge saman dasashin cikin bakunan su! Suna nan zaune gari ya haɗe da hadarin gaske tako ina, tsawa aka daka tare da walƙiya me hasken gaske saida suƙa ƙanƙame juna, anan sai ruwa ya fara sauka dama lokacine na tsakiyar damina. Suna nan an soma yayyafi sukaga hayaƙi irin na wutar itace a gefensu, kamar ka kunna wuta amma ruwan sama yana duka, kusa dasu sukaji muryar ƙaramar yarinya dabazata wuce shekaru goma ba a yanayin muryar ta tana cewa,
"Baba ƙaƙamu mai ƙwame ruwan sama yana shirin kashe miki wutar girkin ki, kuma sannan kinyi baƙi" Kallon juna sukaƴi sannan suka sake baki suna kallon inda maganar ke fitowa amma ba kowa a gaban su! Gaba ɗaya gwiwowinsu sacewa sukayi suka gagara koda motsawa ne daga inda suke. Daga cikin kogon sukaji muryar Babbar mace tana cewa,
"Ai dole nazo in tattare kayana zuwa ciki, baƙi kuma babu ƙwankwasa ƙofa? Basu jira wata fitinar ba suka arce da gudun fanfalaƙi duk iyakar hadari da iskar d akeyi be hanasu ranta a nakare ba, sunyi gudu sama da awa huɗu basu huta ba har zuwa sanda ruwa ya ɗauke suka isa inda ko ruwan ba'ayi da alama ma magrib tayi dan wurin ya ɗan soma duhu, wani fili fallau suka isa suka zube suna mayarda numfarfashi tare da ambatar sunan Allah, Muryar wannan yarinyar suka ƙara ji tana ce dasu,
"Bayin Allah kun jawoni da nisa, Baba Ƙaƙamu tace inzo karɓa mata kuɗin ƙwamen da kuka sha" Daga kwancen dasuke suka soma ja da baya da mazaunan su, basa ganin yarinyar se magana take "Baba fa tace lallai ne in karɓo kafin na dawo, dan idan Kakan mu yazo kunci bashi baku biya ba dik inda kuka shiga saiya nemo ku" kallon juna sukayi acikin ƙaramin hasken dabai gama wadatar wurin ba, da sauri Khaleesat ta zare zoben hannun ta wurga inda take jiyo muryar yarinyar "Bamuda kuɗi amma ga zinare, dan Allah ki dena bibiyar mu" Alamun an ɗauki zobe kawai suka gani, sai iska mai ƙarfi data wuce ta gaban su, da sauri suka ƙanƙame juna, anan sukayi ta addu'a duk wacce suka iya sannan basu shirya ba bacci yayi awon gaba dasu.
******************
Hakeem ya rigada ya sare da rayuwar sa, sabida tako ina ya tabbatar babu wani mahaluƙi a tattare dashi, amma tunda dare yayi gari ya sske wayewa ya lura cewar tabbas akwai namun jeji masu haɗarin gaske a jejin, dan kuwa idan beyi ƙarya ba tabbas cikin talatainin dare jiya ba komai sai hasken farin wata yaji rurar zaki, shin wai mafarki yake ko gaske ne? Shin Gaske ne tabbas wannan dashi yake Faruwa shi Abdulhakeem kokuwa? Koda wasa bai shiryawa rayuwar sa ƙarewa ajeji ba! Daga ƙarƙashin wani ƙatoton dutse dayake zaune ya mike tsaye, wurin yakebi da kallo ta ko ina, sannan a hankali ya zaro wayar sa ya kalli agogo, har lokacin babu alamun
Network, taimama yayi ya sallaci sallan asubahi ya jere gwanayen addu'oi sannan ya miƙe yaci gaba da tafiya.
Tunda labarin abinda ys faru ƙauyen nan ya shiga kunnen mahaifiyar Nihal tasoma kuka hankali a tashe, babu shiri haka ta gayawa mijinta gaskia, inda masifa tamkar ba gobe akan hakan kafin ya aika securities da sojoji akaje garin domin kama waɗan nan ƴan ta'addar amma sun sauya sheƙa, bayan sunyi nasarar kashe mutanen garin sama da goma tare da lalata har amaryar da aka zo bikin ta, hankalin senate president ya tashi dankuwa an nemi Khaleesat da kuma Nihal ba'a gansu ba aka tabbatar kidnapping nasu akayi dan haka aka ɗan tsagaita koda zasu kira waya amma shiru shiru kakeji tamkar an aiki bawa garin su.
