Showing 60001 words to 63000 words out of 67070 words
Chapter 21 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt
nan danan aka shiryashi aka shiga tarayrayar jikan president!
Wayewar gari kowa ya halarto dan haka ta matsa sai an sallameta dukda zubar jinin da take fama dashi, Hakeem ya hana, hankalin ta yanaga bayar da yaron nan dankuwa bata yanda za'ayi ta rasa wannan ikon datakeso ta yi, ta wulaƙanta mahaifinta yanda yake yiwa mahaifuyar ta, ta saka ya saki matarsa, shima Hakeem ya saki matayen sa ta zamto ita kaɗai ke faɗa aji a duniyar ta! Koda suka je gida wanka akayi mata aka kimtsa ta sosai sannan aka shiga hidimar abinda zata ci. Ƴar aikin ta dasuke ɗasawa ta kira ɗaki ta bata umarnin rufewa yaron baki sa seletop ta masa goyon gaba ta fita a unguwar zata bata number dazata kira ta kaiwa jinjirin. Basusha wahalar yin hakan ba saboda hankali gaba ɗaya baya kansu.
Bokan garinsu Khaleesah da kanshi yazo ya karɓi jinjirin, saida ya zauna sosai a mota sannan ya cire hular kansa ya kalli yaron ya ƙyalƙyale da dariya, tunda yake haɗuwa da mata marasa imani bai taɓa haɗuwa da mai hali irin na khaleesah ba! Tayaya mace zata wofintar da abinda ta haifa kacokam ta bada shi a kasheshi? Anya ma khaleesah tanada hankali kuwa? Anya babu ifiritai akanta kuwa? Zai nuna mata yafita iya shege, ba shi aka ƙonawa ɗansa tilo Namiji ba da yakeji dashi, yayi mata magana akan kece kikayi alƙawarin zaki kularmun da yarona ya dawo lafiya ya akayi haka amma saita bishi da zagi dan taga tanada kuɗi to bazai yi mata aikin ba amma tabbas zai ƙona jinjirin nan ya aika mata tokar sa, gwara ma ita zataga tokar ɗan nata shifa sai gani yayi a tukunyar tsafin sa yaro yana ci da wuta yana kiran sunan Baba amma sam bashida hanyar ceton sa!
A ɗayan bangaren kuwa kiran Malamin shaƙiyancin ta ta yi ta sanar masa ta haihu amma jinjirin baizo da rai ba, da mamaki ya miƙe zaune sannan ya ce "Baizo da raiba kokuma bayan an gama shiryasa acikin kayan masu laushi kalar sararin samaniya saiya koma, Hajiya khaleesah duk son danake miki baikai ko rabin son danakewa Jinina ba, karkimun ƙarya don kuwa gaba ɗaya zan iya ɓatar dake a doron ƙasa, ni dama ba karɓar yaron zanyi a hannunki ba, bakuma wai duniya zan nunawa nina miki cikin sa kika kuma haife sa ba, kawai dai inaso ki sani cewar nine uban sa ba Hakeem ba" Cikin takaici ta ce "A Germany na samu cikin jinjirin nan, dan haka ba ɗanka bane ka yarda ko karka yarda kuma yaro ya mutu, dabara yanzu ya ragewa mai shiga rijiya wa inma ya shiga ta kai kokuma ya shiga ta ƙafa" Tana kaiwa ta datse kiran tare da jan tsaki, ta gaji da ikon da Malam ke mata, ɗan iska kawai!
Malam kuma miƙewa tsaye ya yi yana zagayen ɗakin sa, aishi har sanda ta haihu yana kallo acikin ƙwarya har wanke jinjirin da shirinnsa, shi zata yiwa hauka bari ya nutsu har bayan suna tabbas zaije ya karɓe ɗansa, a kashe zai iya kashe Khaleesah akan ɗansa ɗaya tilo, koda taje germanƴ shiyasan da shigar ciki ajikinta nasa na kusan sati biyu itace batada hankali, yanzu akan wannan gudan jinin nasa basai yaga bayan ta ba ya karɓe abun sa!!!!!
Hafsat dariya take kamar wata zautacciya da pt stript a hannun ta, shagwaɓe fuska Nihal ta yi "Aunty Hafsah dan Allah fa" Zaunawa ta yi sannan ta ce wlh sabon ciki ne dake Nihal, tashi maza muje asibiti ayi scan inga ɗan wata nawa ne" Dariya itama Hafsa tayi "Nayi period wancen watan wannan watan kuma ya haura da sati biyu bai zo ba" Rawa Hafsa ta tashi tanayi tana waƙa, itadai Nihal dariya kawai takeyi, Aunty Hafsa akwai abin dariya.
