Showing 51001 words to 54000 words out of 67070 words

Chapter 18 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt

03 Sep 2024

9252

tunda ya tafi Huddy ke ciwo, yanzu abin yakai hadda amai take fama dashi, saidai sam gaba ɗaya bata gaya masa ba tayi zaman ta a sokoto.


Khaleesah kuwa tunda tazo garin su take fantamawar ta tana rarraba ƙawaye kuɗi tanajin kanta saman iska.....


Mom Nu'aiym.
9/26/21, 8:44 PM - Buhainat: *HAPPINESS AND SADNESS*


32.


Hakeem yana zauna a falon sabon gidansu Nihal tayi matashin kai da cinyar sa yana sosa mata sumar kanta wayar sa ta soma bulayin neman ɗauki, a hankali yakai hannun sa ya ɗaga cikin hanzari ya karata a kunnen sa "Ummi barka da war haka" Cikin daƙiƙewar murya ta ce "Barka Sadaukee me kake nufi da matanka? Ɗan ɗage ƙafarsa kaɗan ya yi Nihal ta fahimci tashi zaiyi itama ta ɗage kanta "Ummi ban fahimta ba wani abu ya faru ne?"


"Idan Abi baya ƙasar nan tun kana ƙaramin ka ka taɓa gani ya bar ƙasa nima na tafi gidan mu? Nan da nan ya harbo bakin zaren, jikinsa yana rawa ya ce, "Ummi zasu koma gobe inshaa Allah" Bata kuma magana ba ta datse kiran kawai kallon Nihal ya yi datayi sororo tana kallon sa sannan ya zauna jikin sa a mace "Lafiya dai yaa Sadauki?" Girgiza kanshi yay "Ba komai" Sannan ya ɗaga wayar ya kira Khaleesah, saida ya kira so 3 sannan ta ɗaga muryan ta da alamun bacci ta ce, "Bacci nake inna tashi zan kira ka" Kafin ta katse ya dakatar da ita da ce wa, "Duk abinda kike ki kammala shi a yau ki koma Abuja gobe" Zabura ta yi ta tashi zaune "To amma inna je abujan me zanma acen?" Tsaki yaja "Acen ɗin me kike yi ne? Ki gane yanzu fa akwai aure a akanki" Zata ƙara magana ya ce, "Nadai gaya miki" Ya datse kiran tare ta saurin kiran Huddy daya tuna tun jiya da yamma basu ƙara waya ba, a hankali sallamar ta ta daki dodon kunnen sa ya amsa tare da cewa "Lafiya dai? Gyaran kwanciyar ta tayi sannan ta ce "Banajin daɗi ne tunda nazo yau abin yayi tsanani bana ma iya tashi tsaye jiri sosai nake ji" Da sauri ya miƙe tsaye "Haba Huddy tayaya zaki zauna baki da lafiya tsawon lokaci baki sanar dani ba, kullum saina tambayi lafiyar ki?" Da ƙyar ta ce "Baka ƙadar kanata fama da aiki ma, nasan hankalinka zaka ɗaga shigasa kawai na haƙura da gayama" Cikin takaici ya ce," Gobe ki koma Abuja, zanyi waya a turaki Villa ki zauna agun Ummi na, kije da Rumaisa, Dr. Namu zasu dubaki idan abun yayi tsanani gwara a turoki nan Germany sunada ƙwararrarun likitoci su duba ki"


"Hakeem abin ai bewai yayi nisa haka bane ba, kawai fa da safe nake shan wahala da rana zakaga ina ta walwala abuna zazzaɓin dare shine ma yafi damuna"


"Wait da kike wannan maganar kinje asibiti ne? Tana matsa fuska ta ce "Haka nake zazzaɓi sai kace ka manta,haka nake yinshi kullum, zai tafi dan kanshi wannan ne dai yaɗan zo da sabon salon kuma ya daɗe tunda ka tafi fa" Datse wayar sa yayi nan da nan ya kira yayanta akan lallai gobe ta koma abuja kuma a haɗata da Rumaisa.


Zuwan Huddy Abuja nan da nan aka gano cikina na sati biyar, kuma gaba ɗaya hauka ne kaɗai Hakeem baiyi ba akan murna, amma abin mamaki khaleesah tafi kowa farin ciki da wannan labarin, dan har ta gayawa bokan ta inda yake tabbatar mata idan tayi haƙurri watanni takwas tamkar kwana takwas ne.


