Showing 21001 words to 24000 words out of 67070 words
Chapter 8 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt
na kayi komai ba komai wallahi" Wata dariya ya sheke da ita irin ta manya "Daddy's pet wannan shiyasa nake tsananin ƙaunar ki, kinfi mahaifiyar ki hankali nesa ba kusa ba, yanzu haka tunani nake hanyar dazan ɓullowa shi Mr. President ɗin komai yazo mana da sauƙi" Murmushi tayi sannan ta ce,
"Daddy barin gaya maka yanda wannan aure zai yiyu koda Hakeem baya so acikin ruwan sanyi" Taba sigarin dake hannun sa ya busawa iska sannan ya ce,
"Tun kina ƙarama kike maganin matsaloli na, na tabbatar ko yanzu ma banida matsala ki faɗa ina jinki" Nan ta zayyane masa yanda zasuyi maganin taurin kan Hakeem inda nan take ya kwashe da dariya sannan ya ce,
"Ki warke Baby zan miki abinda kike so,zan baki dalal amaurka ta miliyan goma kije waɗan nan ƙawayen da suka rainaki ki saya musu motoci" Ihun murna ta saka dama khaleesat burinta kenan taga gaba ɗaya tana taka raina amma Daddy baya bata kuɗi komai sai Salima, godiya ta masa sukayi sallama tana wani shaƙiyin murmushi 'Tabbas zata wulaƙanta duk wanda taso a lokacin da taso idan har wannan al'amarin ya tabbata!! Daddy ma saiya yabawa aya zaƙin ta duk abinda yayiwa Momyn ta saita tabbatar ya dawo bawai mahaifiyar taba hatta ita yana mata tsananin biyayya! ........
*BAYAN KWANA UKU*
Hakeem yayi tsananin mamakin jin cewar mahaifin sa yana neman sa da gaggawa a babban falon dayake karɓar manyan bakin sa, amma haka jiki a mace ya shirya ya nufi VILLA 2, inda acen falon yake. Kallon kowa yaƴi a hankali cikin mamaki gwamna kusan uku kuma duk ba na jam'iyar mahaifin sa, sannan kums ga wasu ƴan majalisu su biyu gadai manyan mutane nan taro tamkar na ƴan siyasa, mahaifin Khaleesa daketa sharar ƙwalla ya kalla saika ce ƙaramin yaro, ƙura masa ido yayi acikin fusata amma baiyi magana ba bai kuma gayar da kowa ba ya nemi wuri ya zauna kawai yana ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya. Mahaifin sa sai kallon yanayin sa yake tabbas akwai wata a ƙasa ganin yanda Hakeem yake kaiwa mahaifin yarinyar nan mugun kallo, nisawa shugaban ƙasa yaƴi sannan ya ce,
"Kayi magana Vice chancellor" Gyaran murya farfesa idi yari malami yaƴi sannan ya ce,
"With due respect sir, maganan damuka zo dashi mun faɗeshi a baya ka ce a maimaita agaban Hakeem. Yaron nan yana neman ƴar gidan Alhaji marwan dawaki, bazan ce ga tsawon lokacin da suka ɗauka a tare ba, abin dai duk bai bayyana ba saida wannan abin ya samesu a tare, yayi ƙaryar zaije lagos ashe tare suka hau jirgin sokoto sukaje yawon duniyar su, ita kuwa ta ce wa mahaifin ta abuja zatazo biki, abubuwa dai bazan iya faɗa ba, Allah ne ya tsare jirgin ya jefar dasu gefe acen suka haɗu da Nihal da bandits suka sace ita kuwa a cikin bandits suka taimake ta, to yanzu abinda ya faru shine yarinya tanaso suyi aure sai ce mata yayi bazai auri karuwa ba, alhali ya kore manemin auren ta, yarinya sai kuka take har jinin ta ya hau a sibiti, sannan jiya yaje asibitin ya zazzage ta ga bata lafiya ya dake ta, sannan kuma ba abinda bai gayawa Alhaji marwan ba na zagi aciki hadda rantsuwar koƴa lashe zaɓe na gaɓa saiya sa ka kayar dashi, shine mukazo roƙon iri mu bamaso wannan maganar ta fita dan Allah a bashi haƙuri ya auri yarinyar nan karta zauce wallahi muna tsoro ta faɗa saboda tana tsananin son sa wallahi" Tunda farfesa ya fara magana idan Hakeem suna kanshi, jijiyoyin gefen kanshi sun tashi sun fito raɗam dasu sunyi sutum sutum, gaba ɗaya jikin sa har wani cira yake tsabar fusata, wuri ɗaya yake kallo bayako ƙiftawa, kowa ya san hakeem yasan baya ƙarya shi sam! Ya tsani mai masa ƙarya kuma fiye da kowa! Yana nan yama rasa tunanin mai zaiyi ya tsinkayi sautin muryar Abi ɗinsa yana ce wa,
