Showing 54001 words to 57000 words out of 67070 words
Chapter 19 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt
kim tafi da baby ki masa wanka inji ward servant? Kallon Khaleesah ta yi da mamaki sannan ta ce, "Khaleesah ina baby dana bari a hannun ki na tafi wanka" Ruwan da khaleesah takai a bakinta ne ya kusan sarƙeta ta soma tari, saida ya tsagaita mata sannan ta ce, "Nihal duk anan nufi kike wai wasa kike da kowa har Ummi, wannan wane irin abu ne danla kawo Baby a ganshi bafa ni kaɗai na matsu ba dakikaga inata miki waya, kowa ya matsu yaga Baby" Cikin rashin fahimtar zancen ta ta ƙaraso acikin ɗakin sosai "Khaleesah ninake wasa ko kene? Tayaya zaki ce in bar yaron a hannunki intafi inyi wanka nagaji sannan yanzu kizo kina wasa da kowa anan, su Ummi da momy ne fa" Nan fa musu ya kaure saida Momy ta kalli Hakeem ta ce dashi "Kai waka bari da Baby da Hudaisa" A hankali ya ce "Nihal ce" Kallon sa tayi jikinta yana rawa sannan ta ce, "Yaa Hakeem Allah ita na barwa ina zanje da baby to? Ina akan babyn kace inzo muje nace ka tafi kawai? Miƙewa Khaleesah tayi, tazo kusa da Nihal.ta jijjjigata "Karki yadda ki ce zakimun sharri, muje a tambaya a waje ai akwai masu gadi, wata fita da baby a hannu? Nida ko ganinki banyi ba ni zakiwa sharri? Akan me ma tukunna kike ƙoƙarin wasa da rayuwar jinjiri, kai jama'a, kishin zamani ya zama musiba, wlh saikin fito da jinjirin nan, na fahimci so kike ki mayar da mutane shashashai" Hakeem sai wani kallo yake binsu da shi gaba ɗayan su, ganin yanda Khaleesah ke gumi sannan ta riƙe marar ta tana ihun za'a mata sharri ya sanyashi kallon Nihal a hankali ya taka kusa da ita sannan yana kallon cikin idon ta ya ce, "Gaba ɗaya ban fahimci abinda kike nufi ba Nihal, so nawa zan baki haƙuri akan maganar haihuwar nan da kika dami kanki a kanshi, zaki samu haihuwa lokaci ne baiyi ba, karki ɗauki ruɗin zuciya ko kuma zugar ƙawaye dan Allah ki fitomun da yarona wallahi shine farin cikina" Kuks ta soma yi sannan ta ce, "Haba Hakeem wai me kake tunani ne? Wlh tallahi Khaleesah na baiwa jinjirin nan" Ɗauketa ya yi da mari "Karki mayar danu sakarai mana, khaleesah tazo nan bata sameki ba, ta wuce Villa na kuma cewa ta dawo, mesa zaki mata sharri? Tsananin firgici ya tilasta mata zubewa agun a sume!!
Mom Nu'aim.
9/28/21, 12:26 PM - Buhainat: *TRAGEDY*
34.
