Showing 36001 words to 39000 words out of 67070 words

Chapter 13 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt

03 Sep 2024

9262

kawai ya zamanto sai yanda nayi da mijina, ya kasance nini kaɗai yake kalla yaji daɗi, ya zamana ko tari nayi saiyaji dalili, ya zamana mahaifina ya zama shugaban ƙasar wannan ƙasar na gaba kuma da taimakon sa da kuma na mahaifin sa" Dariya Malam yayi gajera sannan ya ce


"Yanzu abinda mukeso shine,ki kawo mana sumar kansa dana mahaifiyar sa da kuma na mahaifinsa" Da sauri ta kalle sa "Malam tayaya zan samu sumar kan Mr. President? Gwanda ma na Ummi mai sauƙi ne zan iya bincikar inda take wankin gashi da kitso amma shifa? Dariya ya kuma yi sannan ya ce


"Wannan shine iyakar abinda zan miki, akan mahaifinki ya zamto shugaban ƙasar nan kuma aikine na daban, wannan shine matashiyar aikin dazamuyi muga cewar daga uwar sa har ubansa ba mai miki musu, sannan kuma muga cewar shima baya musa miki, idan muka gama da wannan saina mallaka shi kuma aikine da sai gugar jikina ta ɗeɓo ruwan da kika ɗebo daga jikinsa sannan zamuyi shi" Bata fahimci wannan maganar ba, ta biyasa kuɗin sa ta bar wurin sa gaba ɗaya akan zata kawo sumar kan datace inshaa Allah.


**************
Wunu ɗaya cur tana fushi bataci abinci ba bai kuma dawoba shikuwa sai dare, yunwa duk ya gama hallakata ga zugin da wutar nan keyi mata ko tsayuwa bata iyawa. Kai tsaye daga dawowar sa ɓangaren sa ya nufa amma yana shiga ɗakin ya tabbatar cewar bata shigoba data gyara ɓarnar dayayi, koda yake ƙafarta ta ƙone, dukda haka ya dace tayi masa tuwo irin na jiya danshifa yana matuƙar son tuwo, dan haka a sukwane ya nufi ɗakin ta inta ya tarar daga ciki ta saka key ta rufe ƙofar dole saida ya zagaya. A dunƙule ya risketa acikin lallausan bargo, matsawa yayi ya kira sunanta har kusan so uku amma bata amsa ba, tsaki yaja tayaya mutum zaiyi bacci yanzu? Tayaya zata kwanta bata bashi abinda zaici ba, da yunwa kenan take nufi zai kwana? Mesa a rayuwa Nihal ta gama raina masa hankaline. A falon ta yana dawowa ya haɗu da hadiman ɓangaren ta, ɗaya daga cikin su ya kalla


"Yaushe Nihal ta kwanta? ya furta cikin faɗin rai, russunawa tay "Yallaɓai ai Hajiya batada lafiya, tunda aka dafa mata indomie nan bataci ba kuma bata daina kuka ba, har daga bisani kanta ya soma ciwo, dosowar magriba gaba ɗaya sai zazzafan zazzaɓi koda akayi isha ma bata iya tsayuwa, ba jimawa muka kwantar da ita ɗaki ga alama sambatu ma take" Ƙurjinsa ne ya doka , da sauri ya ce "Kenan bataci wannan indomie ɗinba?


"Ea ranka ya daɗe cewa tay tayi fushi bazata ciba, bamusan me aka mata ba, daganan tafi awa huɗu tana kuka, munyi rarrashi har mun gaji amma ina sai gaba abin keyi, Shigowar Hajiya Huddaisa ma ba yanda batayi taci abinci ba amma sam taƙi dole ta Haƙura ta tafi" Jinjina kansa yay tare da dire wani gauron numfashi! "Shikenan ku tafi kawai" Shikuwa ya juya ciki saman gadon ya ɗare tare ta yaye bargon yakai hannun sa ajikin wuyanta "Hasbunallah, Nihal wai zazzaɓin da zafi hakane? Cikin rashin sanin me take ta ce, "Momy dan Allah ki riƙe dutsen nan gashinan zai faɗomun akai, dan Allah ga ruwanan zai haɗiyeni kuma" Wani irin kallo ya mata yanda take tattare wa da hannun ta, da sauri ya zaro wayar sa ya kira momy, tana ɗagawa baiko jira sun gaisaba ya ce,


