Showing 18001 words to 21000 words out of 67070 words
Chapter 7 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt
kawai taji ta dinga ihu" Gajeran murmushi yaƴi dabai wuce laɓɓan sa kafin ya ce,
"Ummi zata murmure ne, lokaci ne kawai" Gaba tayi tana faɗar "Allah yasa" sanda tayi taku huɗu sannan ta waigo ta kalle sa "Ko zaka taho muje mu duba ta ne? Gyaran kishingiɗar sa yayi sannan ya ce,
"Ummi gaba ɗaya jikina ciwo yake, ki gayar mun da ita idan kinje" Bata ja da tsayi ba kawai ta juya ta fita shi kuwa yaci gaba da kallon sa fin awa ɗaya sannan ya miƙe ga zari key na motar sa alamun shi kaɗai zai fita. Saida ya harba sosai akan titi sannan ya zaro wayar sa ya kira nata'ala yana ɗagawa ya ce,
"kace Khaleesah tana National hospital ko?daga ɗaya ɓangaren aka bashi amsa ya kuma cewa "Female surgical ward, Anex room 8 ko? Yana gama faɗar hakan ya datse wayar.
Da sallama ya isa ɗakin datake ya tarar ba kowa sai ita kaɗai idanta yana jikin ƙofar saidai zahiri ita ba ƙofar take kallo ba. Tsayawa yayi ya na kallon ta da murmushi ɗauke a fuskar sa na tsawon seconds sannan ya ce,
"Wai dama beb ɗinnan fara ce haka? Tabbb gaba ɗaya sanda nayi nazari tukunna na gano wacece anan" Murmushi tayi sannan ta kalle shi sosai, ita kanta dabadan muryar Sadauki ba bazata ganeshi ba
"Laa Yaa Hakeem, wai kaine, naga kayi fess kamar baƙin balarabe, sam.ban gane ba" Dariya ya kwashe dashi sosai sannan ya ce,
"Ahh kice baki ya buɗe, lallai ki ban tambaya ba na tabbatar kin samu sauƙi" Tsawon 40mns ya kwashe suna hira, baibar wurin ba kuwa saida ƴan uwan ta suka shigo.
Yana shiga mota kiran huddy yana shigowa a wayar sa, a karo na barkatai yanzumma bai ɗaga ba, ya ajiye kawai. Kirane ya kuma shigowa wannan karon family line ɗinsa ne kuma rington na swt mother ne yake tashi tilas dole ya ɗaga kiran yana mata sallama.
"Hakeem dazaka samu kazo ka duba Nihal, gaba ɗaya yarinyar nan bata cikin hayyacin ta, ina tsoro idan a jejin nan Nihal batayi GAMO da mugun abuba" Cikin taushin murya ya ce,
"Ummi zanje wata rana amma ba yau ba" Jin haka yasanya ta ce,
"Shikenan Hakeem sabgogin ne ko" A taƙaice ya ce "Ea Ummi" sukayi sallama ya ajiye wayar "Akan masa tilas akan auren wannan Nihal ɗin ya faɗa musibar da Allah ne kaɗai ya fitar dashi, abinda yakaishi gayin abinda sam kowa yasan ba halinsa ba ne. This time around zai gayawa Abi dan Allah abar zancen Nihal ɗinnan.
Mom Nu'aiym.
07084161619.
9/11/21, 7:03 AM - Buhainat: *GM*
"Kiji tsoron Allah kada ki mun sharing kuma karki fitar mun da littafi.07084161619.
13.
Agogon hannun sa ya kalla adaidai lokacin dayake ƙoƙarin shiga gidan, gaba ɗaya ya manta da cewar yauce ranar da yayiwa ƴan jaridar Nigeria kaf alƙawarin suzo zai basu labarin abinda ya faru. A yamutse ya isa falon ya nemi wuri ya zauna sannan ya ɗauki wayar sa ya kira mazawaje.
"Ka basu izinin shigowa, zan basu 30mns kawai akwai inda zanje" Haka ya dire wayar sannan ya fito daga motar bayan yayi parking ya nufi ciki inda zai kimtsa sosai kafin ya fito. Dik wani abu daya faru dasu a jejin da ysnda ya haɗu da matan nan saida ya zayyanewa ƴan jarida, artabun su da bandits da komai. Bayan ya kammala ya fita kai tsaye kuwa asibiti ya nufa agun khaleesah.
