Showing 15001 words to 18000 words out of 67070 words

Chapter 6 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt

03 Sep 2024

9255

wata uwar rorar datafi duk nashi ƙarfi, tsalle ɗaya ta faɗa akan Hakeem wanda yayi dabarar zaro kibiyar dake bayan sa yana maici gaba da kokawa da ita ya daɓa mata a ƙahon zuciyar ta sannan ya cillar da ita yayi hanzarin zare takobin sa ya yanka wuyan ta a wahale. Anan ya zube yana mayar da numfarfashi na kusan mintuna uku sannan ya zari Nihal ya saɓa a bayan sa ya ruga da gudun fanfalaƙi yabar cikin cahe ɗin dayake na dutse ne! Gaba ɗaya aguje ya soma laƙuben hanyar barin jejin inda ba kalar naman dajin dabai haɗu dasu ba amma wannan karon ba wanda ya kulashu.


***************
Mahaifiyar Hakeem tana kallon Momyn Nihal ta ce,


"Ashe dama ƙaddarar rayuwar Nihal da Hakeem bata tsaya anan ba, ashe lokaci ɗaya zasu tafi lahira su barmu da kewa" Kallon ta ita ma take cikin rashin madafa sannan ta ce,


"Your Excelency nifa na rasa dalilina na gagara yarda cewar tabbas yaran nan mutuwa sukayi. Kinga dai Hakeem bayan shi an tabbatar mana da cewar anga passengers sama da talatin da jirgin bai watse ta gefensu ba suka faɗa dazuzzuka, kuma shi hakeem yana cikin su sabida VIP ne kuma jirgin ance wutsiyar sace ta watse banda gaba gaban, duk wanda yake VIP.an ɗakko su a jeji wasu a ruwa, amma shi ai bamu neme shiba ko? Ita kuwa Nihal yanda suke dason kuɗin na da tuni sun kira sunce azo a kawo kuɗi a karɓe ta, ƙawayen ta sunce sunga fitar su ta window itada ɗayan ƙawarsu dasuka ɓata a tare. Nafi tsammanin sun shiga wani wurin ne sun gagara fita" Sauke nannauyar ajiyar zuciya Ammin Hakeem tayi sannan ta ce,


"Ana kan neman su fa, kuma tabbas ko jiya anga wasu a jeji naji labarin har a news, saidai shi Hakeem ne ba'a gansa ba, amma idan haka kike tunani bara zanwa His Excelency magana a tura neman dukkansu, su Nihal nemesu a jejin nan dake kusa da ƙauyen da suka je" Haka suka tattauna sosai ƙafin suka rabu.


******************
Wayar da ya janyo yana dubawa time yake kallo, ɗagowar da zaiyi saiya hango bukkoki tare daashuna jere a gefensu sama da ɗari. Da sauri ya ɓuya a bayan bishiya. Anan ya laɓr har dare ya raba ya daina jin ihun mutane sannan ya bar Nihal anan ya kutsa domin sato Khaleesa! Saida yaje tsakiyar wurin sai yaji surutai a bayan sa yana waigowa yaga bandits ɗin nan sun masa zobe! Ita kuwa Nihal kawai tsoro taji tafito daga bayan bishiyar tabiyo shi ashe ashe sun ganta suka kamota zasu zo da ita camp kawai saiga Hakeem aiko suka damƙeshi!!!! Kallon kallo ake tsakanin su da khaleesa har zuwa sanda gari ya waye hasken safiya ya bayyana suka nemi yin sallar asuba aka zanesu! Nan Oga ya fito da rawanin sa da wata zabgegiyar bulala a hannun sa aka kawo masa kujera ya zauna sannan ya kalli Hakeem ɗauke da bundigogin daya saya da hannun sa yayi wata dariyar mugunta kafin ya ce,


"Kai ubanwa kazoyi a gona ta" Kallon tsanata Hakeem.ya wurga masa kafin ya ce,


"Nazone in tafi da ƴar uwata da kuka ɗauko dabata mutu komai ba, dan Allah ku bani ita mu tafi" Dariya Oga yayi sannan ya ce,


"Wanda baizo gona taba ma neman sa nake bare kai daka kawo kanka, ai senashi uwarka tukunna yaro xan saurara maka, ya akayi akaga bundigana a hannunka, ko kaine kashe harɗo da mangal" Shiru Hakeem yayi inda Ogan nan ya zabga masa mugun mari saida ya gigice dukda zaman sa soja ya kalle sa cikin tsana ya ce,