"Momy Nihal batada lafiya,jikinta zazzafan zazzaɓi, kuma tanata surutai wai dutse zai faɗo mata ruwa zai haɗiyeta waye waye, hadda cewa take waiga mutane nan akanta" Ƴar dariya mom tay "Auu Hakeem mantawa kayi haka Nihal take zazzaɓi tun tana ƙarama? Ai indai zazzaɓi yayi mata zafi toko aikin kenan sannan kuma batashan magani saidai allura, alluran ma saikayi da gaske, Nihal tanada kafiya Hakeem, saikayi haƙuri abu kaɗan saita wuni tana kuka kuma ta wuni da yunwa sannan duk ranar datayi kukan nan toko tabbas saitayi ciwo kuma sannan taita sambatu" A ruɗe ya ce, "Momy yanzu asibiti ya dace muje ko?


"Ka rabu da ita zuwa safiya, kabar wani a tare da ita tunda yake kaga batada lafiya"


"To kawai yace ya ajiye wayar yana jere mata sannu, gaba ɗaya hankalinsa ya tashi, zare mata kayan nauyin data tula.ajikinta yay sannan ya shirya bacci shima, da ƙyar ya tasheta zaune ya bata youghurt tasha kaɗan, sannan ya kwantar da ita ajikinsa dake yalwar sanyi yayita murza jikinsu a haɗe har zuwa lokacinda ya soma fita hayyacin sa shima. Da ƙyar ya rarrashi kansa ganin ita harta soma bacci tana haɗa gumi shima ya yi baccin.


Da asuba tana farkawa taga yana saƙƙah fitila a buɗe, bata iya tuna komai daya faru ba taci gaba da kwanciya saboda jikinta ba ƙwari. Saida ya idar da sallah sannan ya taso yazo kusa da ita har lokacin tana cikin bargo "Sannu Nihal, ki tashi ki daure kiyi salla kar lokaci ya shige" Bakinta ta murguɗa masa sannan cikin tsiwa ta ce, "Ina ruwanka dani wai?" Murmushi yay "Nihal kinsan Allah zan zaneki, maza ki tashi tunda kin warke kije kiyi sallah" Yamutsa fuska tay tana ƙunƙuni "Dama mana gwara in kama kaina dakai, ka soma dukana dan mugunta zaneni ai nasan tabbas zaka aika" kallon ta yay "Me kika ce?" Tana shirin yane bargon ta ce, "Abinda kaji" ciki ciki, ta faɗa dan haka baiji me tace ba amma tabbas yasan baƙar magana ce "Dawa kike?" ya faɗa yana tsare gida, kuma murguɗa masa bakinta tay "Wanda ya tsargu dashi nake" Zabura yay tamkar zai dake ta ta fice daga cikin bargon tana mai ci gaba da faɗar baƙar magana, amma me tana gano a tsirara take iya pant ne ajikinta ta ƙwalla uwar ƙara tare da sanya hannayenta ta rufe ƙirjinta, ihu take tamkar ranta zai fita da tabbas zai iya janyi ɗaukacin mutan gidan zuwa ɗakin da tunanin wani mugun abu ne ya same ta! Da sauri yayi wurin da take ya sanya hannu ya rufe mata baki tare da manne ta da bango, kallon juna suke har zuwa lokacin a tsorace fake ga kunyar data rasa inda zata dosa dashi "Shhhhhh kina hauka ne zaki taramun mutane ihun me kike" Idonta ne ya kawo ruwa sosai nan da nan saiga hawaye! Janye hannun sa yayi a hankali daga bakinta, cikin kuka ta ce "Abinda kayimun kaida Allah yaa Hakeem, dama ashe ba mafarki bane danaji kanata taɓamun jiki, gayamun medame kamu n? Hadda fyaɗe ko? Da mamaki yake kallon ta aranshi ya ce, 'Anya Nihal batada taɓin hankali kuwa?' Hannunta takai ta shafi pant ɗinta sai wata ƙarar ta biyo baya "Ka cuceni wlh saika biyani jikina daka taɓa, yanda ka tsaneni meyasa ka taɓani mugu kawai, auren soyayya mukayi da zamuyi irin wannan abin maganin bacci ka bani ko?" Hannunsa yakai ya matsi bakinta sosau saida idonta suka fito