Nihal tana kwance a ɗaki da waya a hannun ta tana azkhar na yamma Hakeem ya shigo, kwanciya yayi sosai a kusa da ita, ga babu komai ajikin sa sai boxer dayake sanye dashi, bata kalle saba bata kuma fasa azkhar ɗinta ba amma haka suke jiyo sautin bugun zuciyoyin junan su sai lumshe ido yake, yanayin ƙamshin dake tashi daga jikin ta shine babban abinda ke ɗimauta sa idan ya kusance ta hannun sa ya ɗaura a saman waist nata yana lumshe ido, "Nihaly my baby" Ya furta a hankali, dariya siririya tayi sannan ta ce "Ban taɓa ganinka acikin farin ciki irin wannan ba, albishir wane iri kazo mun dashi" Hannun sa dake kan waits ɗinta yake yawo dashi zuwa bayan ta har saman mazaunan ta a hankali, santsin rigar ya haɗe da laushin fatar ta abun ya matuƙar yi masa daɗi, "Nihal i will soon become a father" Kallon sa tayi nan da nan ƙirjinta ya doka amma saita kanne ta kawar da abinda yazo mata ta ce "Ban fahimce ka ba? Yana ƙara murza bayanta ya ce, "Huddyna cikine da ita fa, ɗazu ake gayamun, batada lafiya na turata abuja gwajin farko ya nuna cewar cikine" Dariyar ta ta faɗaɗa sannan a hankali ta furta, "Ina tayamu murna dukkanmu, dan wannan is a blessing to the whole family, saura khaleesah, itama ina matan tana ɗauke dashi kokuma zata samu a nan gaba" Jikinshi ne yayi mugun sanyi, nan da nan yaji tausayin ta ya kamashi, itama fa macece meyasa baya bata haƙƙin sa shin yama taɓa zama ya yi tunanin yanda ta keji? Ko mara hankali yaji maganar ta yasan inda ta dosa, kafin ya dawo duniyar tunanin sa ta juya masa baya.


Ƙara rungumarta yayi ta bayan bakinsa saitin kunnen ta ya rungumota sosai sannan a hankali ya furta, "Kinawa wasu addu'a ke bazakiwa kanki ba Nihaly, ni ina fatan kema ki samu naki cikin ki haifamun yara kyawawa kamar ki" Bata juyo ba kuma bata kulashi ba sai sauyawar numfashin ta yaji alamar tana sauke nunfashi tare sa ƙoƙarin danne kukan dake shirin ƙwace mata, cikin jin zafi ya soma rarrashin ta "Haba Nihaly, na tabbatar abinda yake faruwa a tsakanina dake laifin duk na wane, amma shin ya zanyi tayaya zan taɓa abinda yake mai muhimmanci a rayuwar ki bayan nasan kinsha faɗamun cewar kin tsaneni? Akan wane dalili zan miki haka bayan na tabbatar cewar ba lallai kiyi rayuwa mai tsayi a tare dani ba tunda yake bakya sona, auren nan naga tilas aka miki ko? Wani murmushi mai ciwo ta yi "Hakane Hakeem,kayi tunani mai kyau sosai, idan ka rabani da budurcina tamkar ka rabani da farin cikina ne, ita mace idan batason Namiji inhar ya tara da ita idan harshi yana sonta mai sauƙi ne, saɓanin Namiji ace baya son mace babban illa ne ya tara da ita, kaga ko gwara kawai muyi hakan"


"Nihal, ni bantaɓa gaya miki bana sonki ba, ina sonki sosai fiye da yanda nakeson kaina ma, waɗan nan maganganun da kike da ne bawai yanzu ba ne" Hannu takai ta share hawayen ta sannan ta ce, "Amma Hakeem wannan tunanin kaɗai da kayi adalci ne? Saboda kanada wasu matan kokuma so kake ka ce dani auren soyayya kukayi da khaleesah? Saidai idan soyayyar ta jeji ce bansan an ƙulla shi ba, bayaga haka kuma ni ai bawai na sanar dakai ina buƙatar hakan daga gare ka bane, amma sanda kai kake ciyar da rayuwar ka a gaba ni tawa baya kawai takeyi shekaru na yana tafiya, kaga tunda har wannan shine tunanin ka matsayin ka na babba gwara kawai ka sakeni inyaso batare daka ɓata lokaci na ba inje inda zan haihu in more nima" Tana kaiwa nan ta miƙe tabar masa gadon da ɗakin gaba ɗaya.