Ummi ce ta riƙo hannun sa ganin kowa yayi kan Nihal ta ce," Wane irin mahaukacin tunani kake? Tayaya a rayuwa zakawa Nihal zargin sace jinjirin da aka haifa maka, shin idan ma ta sace sa ta kaishi ina? Me kake tunani ne haka akan ta? Banaji zata mana ƙarya akan yaron" Yana share ƙwalla ya ce, "Ummi kinaji fa khaleesah ta ce batama ganta ba, tayaya za'a ringa wasa da rayuwar jinriri kamar haka, yanzu idan har Huddy ta farka me zamu gaya mata?kuma tayaya zata nemi yin wasa da hankalin mu Ummi, abin nan mai sauƙi ne ta tashi kawai ta gaya mana ina takai mun yaro na" Ummi a hankali ta mayar da dubanta zuwa ga Nihal da aka yayyafawa ruwan sanyi ta farfaɗo, akan kujera aka ajiye ta saboda Huddy tana kan gado a cikin ɗakin tana baccin ta duk wannan hatsaniyar da akeyi batako motsa ba saboda sun mata allura ta huta abinta. Hannun Momyn ta ta cafko tana kuka ta ce, "Dan Allah Momy ki tasheni a wannan baccin dake ɗauke da mummunan mafarki, wlh idan ban farka ba zuciyata zata iya bugawa in sheƙa lahira, banaji na daidai, banida ƙwarin zuciyar ɗaukar wannan musibar ya rahman karka jarrabeni da wannan mummunar ƙaddarar" Ummi ce ta matso kusa da ita tana shafa kanta a kanta garin zuba mata ruwa duk an jiƙa mata sumar kanta,
"Nihal kalle ni" Ba musu ta wara idon daya kaɗa ya zama jajir ta kalle ta,
"Wannan ba wani abin damuwa bane zaki tashi hankalinki a banza, ni da ke da kuma kowa dake nan muna miki kyakyawan zato na kuma tabbatar kinsan cewar kowa anan ya san cewar babu inda zaki kai jinjirin da aka haifa ɗinnan, nutsuwa zakiyi kimun bayanin wa kika baiwa jinjirin? Wani yawu ta haɗiya mai ɗacin gaske, sannan cikin jimami ta ce "Gaba ɗaya tunda Yaa Hakeem yazo zai fita sai ya ce in ajiye jinjirin kusa da maman shi tunda yana bacci inzo muje mu sanar dake, sai na gaya masa ba'a haka, jinjiri dukda dai asibitin akwai tsaro sosai tayaya za'a ce a barshi bayan mahaifiyar shi allurar bacci aka mata. Haka na tilasta masa tafiya Villa ya ce hadimai zasuzo inje na huta da wannan na zauna shiya tafi. Tafiyar sa babu jimawa kawai saiga khaleesa bayan tazo saita tilastamun inje inyi wanka tunda ita gashi yanzu tazo, da wannan na bata jinjirin ni kuma nafita driver ta daya kawo ta na shiga motar sa akan zai maidani gida dama kuma ita tace inje ya kaini gida amma a hanya sai motar sa ta ɓaci danaga haka sai kawai na hau taxi amma ku tambaye shi kuji yaga na fita da jinjiri? Nini kaɗai na fita ita na barwa shi anan" Khaleesah dake gefe kawai saita saka kuka ta ce akira driver suka kirashi kuwa ya ce yanzu ya gama gyaran mota, nan da nan akace yazo asibiti, ya kwaso ya zo. Ummi da kanta ta tambaye shi inda a take ya ce,
"Ur excelenct a tabbas nina fita da Hajiya da asibitin nan amma saidai akayi rashin sa'a a hanya mota na ta lala ce, naso akira mata wani driver saita nunamun sauri takeyi na tara musu taxi suka wuce, dan yaron yafi bani tausayi sai cancara ƙara yake, ga alama yunwa yake ji, ta daice wanka zata masa, amma bayan nayiwa mai taxi ɗin bayanin unguwar mu saina ga bayan sun ɗaga sun sauya hanya, wani abu ne ya faru? Cikin ƙanƙancewar ido Nihal ke kallon sa, tama rasa bakin magana, khaleesah dake kukan munafur ci ta ce, "Alhamdulillah, kowa dai ya ji yanzu, idan har akwai abinda ake nema ni bana cikin sa, beside nasan halin Nihal tabbas wasa ta ke" Saikuma ta taso tazo wurin Nihal ta riƙe hannun ta "Nihal ni nasan akwai abinda ya faru dake a hanya, gaya mun menene? Ƴan iskan gari ne suke karɓe jaririn? Tsakanina dake babu yiwa juna sharri mu ƙawaye na Alkhairi ne ya GAMA mu, i will understand you gayamun a gida kika bar yaron aje a ɗakko shi? Gaba ɗaya bata gane komai sai bin ta da kallo take yi komai kama ya ke mata da mafarki, ji take tamkar tana shillo a sama, zuciyar ta a maimakon ta mata nauyi saiya zamana shillo take tamkar akan gajimare gaba ɗaya ji take tamkar babu zuciya a ƙirjinta kukan ma ta kasa yi.