"Idan kika ƙara cewa na miki fyaɗe saina jimiki ciwo agidan nan, kalleni da kyau sunana Sadaukee matana uku kuma matana biyu babu ƙwaila irinki, ke yaushe ma kika girma? Idan ana maganar manyan mata ki daina sako kanki taƙamar kunkuru kike wakikafi kunkuru acikin matana? Kinsan saina miki hankali agidan nan idan bakida shi, idan wannan abun kikewa ihu dama ba kasuwa naje na siyoki ba gwanjonki akamun bare kice shiya jani, kije ki jiƙashi kisha, sakarya kawai da batada wayau" Ya karashe maganar da ture bakinta" Sororo ta tsaya tana nanata kalmar gwanjo, saikuma harya juya ta ruga da gudu ta ɗare masa wuya kamar biri tana yagar wuyansa da fuskarsa da faratanta "Kaine gwanjo, bani bace gwanjo mugu kaci zalina" Da ƙyar ya ɓallota daga bayansa ya wurgar akan gadon tare da nuna mata ɗan yatsa "Tausayinki kawai ya sanya na kwana atare dake yau har kike mun kallon raini, wlh Nihal ke baki isa macen dani sadauki zan ɓata lokaci da ƙarfin jijiyoyi na akanta ba, da ace yau na sauke ƙarfin sadaukanta kana akanki gwanda ace na rasa mazakutar gaba ɗaya,kin iya raini ni zaki gwada yin dambe dani, tabbacin bayan tarbiyar da momy ta baki akwai wata dakika aro a maƙota, daga rana irin ta yau ko part ɗina kar in ƙara ganinki, kusancin damukeda da juna shine ya kawo wannan rainin inaga" Hijabi ta soma laluba ta saka sannan ta miƙe kawai ta shige toilet da zumma tabbas idan tana numfashi saita nunawa Hakeem ta isa mace kuma tafi ƙarfin wulakaƙanci daga irinsa, idan har tana numfashi dagashi har matansa saisunga iyakarsu a hannunta.


Huddy ma bokan da Khaleesah taje gunsa itama wurinsa taje neman taimako mai zama kamar malami. Kallonta yayi daga malamanta ya fahimci kishiyar waccen khaleesah ce, aransa yace tabbas zai jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Nan da nan ya bata aikin kawo gashi kamar yanda ya baiwa khaleesah. Yana murna cewar tabbas zai tabbatar sun kashe ƙansu da kansu, zaiyita amfani da aikin wata yana ƙalata na wata!


Mom Nu'aiym.
07084161619.
9/18/21, 9:31 PM - Buhainat: *HM*
24.


"Malam ni so nake gaba ɗaya ya tsani matarsa ts uku fiye da yanda ya tsani mutuwar sa, sunanta khaleesah, ya zamana nini kaɗai nice tauraruwar sa, yanada mata amma ita sam bata gabansa wuƙaƙanta ta yake safe rana dare, wannan mayyar ita na tsana ita nakeso inga iyakarta kuma nasan tana shige shigen malamai" Nisawa yayi sannan ya ce,


"Na fahimceki, ai idan hakan kikeso dole saikinyi wannan aikin na farko dana baki, neman sumar kan uyayensa dashi kanshi mijin naki. Ita kuma matarsa da bakya so saikin nemo mana ƙumbar data cire sannan saimuyi ƙokarin saka mata warin jaɓa ajikinta indai ya raɓeta wari zaiji, wannan shine makarin turaren datake amfani dashi dake tilasta masa saduwa da ita' Jinjina kanta tayi "Babu damuwa Malam, da ikon Allah duk zan haɗosu na kawo in Allah yaso" Godiya ta yi ta ajiye masa abun sadaka kamar yanda yake cewa sannan taɓar wurinsa kai tsaye Villa ta nufa da nufin wai taje gayar da Ummi.


*****************
Tunda ya dawo daga ɗakinta yake zirga zirga tamkar wani mai yunƙurin naƙuda, anya ya kyauta kuwa abinda ya gaggayawa Nihal? Adalci ne ya kalli ƙaramar yarinya irinta ya gaggasa maganganu kamar haka? Daidai ne ya miƙe ƙafarsa koda baya sonta ya aikata aiki irin na jahilai ta hanyar gaggaya mata maganganun duk da sukazo a bakinsa? Dana sani mara misaltuwa ya kamashi, yayi yunƙurin komawa ya bata haƙuri amma saiyaji bazai iyaba, Nihal fa ƙanwarsa ce tayaya zai bata haƙuri? Ita ɗinma aita masa rashin kunya sosai.