Mom Nu'aiym.
10/2/21, 12:46 PM - Buhainat: *REGRET 2!*
38.
Maƙale da waya a kunne tana murmushi,kwance tamkar zata koma gaba ɗaya acikin katifar, wani narkewa take acikin lallausar katifar shauƙi yana ɗebar ta, muryan ta cen a maƙale ta ce "Gaba ɗaya yaa Hakeem ko mai kamada kai nake so in haifa, kwata kwata bana son in haifi mai kama dani, tunda ka ce Babyn khaleesah da ita yake kama" Murmushi shima ya yi sannan ya ce, "Nikuma mai kamar ke nake in haifa, black but beautiful, kuma mace nake so, inta yawo da ita agari" Siririyar dariya ta yi "Ya Sadaukee yaushe zan dawo to? Gaskia inaso nazo naganka kuma inga New born" Dariya ya yi "Karki damu da kaina zanzo na ɗakko ki nanda kwana uku kinji" Ƴar ƙara ta sake "Happy me soon zan ganka" Yana shafar kansa ya ce "Kawai ke bakida buri face kiga cewar kin tastemun ruwan jiki tas" Turo baki tayi tana shagaɓa "Kai wai gaba ɗaya ba'a sirri dakai" Dariya yayi sannan ya ce "Wayyo Ƴaa keem, zan suma, kayi haƙuri jiri nake ji" Kuka ta somayi masa na shagwaɓa "Haba dan Allah ya Hakeem, wannan wasan ƴana bani kunya dan Allah ka daina mun" da kanshi ya datse kiran yana dariya yau yayi tsokana ya tabbatar a kwai babban fushi yau.
Khaleesah saida ta gama shirin ta tsaf sannan ta fito, mutane masu zuwa barka ta tarar sun cika falonta, da wanda ta sani da wanda bata sani ba, suna zazzaune. Wuri ta samu ta zauna sannan ta gaisa dasu da fara'a ɗauke a fuskar ta. Ganin anyi jigum ya sanya ta kalli mai aikin ta dake tsaye wurin ta ce da ita "Jainaba ki kawo Baby mana bakiga baƙi ba" Ɗan russunawa ta yi sannan ta ce "Bara na karɓo shi Aunty Huddy ce ta karɓeshi" Batafi 5mns da tafiya ba sai gashi ta dawo tana gunsheshen kuka wiwi. Da azama Khaleesa ta miƙe "Ke lafiya meye haka? Kowa saiya soma tambayar ta cikin sheshekan kuka ta ce "Auntƴ Khaleesah ne wai ita lallai ban.bata yaro ba, kuma wlh har nan ta zo ta karɓe shi a hannu na" Dafe kai tayi taje taga taga zata faɗi cikin ƙaraji ta ce "Wlh tarihi bazai maimaita kansa akaina ba, yaron ta da aka kashe takeso ta sauke haushin akan nawa yaron, tayaya zan rayu idan babu yarona, wlh saikun fitomun da ɗana. Wasa wasa fa ƙaramar magana ta zama babba, dankuwa kaf gidan aka tambayi yaro kowa ya ce bashi bane bai karɓa ba. Hakeem gaba ɗaya daina tunanin komai ƙwaƙwar sa tayi sai Nihal ce da aka kira ta mai waya yanata kuka sanda ya ɗaga wayar cike da tausayi, "Yaa Hakeem calm down, kayi haƙuri mummunan ƙaddara ne suketa bibiyar mu, kaga wannan abunda zaka kwantar da hankalin ka ka gane ne da farko ance ni yanzu kuma Huddy, kaga abin fa yafi ƙarfin gida yanzu kam dole saikun sako hukuma aciki, azo gidan ayi bincike sosai waya fita waya shiga, jinjiraye a ringa wasa da rayukansu sai kace tsuntsaye gaskiya ya dace ka tashi tsaye, gidannan akwai iyayen cameras ina? Cikin takaici ya ce, "Nihal akwai amma banda cikin gida, wajene kawai muba hotel zamu saka cameras a ɗakuna, a falone kawai muka saka shima nawa" Nisawa ta yi sannan ta ce "Yanzu ka kwantar da hankalin ka Yaa Hakeem, kaifa soja ne babba mai ƙarfin zuciya, ya dace ka zama jarumi, ni na tabbatar Aunty Huddy bazata taɓa aikata wani abu mai kamada wannan ba, so karka zargeta, acikin gidan ka idan akwai abun zargi to Khaleesah ce, amma banaji itama zata cutarda jinin ta"