"Hakeem haka ne? Kallon mahaifin sa yayi ido cikin ido sannan da ƙyar ya ɗaga murya ya ce,
"Abi nifa yarinyar nan bance zan aure ta b......" Cikin tsawa Abi ya ce,
"My friend will you keep quit!! Kasan ba aurarta zakayi ba meya kaika neman ta da lalata, ka lalata masa yarinya kuma har kana iya kallona ka gayamun ba aurarta zaka yiba, ka sani duk videos na sintirin da kake zuwa asibiti kaɗai ya isa ya tabbatar mun maganar su gaskiya ne, cctv na asibiti an basu record na komai gashi sunzo dashi, ka tabbatar waɗan nan mutanen da kake gani suna ma sona, da wasu ne da wannan zasu lalata siyasa ta, sabida wallahi baka bina bashin rantsuwa saika auri yarinyar nan, ko yau na faɗi na mutu idan baka aure ta ba ban gafarta maka ba, shashasha kawai da baisan me yake masa ciwo ba aka, ga tashi ka bani wuri ka kuma shirya aure end of this month on 27, and the wedding most be grand wedding kamaji na gaya maka" Sunkuyawa ya yi cikeda ladabi ya ce "Kayi Haƙuri dan Allah Abi karkayi fushi dani, duk abinda kace haka zakayi, ya kalli farfesa ƙwalla a idansa ya ce, "Dan Allah ku bashi haƙuri, banaso ya yi fushi dani da kunsani bazaku gaya masa ba ku gayamun zanyi abinda kuke so,banason ɓacin ran mahaifi na kun sani ba lafiya ce ishashiya dashi ba" Kafin wani cikin su yayi magana president ya kuma cikin tsawa "Hakeem get out from here!!" Da sauri ya miƙe ya fita yana layi tamkar wanda yasha ya bugu, da farko ya zata GAMON sa da khaleesa Alkhairi ne tunda har ya taimake ta ashe zuwan ta a rayuwar sa tazone kacokam dan kawai tayi fatali da rayuwar farin cikin sa, ashe ba kowane alkhairi ne yake ɗaurewa alkhairi ba a rayuwa? Meyasa yazo ne a mara sa'a wai shi? Daga wannan sai wancen shi gaba ɗaya bazai taɓa hutawa ba, tafiya yake amma sam bai san inda yake jefa ƙafar saba, tunanin sa kuma ya tsaya cak! Baya gane komai sai surutan da farfesa ya watso cikin harshen hausa, susu kaɗai ne suke amon amsa kuwwa acikin kunnayen sa biyu, abin mamaki tun yana fahimtar kalaman harya gaza gane komai, duniyar ta soma juya masa inda yakai hannun sa ya kare hasken ranar daya haske idan shi sabida tana shirin faɗuwa daga haka kuma saigashi ya tafi luuuuu ya zube wurin a sume!
Bana tantama yanzu ne zaƙin wannan littafin yake shirin zuba muku citta!ku buɗe kunnuwan ku ku kuma bani aron hankalin ku, ku fahimci shin wane irin GAMO ne wannan.
07084161619.
9/11/21, 5:20 PM - Buhainat: *GM*
*Kiji tsoron Allah karki taɓa abinda ba naki bane, kiji tsoron Allah ki barmun abina a inda kika gani, kiji tsoron Allah idan kinason saya ki nemeni da wannan number 07084161619.*
16.
Mutanen dake wurin suka ɗagashi sama zuwa ɓangaren sa cikin jimami, lokaci guda labarin rashin lafiyar sa ya isa kunnen Ummin sa. Hankali a tashe tazo dubashi tare da neman Dr. Dake Villa yazo du bashi yamai allurar bacci ya sanar stress ne kawai zai miƙe.