"Bakada hankali ne kake duka na? Ka sakemun ƙanwata idan kuɗi kake so zansaka a akawo maka" Dariya sosai Oga yayi sannan ya ce,


"kai wanene? Ƙaramin ɗan iskan jeji mai yawo da mata? Bari kaji bakada kuɗin dazaka biya rayukan yarana daka kashe! Kashe ka zanyi bayan nasa samari hamsin hamsin sunyi waɗan nan matan fyaɗe a gaban ka sun mutu na baiwa karnuka sun cinye gawar su sannan in kashe ka!! Ƙirjin Nihal yana dokawa jin wannan maganar ta ce tana kallon ogan tana kuka,


"kayi hakuri malam, karka kashemu kaji, ƙaddara ce ta kawomu wurin ku, kaga wannan ɗan shugaban ƙasa ne jirgi ya faɗi dashi yazo nan, mukuma yan ta'adda irinku sukace zasu mana fyaɗe muka tsre ashe jeji ne mukazo shine muka ƙare a nan, ni mahaifina shine senate president ita kuma ƴar gwamna ce waccen" Ta ƙarashe maganar tana nuna khaleeesah" Wata mahaukaciyar dariya Ogan nan ya fashe da ita sannan ya ce,


"kawai yau idan akace Allah yana sonka magana ta ƙare, naji labarin ana neman ku keda wannan wato dama kune kuka kawo kanku, kai kuma ai ubanka ya zata ka mutu taɓaɓɓe an zata lagos zashi amma sai ga shege a jirgin sakkwato, wlh shine tabbas, kuma na ganku a jaridu, ba iyayen ku sunce bazamu taɓa kaiwa gareku ba! Ba sunce kun mana nisa ba, maza maza ku ɗakko manƴan wayoyi zan fara cin wannan mai bakin surutu kuyiwa senate president video ina amfani da ƴarsa, kuyiwa gwamna ma, shugaban ƙasa shi doƙe ɓiliyan biyar zai bani in bashi ɗansa, amma fa kafin na bashi ɗan nasa saina cire ƙafar sa ɗaya ya zama ɗan shugaban ƙasa gurgu. Suma matan na fasa kashe su, kawai so nake ayita kallon su ina amfani dasu kiwa yaƙi aurar shegu kuma ɓiliyan ɗaya ko wacce ubanta zai kawo ƴaƴan ɓarayi kawai! Jikin Nuhal yana rawa ta soma musu gashi yaran har sun fara video ya zabga mata mari ya yaga rigar jikin ta, hakeem ya zaburo wani ya saka kan ɓudiga ya kwaɗa masa akai take ya zube wurin a sume! Ya wurgar da Nihal kwance a ƙasa ya zare mazagin wandon sa yayi kanta, sai ihu suke suna sai oga, suka tashi Hakeem da ruwan sanyi ya farka a zabure yana ji yana gani ogan nan yake ɓarar ƙafafun Nihal tana ihu tana maƙewa amma sai marinta yakeyi


"Hakeem ka taimake ni" Yajiyo sautin muryar ta a raunace gashi a rirriƙe,kawar da kanshi yayi daga dubanta yana zubar da ƙwallah!!!!!!!


Anan zamu dakata da free pages namu wanda yakeson ci gaba ya tuntuɓeni da wannan lambar 07084161619.


Mom Nu'aiym.
9/11/21, 7:02 AM - Buhainat: GM
11.


Jikinta yana rawa sosai idanta yakai akan wuƙar dake rataye awuyan wani ya riƙe mata ƙafa ɗaya, da azama ta yunƙura ta zaro wuƙar kai tsaye ogan nasu ta cakawa wuƙar a wuya, tayi kukan nura ta cakawa na gefen sa, gaba ɗaya ƙaramar hauka ta shiga kusan mutane shida ta cakawa kafin su rirriƙe ta, sai ihu takeyi tamkar hauka sabon kamu. Gaba ɗaya su kuma sai sukayi wurin ogansu suna jijjigashi ganin baya numfashi ya sanya suka fashe da kuka, ɗaya daga cikin su ya zabgawa Nihal lafiyayyen mari