Sanye ajikin sa fari yadine mai asalin laushi da sheƙi, yayi masa ɗinkin big man yayi matuƙar karɓar fatar jikin sa, agogon hannun na fata ne baƙi, zallan sheƙin da fatar keyi kawai zai iya makarar da mai kallon agogon, takaƙmin sa da hular kansa duk baƙaƙe ne, iya kyau yayi kyau mu samman ƙamshin jikin sa mai daɗi zai haifarwa mai ƙaramin ciki da kasala. Tunda ya isa a harabar asibitin ake masa ihu da kirari irin na ƴan diyasa, kasance war shishi kaɗai ne ya sanya hannu kawai yake ɗaga musu cikin rashin sakin fuska, dama Hakeem ba ma'aboci dariya bane ba sosai saidai bashida baƙin rai. Da sallama ya shiga ɗakin inda ya tarar mai girma gwamna yana zaune yazo duba yarinyar shida mutane da yawa. Gaisuwar girmama wa yayi masa dukda siyasar gwamnan da shugaban ƙasar kowa partyn sa daban, matsawa yayi kusa da khaleesah dake ta faman shagwaɓe fuska ganin sa awurin. Harɗe hannayen sa yayi ya tsaya yana kallon ta da murmushi a fuskar sa
"Ƴan mata yada tabare fuska" kawar da kanta tayi a shagwabe, gwanda ka koma don ni fushi nake kwana biyu bakazo duba ni ba" Ɗan ɗage girar sa yayi sannan ya sauke gauron numfashi,
"Afuwan kinji sabgogin da yawa, inata samun baƙi ne daga ko ina ma" Murmushi ta yi sannan ta ce
"Ba komai, meka kawomun" Sosa ƙeya yayi kaɗan yana murmushi
"Ba komai fa, kawai nazo induba jikinki ne amma na sanar da Mazawaje lallai a kawo miki abinci daga Villa yau, irin yunwar kusan wata ɗaya dakikasha a jejin nan gwanda kiɗan murmure" Mahaifin ta sai washe baki yake tamkar gonar auduga,
"Ai yallaɓai daka barshi kawai, muna iyakar ƙoƙarin mu anan, zata murmure inshaa Allah, wahalar dakayi ma saidai Allah ya saka maka" Waigowa ya yi suka kalli juna ya ce,
"Na sani ai, sunana Sadukee Hakeem Daddy" Kunya ce ta kama gwamna nan da nan ya shiga dariyar wayancewa "Ba damuwa Sadaukee zanke cewa, sannu da ƙoƙari fa" Kallon sa ya mayar zuwa ga Khaleesah, cikin sigar tsokana ya ce yana kallon ta,
"Ƙwarangwal nizan tafi, ga Daddy da baƙi da yawa, kiyi ƙoƙari ki zama tuleliya kafin kibar nan" Dariya sosai tayi "Allah yaa Hakeem ko to" Juyawa yayi yabar wurin hsr yakai ƙofai ta ɗaga murya ta kira sa "Yaa Hakeem?" waigowa yayi ya kalleta batare daya amsa ba,
"Kaje wurin Nihal kuwa? Tazo dubani amma har yanzu bata cikin nutsuwa dan Allah kaje" Ɗaga kanshi yayi alamar ok sannan ya fita batare daya kuma cewa kanzil ba. Zama yayi acikin mota ya shafi sumar kansa bayan ya ture hular sa baya, aranshi yana kissima yanda zai je wurin Nihal baya son tuna baya amma idan yaje mezaice mata, batada lafiya is that enough reason for him to visit? Hular sa ya mayar gaba sannan yaja tuleliyar motar sa ƙirar prada jeep baƙa wuluk ya nufi gidansu, bazai iya ƙin zuwa ba after all khaleesah tace yaje.