Mr president bai ɓoyewa mahaifiyar Hakeem komai ba, ya tabbatar mata ya gama yanke hukunci akan Hakeem! Dukda ta tabbatar dole akwai inda akaiwa yaronta ƙazafi amma sam hakan baisa tayi musu ba akan halin yaran zamani, addu'ar shiriya tayi masa sannan ta ce da mijinta
"Abi yanzu kuma ya zakayi da Nihal?" kallon nutsuwa yayi mata "Haka zai haɗasu ya aura har wannan ƴar sokoton, shiyaji zai iya" Kallon sa tayi da sauri,
"Kayi haƙuri ya suri biyu abar zancen wannan ƴar sokoton, yarinyar gaba ɗaya ni bata kwanta mun ba" Shiru yaƴi yana dogon nazari ,gaba ɗaya haushi hakeem yake bashi sosai bako kaɗan ba.
*Bayan kwana biyu*
Hakeem ya samu sauƙi sosai amma gaba ɗaya ko ƙofar gida ya kasa fita, tunda ake sharri bai taɓa jin labarin irin sharrin nan da aka ƙulla masa ba, manya manyan mutane madu daraja suzo su zuba rashin ɗa'a akan wani dalili dabai san shi ba, da wanne ido zai kuma kallon Abi shi Hakeem? Mahaifin sa yana masa kallon fasiƙi mazinaci meyayi saura a rayuwar sa na farin ciki? Tayaya zai iya wanke kansa awurin mahaifi da mahaifiyar sa, koda wane lokaci ummi tazo dubasa yana gani tanaso ta tambaye shi gaskiyar lamarin nan amma ita kanta kunyar tambayar take bare shi, zancen zuci yakeyi har zuwa sanda mahaifiyar sa tashigo ɗakin da sallamar ta. Wuri ta samu agefen gado ta zauna sannan ta kalle shi cikin nutsuwa da sakin fuska ta ce,
"Hakeem inaso wannan abin daya faru ksrya dame ka, ni ban tara sani ba na sani cewar sani yana wurin Allah amma hakeem na tabbatar wannan bayanin shiri ne irin na siyasa, kayi haƙuri ka ƙyale su, ka auri yarin yar, wata rana sai labari dan Allah ka tashi ka kimtsa yanda mahaifin ka ya buƙata muje mu duba ta" Bashida ƙarfin dazai iya mata musu dan haka kawai ya tashi yayi feshe feshen sa ya kama hanya itama tabi bayan sa.
Da sallama Ummi ta tura ƙofar ɗakin tare take da escort da mata ƴan siyasa sunkai su goma, saishi Hakeem daya jagoranci tafiyar tasu. Khaleesa jiki ya warware tana zaune tanashan Apple itada wata mata dattijuwa haka. Da azama ta miƙe tsaye tare da rarumar hijabi ta saka, dukda ciwon da ƙafar ta ke mata bai hanata zubewa a ƙasa ba tana mai kwaranyo wa Ummi gaisuwa, kallo ɗaya ta gane ta, haba shekarun su kusan biyu da hawa karagar mulkin gwamnati. Taku biyu Ummi tayi ta isa gare ta hannu bibbiyu ta saka ta tasheta tsaye ta zaunar sannan ta ce,
"Ki zauna abinki ƴata khaleesah yaya jikin naki? Ɗan ɗago ido tayi ta kalli yanayin Ummi sannan ta ce,
"Da sauƙi sosai Alhamdulillah ai na murmure" Jinjina kai Ummi tayi sauran mutanen dasuke tare suka ƙaraso suka gayar da ita da jiki sannan ummi ta ce dasu
"Ku barni da Hakeem" kowa watsewa yaƴi ciki hadda dattijuwar dake jinyar ta wacce take murnar ganin matar shugaban ƙasarsu mai adalci. Zama akusa khaleesah Ummi tayi sannan ta riƙo hannun ta ɗaya cikin nutsuwa ta fara magana,
"Dikkanin abinda ya faru labari ya riskeni akan abinda yake tsakanin ki da Hakeem, naji zafi sosai daya kasance ace kun cire tsoron Allah keda shi kun mayar da saɓon sa kofin zumar ku, ina mai baki haƙuri a matsayina na uwa akan abinda ya aikata wa rayuwsmar ki, idan Allah yaso daga yanzu shine zai zama garkuwa agare ki" Kuka khaleesa ta ƙirƙi nan da nan ta zube agwiwowin ta cikin sheshekar kukan da ta ke ta ce,