"Kawai ni komai ya isheni, tayaya ƙananun yara, wallahi tausayi yaron nan yake bani, yanda akayiwa wancen kawai nake gani a idona ina tausaƴin wannan, amma ba komai Allah ya kuɓutar dashi daga hannun azzalumai" Jinjina kai tayi "Amma yaa Hakeem kasa ido akan khaleesah, dukda yake duk wayar datake yi Hafsa tana kwafewa tayi hacking layinta itama, gaskiya Yaa Hakeem ka tashi tsaye amma ana nema a mayar dakai wani iri" Cikin gamsuwa da bayanun ta ya ce "Babu illah Nihal, zan saka ido sosai inshaa Alllah. Sallama sukayi akan zata dawo washe gari sannan suka ajiye wayoyin inda ya rage raɗaɗin daya addabeshi ya shiga binciken gaske ance uwarsa sumanta uku, tana faɗae irin yanda akace anyi da wancen Babyn tana ihu.
**************
Cikeda nutsuwa ya isa ɗakin na Huddy inda ya tarar tana zaune akan sallaya ta harɗe hannayen ta a saman gwiyoyin ta, counter riƙe a hannunta ta kafe wuri guda da ido tamkar wata zautacciya! Zahiri idonta yana kan wurin datake kallo amma kwata kwata hankalin ta banan ya ke. Shi ɗinma a ƙasa ya zauna suna fuskantar juna a hankali ya ce, "Huddyn Hakeem bakida bashin kowa akanki dazaki tilastawa kanki zama acikin damuwa irin wannan, haɗuwa da khaleesah arayuwa mummunan GAMO ne da dukkanmu mukayi, banida haufi a kanki na fahimci komai da kowa, inada shakka akan uwa ta cutar da abinda ta haifa duba da yanayin da saƙonnin da aka turomun sukazo dashi na tabbatar ko yaronki khaleesah ce ta cutar dashi, kawai burinta tadaina ganin giccin ku a duniya ta sai ita kaɗai, wasu matayen gaba ɗaya akan neman duniya sun aminta da damalmala lahirar su! Basajin has gaba ɗaya burikansu yana tafiya ne akan yanda zasuyi su mulki alƙaryun da suka tsinci kansu aciki, amma ki kwantar da hankalinki ki tashi ki tsala ado kamar yanda kika saba ni nan inada maganin kowace shegiya a hannun na! Sai a sannan ta kalleshi ido cikin ido. "Ba zafin abinda akamun ya sanya ka ganni a haka ba Hakeem, zafin abinda nayiwa Nihal, dama saida ta gayamun tana tsoron Allah ya isan danake mata ya dawo kaina saboda batada haƙƙina akanta, gashi tunkan aje ko ina na fara girbe abinda na shuga ina cikin tsananin nadama, idan taji wlh dariya zatamun, idan taji zatace dani Allah ya ƙara, amma da adane sanda mukeda kusanci da aminci na tabbatar dazata tsaya ta ceceni! Kaiconi kaico kaina da idona ya rufe naƙi ganin gaskiyar datake ta gayamun, idanda zanwa Nihal adalci ita ce ta raini cikin nan" Hannunta ya kamo ya riƙe yana murzawa a hankali "Baki fahimci wacece Nihal ba har yau, ki sani ita a duk inda Allah zai haɗaƙu to gamo ne na alkhairi,tunda na gaya mata bata nutsu ba, tunda na gaya mata bata gajiya da kirana tana kuka, tana nan zuwa gobe gareki ta share hawayen idon..wayar sa datayi ƙarace ta sakashi katse zancen ya ɗaga cikin tausahin murya "Yaa Hakeem koda na kira Huddy bazata ɗaga ba, da sauri ya saka speaker "Please stay by her side, nasan halin Huddy zata iya zama ita kaɗai taita kuka zatayi ciwon kai,tanada saka abu arai, nasan yanda naji wancen lokacin ina tsoron wani abu ya sameta bana nan, dazaka amince danazo yau" Cikin fusata ya ce, "Amma tun ɗazu na gaya miki bazaki kamo hanya yau ba ko? Tayaya zaki niƙo hanya har nan alhali ba jirgi ba ne, ni an gaya miki karen hauka ne ya cijeni?" Yawu tayiwa haɗiyar ta kaici sannan ta ce "Em tom na ce dan Allah ka zauna akusa da ita" Baice komai ba sai murmushin yaƙe ya kashe wayar, kuka huddy ta rushe shi, bayan Hakeem har Nihal aka shiga tsakanin su yanzu kuma reshe ya juye da mujiya!
