Showing 36001 words to 39000 words out of 108136 words

Chapter 13 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt

08 Nov 2024

17220

dan lokaci guda hankalinshi yayi kololowar tashi amma sabida maganar da na faɗa masa take yaji kome ya fita masa akai. Mikar dani yayi cikin nutsuwa sannan ya mai dani inda ya tashi kayana ya kwaso min, ya ɗaga ni ya saka min,sannan zaunar dani a kasa shima ya sauka kasan yana kallona tausayi na bashi, cikin son na,sake dashi yace.
"Baza'a bani ruwa nasha ba?"


Mikewa nayi na shiga masa hidima ina share kwalla, har na gama na ajiye masa a gabanshi sannan na koma jikin kujera, na zauna, duk nahaɗa kaina da gwiwuwena ina matsar kwalla, ruwa yasha sai fruit ɗin da yaci kaɗan, sannan ya zuba min ido.


Sai yake jin ba daɗi da ɓata min da yayi janyoni yayi ya shiga rarrashina, ni kuwa nasake narkewa ina zuba kuka duk ya rasa yanda zai mu da yagaji da rarrashi kawai sai naji bakinshi a cikin nawa, ware idanuna nayi cikin faɗuwar gaba, ina son kwace kaina amma ya haɗe fuskarmu dan dole na daina shegen kukan. Kai Malamai ma sun iya farlatan luv ba zan iya faɗa muku yanda bawan Allah nan yayi dani ba, dukda ina son kwace kaina amma na kasa, abinka da gwauro😂 bai san lokacin da yasake layi ba dan kafin na farga naji hannunshi a cikin rigana, yunkurin tureshi nake amma bansan ta inda zan fara ba, shi kuwa ko a jikinshi dan janyoni yayi ya shige dani jikinshi sosai ban kuma abinda yake min gaba daya ya fara kure tunanina bansan lokacin da na fashe da kuka ba, wanda firgitar dani dan alamarinshi yana shirin kure tunanina ne,a galaɓaice ya zuba min idanu wanda sukayi jajur gashi sunyi kananu wanda ya nuna abukace yake dani. Taya ma ba zai sussuce ba da a riga yake ganinsu yau kuma ya bani haushi na kwaɓe masa ai dole ya hauka ce min. Dakyar yake maida numfashi, cikin wani irin murya wanda har bari yake yace.
"Kiyi hakuri da Al'amarina, kinji basan ya akayi na wucce gona da iri b..." mikewa yayi cikin rashin kuzari ga rigarshi duk ta sha squeezing, mikar dani yayi janye hanuna nayi naja da baya, cikin muryan masifa nace.
"Daman kace jikina kake hari shi yasa ka damu da ka aureni gashi tun banje gidanka ba ka...."


Ban kai karshen maganar ba ya haɗani da bango kauda kaina nayi dan wani dunkule hanunshi yayi sannan ya naushi bango tsorone ya kamani nasa hannuna na kare fuskana cikin tashin hankali, ranshi yayi mugun ɓaci fisgo hanuna yayi cikin ɓacin rai yace.
"Insha Allah ba zan taɓa rabaki da Kimarki ba sai da amincewarki amma kisani dalilina na,zuwa katsina nazone na shaida miki kishirya dan ranar da aka kawoki ranar za'a kawo min wata wacce nasan babu abinda zaki nuna mata, na Y'a mace, bazan miki dole ki soni ba kuma bazan takuraki ba. Sai dai kisan irin kalman da,zaki na faɗa min domin gidan da zaki shigo gidane da ko y'ay'a ka sake layi toh kallon mara ɗa'a zasu maka, sannan da kike cewa jikinki nake bi me,zanyi dake mi kike da shi miye a jikinki da zai dame ni har ke macece da zaki ce ina bin jikinki toh ba zan kuma bin inda jikinki yake ba balle har ki raina min hankali."


Fita yayi daga gidan baki ɗaya ni kuwa na durkusa a gurin kuka na cigaba dayi sosai kaman raina zai fita.


Koda yafita almajirai ya samu ya mika musu kayan da yazo min dashi inda yayi tafiyarsa. Ranshi yayi matukar ɓacci amma bayajin zai bar katsina a wannan ranar.


Tunda yafita na durkushe a gurin ina kuka, wiiwii mikewa nayi cikin azama nafita, na shiga ɗakinmu ganin tulin kayan da aka jibge min yasa na tsallake na shiga, ɗakin wayar da yabani na ɗauka layinshi na shiga nima, koɗa kiran ya shiga, yayi har ringing uku bai ɗauka ba, sai can kaman zai tsinke ya ɗauka kukane ya daki kunnenshi shiru yayi, can ya ce.
"Zan kashe wayar fa."