"Dan Allah dan annabi kiyi hakuri, wallahi Ummi Nagartacce ne, mutumin kirki ne sharrin mahaifina ne dana siyasa yaje ya ƙulla masa, ba laifina bane cewa nayi zanje awurin Mr president in gaya masa gaskiyar cewar son abin duniya ne ya saka mahaifina yiwa hakeem haka, amma yace zai tsinemun inna gayawa Mr. President, Ummi karki zargi Hakeem wlh yaronki sadaukee ne, kuma bana son tsinuwar mahaifa ta bini da tuni naje na gayawa mahaifin sa gaskiyar abinda na sani. Kuyi haƙuri, kuyi haƙuri kuyi hakuri, bantaɓa fatan komai saina taimakon mahaifiya ta data zamto bora agidan mijin ta, dan Allah Ummi ki baiwa Hakeem haƙuri, wlh ba laifi na bane" Kallon tausayi Ummi ta wurga mata, tana son mutum mai gaskiya,ɗagota ta yi daga duƙen datake ta zaunar,
"Na yadda dake ƴata, na yarda da dukkanku, ammafa ki sani wannan maganar koda ace nizan gayawa Abi ita bazai yarda ba zaice kawai ina kare yaro nane dake. Kamar yanda Hakeem yabani labarin kun Gamu ne a jeji, inaga wannan itace ƙaddarar ku, ku yarda da ƙaddara ina muku fatan alkhairi. Saidai kuma dama nace innazo zan sanar dake Hakeem yanada dama wacce zai aura, a yanda naji ma ƙawarki ce Nihal, tun kafin ɓatanku aka rigada aka shirya auren saboda haka yanzu ma auren a tare za'a yishi wannan ita ce ƙaddarar dukkanku, saboda haka kuyi haƙuri" Kukanta ta ƙarawa sauti
"A'a Ummi, bazan auri Hakeem ba, wlh inada wanda nake so, ki taimaka mun in samu in aureshi,shine samuwar farin cikina Ummi, na taso acikin rayuwa ta rashin ƴanci nida mahaifiya ta da ƙannena dukda yake itace babba, ban taɓa samun wani farin ciki ba sai zuwan Yaƙub a rayuwa ta, saura wata ɗaya auren mu na haɗu da wannan ƙaddarar dan Allah ummi kimun rai, kiyimun tsaye in samu farin cikin raina" Shiru Ummi tayi tana kallonta cikeda tausayi yarinyar sai kuka take tamkar ranta zai fita. Hakeem ma yayi tsaye tare da harɗe hannayen sa a ƙirji what a selfish father ga khaleesah!? Wannan wane irin mugun abune akan siyasa ka gina auren ƴarka bisa ƙarya, yarinyar is crying in a deep pain why on earth was he thinking dazai zaɓi cutar da ƴar sa akan dukiya, shi Alhaji Marwan kuɗi bazai ishesa bane? Kafin zuwan siyasa ai yanada kuɗin sa. Duk kanninsu zance zuci suke sanda wani mutum ya faɗo a fusace cikin ana rireiƙeshi akan Her excelency ne aciki yana dagewa akan lallai saiya shiga,hayaniyar shigowar sace ta katse tunanin Hakeem da Ummi, ummi ta ce su barshi ya shigo, khaleesah na ganin sa ta miƙe tana nunashi da ƴatsan ta
"Yauwa Ummi kinga yaƙub nan, shine zaɓina lecturer ne a gwagwalada sabida yana mara ƙarfi shisa Daddy baya sonsa" Tsaki yaja sannan ya ce a fusace,
"Niba wawa bane khaleesah, harni mahaifin ki zai kalla wai ya bani akan na janye maganar aurenmu, dan yana taƙama ya samu yaron president ,niba makwaɗaici bane kamar ku kuma koba ko ƙwandala bazan aureki ba, na fasa, damacen na zata gidan arziki kika fito irin albarka, ashe ƴar mayaudari ceke sabida haka babuni babu ke" Dafa kanta tayi cikin jimami ta ce,
"Innalilƙahu wa inna ilaihiraji'un, nashiga ukuna ni khaleesah! Menayiwa Abbana ya tsaneni, meyasa zai tsaneni? Tun ina ƙarama ta yake sanya hannu wurin tattalin rusa farin cikina dana ƴan uwa na, meye laifin mu dan kawai munzo a mata, bayan yace baya ƙaunar mu mu ƴaƴa mata ne yanzu kuma sayar dani zaiyi, yaa Rahman ka jiɓanci lamari na, ya raheem yayi zaɓi na alkhairi" Yaƙub tsaki yayi ya fita a fusace cikin nuna tsananin ɓacin rai, alhali Hayar shi akayo, alhali anyi ne saboda a nunawa Ummi inganci da kyawawan halayyar Khaleesah! Zubewa take shirin yi Ummi ta tare ta, cikin sigar rarrashi ta ce,