Ƙarar bundiga ita ce ta ruɗar da ilahirin mutanen gidan nan suka shiga rububi, gaba ɗaya farfajiyar gidan saita cika yaro da babba aka zubawa Hakeem da wasu sosjoji sama da ashirin ido dasuke sanye da kayam soja suna harbawa iska bullet ido! Hakeem saida kowa ya nutsu sannan ya saita ƙafar jainaba akaro na farko datayi fitsari a wando kenan ya ce, "Zan tambayeki so ɗaya jal bazan ƙara tbayar ki ba, nasan gaskiyar komai zan tambayeki ne saboda kawai ki ƙaryata kanku da kanku, ina kika kaimun yarona? Muryanta yana rawa da jikinta ta kalli Khaleesah data haɗe rai sai ta tuna irin azabar da Khaleesah zata mata tasan hakeem bazai iya harbin ta ba ta ce "Aunty Huddy na kaiwa shi ita ce...daram kaji sautin bindiga sai a ƙafar Jainaba saita ta tashi sama sannan ta faɗo ƙasa ya ɗauke kansa daga dubanta sannan ya ɗaura bundigar a saman kan direban cen munafuki "Ina kuka kai sabon jinjirin Khaleesah kaida asararriyar cen? Wani yawu ya haɗiya sannan ya tuna abinda aka ce za'ayiwa ƴarsa idan ya tona asiri nan da nan zufar wahala ta ƙwace masa cikin takaici ya soma murmura baki, saita kansa Hakeem yabƙara yi "Kanada ja kenan akan fasa kanka da bullet danace zanyi, ko bayan shugabancin ƙasa akwai ƙarfin ikon tsaron ƙasa dake kaina kana daga cikin criminals na ƙasa sai in harbeka in kashe banza! Zubewa yayi awurin hsnnayen sa a sama "Yallaɓai wallahi ba laifina ba ne, hajiya ce ta tilastani ta, sace mun yarinya ta ce zata saka a mata fyaɗe idan har banyi abinda ta ce ba, agabana ma tasa wani gardi yayita jagalgala jikin yarinyar shiyasa amma banda abinda ta gayamun bansan komai ba ɓankuma yiwa kowa ƙage ba, ni koda na ɗauki Hajiyar gidan senate bata ɗauke ba jinjiri kuma tabbas ban ƙaraso da ita gida ba amma nine ma na baiwa taxi driver kuɗi tare da kwatanta masa inda za'aje da ita, sannan nine tare da wannan matar ta asibiti muka kai yaron hsr wurin boka a mota, saidai wlh bansan me za'ayi wa yaron ba saida ta faru, yanzu kuma data ce lallai afita da yaron data haifa a cikin sirri saina tare yar aikin Jainaba muka kai yaron wurin wani yana zaune a mota,bansan me za'a mada ba" Da ƙarfi Hakeem ya kwaɗawa driver nan bayan bundiga saida ya suma! Sannan a fusace ya kalli Khaleesah daketa zare ido, a hankali ya taka a kusa da ita ya damƙi haɓsrta ys matse haƙorin sa a dantse ya ce "Ke ina yaron da kika haifa?" zare ido ta soma yi sannan ta ce "Sharri sukamun saidai ko ka tambayi Huddy" Mai gadin waje ne ya shigo cikin gida da leda a hannun sa da takarda, russunawa ya yi sannan ya ce "Wani mutum ne yazo ya kawo wannan ya ce a baiwa hajiya Khaleesah" Saketa Hakeem yayi ya miƙawa wani soja bundigar sa sannan ya karɓi takardar ga abinda aka rubuta aciki.