Tayi kukan data rasa dalilin sa, zuciyar ta sam bata mata adalci ba, idanda adalci zuciyar ta zata mata tabbas da bazata fara sakewa da sabawa da Hakeem, ashe abinda yake nufi kenan ya sanya koda wane lokaci yake yagalgalar ta amma baya bari abun yayi nisa, kallon wannan kaɗai ya isa yasa ta gano ƙiyayyar dake tsakanin su babba ce ya tsane ta, abinda duk ke shiga tsakanin su yana yine domin rage zafi. Bayan magrib ba abinda take data rage masa banda fara'a, gaba ɗaya taƙi ta sake masa fuska. Yanda ta zuba masa abincin sa shi kaɗai tazo zats raɓa shi ta wuce ya riƙo hannun ta ya dawo da ita gabansa sannan ya ƙara jan kujerar dining dayake kai tayi baya ya ɗaura akan cinyoyin sa, baiyi magana ba suka ci gaba da kallon juna yakai hannun sa ya dakko plantain ɗaya ya nufi bakinta dashi, kawai da kanta tayi sannan a hankali ta ce, "Na ƙoshi" Ɗan ɓata fuska yayi sannan ya ce, "Banason musu kawai ki karɓa" Karyewar zuciya ta samu, zuciyar ta tana nufin cewa bazata iya saɓawa mijin ta ba, yanda ya ƙara ɗakko plantain ɗin ya nufi bakinta haka ba musu ta wage bakin ya saka mata aciki, taunar farkonya sakko ne ta zubar hawaye mai zafi, bai kulata ba haka ya dinga bata abincin har ruwa saida tasha tana kuka, ganin ta soma kauce kanta ya sanya ya fahimci ta ƙoshi. Kai tsaye batare dayaci komai ba ya ɗagata zuwa bed room nasu. Rigar jikinta ya soma zarewa wanda bata koda motsa ba har zuwa sanda ya gama rage mata kayan jikinta ta dawo iya pant ne ajikinta ko bra babu! Tamkar statue haka take kallon sa har ya ɗakko towel ya ɗaura mata sannan ya ce "Kije kiyi wanka" Bata ce masa komai ba ta wuce toilet ɗin. Ta jima sosai a ciki dan kuwa tafi 40mns sannan ta fito ɗauke da wannan ƙamshin dake tayar masa da hankali, ganin sa a shirye cikin kayan bacci ya bata mamaki saboda ƙa'idane sai 10 yake wannan shirin, ita ɗinma ga rigar bacci nan mai kyau ya ciro mata share shara, ɗauke kanta ta yi sannan ta zauna ajikin mirror ta soma shafe shafen data saba idan zata kwanta dama tayi sallan isha atare ma sukayi. A hankali ta taka ta isa gun rigar ta ta ɗauka ta sanya hannayen rigar sannan ta soma ƙoƙarin haɗo madaurin rigar da ake ɗaurawa ta gaba, jin an ragewa ɗakin haske ya sanya ta ɗago fuskar ta acikikn hasken dim light dake jikin bedside suka kalli juna sannan da sauri ta ɗauke idanta a nasa ƙirjinta yana tsananin dokawa! Takowa ya yi ya iso a daidai lokacin data ke ɗaure igiyar hannu ya saka ya riƙe mata hannu sannan ya tura ɗaƴa hannun sa ya kunto towel ɗin ya zube a ƙasa, ɗaurin datayiwa igiyar rigar ya soma kuncewa sannan a hankali ya cura duka hannayen sa acikin rigar ta yajasu zuwa bayan ta. Rungumarta sosai yay sannan ya shiga ƙoƙarin shafa bayanta bakinsa a saitin kunnen ta ya ce, "Badan halina ba sai domin Allah ki tayani yaƙin kawar da budurcinki cikin salama, ina tsoron inzo miki da abinda bakyaso Nihal tunda na taɓa roƙonki akan aikata hakan baki bani amsa ba, idan kin yarda zan moru daga ni'imomin da Allah ya miki" Batace masa ko mai ba harya zura harshen sa a kunnen ta yasoma mata ƴar matashiyar kuwwa aciki abinda ya tashi tsigar jikinta nan da nan. Cak ya ɗagata zuwa kan gado sannan ya shiga aika mata wasu saƙonni masu rikita lissafi. Bazata iya rayuwa babu wannan shafar marar da Hakeem ke mata ba, tabbas yana daga cikin abinda take so fiyeda komai a rayuwa! Sanda ya iso da bakinsa akan dukiyar fulanin ta suma ne kawai bata yi ba wannan ya tilasta mata soma kiran sunan Daddy, "Wayyo momy, wayyo Daddy" Amma bai kulataba har zuwa sanda hannunsa ya isa zuwaga kwamishin jin daɗin maza na ƙasa, yanayin ruwan dake ambaliya agun mai santsi ya dulmiyar dashi, gaba ɗaya bai saurara mata saida ya tabbatar a wannan daren ya kawar da budurcin ta! Nihal tayi kuka tamkar ranta zai fita gani take tamkar abinda Hakeem ya mata ƙiyayya ne zallah musamman yanda ya tashi ya barta a kwance daidai da hannun ta bata iya ɗagawa!