Bansan mi yasa ba sai nacire wayar a kunnena na kashe, kallona Ramla tayi cikin kuka tace.
"Bansan mi yayi miki ba kuma bana son sani amma kisani Babu namijin da zai ɗauki wannan kukan naki. Haba ke kuwa kinsan fitina a ranki kinsan Allah matukar kika shiga gidan da wannan halin naki zaman gidan sai ya fi karfinki dan na lura baki da hankali haba don Allah kuka sai kace ɓaure wallahi ko kishiya yayo miki da wannan kukan naki zata gama dake sam baki da hankali."


"Toh nidai nace bana sonshi dolene" faɗa mata nayi katsaye babu wani shamaki.
Baki sake take kallona cike da bakin ciki, taɓe bakinta tayi sannan tace.
"Sai me dan baki sonshi? Allah ya bashi wacce zataso shi kaman me ke kuma su maidake bora, kina ji kina gani suta shagalinsu kuma baki da tacewa Wawuya kawai wallahi idan kika ɓata ruwanki Yanzun hmmm sai kin rasa na kwaɓi nan gaba."
Tana gama faɗin haka ta juya, min baya, wani sabon kukane ya kwace min na zauna a gurin.


*
*
Koda ya isa masaukinshi xuɓewa yayi akan kujera,dafe da kanshi yayi cikin damuwa yaushe A'ieesha zata bar shirme wani shashi na zuciyarsane ya ce.
_Ba dole tayi shirme ba, yarinya ce fa, kaine kayi shirme da zaka zo mata ta haka_

Zubur ya mike ya rage kayan jikinshi sannan ya faɗa wanka dan, yana kokwanto kanshi dangane da abinda ya faru, shi da yake wanka sai ya buge da murmusawa cikin jin daɗi da wani shauki, gaba ɗaya sai yaji shi cikin wani irin yanayi na daban amma tunowa da kundin rigimarta sai yaji kome ya kunce masa. Haka ya gama wanka ya fito, yana tsane jikinshi. Bai kuma bin takanta ba,




Washi gari.....
Sako ya turo min akan ya tafi, ban gani ba dan wayar a kashe take Yan uwan Baba na nan katsina da Yan uwan mamana sunzo a cikin yan kwanakin da suka rage.....








*
*
Biki bidiri yau takama Al-hamis dan haka waleema aka shirya dan akwai bakin Yobe suna hanya, duk wata hiɗima da zirga zirga da Amarya keyi toh duk banyi ba, sai dai su Aunty Zubaida, rigima na tsiro da shi, na duk abinda akace za'ayi min toh sai na ɓata musu lokaci tun suna sharewa har suka gaji suka fara mita ko ajikina, tun ranar talata suka kaini gurin gyaran gashi, shima nayi ta kiriniya daƙyar me saloon ɗin ta gama min, dake da Aunty Hajra ce, rankwashina tayi, da aka gama, koda aka fara lalle nan ma, nayita mutsul mutsul, har sai da aka sake kifa min mari,(😂 wannan aure ko jaraba) dakyar aka gama min, muka dawo gida yanxun kan na daina kuka sai buhun iskanci da nake musu, muna shigowa Wata cousin ɗin Innaji suna Aunty Maryam ta mika min, wani kwanin sha, da madaran shanun wai nasha da ɗuminsa ta miƙa min. Tura mata baki nayi na fara kunkuni ina mingira kaina na fara cewa.
"Nifa an fara damuna da shaye shaye, haka kawai anaso a lalata min kayqn cikina, idan cancer ta kamani waye zai zauna dani don Allah kubar asaran kuɗinku dan cututtuka sun yawaita akayan itace, ni tsoro nake ji kar kodata ko hanta su lalace."


Duk gidan suka sake baki suna kallona yanda nake sake magana a sakalce, lekowa innaji tayi ta min dakuwa tare da cewa.
" Zakice kwal ubanki idan na kama shegen bakinkin nan me kama da na saurayin Kada."


Aikuwa sake turawa nayi gaba ina kunkuni, haka suka titsiyeni na shanye, har da lashe baki dake bani da birbiɗin kunya nacewa Aunty Maryam.
" Don Allah ina kika sami fresh milk haka wallahi yayi min daɗi ga garɗi har wani kamshi kamshi kanunfari yake."


Mika min wani gora tayi fuskarta a haɗe tace.
" A gidan kanoyarki nasamu, karɓa maza ki ajiye kita lasa bance ki masa shan ruwa ba, lasarsa zakiyi kina jina ko yar banza mara kunya zaki sani indai halinki nan baki sake ba wucce kije kiyi wanka ga sabulu nan kiyi dashi."




Wuccesu nayi ina kunkuni abuna, sukuwa suka shiga hiran shirme na, wasu nagani tsabar iskancine wasu naganin Yaranrace kawai kw ɗawainiya dani.






Musaman suka ɗauko me kyalliya tazo ta fente min fuska, ana cikim kwalliyar aka ce Yan yobe sun iso nan aka shiga kai musu abinci gidan Imamu dake can gefen unguwarmu, aka kaimusu sannan aka shaida musu,akwai waleema ko zasu samu zuwa. Suka ce toh.