Tunda ya isa yake zaune a mota yana kallon number wayar ta, saidai yasan batayi wlcm back ba tunda shishi kaɗai ya tsira da wayoyin sa. Mai gadi ya haƙura ya tura acikin guads dake wurin inda sukayi masa iso a falon baƙi kai tsaye. Yayi tsaki fiye da so goma kafin daga tashigo falon bako sallama ta nemi wuri ta zauna, abinda yake hassasa wutar ƙiyayyar sa da Nihal kenan! Wannan wane irin wulaƙanci ne? Yans tsakiya da tunanin da yake ya tsinkayi muryar ta kamar amma ta tilas tana furta kalmar
"Sannu" Kallonta yayi na daƙiƙa kusan goma kafin shima da ƙyar ya ce "Yauwa" A taƙaice ya kame bakin sa. Bayace ta maimaita kanta dankuwa sunfi mintuna goma babu wanda ya kuma yin magana. Saida ta gaji sannan ta ce a gyatsine "Momy ce ta ce kana nan inzo" Saida ya gama ƙarewa wacce akace tayi GAMO kallo sannan ya ce, "Khaleesah ce tace inzo" Ƙirjinta ne yayi mugun dokawa, batun yau ba abinda yakesa batason Hakeem sabida wannan rainin wayon, wato yau bama maganar Ummi tace yazo bace, magana ce akan wata budurwar sa tace yazo!!! Batace masa komai ba har wayar sa tayi ƙara, a hankali ya ɗauki wayar yana lambar sai kuma ya ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnen sa
"Ya Hakeem sannu da ɗawainiya fa, an kawo abinci har bammasan inda zan tura shiba, amma naga hadda wannan gyaɗar yara dake sakasu ƙiba aka kawo wai ita na meye" Washe baki yayi yana dariya
"Banaso inga kina ramewa Khaleesah, shiyasa nace a kawo miki catton goma, kiyita sha harki zama orobo" Ɓata fuska tayi tamkar yana ganin ta sannan ta ce, "Allah ya Hakeem mugunta ne, haka fa aka ƙeroni wlh a bushe" Dariya ya kwashe da ita kalmar ƙerowa data ambata ya bashi matuƙar dariya yayi mai isarsa hadda ƙwalla, kafin ya ce "Nazo induba Nihal kamsr yanda kima buƙata, naga ita lafiya lau take ma kune kuka damu" Dariya tayi kafin ta ce, "Ba haka bane ba, da gaske she's not her self"
"To Allah ya bata lafiya" Haka yace sannan sukayi sallama. Nihal tsabar baƙin ciki kasa ɗaure wannan abun tayi sanda tayi ƙwalla a kaikace ta share. Sannan ts miƙe fuu batare data kalleshi bama ta wuce abinta cikin gida abinda yayi mugun ɓata masa rai , yasha alwashin bazai ƙara zuwa gidan nasu ba.
Kan gadonta ta faɗa kawai ta rasa dalilin kukan ta, gaba ɗaya tinda ta dawo ta tabbatar wa kanta tayi GAMO da wani Hakeem daban ba wanda ta sani ba, tayi gamo da wani Hakeem daban ba wanda ta saba wulaƙanta wa ba, agidansu an rasa meke damunta amma tabbas ta sani Hakeem ne damuwar ta, inama zasu koma jejin dayake mata hidima da dariya tamkar bashi ba, a zuciyar ta ta ce 'Hakeem soyayyar ka tana mun barazana' Da sauri ta miƙe, Hakeem kuma? Soyayya? Ni? Allah ya tsareni na tsaneka hakeem!!! Ta furta a sarari.
Ɓangaren Hakeem kuwa, yafi 20mns da mota bai tashe ta ba, yarasa dalilin dayasa zuciyar sa taƙi kwanciya, anya ma ya dace ya kalli idanta ya ce mata khaleesah ce ta ce yazo? Kodai zai koma ya bata haƙuri ne? Shin yauce ranar farko dasuka fara haka? Meyasa yanzu zai damu? Tsaki yaja sannan yace a sarari "Tausayi kawai take bani"... Yaja motar sa da ƙarfi yabar wurin.
07084161619.
Mom Nu'aiym.
9/11/21, 11:04 AM - Buhainat: *GM*
*IDAN KINSAN BAKI SAYABA KARKI TAƁA MUN LITTAFI, KIJI TSORON ALLAH.07084161619.
Ƙanwarta dake kwance akan kujerar dake cikin ɗakin ta kalle ta tare da miƙewa zaune "Anty Niha lafiya dai?" Kawar da kanta tayi daga duban ta sannan ta ce,
"ki gayawa Aƙilu zamu fita yanzu" Zabura ƙanwar ta tayi cikeda ɗoki, "Yauws Big sis, gaba ɗaya ina matuƙar ƙaunarki, shiyasa da bakya nan nasha wahala sosai ba mai kaini yawo" Toilet ta faɗa bayan ta ɗaura towel, gaba ɗaya jikinta ta sakarwa shaya tana mai lumshe ido, duk inda taso tabar tunanin tunanin wannan wulaƙancin da Hakeem ya mata abun ya gagare ta. Tun sanda ts shiga jeji ta huta da kuma manta da matsalolin Hakeem yaya yanzu zai zame mata ƙarfen ƙafa! Bazata samu sassauci ba har sai ta samu yin magana da Zaid, shishi kaɗai ne a duk duniyar nan zai kwantar mata da hankalin ta yakuma mantar da ita duk wani nau'i na baƙin ciki da Hakeem yake shirin wurgata aciki. Tarasa meyasa Ummin sa take turosa yazo ya mata izgili, takuma rasa dalilin sa na zuwa inba rainin hankali ba........ Sanda takusan shafe sa'a ɗaya a ban ɗakin ƙafin ta fito, a gaggauce ta kimtsa itama Arwa ta shirya suka fito, dama momy bata nan saboda haka babu wanda sukawa sallama suka fita.