Ummin Hakeem tana zaune abin duniya ya dame ta sosai tana tunanin Hakeem, gaba ɗaya wayoyin sa a kashe, kodai gudun auren nan ne da Nihal ya sanyashi guduwa? Bai taɓa kwatanta yi musu haka ba koda wasa, tunda suke dashi koda zai rufe layukan sa duka bazai taɓa rufe layin gida ba, President da kanshi ya kirata a waya baya gida lokacin dama ba zama yake ba, Tana ɗaga kiran sa ya ce,
"Fatima kikace Hakeem jirgin 11 yabi na zuwa lagos a wannan ranar? Da sauri ta ce,
"Tabbas haka ya gayamun, kuma ina barin gidan shima yafita"
"Daga ranar dayace dake zaije Lagos har zuwa yau babu wani mai koda sunan Abdulhakeem dayaje lagos daga abuja, anya babu abinda yake faruwa dashi kuwa, na saka amun tracing layin sa, amma gaba ɗaya nuna ake tamkar area da layukan suke ba'a Nigeria bane ba" Gumi me tsanani ya taso mata lokaci guda tashigs firfita da hannun ta katsam sekuma idan ya sauka akan jaridar dake kusa da ita dake ɗauke da hoton Hakeem da kuma date da aka buga labarin, muryan ta yana rawa ta ce
"Ibrahim ka duba jaridar Daily trust ta uku ga watan nan, ban samu na duba jaridar ba amma yanzu front page ɗin yaja hankali na sosai" Gyaran zaman sa yayi cike da isa kafin yace
"Ina Villa 3, ki ssmeni da jaridar yanzu" Bata ɓata lokaci ba wurin zarar News paper ɗin ta kuma ja mayafinta,.muƙarabanta suka bita a baya fuuuuuu tamkar zasu tashi sama har Villa 3.
Zama tayi a hargitse ta miƙa masa jaridar shikuwa a nutse ya soma dubawa,
"JIRGIN DAYA TASHI JIYA ZUWA ABUJA DAGA JIHAR SOKOTO HADDA ƊAN SHUGABAN ƘASA ABDULHAKEEM IBRAHIM TASA ACIKI!!"
-Har yanzu bamu samu ƙwaƙwaran labari game da mutuwar Abdulhakeem ba, amma tabbas jaridar mu ta tabbatar jirgin hardashi acikin sa, dan kuwa sun samu tattaunawa yana shirin hawa jirgin inda ya tabbatar mana cewa yazo yin wata ziyara ne dats shafi rayuwar sa bats aiki ba, amma abin mamaki har yanzu bamuji sunan sa acikin waɗan da suka samu wannan mummanan hatsarin ba ko meye gaskiyar lamarin sai Allah.-
President Ibrahim tasa hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba, nan da nan zufa ta rufe shi ya soma kiran waya akan tabbacin hakan a garin na sokoto take aka aiko da shaidar jirgin days ɗauke shi zuwa sokoton da wanda ya hau ya juya tabbas Abdulhakeen ya mutu shima!!
****************
A hankali suke tafiya cikesa rankaji, ko waccen su yunwa tayi kusan ta hallakar da ita, zuwa wani lokacin gaba ɗaya sun gama galabaita, banda ruwa babu abinda Khaleesat ke nema, gashi acikin kwans biyun nan ruwan saman ma andena yin sa, suna tsoro yau ace suci wasu ƴaƴan itatuwan ace saisun biya, tun khaleesah tana daurewa harta zube a ƙasa batako iya magana, hankalin Nihal ya tashi ta shiga neman yanda zatayi da ita amma ina ga dare yayi dole ta fita neman koda tafki ne ta nemo ruwa a hannunta ta bata tasha. Motsi takeji wanda ya sanya ta soma tafiya baya da baya, haka Hakeem ma, motsi yakeji wanda hakan ya tilasta masa soma tafiya da baya da baya yana kallon gaban sa, bayan su ya daki na juna wanda atare suka ƙwallah ƙara!!!