Nihal bayan tayi wanka ta kunce ɗauri da dressing na asibitin da aka mata dama ta saka a ranta cewar bazata ƙara komawa ba, zama tai akan gadon ɗakinta tana azkhar har gari ya waye sosai sannan ta ɗauki wayarta ta shiga kafar sadarwa ta whatsapp. Kai tsaye sunan wata ƙawarta Mamu ta nema sannan ta mata sallama amma saitaga bata online. Batajin zata iya hakura, agogon wayarta ta kalla taga takwas ƴa gota dan haka ta dannan kiran wayar Mamu. Ringing biyu ta ɗauka suka gaisa sannan ta ce da ita "Mamu dama magana nakeso muyi idan ke kaɗai ce" Gyaran kwanciya Mamu ta yi sannan ta ce "Honey ya yi tafiya, so am all ears amarya" Murmushi tay sannan ta ce,


"Mamu matsala ce dani, nasan kece kika taɓa fama da irin matsalar danake ciki a yanzu, wannan shine dalilin daya sanya na nemeki dan Allah mamu ki taimakeni" Tashi zaune Mamu tay cikin tausayawa, jin yanayin muryar ta ce,


"Menene matsalarki Nihal?" Muryanta yana rawa ta ce,


"Mamu kinsan Zaid shine saurayin danafiso a rayuwa shekaru kusan huɗu muna tare dashi, bayan nan kinsan da Hakeem dani tamkar ƴan uwan junane koda na tashi gidanmu naga Hakeem momy take riƙonsa. Lokacin da aka bijiro da zancen za'a haɗamu aure Mamu idan baki manta ba na sanar dake banason Hakeem, shima kuma Hakeem baya sona, daga haka mukaita takun saƙa harnazo na samu wannan matsaƙar ta bandits ai kinsan labarin komai. Muna dawowa matsaloli suka taru sukamun yawa, kuna saiya zamana na damu da Hakeem sosai bayan dawowar mu. Bansan ya akayi na amsa tayin iyayen muba bayan shafe shekaru suna roƙonmu akan mu auri juna. Mu uku aka ɗaura masa aure damu a matsayin matasan, ɗayar ƙaddarace ta sakashi auren ta ɗayar kuma itace zaɓinsa nikuma zaɓin iyaye ce, Mamu gaba ɗaya na kasa gane kan Hakeem, magana yake gayamun duk yanda tazo masa, har yanzu bansan menene aure ba, jiya danyaga banida lafiya haka yaso ya lalatamun rayuwa danna masa magana har yana cewa gwanjona akai masa yafi ƙarfin ya tara dani. Mamu nasan keda Isma'il auren haɗi ne, kuma nasan kunsamu matsaloli da tawa fin waɗan nan ma danake lissafowa, amma yanzu ko makaho ya laluboku ya tabbatar kuna son junan ku, dan Allah Mamu ya zanyi inso Hakeem kuma Hakeem ya soni? Wlh harga Allah bana sha'awar rayuwar zawarci, sannan zaid tunkafin nayi aure na fahimci sam baya sona, saboda jikina yake ƙoƙarin taɓawa" Nisawa Mamu tay bata manta kalar azabar datasha a hannun Isma'il amma gashi nan yanzu ya zama tarihi "Nihal bansan daya zan miki bayani ba a yanzu amma dai ki sani akwai jan aiki a gabanki, sannan kuma tabbas keda Hakeem ba ƙiyayya a tsakaninku sai wadda sashin zuciyoyin ku ke nuna muku cewar kuna yiwa junan ku. Dole saikin tashi tsaye da addu'a, yawan nafilfili da kuma juriya. Amma zan baki wata shawarar na tabbatar zaki ɓulle inshaa Allahu, dannima Anty Niyya tamun hanya ta haɗani da matar har Allah yasa na dace."


"Wace matar kuma?" Nihal ta tambaya cikin zaƙuwa "Sunanta Aunty Billy, idan kika kirata zata miki abu biyu da farko zatayi attending naki taji meye matsalarki zata kuma baki shawarwari, idan har special consultation kikeso kuma saikin biya ya danganta daga yanayin abubuwan dakike so, kinga tana bada shawarar yaɓda ake janyo hankalin namiji ya dawo gareki, tana sayar da suplement masu matuƙar kyau, tana koyar da yanda ake haɗa haɗaɗɗun suplememt da inhar kina amfani dasu kin wuce raini agun namiji, tana bada shawara abinda ya shifi yanda ake tafiyar da miji akan shinfiɗa, indai kikaje wurinta da izinin Allah har ƙarin wasu addu'o'i zata baki, ga ɗora mutun akan ƙa'idar addinin islama, tanada group da ake bada shawarwari harda tarbiyan yara saidai akwai na kuɗi akwai free" Nisawa Nihal tay


"Yanzu Mamu kina ganin idan naje gunta zan samu biyan buƙatar raina? Dariya Mamu tay "Sak irin tambayar nan nayi ranar farko da aka haɗani da ita, yanzu kinga duk matsalolina da Isma'il sun zama tarihi, na kara samun kusance ga ubangijina saboda ta nusar dani yanda zan tafiyar da addinina a nutse baƴaga haka kullum ina samun sabon karatu daga wurin ta" Godiya Nihal ta yi mata sannan ta ce "Yanzu ya zamuyi?