"Kika kashe oga, wlh yankan rago zan miki" Hakeem dasuka sake agigice bundiga ya raruma, da ido ya haddace adadin mazan dake wurin masu ƙafiya su tara ne, duk sauran rundunar su sun tafi operation, kai tsaye jikin sojojin ya motsa, ak47 ɗinda yayi sa'a da ita ya daddage ya harbe su duka acikin daƙiƙa uku! Wanda sukaji rauni acikin su ya ƙarasasu da bullet Mutanen dake jejin nan waɗan nan maguzawan suma ya kuncesu, waɗan da dama suna nan ya kuncesu hausawa ne ƴan uwansa da kuma inyamuri biyu sai bayarbe uku. Haka yasa suka ɗaura juna akan mashunan su suka shiya ɗauki Nihal daketa kuka ya nemo mata riga a bukkar su ya bata da zani suka saka ita da khaleesat. Hatta matan daya sama a bukkar saida ya harbesu ya dauke jakunkunan kuɗi ƙwaya uku suka ɗare mashunan suka haura keji!


Sunyi tafiya mai matuƙar nisa ga alama jeji suka luɓa ko yanzu, man mashuna suka soma ƙarewa dole aka shiga shirin barin mashina anan ahau ƙafa. Nihal gaba ɗaya a yamutse take dan sam hankalin ta baya jikinta zamu iya cewa kisan datayi ya taɓa kanta sosai harma batasan me take ba. Wani wuri da nisa sosai suka yada zango gaba ɗaya a galabaice suke, anan ɗaya daga cikin su ke cewa da Hakeem.


"Wannan babban jeji ne yallaɓai, ni soja ne kuma daga fita operation suka kama ni, nasan hanyar nan inada map ma saidai gaskia ko yanzu saimun cire son jiki munyi gaba, danma wannan ta kashe wanda yafisu sanin jejin amma ai da yanzu sun cimma na, matan nan su huta mu bar nan wurin" Nisawa Hakeem yayi cikin dana sanin abubuwa da yawa, idansa ya ssuke akan khaleesah, ƙafarta yanda tayi wani irin kore ya tilasta masa zubarda ƙwalla, cikin raunin murya ya ce yana kallon ta,


"Sannu khaleesah, anya zaki iya tafiya kuwa,ƙafar nan taki tana bani tsoro, wani green color nake ganin tanayi ga wani maiƙo saikace inda ake tatsar mai" Kallon sa kawai ta yi amma batace masa komai ba har sanda ya ƙaraso ya ɗaga ƙafar, dandannawa yashigayi a hankali yanaso yagane shin ruwane acikin ƙafar kome saidai me gaba ɗaya sai ya kula bata motsa ƙafar, batajin ma ana taɓawa, da sauri ya kalle ta a karo na barƙatai,


"Khaleesah kalleni" Ɗagowa tayi sukayi ido biyu,
"Idan na taɓa ƙafar nan dake miki ciwo kinaji?


"Ban fahimce ka ba? Kawar da kansa yayi ya mayar da dubansa zuwa ga ƙafar, hannun sa yakai ya danna da ƙarfi ko motsi batayi ba. 'Kaddai yarinyar nan ƙafarta ta gama ruɓewa?' ya ayyana a ranshi, cikin tausayi ya ce yana kallon mutumin daya kira kanshi da soja,


"Aikin me kake a sojoji? Sosa kanshi yayi sannan ya ce,


"Yallaɓai Nurse ne ni a sojoji, ina tsakiya da duba wani patient dayayi artabu dasu fagen yaƙi kawai suka mana zobe a camp ɗinmu, ƙarshen ta wanda suka ɗakkomu a tare kasheshi sukayi, wannan jakar dakaga na ɗakko ta aikice, nida likitan mu suka ɗakko duk wani wanda yayi rauni acikin su mune muke duba musu shi sun hana muna motsi, shi wancen likitan soji dasuka kashe ai idan suka kawo marasa lafiyan su allurar dake dasƙarar da jini yake musu basu sani ba sai mutum s hankali ya mutu, shine suka gane suka kashe shi, niko yanzu shisa na ɗakko gaba ɗaya jakar ta kayan aikin damuke musu aiki dashi, acikin wanda suka fita operation akwai huɗu danake koyawa aiki akan tilas, gwara karsu amfana da jakar" Sauke numfashin samun sassauci ya yi,


"Bani jakar,inaso zan duba ƙafar nan kafin mubar nan" Baiyi musu ba matso da jakar yana buɗe masa" Kallon kayan yayi sosai sannan ya bincike su tas, sanda ya saka hand gloves, sannan ya ɗauki abubuwan dayake so yayi amfani dasu ha haɗa da abubuwan kashe ƙwayoyin cuta ya wankesu sosai sannan ya mata shinfiɗa da wani xani aka kwantar da ita, shida ɗayan sojan nan suka cire wannan abun da maguzawan nan suka liƙa mata lokaci ɗaya wari ya soma tashi, nan da nan suka wanke wurin suka mata available injection dake cikin kayan sannan suka sake rufe wurin da waɗancen suka fasa, Nurse ɗin mai suna khamis ya ce