***********
*Bayan kwana ɗaya*
Babu jinjiri babu kuma alamar sa, gaba ɗaya kan Nihal baya gane komai, tun jiya a asibiti bata ƙara yin magana ba bata kuma ƙara yin koda kuka bane, ko ruwa bata nema ba, sallah kaɗai ke tashin ta. Hankalin mutane ya tashi musamman dayake abin na siyasa ne! Mr president dawowar gaggawa yayi daga tafiyar da yayi a ghana. Da kanshi ya ajiye Nihal shida mahaifin ta saida ya tattaro nutsuwar sa sannan ya ce "Nihal 'ƴata wani magana nakeji danake da yaƙinin bazaki aikata wani mummunan abu ga koda kiyashi bane bare ɗanki, sanar dani yanda abin ya faru" Tunda ake tuhumar ta hatta uwar data haife ta bata yi mata magana haka ba, wannan ya sanya a hankali ta buɗe bakin ta ta bashi labari tiryan tiryan sanan ta ƙarashe maganar cikin kuka da ce wa "Abi Yaa Hakeem fushi yake dani, tayaya zan cutar da ɗan yaa Hakeem, koda wani jinjirin ne daban bazan cutar dashi ba bare kuma yaron Yaa Hakeem, Abi, Daddy wlh summa tallahi Billahi awurin khaleesah na bar yaron nan" Rarrashin ta sukayi a zuwan zasuyi bincike sannan suka sallame ta.
Khaleesah har ɗaki ta tarar da Huddy da tunda ta farfaɗo take kuka, kuma ta tabbatar ƙarya ne, Nihal bazata taɓa cutar da abinda ta haifa ba. Zama ɗan ɓesa da ita khaleesa tayi sannan tana yamutsa fuska ta ce, "Bansan yanda kika ɗauki wannan al'amarin amma tabbas ni a wurina wannan al'amarin mai girma ne, naga kina mun wani kallo tamkar kinfi yadda da bayanin Nihal akan wannan shiyasa nabi diddigi na kashe maqudan kuɗaɗe na binciko ainahin menene matsalar! Dawa tayi waya a wannan ranar kuma me suka ce shine abinda naje har MTN office nema da kaina nida jami'an tsaro na duba amma abin mamaki saigashi ita da uwar ta suka shirya komai tun wata biyar da suka wuce suke neman yanda zasu mallake shugaban ƙasa ya ɗaura mahaifin ta a matsayin ɗan takara na gaba a wannan ƙasar a maimaikon wanda zai ɗaura. Bayanan sirri dake tsakanin su daga wata ɗaya zuwa wata na yanzu gashinan raɗau ki zauna ki karanta da kanki ki gani. Najene kawai in samu print out na wayoyin data amsa jiya da kuma inda ta zaga saiga shi ashe rabon tonuwar asirin ta ne. Gadai number ɗin dasukayi waya jiya nan da saƙonni saiki zurfafa bincike na tabbatar ba lallai ki yarda da nawa ba" Tana idar da wannan maganar ta miƙe ta fita a binta da ƙaton ciki a gabanta tana turashi sai kace tamkar akanta aka fara ciki! Huddy da hanzari ta rarumu print out ɗin saidai bata gane komai ba wannan ya tilasta mata nufar part ɗin Hakeem da gudu inta nuna masa tare da jere masa bayanin da Khaleesah ta mata zama yayi ya soma duddubawa abin ba kyaun sauraro, a hanzar ce ya miƙe tare da yiwa motarsa key ya bar gida.
Abubuwan daya gano daga MTN office jikin sa yayi matuƙar sanyi. Bayani kai tsaye ya nuni ne da cewar tabbas Nihal da mahaifiyar ta wurin Boka suka kai masa jinjirin sa wai saida jininsa za'ayi tsafi a mallake mahaifin sa da kowa sannan ya zamana ita kaɗai take sakashi ita ke hanashi, akan me Nihal zatayi haka? Anya Nihal ɗin sa kuwa? Yarinya mai son gaskiya da tsananin riƙo da addini? Meyasa zata aikata hakan kuma tana nema ta ƙalawa Khaleesah sharri?!!! Wayar sa ya laluba tare da kiran abokin sa Prince Mood, yana ɗagawa ya ce "Prince ka sanarmun zakazo Abuja ko?" Yana murnushi ya ce "Aikai ɗan halak ne, yanzu nake shirin kiranka Hafsa ta matsa saina kaita agun Nihal tun haɗuwar su Germany ƙawance ya ƙullu, munzo sai kiran waya ɗin Nihal take amma bata samu" Nisawa Yay sannan ya ce "Ba damuwa dama ina son ganin ka, Nihal ta sanarmun dama zakuzo tare kuma agunta zata sauka bara saina baka address ko nazo muje mu kai ta ne?