Mom Nu'aiym.


*Uzuri dan Allah, wlh yarana basuda lapia.*
9/26/21, 8:44 PM - Buhainat: *FAITH*


33.


*A gurguje plss*


Da ƙyar ta iya tashi ta kai kanta toilet, a durƙushe ta haɗa ruwan zafi ta shiga ciki ta zauna tsawon 30mns dukda azabar datake ji, wanka gaba ɗaya ta yi sannan ta dawo ta kwanta, har asuba bata samu bacci ba shikuwa bai waiwaye ta ba. Takan karanta litattafan hausa sosai, ba haka take gani anayi a novel ba, A yayi sambatu, yaƴi surutai ya mata magiya ya faɗa mata kalmomin ƙauna amma shin me hakan yake nufi? Hakan kuwa anya bayana nuni bane kawai daga zallan daɗin daya kasance aciki? Da ƙyar ta jira ƙarfe bakwai ta buga sannan ta kira Aunty Billy. Tana ɗaga wayar kawai ta saka mata kuka "Hasbunallah Nihal, meyayi zafi haka? Wani abu ya faru ne?" Cikin sheshekar kuka ta ce, "Aunty Hakeem baya sona, gaba ɗaya ni baya kula dani, bayan yazo yamun daɗin baki yayi abinda yakeso dani bai ko kwana ɗakin ba, aunty wlh gwara mijin Novel a littafi nasan ba haka akeyi ba" Murmushi Aunty tay "Kai ƙanwata kice an girma yau, to kinga ba kyau faɗar abinda ya shiga tsakanin mata da mijin ta, amma abinda nake so ki gane shine maza kala kala ne, wani baisan ya ake tattalin mace ba sai mace ta nuna masa, a littafi marubuta suna rubutawa ne saboda ƙarawa abun armashi da jan hankali, da ace shima makarncin ƙitattafai ne kamar ki zakiga tabbas ya baki hankalin shi da kulawa amma dake bayayi bai san haka ake ba saike ki nuna masa. Akwai wata baiwar Allah ita matsalar mijunta kunya ne dashi kamar mace, kai yamafi mata kunya da ƙyar muka shawo kan matsaƙar ya rage amma bai daina ba, ta yiyu Hakeem yanajin kunyar ki ne kokuma tayiyu shi nashi salon kenan, karki karaya ki bari muga zuwa dare me zaizo dashi" Cikin tausayin kanta ta ce , "Shikenan Aunty nagode" Nan dai sukayi sallama inda tana kwanciya saiga Hakeem a ɗakin a sukwane, yana ta zabga fara'a ya zauna kusa da ita ya kai hannu ya shafi fuskar ta "Nihal sannu, ya wurin ba zafi dai yanzu ko" Zumɓuro baki ta yi tare da kawar da kanta, "Bayan ka tafi ka barni ko tsayuwa bana iyayi wurin da zafi mana, zafi sosai da zogi mai raɗaɗi" Sunkuyawa sosai yayi ya soma shafar sumar kanta "Ayyah my baby, am so sorry, you were too swt, cant get enough of you idan na tsaya wlh zan iya ɓallaki and u have a very tight and sweet p***y that i ever dream of, gabaki ɗaya ban runtsa ba, idan na dawo zan miki sosai kuma zafi zakiji" Juya masa baya tayi cikin shagwaɓa "Nika rabu dani nayi hushi" Binta yayi yana rarrashi daga nak ya ce, "Ki tashi ga pain killer kisha ga kuma tea nasan you must be hungry" Haka ta zauna tasha saboda batada zaɓi.