"Wai meya sameta haka? Hakeem yana duban yanayin ta ƴa ce,


"Maciji ne fa ya sare ta, its a long story amma khaleesa tasha wahala a rayuwa" Da sauri Khamis ya janyo jakar ya buɗe wani zip dake bayan ta yana janyo wani abu ya ce,
"Gaba ɗaya danasan macijine da tuni am bata wannan tasha, ganin wannan ramin ban zata maciji bane wlh, wannan ko shekara dafin maciji yayi ajikin mutum amai kawai zaiyi" Haka ya ɗakko ya bata bama wani wadattacen ruwa haka tasha ko minti goma batayi da shanshi ba gaba ɗaya inda yayi green ya soma tsatsafo da wani abu baƙi da green daidai inda zufa take fitowa mutum nan take ta soma aman jini baƙi shima da green, ta galabaita sosai kafin ya tsagaita sai bacci. Hannu Hakeem ya bashi suka gaisa yana fara'a ya ce,


"Kowane ɗan adam kaga ya faɗo a rayuwar ka kada kayi musun zaman hakan alkhairi agare ka, ashe kisan maguzawa da kisan bandits danayi sanadine dazai kuɓutar daku ya kuma taimaki khaleesah, ita kuma Nihal na fahimci hakan ya zama babbar barazana agareta, tunda idan ka kslƙe ta da kyau zaka fahimci sam bata cikin nutsuwar ta da hankalin ta hasalima ko ƙudane ya taɓa ta sakaga tana yi tamkar zata tashi hakan kuwa alama ce dake nuni kai tsaye da cewar kisan datayi ya haifar da wata matsala a kan ta tunda ba sabawa tayi ba, abin kuma ya bata shock wanda shine yaƴi harbi zuwaga ƙwalwar ta" Shiru duk wurin ya ɗauka kafin Hakeem yaci gaba da magana


"Ku tashi muyi gaba nizan goya khaleesah" Haka suka tashi ya saɓata a baya ya kamo hannun Hakeem, acikin yarbawan nan akwai mace ɗaya itama ta galabaita. Haka suka tasasu agaba zasu wuce sai dai me tashin kukan bindiga tun daga nesa suka jiyo nan da nan suka razana, Hakeem ya ce


"Da inda suke zuwa nan zaikai kilomtr ɗaya tafiya akan mashin a yanda nakejiyo sautin bindigar, maza a ɗaura kowa akan bishiya musam man matan nan" Suna ƙoƙarin ɗaura khaleesa daketa bacci kawai suka ƙaraso inda suke!




*Kada ku fitar mana dan Allah, mai buƙatar saya kuma ya nemi wannan lambar.*


07084161619.
9/11/21, 7:03 AM - Buhainat: GM


12.


Da sauri suka haye Hakeem ya ƙarasa miƙawa na sama ita shima ya ɗare. Lokacin ne ya fahimci sojoji ne suke farautar su da jirgin soja sukuma suna gudu lokaci ɗaya suna musayar harsashi da sojojin nan! Kallon khamis ya yi cikin ɗaga murya dan ba akan bishiya ɗaya suke ba ya ce,


"khamis take charge immediatly, its our soldiers, fire the bandits" dama sun baiwa wani police officer dake cikin su bundiga, nan danan sukayiwa bandits ɗinnan harbin akawo wuƙa. Hakeem yanada ƙwarewa sosai a harkar cikin lokaci ƙalilan ya sauke bandits sama da talatin, sojojin dake saman jirgi da masuyin saukar angulu da rigar iskama ficewa sukayi daga hayyacin su suna mamakin daga ina harbi ta saman bishiyoyi haka. Haka sojojin nan suka dakata da harbi suna kallon masu aiki nayi har sanda bandits ɗinnan gaba ɗaya suka mutu sama da mutane ɗari da hamsin sojojin nan sunyi nasu su Hakee ma haka. Saidai wuri. Harbo harsashi daga jirgin dasuke sun ajiye Hakeem tsarabar bullet a hannun sa, abinda baiko damu ba, zai iya cewa wannan shine karo na shida harsashi yana huda shi ya ratsa jikin sa. A hankali suka fara sakkowa daga kan bishiya suna sakko da matan nan. Sojojin nan gaba ɗaya dai sukayo kansu suna musu sannu Hakeem ya kalli wani soja daya sani ya sare masa shi sam bai gane hakeem ba yanda ya yakuce ya fita hayyacin sa. Yana murmushin wahala yace