Hakeem ransa a jagule ya isa gida, shi ɗinma wanka yayi ya kwanta a rigingine ya lumshe idon sa. Abubuwan sun taru sun masa yawa sosai aka, mesa zai damu da Nihal? Ita wacece da zata wulaƙanta shi? Hsr abada zai gayawa momy bazai ƙara zuwa gun Nihal ba. Da farko yaso ya haƙura ya auretan amma ya fahimci tsanar datayi masa kasheshi ne kawai bazata iyaba shi ɗinma bashida tabbas akan hakan, abinda yace bazaiyi ba shine ya ke shirin yi duk akan Nihal. Wayarsa tayi ƙara da sauri ya zabura jin rington na mahaifinsa, cikin girmamawa ya ce "Abi Barka da warhaka" Gyaran murya Abi yaƴi sannan ya ce
"Ya akayi ka turo baƙi awuri na batare da sanina ba" Gyaran zamanshi yayi da azama "Na'am Abi niban turo kowa ba" Gajeran tsaki yaje kafin ya ce "Kasan Allah Abdulhakeem, dukkan ƴan matan nan ƙwaya uku next month zan ɗaura maka aure dasu! Kace Huddaisa ƴar mutan sokoto, momynka tace Nihal yarinyar senate president and i ask u kace ka yarda, yanzu yaya zaka Alhaj Marwan dawaki? Gidan uban wa zakaje da mata uku @ ur age? Sabida kana taƙamar kai sadaukee ne, bakada wayau ne mata sunfi yaƙi zama musiba ingaya maka" Rasa ma yayi me zaice mahaifin khaleesah kenan fa? Cikin sarƙewar Murya ya ce,
"Abi please listen to me abinda kake tunani wlh sam ba haka bane ba...ƙit ya Abi yayi hanging call ɗin abinda ya tashi hankalin Hakeem, mahaifin sa bai taɓa yi masa haka ba! Meyayi zafi yaushe ma ya aika mahaifin sa khaleesa gun Abi? Key ya zara ba shiri ko wayoyin sa bai tsaya ɗauka ba ya nufi asibitin da khaleesa take kwance a ruɗe. A hargitse ya faɗa ɗakin yau bako sallama, turus yayi ganin Nihal zaune tanacin Apple suna hira itada khaleesah, tana ganin sa ta miƙe tare da gayar dashi, mamakin yau Nihal ta gayar dashi ya sanya ya tsaya yana kallon ta kawao. Khaleesah tana washe baki ta ce "Sannu da zuwa Yaa Hakeem, ba ka ce sai dare zaka dawo ba? Har lokacin shida Nihal kallon juna suke, itace ma ta ɗauke kanta daga duban sa ta ce da Khaleesah "Beb am going now, u have a guest" Ta hugging nata tare da paking goshin ta sannan taja kumatunta tana murmushi ta ce, "Get well soon my dear" Murmushi itama ta mata "Thank u dear, ur more than a friend, gobe zaki dawo? Tana murmushin yaƙe ta ce
"Zan dawo gobe, bazan manta da ɗan waken ba kuma" Da haka tabar ɗakin duk wani motsinta Hakeem yana kallo. Saida ta ɓacewa ganin sa sannan ya kalli Khaleesa sosai ya ce,
"Meke nan kukayi keda Daddyn ki? Nine nace zan aureki dazaki tura mahaifin ki awurin Abi na wai da sunan ni nace inaso zan aureki" Da mamaki ta kalle sa, fuskar ta ɗauke da tambayoyi kala kala
"Haba mana yaa Hakeem, tayaya daddy na zaiyi haka nina tabbatar bazaiyi ba, abinda kawai nasan munyi magana akanshi shine dayace zai sauya sheƙa zuwa jam'iyar Shugaban ƙasa banda haka wlh ban sanar wata magana mai kamada wannan ba beside inada mijin dazan aura dabadan wannan ƙaddarar data samemu ba da yanzu gobe ɗaurin aure na" Shafa sumar kansa yayi a wahale "ƙiramun Daddynki a waya" Ba musu ta janyo wayar ta tayi kiransa ya ɗaga tare da cewa
"Ƴar baiwa" Wannan sunane da Daddyn ta bai taɓa kiranta dashi ba hakan ya sanya tayi shiru saida ya kuma ce wa "Ya akayi? "Yaa Hakeem ne yakeson magana da kai" Saida ƙirjin sa ya doka jin ta ambaci Hakeem amma haka ya daure ya ce,