Mom Nu'aiym.
*✨TAURARI✨*
*WOOOHOHOOO* A inda ba ƙasa anan gaddamar kokawa🤼♀️🤺🤺, Akace Malam yazo salla tazo👩🚀. Ina gwanayen ku niga nawa Taurari masu haskawa, marubuta masu alƙalamin lu'u lu'u🖌️🖌️. Haziƙai na masu Fikrah, Shalele na masu amfani da Basira wurin sanya nishaɗi a zukatan makaran ta litattafan su, ina magana akan shahararriyar marubuciyar da akeji da ita me basira kuma fikirarriya wato SADNAF💃🏻💃🏻. Da kuma Tauraruwar ku datake baku nishaɗi wato BILLY GALADANCHI💃🏻💃🏻. Sunce a sanar daku cewa wannan karon sunyi tattaki zuwa wani sabon salo domin faɗakarwa da ni'imantar daku, sun ɗaura ɗamarar yaƙi domin nisha ɗantar daku kamar yadda sukayi a litattafan su da sukayi fice suka kumayi zarra a wannan shekarar *NAGA TA KAINA DA KUMA TSINTAR AYA💃🏻💃🏻.
Wannan karon ma sun shirya tsaf domin faranta muku da sababbin litattafai, Inda shahararriya kuma gwanata tace zata baku tukuicin littafin HUDA💃🏻💃🏻💃🏻 carkwai mazaƙwai. Yayinda Haziƙa BILLY GALADANCHI tace zata baku tukuicin littafin GAMO Dik akan farashin naira Ɗari biyar a duka biyun💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Sukace a baku wannan sassaukan lissafi.
2 books: 500
1 book: 300
VIP 2 books: 800
VIP 1 book: 500
Oya shake body💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Domin samun damar yin wuf da waɗannan litattafan ku tura kuɗin ku ta wannan lambar Acc ɗin.
2029764071.
First Bank
Nafisa Nuhu.
Shaidar biya ta wannan lambar
08033719070.
Idan kuma katin waya zaki tura,seki tura katin mtn ts wannan lambar wayar.
07084161619
Shaidar biya ta
07084161619
Muna maraba daku.
Mungode💃🏻💃🏻💃🏻
9/11/21, 6:59 AM - Buhainat: *GAMO!*
*NA: BILLY GALADANCHI*
4.
Neman hanyar gudu dukkansu sukayi sai kuma suka dakata suka waigo suna kallon juna acikin hasken dabai wadaci idanuwan su ba kasancewar duhun magriba ya rigada ya kunno kai, sun ƙurawa juna ido na wani lokaci kafin daga bisani Nihal tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un! Dan Allah aljanu kuyi haƙuri, bazan ƙara sha muku ƙwame ba, kudena zuwa a siffar mutanen dana sani bazan taɓa aminta daku ba" Juyawa tayi da gudu zata felle tana ƙwallawa ƙawarta kira a hargitse, tsayawa yayi yana kallon ta harta ɓacewa ganin sa 'Me Nihal takeyi a wannan ƙurmin jejin?' ya tambayi kansa a zuci,
'Shin wai anya ba mafarki yake ba kuwa? Amma kuma ta yiyu ba mafarkin bane ba tunda ya tabbatar ya hau jirgin kuma ya tabbatar anyi announcing cewar jirgi ba laifi har wasu suka saka rigar iska, da sanin sa kuma sanda jirgi ya fashe, ganin sa kan kujerar jirgi a jeji ya tabbatar masa cewar tabbas ya faɗo ne kuma Allah ya tseratar dashi. 'To kodai Nihal ma tafiyar da akace zatayi sokoto itama taje? kuma tana cikin jirgin daya faɗi dashi?' Ya ayyana a ransa, wannan tunanin kawai ya sanya yabi hanyar dayaga tabi da gudu shima yana kiran sunan ta aranshi yace 'Tabbas kenan akwai wasu mutanen da suma suka faɗo tanan daga jirgin nasu kuma Nihal tana cikin su!
"Ki tashi mu tafi Khaleesah,