"Tunda suka dire Hafsah wurin Nihal suka zauna a mota gaba ɗaya saida Hakeem ya bayyanawa Mood da muwarsa ya ƙara da cewar "Prince na rasa tunanin me zanyi, Nihal fa ake magana fisabilillah! Abinda bata sani ba duk a cikin mata na ita aka mun auren dole da ita kuma amma ita ce mafi soyuwa agare ni, wlh Prince inason Nihal nama rasa wanne tunanin zanyi, bana fata ace wannan maganar danake gaya maka zahri ce so nake ace yau mafarki nake" Sauke nannuyan ajiyan zuciya Mood yayi sannan ya ce "Gaba ɗaya wannan abin a hargitse amma fisabilillah Hakeem wane halin banza ka taɓa kama Nihal dashi dazai baka tabbacin wannan abun ta ikatashi da gaske? Ka sani mata fa shu'umai ne, kawai shawarar danake baka shine ka baiwa Hafsa wannan binciken ina mai tabbatar maka da cewar zata naɗo bakin zaren" Kallon sa ya yi cikin damuwa ya ce "Waɗan nan information fa na text da waya hadda number data yiwa saving da Boka mecece makomar su, gashi kishiyar ta ce ta kaso na farkon" Murnushi Mood ya kuma yi sannan ya ce "Shiyasa nake gaƴa mata akwai lauje acikin naɗi, amma bari in latso maka hafsatun inyaso zata zo kaji".
Mom Nu'aiym
9/28/21, 12:26 PM - Buhainat: THE RETURN OF LEGEND
35.
Tunda Hafsa ta zauna saita take kallon takardun na tsawon lokaci a hankali ta kalli Nihal sannan ta ce, "Mesa bakida wayau ne, akan me zaki bari kishiya ta yi wasa da hankalinki har haka? Meyasa alokacin baki nuna mata kalar taki haukan ba? Ina zakije da ɗanyen jinjiri Allah na tuba, kuma ina kema Allah ya kawo rabo? Koba haka mukayi magana ba tun last week abinda naketa yiwa zagwaɗi kenan danni fa na gama haihuwa, ko yanzu na tara da yawa ai" Da sauri Nihal ta kalli Hakeem sai kuma ta riƙo hannun Hafsa tana dariyar wayance ta ce, "Kinga wasa fa nake miki, kinga alamar ciki ajikina ne? Hakeem zubawa Nihal ido yayi na tsawon lokaci sai kuma ya mayar da dubansa zuwaga Hafsa sannan ya ce "Ranki ya daɗe yanzu menene abinyi?" Jinjina kai ta ɗanyi tana nazari sannan ta ce, "Asibitin da aka haihu, babu nurses ne, ba likitoci ƙaramin asibiti ne duk faɗin asibitin ba cctvs ne, ina drivern daya yi ƙaryan da jinjiri ya ajiye ta a kan hanya, nan gidan akwai CCTV camera's i believe mesa bazakuyi tunani straight, sannan waɗannan takardun data kawo daga MTN office da wanda kai kaje suka baka duk tabbas hakane anyi shi anyi wannan maganganun through text messages amma shin meyada sai ta hanyar saƙo kawai? Ina voice babu ne a cen ɗin? Sai shaidar lambar waya da kuma lokacin kira? They are using both number ta dana maman ta, tuni suka shirya komai. Hakeem ka daina zargin Nihal babu inda Nihal zataje da yaronka da sunan cutarwa, nayi waya akwai kayan aikin dana baro agida na tashi driver zai kawomun amma yanzu ku tashi muje asibitin da aka haihu tunda private ne" Miƙewa tsaye sukayi dukkansu Hafsa ta ce, "Yaa Mood mu basu wuri suyi magana sun kwana biyu suna fushi da juna, su samemu a mota" Ta cura hannun ta acikin na mood "Ɗan kurma na muje" Murmushi ya yi yabi bayanta har waje.