"Ki bashi wayar" Hakeem yana karɓar wayar ya ce
"Me ka kagayawa Mr president? Dukda ran Daddy ya ɓaci amma a haka saboda son duniya ya wayan ce, '"Abun alkhairi na gaya masa da cewar kun haɗa kanku kaida Khaleesah" Cikin fusata ya ce,
"Nina gaya maka haka!! Yaushe nace dakai ina son ƴar ka, wannan ai rainin hankali ne, abinda ka ƙulla wlh kaje ka kunce! Da mamaki waɗannan kalaman khaleesah ta kalleshi, shikuwa bai jira cewar mahaifin ta ba ya hanging call ɗin tare da wurga mata wayar. Cikin zafi ta ce,
"Me kake taƙama dashi dazaka gayawa mahaifina magana" Kallon ta ya yi "Ke karki rainamun hankali mana, wannan duk ina gaya miki siyasa ce, niba wawa bane, kuma nasan abinda nake yi, bance zan auri ƴar saba meya kaishi cura kai, this will be the last time da zanzo nan, i hate lie's and liers, shameless people kawai" Yana kaiwa nan ya fita daga ɗakin a fusace. Khaleesa abin ya mata zafi ta ɗauki wayarta ta kuma kiran Daddy yana ɗagawa ta ce,
"Daddy meyasa kayi haka? Tsawa ya daka mata. "kina hauka ne, sai kuna soyayya zakuyi aure, karma naji kinmun musu wlh kina farawa zamu saɓa nidake, aure zan haɗaku koda baya so, ni nasan sharrin dazan masa, dole in ciyar da siyasa ta a gaba wlh! Shiru tayi dan tasan mahaifin ta tsaf zai ƙulla sharri inyaso, gabanta banda faɗuwa babu abinda yske yi!!!!
Mom Nu'aiym.
9/11/21, 11:04 AM - Buhainat: GM.
*Bazan miki Allah ya isaba akan yaɗamun littafina, Amma tabbas Allah zai sakamun.Baki saya ba karki karanta mun,.idan kina buƙatar littafina ki nemeni.ki saya, ƴan son banza association kuji tsoron Allah muna sane daku.*
15.
Shiru tayi tana nazarin abubuwa da yawa,.na farko dai har abada bazata taɓa yafewa Hakeem akan izgilancin dayayiwa mahaifin taba, na biyu kuma maganganun mahaifin ta take tunawa, me yakeso ya ce kenan? Auu nuna mata yake tabbas ƙaruwar suce idan ta auri ɗan president,kenan idan tayi sa'ar auren yaron president babu wani raini da kishiyar babarta zata ƙara kawowa babarta, na wulaƙancin datake mata akan batayi boko ba, ta karɓe matsayin first lady sabida itace taje makarantar boko, tun tasowar ta mahaifiyar ta ce uwargida amma gaba ɗaya wulaƙanci take gani, babu kalar malaman dabasa shiga amma kamar momy ƙarama tafisu hatsabibanci, shin ko wannan shine abinda malam mai mabusa yake faɗa na cewar zataga alkhairi? In hakane zata jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan? Taƴi nasarar aure babban mutum kuma ta wulaƙanta wanda taso a lokacin dataso!! Da wannan tunanin tayi wani lallausan murmushi a sarari ta furta "Tabbas zuwana jeji nayi GAMO da katar" Walwala idanta tayi sannan ta janyo wayar ta ta kira Daddyn ta, yana ɗagawa cikin shagwaɓa ta ce,
"Daddy na soma fahimtar ci gaban ka shine in auri yaron shugaban ƙasa, tabbas idan nayi haka naja maka girma awurin mutsnen dasuke yi maka gani gani, bayaga haka kuma Daddy na tsiyasarka zata ƙara farin jini, nan gaba kaɗan idan shugaban ƙara zai kuma takara kaima kanada matsayin gwamna kenan dan tabbas koda ka faɗi sai kaci balanta na na tabbatar kai mai farin jinine mahaifi na, na fahimce ka akan farin cikinka zan iya sadaukar da soyayyar danake wa Aminullah, saboda haka Daddy