"Zan turo miki number wayarta ta whatsapp, zan gaya mata kuma na baiwa ƴar uwata number ta, kiyi ƙoƙarin fara kiranta a waya dantayi saving number ki daganan saiki mata chat ta whatsapp." Godiya sosai tayi mata sannan sukayi sallama kai tsaye ta ƙara hawa whatsapp inda ta kwashe number tayi saving sannan ta fito bata damuwa da safiya bane ta kira wayar matar. Bata ɗaga ba wannan yasa ta haƙura ta koma ta kwanta har bacci ya kwasheta sai wuraren 11 sannan ringing na wayar ta ya tada ita inda tana dubawa taga number data kira "Aunty Billy" Tashi zaune tayi da sauri ta ɗaga wayar dake daf da yankewa. Gaisawa sukayi sannan ta gaya mata Mamu jega ce ta bata number ta nan tayi mata introducing kanta, bayan ta kammala ta ce .


"Inada sabgogi da dama dazasu iya sakani mantawa da maganar ki idan banyi da gaske ba, yaya kikeso abun namu ya zama? Munada abubuwa kala kala. Irin da farko munada specail consultation damukewa mutum acikin kwana 3 mu gama wanda zaki biya 3k. Munada class na free inda zaki ƙaru sosai, munada class da ake biyan 500 munada na 1k. So wanne kikeso? Cikin zaƙuwa ta ce,


"Kuɗi basuda matsala awurina, matsalar dake damuna itace babbar matsalata Aunty Billy, please here me out saiki bani shawara" Jinjina kai Aunty Billy tay "To Bismillah ina sauraren ki"Zama tayi gaba ɗaya ta bata tarihin rayuwar ta mijin ta yanayin aurensu da komai ba abinda ta rage mata. Saida ta gama bata labarin ta tsaf sannan ta sauke numfashi mai tsayi ta ce.


"Da farko dai abu na farko dazaki farayi shine cirewa rayuwar ki cewar bakyason Hakeem kikuma tunanin cewar shi Hakeem baya sonki" cikin tausayin kanta ta ce "Aunty yaya zan ƙaryata gaskia? Murmushi Aunty Billy Tay "Ai keda Hakeem tun tuni kukewa gaskiya gaddama, dazaku tsaya ku faɗa tsakaninku da Allah dakin tabbatar da abinda na faɗa, shin ko kinsan soyayyar mijinki ne ta sanƴa har kika nemeni? Shiru Nihal tay aunty Billy taci gaba


"Kina son Hakeem, shi ɗinma yana sonki abinda yake cutar daku abu uku ne. Da farko dukkanku baku yarda kuna son juna ba, na biyu dukkanku kun yarda da cewar waɗansu kukeso daban ba junan ku ba, na uku girman kai! Ke bakya girmama shi ta hanyar magana sannan shima baya girmamaki ta hanyar magana, kunason kuganku a kusa da juna amma da zaran kun haɗu sai faɗa, kunason zama wuri ɗaya amma kun haramtawa kanku zama wuri ɗaya saboda tunanin da kuke na cewar bakwa son juna, shin anya Nihal kinawa mijinki abinda ya dace ki masa ta hanyar kirsa, kisisina, karairaya, da sauran su? Ki sani fa saikin ankarar dashi irin son dayake miki zai gane yana sonki. Matsalar matan hausawa girman kai, kuma kinji ance rawanin tsiya ne, ki nemo bumper short ki riƙa sakawa, ki rage zama serious agaban sa ki dinga yin komai da zallan ƙuruciya, ki daina masa magana kamar sa'ansa, komai ya ce dake ki yi shi da hanzari, ki daina nuna masa ƙiyayyar sa ki dage da yawan addu'a, and lastly ki nemi ajikinki, ina ayyuka sosai a yanzu amma knshaa Allah zan turo miki wasu daga cikkn audios

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login