_Tsammani kike kinfi kowa wayo,kin kashemun tilon ɗana bayan saida kikayi alƙawarin zaki bashi kariya, sai gashi an ƙonashi ƙurumus, to aikin danace zanmiki ki mallake mijinki da zuri'arshi idan bani jinjirinki na fasa, ga gawar jinjirin ki nan.na ƙonashi da ransa yanada ihu har saida ya komawa mahaliccin sa!! Kiyi duk abinda zakiyi mai ƙaramar zuciya kawai_
Hakeem sake maimakta karatun dakardar nan yayi a sarari kowa ya soma ja baya ya kalli mai gadin ya ce "Zazzage duk abinda yake cikin ledar nan" A hankali jikinsa shima ya fara rawa dama yaji ƙauri ya ɗage kan viva poly bag ya zazzage saiga jinjiri a ƙasa an ƙonashi gaba ɗaya a kakkafe yake fatar dukta saɓule gwanin tausayi, tare wurin aka ɗauki salati, ita kuwa ta kafe yaron da ido batako ƙiftawa!
Mom Nu'aiym.
10/5/21, 11:30 AM - Buhainat: *FRAME*
39.
Asaman gwiwowinsa ya zube gaba ɗaya tare da fasa wata uwar ƙarar data kusan tarwatsa ilahirin! Huddy ce ta tallafi kafaɗun sa, itaɗinma ganin jinjirin a haka kuka takeyi "Calmdown please Hakeem, surely u'll overcom this, be brave" wata uwar ƙara ya kuma ƙwallawa sannan ya miƙe ya cafko wuyan Khaleesah data kafe wurin tamkar wata mutum mutumi haka ya shaƙe ta da ƙyar aka ƙwace ta. A lokacin gidan ya cika danƙam harda maƙota, nan take wanda basa iya gani su ƙyale suka fara video a ɓoye kafin ka ce mene duniya ta ɗauka.
**************
A hannun hukuma aka damƙa Khaleesah domin bincike amma abin mamaki bata baiwa kowa wahala duk abinda aka tambayeta zata bada amsa tiryan tiryan, sannan banda haka bata magana, batacin abinci bata komai, mahaifinta kuwa yayi tsaye akan cewar sharri akayi mata.
Agaban shugaban ƙasa mahaifin khaleesa ne a durƙushe yana gayar dashi sannan daga bisani ya ce, "Your Excelency akan maganar khaleesah ne, nikeso kar a duba abinda ido ya gani a baibai, so nake ka dubi girman Allah ka bada dama ayi bincike, banaji mace zata haifi yaro takuma bayar a kashe hankalima bazai ɗauki wannan maganar ba samsam, gaba ɗaya a burkice ta ke tunda taga yaron nan, bana raba ɗaya biyu ta shiga ɗimauta ne gashi an ɗaure ta tamau batada hanyar kare kanta" Nisawa Mr.president ya yi sannan ya ce "Banida tabbacin abinda aka faɗa amma koma wacece acikin matan sa take aikata hakan tayi babban laifin dabazai yafu ba, saboda haka na baka dama kaje kayi bincike sosai saboda gudun kada ashiga haƙƙin wani, na tabbatar cewar bazakayi abinda zai cutar damu ba. Godiya ya masa sannan ya bar wurin.
Yanayin yanda ya zauna ma kasan bada wasa yazo ba. Ya zazzaga yagama ganin direba da ƴar aikin Khaleesah, a offuce na dpo sai zubewa yake yana kaiwa gwamna gaisuwa, bayan sun natsa ya ce "Mutanen da aka kawo nan dasuka aikata laifi tare da khaleesah duk na zaga na kuma gansu, akwai maganar danakeso inyi dasu ka saka a kawomun su har gida yau da yamma ƙarfe huɗu" Russunawa ya yi tare da cewa "Yallaɓai aida waya ka kirama ya wadatar da kaina zan kawosu har gidan inshaa Allah" Miƙewa ya yi sannan ya gyara babbar rigar sa ya ce, "Wannan ziyarar inaso ta zama ta sirri, sirri mafi sirri acikin duk sirurrukan daka taɓa yi arayuwar ka, bana so koda zuciyarka tasan da wannan sirrin bare harshen ka yayi izgilin furtawa koda inuwar ka ne bare ganhar jiki da ruhin wani" DPO washe baki ya yi "Ai ranka ya daɗe banaji ma na sani bare na ƙarar, ko labari ma banjiba, inani wasa da abinda yafi ƙarfina uban marayu masu iyayen ma ka goya" Gaba kawai ya yi muƙarabansa suka