Showing 66001 words to 67070 words out of 67070 words

Chapter 23 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt

03 Sep 2024

9253

Gas bayan kammala girkawa Nihal moimoi datace tanaso amma saiyaƙi ya ɗauke duƙar da fuskarta tayi tana leƙen ƙasan tukunyar tanason sanin dalilin gas ɗin naƙin mutuwa amma saitaga tamkar wutar tana bin hannunta, hannun tabi da kallo har zuwa sanda ƴakai zuwaga hannun rigarta nan take wutar but ta kama ilahirin jikinta!!!!


Wannan shine ihun daya gayyacesu zuwa kitchen ɗin Nihal inda dama anan take mata girkin.


Mom Nu'aim.
10/6/21, 11:15 PM - Buhainat: *SAD INDEED, THE END*


41.


Hankalin isarsu kitchen ɗin gaba ɗaya huddy ta rikice batasan me take so ba, wannan ya sanya gaba ɗaya ta afka ajikin Nihal inda sukayi tarayya wurin ƙonewar!! Ihunsu a tare ya kira mutanen gidan gaba ɗaya suka rankaya anan. Baba surayya itace ta ɗebe zanin jikinta ta jiƙashi a ruwa ta rufawa Nihal da bako ina jikinta ya kamaba, inda Huddy ma aka shiga watsa mata ruwa da ƙyar aka kashe wutar da na jikin Nihal dama kaya ne ya taɓa amma baijega fatarta sosai ba sai inda ba kaya, Huddy kuwa hasbunallah!! Gaba ɗaya tama daina motsi, Hakeem dayayi mutuwar tsaye matsawa ya yi kusa da ita ya cicciɓe ta amma me suturar data ƙone ajikinta ta haɗe da fatar ta suna saɓule wa, miƙewa tsaye yayi yana ja da baya a hankali, saida ya isa ƙarshen ginin ɗin kitchen sai kawai ya zube awurin asume. Dole ambulance aka kira ta wuce da su asibiti, gaba ɗaya Nihal ɗinma a rikice ta ke, anan aka nata dressing amma Huddy kallon farko game hankali yasan koda ta rayu bazata mori rayuwar ba hatta fuskarta a wani gefen ta ƙone, batama taɓuwa dan sabulewa takeyi haka akayi mata dressing Hakeem bai farfaɗo ba har sai wsshe gari inda ya tarar gaba ɗaya Nihal ƙunan kaɗanne amma Huddy hatta gashin kanta ya ƙone, tunda abun ya faru batayi magana ba har sai bayan sati biyu ana mata kallon taji sauƙi za'a fita da ita waje sannan ta soma magana, Hakeem duk ya je ganta sai yayi ta kuka tamkar wani ƙaramin yaro. Yauma hakane dayaje hannunta dake a ƙoƙƙonge ya kalla kamar yanda ya saba surutan sa haka ya ce


"Huddy wannan shine abinda yayi mun nauyi a ƙirji ransr da wannan mummunar ƙaddarar ta sameki. Wannan shine abinda nake gayawa Nihal take cewa inyita addu'a, tabbas Allah mabuwayi shine sarkin sarakuna, wlh shishi kaɗai ya isa ya mayarda mai lafiya mara lafiya acikin daƙiƙa ƙasa da ɗaya, kalli yanda haliutarki ta sauya kome zaki zama arayuwa zan rayu dake Huddy, zan soki fiye da soyayyar dana miki a baya, ke mai kirki ce kuma inshaa Allahu zaki tashi kinji" Da ƙyar ta iya ɗaga baki ta ce "Hakeem bazan rayuba ninasan, zuciya,gangar jiki da ruhina suna kusantoni sosai kusada kushewa ta, idan da abinda na aikata agareka ka yafemun, ka gayawa iyaye da abokan hulɗata duk su gafarce ni, ka taimaka ka nemamun yafiyar kowa da kowa, ni wannan ita ce kaddara ta, kuma tabba Gamo na dakai alkhairi ne Yaa Hakeem, dalilinka na daina shirka na tuba, kacigaba damun addu'a Allah ya gafarta mun" Kuka ya ƙwace masa "Haba Huddaisa wannan wace irin magana ce, gashi nan an samu ci gaba kin soma magana, da ikon Allah zaki miƙe, inshaa Allahu zaku warke zamu rayu cikin so da ƙaunar juna ki daina faɗar wannan baƙar maganar kinji" Wani wahalallen murmushi ta yi sannan ta ce "Ka yafemun" Saikuma ta soma shaƙuwa daganan sai kakarin mutuwa, yana kuka yana kalimatushahada har Allah ya bata ikon amsawa daga nan ta amsa kiran Allah!!!! Kuka kam anshashi tunba Nihal ba data ɗaura alhakin komai akanta tunda ita ta tilasta akan saita mata alale.