"Khaleesah Calm down mana, duk wannan kururuwar da kike idan fa haka Allah ya tsara babu yanda zamuyi, shin kika sani ko aurenki da sadaukee shine alkhairin ki? Yanda naga kinada tawakkali haka nakeso ki ƙara, kawai kiyi addu'a, wannan yaron daga ganin yanda ya miki shima ba tarbiyar ce dashi ba, shin zakiso ki auri wanda idan yayi fushi bashida hankali? Maza kiyi haƙuri ki share hawayen ki kinji?" Shiru tayi sai ajiyar zuciya take. Haka Ummi ta miƙe tana kallon sadaukee ta ce,
"Inada taro shabiyu na safiyar nan, zanje taron yanzu, dan Allah try and calm her down kaji my son" Murmushi yayi saboda hsrga Allah khaleesa ta bashi tausayi. Ummi tana fita khaleesah ta sakko ta durƙusa kusa da Hakeem tana haɗe hannayen ta duka biyu
"Yaa Hakeem wlh inason yaƙub dan Allah ka taimaka ka bashi haƙuri" Kafaɗunta ya ɗago cike da tausayi ya miƙar da ita tsaye cikin sigar rarrashi ya ce
"Calm down mana leesah, mummuna ne fa yafini kyau ne? What if i become a very good and caring husband u ever dream of? Ki daina tilastawa kanki abinda bakida maganin sa, ni dake duk bamason auren nan, Nihal ma batason aure na kowannen mu acikin mu uku yanada wanda yakeso amma ya zamuyi if this is what destiny provide for the both of us? Always have faith and trust in Allah, he created us, he love us and will surely choose what is the best of all of us, so pray and pray again then have faith kinji" Tana zubar da ƙwallah ta ce,
"Yaa Hakeem ya zanyi da soyayyar yaƙub? Girgiza kansa yayi ya ce, "Just start hating him, kawai ki tsane sa zakiji ya fita a ranki" Jinjina masa kanta tayi alamun to. Ya ce, "Ki kwanta ki huta zanje da dare zan dawo kinji" Nanma batayi magana ba har ya fita. Ihu ta saka da tsalle tayi hanzarin kiran momyn ta cikin ƙaraji ta ce, "Momy they are the best of people we won!!! Ki biya wannan mai sayar da fruits ɗin kuɗin sa, aikin sa yayi tasiri" Murna uwarta ta hauyi suna ihu saikace wasu zautacci.
*************
Hakeem bayan ya buɗe mota ya shiga bayanshi yayi resting ajikin back rest na sit ɗin tare da runtse idan sa, mekenan yake shirin faruwa dashi, tabbas acikin iyaye akwai ɓara gurbi, mahaifin khaleesah ys gama cutar da ita, bai taɓa ganin maha'incin mutum ba kamar mahaufin ta, yanda take kuka kana kallon ta kasan cewar she's in deep pain, as a governor how can he stood so low!! Baya son khaleesa bai taɓaji yana sonta ba amma inshaa Allah he promise himself cewar he will make her happy for the rest of his life indai ya aure ta, Huddyn sa itace a ransa har gobe haka zai daure ya biyawa iyaƴen sa ƙudirin su da burikan su, shima kuma ya mallaki khaleesah ɗin sa kar baƙin ciki ya kashe sa.
Mom Nu'aiym.
Idan tabbas kinaso kuma tsakani da Allah halin saya ne bakida kimun magana.
9/12/21, 11:19 PM - Allah Akbar left
9/14/21, 3:33 PM - Buhainat: *BM*
*ƳAN SON BANZA READERS ASSOCIATION BA RUWANKU DA LITTAFIN NAN, IDAN NA KAMAKI KINA MUN SHARING KOTU CE ZATA RABAMU DAKE.*
07084161619.
17.
A sukwane ya shiga cikin gidan, gaba ɗaya yau kuma sai zuciyar sa ta karkata akan Huddyn sa, idan dai har ba muryanta yaji ba babu wani zaman lafiya. Kayan jikin sa ya zare sannan ya kwanta akan makeken bed ɗinsa mai ɗauke shinfiɗa ts alfarma. Wayar sa ya laluba sannan kai