A hankali Nihal ta tako har zuwan gaban Hakeem dayay tsaye tamkar statue yana kallon ta kawai, hannayen su ta saƙale dana juna sannan tana kallon sa cikin ido ƙwalla yabtaru a nata idon ta ce "Yaa Sadaukee na,kayi haƙuri kuskure nane, kuma ganganci nane, sakaci nane dana bari har wani abu ya samu Babyn mu, Allah ya sani Hakeem ko karen gidanka bazan iya cutarwa ba bare abinda ka haifa, ka yarda dani khaleesah na baiws jinjirin nan na fita, danasan cewar zai zama sanadiyar rabashi da mahaifiyar dako shayar dashi bata taɓa yi ba wlh dakoda zan shekara da datti ajikina bazanje yin wanka ba inbarshi a hannun ta" Lokaci guda kalamanta suka ratsashi, yaji hankalin sa ya matuƙar kwanta da maganar ta, ya kuma ƙara tabbatar wa kansa Nihal bazata cutar da jinin sa ba, hannunsa ya zare guda ɗaya yakai a saman mararta ya shafa tare da lumshe sannan ya ce, "Da gaske akwai ajiya na anan? Sunne kanta ta yi ƙasa cikeda kunya amma bata bashi amsa ba, hakan ne yasa ya fahimci tabbas akwai ɗin, rungumar ta gaba ɗaya yayi "To amma meyasa baki gayamun ba? Gyaran tsayuwar ta ta ɗanyi sannan ta ce "Bansan mezan ce maka ba ne ba" Ƴar siririyar dariya ya yi, "Amma dai baki kyautamun ba, wstan sa nawa?" Janye jikinta ta yi daga nasa "Ana jiranmu a waje fa" Hannun ta ya kamo ya riƙe suka jeru wani kallo yake binta dashi na so da sha'awa har suka isa mota. Khaleesah dake video yanda suke riƙe da hanun juna har mota ta ruga da gudu zuwa ɗakin Huddy ta tarar tana tare da ƴan uwanta dasuka zo mata jajen wannan abun. Kallon Huddy ta yi cikin yanayin ɓacin rai ta ce "Anya Huddy kinsan zafin naƙuda kuwa? Abinda ake miki gaba ɗaya na kula ni yakewa zafi kekuma ko oho, yanzu kalli yanda Hakeem yake riƙe da hannun Nihal suka fita suka bar gidan saika ce ba gudan jinin sa ta halakar ba, fisabilillahi yanda akayi an kyauta kenan kamata yayi ace yanzu Nihal tana hannun hukuma ne, amma meye hakan? Dan kawai anga iyayen ki ba masu ƙarfi ne, akan me za'a rabaki da ɗanyen jinjirin ki kuma kowa yayi shiru" Ta ƙarashe maganar da muryan kuka tana cilla wa Huddy Video data kunna mata nan suka zubawa wayar ido anan aka tashi meeting na yanda za'a ɗauki fansa.
****************
A asibitin kuwa Hafsat saida aka tara mata duk wani ma'aikaci dake kan duty a wannan ranar sannan ta nemi wuri ta zauna, takan Admn officer ɗinsu ta fara da cewar "Wannan babban asibitin aka sace jikan shugaba ƙasa guda sannan magana ta mutu murus ba ruwanku kunci gaba da harkokin ku kamar ba komai, wannan wane irin sakalci ne? Gaba ɗayan ku lisence ɗinku zamu karɓe a rufe asibitin sannan kuma zamuyi ƙarar ku akan yaranmu daya ɓata saboda negligence naku" Kallon ta yayi cikin nutsuwa tabbas ya shaidata, matashiyar matar dabata haura shekaru 28 ba da ake damawa da ita a harkar system da kuma kama ɓarayi a turai ma ba Nigeria, matar prince mood tsohon kurma, cikin mutuwar jiki ya ce "Munyi ƙoƙarin ɗaukar mataki da bincike mai zurfi saiga letter daga wurin Mr president dasa hannun sa akan karmu tashi maganar tafita a hannun ƴan jarida, issue ne na gida zasuyi resolving nashi agida" Yana rufe baki ta ce, "Fine mu ƴan gidane, saboda haka zanyi bincike akan kaina anan asibitin" Direban daya tabbatar ya fita da ita gashi anzo dashi sai zare ido yakeyi danya tabbatar Hafsa saita gano zaren bayau ya saba jin labarin ta ba musamman yanda take damƙar masu laifi a hannu. Mutumin ya ce "Ba damuwa zamu baku duk haɗin kan dakuke buƙata" Miƙewa