*Bayan wasu watanni*


Nihal sai jijjiga Litle Hudy take amma banda ihu babu abinda takeyi, yarinya duk rarrashin da zaka mata gaba ɗaya kamar tunzurata kake, ta iya kukan banza kamar me, Hakeem ne da kanshi ya karɓeta ya soma rarrashin ta, da ƙyar ta yi bacci, kallon Nihal yayi cikin tausayi sannan ya ce "Sannu Nihal, Hudaisa tana yawan baki wahala ace yarinya sai dare ya tsala taita mana ihu" Dafa kai ta yi sannan ta ce "Ni yau gaba ɗaya da tunanin khaleesah nake ɗawainiya, anya yaa Hakeem ɗan adam bazaiwa kansa faɗa yaji tsoron Allah ba?" Murmushi ya yi sannan ya ce "Ki manta da wannan aitaga sakayya, ni gaba ɗaya tausayin da take bani baifi warin datake ba, tun abin yana a ɓoye harya bayya na, gaba ɗaya yanzu namiji indai Namjine ko ƙaninta ne ko yayanta keko ubanta warinta amai yake sakashi, wannan shine ƙaiƙayi koma kan masheƙiya" shafa kanta tayi "Dana ganta saida na yi ƙwallah, gaba ɗaya tamkar ba khaleesah 'yar ƙwalisa ba, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyar mu" Cakulkuli ya soma yi mata yana faɗin "Rabu dani da zancen wannan mummunan GAMON! Hannunsa ta soma riƙewa "Zan daina amma ka barni" Gaba ɗaya bai saurare ta ba haka ya ringa yi mata saida yaga tana shirin shiɗewa sannan ya dakata, nan da nan suka afka shafin ma'aurata suna shirin kashe bus Huddy ta cancara uwar ƙara nan da nan gaba ɗaya suka kalli juna suka kwashe da dariya Hakeem ya ce, "Wainikam yaushe zaki yaye ta ne, ysrinyar nan tsakani da Allah bata ƙaunar muke kashe arnan nan,ki yaye ta mu tattara mu kaiwa Ummi tayita kaya" Dariya suka kuma sakawa sannan ta soma bata nono, saida ta kwantar da ita sannan suka tsunduma aikin neman lada!!
********************** ⬇ **************************
********** Arewa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.arewanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.











Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AREWA NOVELS hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Arewa Novels ****************
********************** ⬆ **************************


*TAMMAT BI HAMDILLAH!*


*Abinda muka faɗa daidai Allah ya bamu ladan sa. Inda mukayi kuskure kuma Allah ya gafarta mana ya yafe mana.Allah ya bamu ikon aiki da abinda aka rubuta na alkhairi Ameen.*


*BANAN MUKASO TSAYAWA BA, AMMA DALILAI DA DAMA SUKA TILASTANI DATSE TSAWON RUBUTUN, INA FATAN A HAKAN MA KUN IƘMANTU KUMA SAƘONA YA ISO GAREKU, NAGODE DA ƊINBIN ƘAUNA ALLAH SAKA DA ALKHAURI.*


*'YAR MUTAN GALADANCHI KE MUKU FATAN ALKHAIRI.*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login