Lokacin dawowar Nihal Nigeria yayi Hakeem yaƙi yadda juyin duniya Ummi tayi akan za'a turo masa Huddy Nihal ta kona ya ce saidai Huddyn tazo su haɗu amma Nihal bazata koma ba wannan abun ya nunawa su momg cewar tabbas yanzu akwai soyayya a tsakanin yaran biyu. Haka huddy tazo ba lafiya saima zaman na Nihal yayi amfani dan kuwa Huddy kaya ce zalla. Time da Khaleesah zatazo a lokacin su hudaisa suka koma, inda ita kuwa taje sai iskanci take. Gaba ɗaya Hakeem ya rasa dalilin dayasa yanzu ya tsani Khaleesah saidai zuwanta yayi amfani tunda tana zuwa saiga ɓullar ciki a jikinta ɗan tayi batafi wata ba ta kwasa cikin.


*BAYAN WATA SHIDA*


Abubuwa da dama sun faru, cikin Huddy watanin sa 8 yayin da cikin Khaleesah keda wata 6, duk yanda kake tsammanin abubuwan da khaleesah keyi yafi da nan domin kuwa da wannan cikin take sheƙe ayar ta da Malam, shi Hakeem ma bata bari ya kusance ta, ta ce dashi ciwon mara take idan ya kusance ta yanzu, dan haka ya shafa mata lafiya, ita Huddy dukda tana cikin wahalar wannan cikin amma haka take fama da ɗawainiya ga mijinta tuburan!


Nihal tana zaune tayi matashin kai da cinyar Hakeem sanda wayarta ya soma bulayin neman ɗauki, bata ɓatawa kanta lokaci ba ta ɗaga kiran musamman ganin cewar Huddy ce, muryar Huddy ce ta zaburar da ita datake cewa tazo batada lafiya, duk tambayar da Hakeem ke mata bata saurare sa ba dole sai bayan ta yabi, acen suka tarar Huddy naƙuda ce ta taso mata gadan gadan, dan haka suka kwasheta zuwa asibiti kai tsaye. Cikin ikon Allah kuwa saiga shi ta haihu yaro namiji kyakyawa mai tsananin kamannu da mahaifin sa. Murna awurin dukkansu ba'a magana, Hakeem ne ya ruga gida domin sanarwa da Momy, yayin da yana fita asibitin khaleesah tana shigowa anan suka gaisa ta karɓi baby sannan ta ce da Nihal "Kin iya wawta, amaimakon kibi Hakeem ko wanka kiyi basai kije ki dawo ba tunda gani, amma saiki tsaya duk kin yamutse" Murmishi ta yi, "Ba kowa ne anan, ƙanwarta taje haɗo kayan buƙatar su danga alama sai an sakawa Huddy jini, kinga jinjirin dole nizan riƙeshi" Miƙa hannu ta yi ta karɓeshi tana dariya "Ohhh little Hakeem, kinga kamannu, kinga ki tafi tare da driver daya kawo ni inyaso saina zauna kafin ku dawo" Dama Nihal ta gaji dan haka tayi saurin amsawa da to sannan ta fita bayan ta bata komai da za'a ɓukata da bayanin su.
Duk su Ummi da kowa har momyn Nihal sukazo amma babu wanda yaga baby, kowa, ya tambayi Khaleesah Baby saita ce yana hannun Nihal ta tafi masa wanka dan haka aka zauna jiran dawowar ta, abinda ya ɗauketa kusan 2 hours kowa sai kiranta yake bata gane komai ba saita ce tana hanya. Isowar ta asibiti da sallama tashiga ɗakin duk aka zuba mata ido, Momyn ta ce ta ce "Ke ina baby, ko tare da wani kike? Nihal da mamaki ta ce , "Momy wanne babyn? Kowa saiya ƙara zuba mata idanu, Momy ta ce "Ahh Babƴn Hakeem mana ina khaleesah ta ce suna zuwa basu same ki ba akace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login