"Sunana Abdulhakeem yaron mr president" Da sauri duk suka sara masa, mutumin da akan ƙwarewar sa a yaƙi da dabarun yaƙi aka bashi chief of defence na Nigeria gaba ɗaya. Mahaifinsa ya tilastashi ajiƴewa sabida an masa chaa aka akan Hakeem. Nan suka fara sowar ganin sa. A takaice suka ringa video na victory nasu suna kuma video tare da Hakeem akan samun nasarar halaka bandits da yayi da kanshi! Waya sukayi dake su sojoji komai tsananin jeji akwai abinda suke connecting suyi communicating da juna, nan da nan jirage suka yawaita awurin aka kwashi mutane zuwa Babban birnin tarayya, Hakeem saida ya jira mota tazo ta ɗebi wanda basu mutu ba acikin bandits ɗinnan ya shirya sosai akan seyayi ƙwaƙwaran bincike ta hanyar su!


*Yanzu muka fara labari*


Kai tsaye Asibiti aka wuce da Nihal da kuma Khaleesa, itama taƴi arziki da ƙafarta bata gama ruɓewa ba amma wani yanki daga ciki na nama ya zagwanye dole zasu kwashe su zubar sannan a ɗebi naman cinyarta a mata ciko dan babu yanda za'ayi abar wurin haka. Nihal kuwa sam tsabar shock bata yi wa kowa magana, gaba ɗayan ta ta rikice koda kusa da ita aka matsa zabura takeyi da sauri cikin ɗimauta.


Hakeem bayan labarin dawowar sa gaba ɗaya ya karaɗe Nigeria ƴan jarida sai sintiri sukeyi akan sonjin labarin abinda ya sameshi a jeji amma bai saurari kowa ba yace sai wani satin idan Allah ya sa ya murmure. Labari ake da kuma yaɗa videos nashi akan cewar ashe ba ɓata yayi ba bakuma mutuwa yayi ajirgi ba yaje ne ya yaƙi bandits a asirce kuma yayi nasa mutane sai ihu suke akan sadaukee hakeem babban soja, nan da nan soyayyar da mutanen Nigeria kewa shugaban ƙasa ya koma akan ɗanshi dayafi so.


Yana zaune a saman sopa ya nutse sosai baya tunanin komai da kowa sai rayuwar su a jeji, sunsha wahala matuƙa, koda wasa bai taɓa tsammanin cewar zasu dawo gida lafiya ba. Khaleesat itace macen datafi tsaya masa arai, yanada tabbacin cewar khaleesa tana cikin mawuyacin hali akan ƙafar nan. Ummi ce ta shigo da sallama ya ɗaga ya kalle ta zai tashi ya gayar da ita ta dafa faɗar sa


"Ka zauna abunka Hakeem, Alhamdulillah Allah abun godiya, duk sanda na kalle ka agabana sai inji kamar daga yau karka kuma fita ko nan dacen, kana ɗeban kewar ka da fargabar dana shiga na tsawon lokaci a tunanin ka mutu, se yanzu na tabbatar da tabbas jini abune na daban, sai yanzu na gano dalilin daya sanya zuciyata kwata kwata taƙi aminta da mutuwar ka, Alhamdulillah Allah abin godiya" Murmushi yayi shima mai sanyi,


"Ummi na ki gafarce ni na miki ƙarya, dan Allah ki yafemun bazan ƙara ba daga yanxu inshaa Allah" Dafa kanshi ta yi,


"Na yafe wlh har abada Hakeem sadaukin Ummi, Allah yayi maka albarka kaji" "Ameen" ya furta a sirance kafin ya kwantar da kansa jikin kujera.


"Sadaukee zanje na duba jikin Nihal. Yarinyar nan gaba ɗaya a rikice take,ko magana batayi" ɗan taɓe baki yayi kafin ya ce,


"Shock ne kawai ku rabu da ita zata dawo normal soon inshaa Allah" Kallon sa tayi tana nazartar yanayin sa


"Ance gawarwakin data gani da yawa ne suka rikita ta, jiya ma ana kalon tv agidan su ƙarar bundiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login