Karfe hudu aka fita dani gurin waleema wanda akayi shi a kofar gidarmu. Yan uwan Imamu duk sun hallara manyan cikinsune basu samu zuwa ba, Amma matar Abba lawan tazo, da Balkisu da sauran yan uwanshi da suke yan uba mata da matan wasu kanensa, wasunsu kuwa sunyi gudun zuwa maidugurine, shine suka zo nan.


Duk wacce ta ganni sai kiji suna cewa "Masha Allah Baba Imamu Ya iya zaɓe," sannan su juya da barbanci nan zasu ta yabona, dake naga yanda suke haba haba dani, take nima nasake dasu har nakarɓi Yarinyar Balkisu dake bata da kiwuya muka zauna abinda ya daɗa burgesu kenan har aka tashi a waleeman aka ware musu nasu kome na gidan maza, an basu jakuna kusan talatin da dukda basu kai haka ba, sai aka musu tuwon girma miyan Nama, yan uwana da dangina suka saya min kima a idanunsu.






Tunda aka tashi nake kuka dan jikina yayi matukar sanyi da irin nasihohin da akayi na mace tabi mijinta koda bata sonshi sai naji kaman dan ni akayi wannan wa'azin.


Koda muka koma gida nan ma iyayena suka ɗaura min akan wanda akayi min musanan yanda zanja Yan uwansa a jiki dan izuwa yanzun sun sami labarin yau aka ɗaura masa aure da Yar uwansa inda sukayita bada hakuri, akan haka dan kar iyayena suga kaman cin fuska aka masa tohfa nan Yan uwana suka min Caaa kuma a yanda Yan uwanshi suka nuna basu son auren babu yanda suka iyane dan sunfi sonshi dani, haka ya kwantar da hankalin Iyayena da sauran mutane kunsan nasihar da akayi min a daren yau akan Yanda zanja yan uwanshine a jikina banda rashin kunya ko rashin hankali ta hanyar kyautatawa,zalla bayan sun gama suka buɗe babin Mahaifiyarshi. Nan ma haka suka cika min kunne da abu ɗaya Kaiiii dakyar suka bar ni na kwanta a ranar, karfe uku aka tashe ni nan nayi wanka dan sunce hudu da rabi zasu ɗauki hanya su isa da wuri tunda akwai hidima a can. Ina farkawa na samu an gama haɗa min kayana wanka nayi nazo na karyawa a nan na,fashe da kuka..........#Vote#Share#Comments##Mai_Dambu........
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }


🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Mai_Dambu*

*Wattpad:Mai_Dambu*


*24*
Abincin da ban iyaci ba kenan suma sai da nabasu tausayi, mika min kwanon shan irin najiya Aunty Maryam tayi karɓa nayi na kafa kaina sai da nashanye, sannan ta kamo hannuna, tace.
"Cire rigar jikinki jiya kinyi bacci naso na mikii kafin ki kwanta amma naga kinga."


Cikin kuka nace mata.
"Nikan mi ye amfanin wannan abubuwan da kuke bani ne, ni nagaji indai dan wancan mutumin ne ku daina dan basonshi nake ba."
Ɓata fuskarta tayi cikin jimami da abinda nace taɓe bakinta tayi sannan tace.
"Ai wannan sabida mugun nufin kishiya da mugayen mutane ake miki tsarin jikine namu na fulani idan kika k'i amiki toh ba makawa kishiya rainaki zatayi tasa miji da mutane su juya miki baya ko bakya sonshi bazaki so ya wulakantaki ba ko? Toh tunda haka ai dole aja miki mutunci a idanun kishiyarki da mijinki amma idan bai miki ba sai mu bari."


Ɗaga kai nayi sama ina nazarin abinda tace shiru nayi itama ganin haka ta mika min towel tace na ɗaura nacire kayan jikina, ba musu nacire towel ɗin Iya cinyata wani roba ta buɗe wanda takwaɓa lalle a ciki wani farin roba me murfi nan tashiga shafa min a jiki, cikn mintuna goma ta gama, sannan ta ɗauko kaskon wuta ta zuba wasu turarrikar irin yan maiduguri. Umartata tayi na tsuguna, akan gaushin nan nayi. Can da zafi ya dame ni nayi wiki wiki, da idanu nace.
"wallahi konewa zanyi fa, zafin ya dame ni." Banza Aunty Maryam tayi dani kaman bata ɗakin, zani ta ɗauko ta rufa min aikuwa na fasa mata ihu" wayyo zan mutu" da sauri Innaji ta shigo taga halin da nake ciki ɗaga rufuwar tayi tace.
"Barta haka Maryam in nice ma sai tasan ciwon kanta zan nima mata wasu abubuwan yanzun bata san darajar abinda kike mata ba, ku hanzarta, dan har an fita da kayanta waje ana sakawa a mota.






Wani munafikin kuka nasake ina kunkuni, abin mamaki lalle har ya bushe tasa keyana tayi zuwa ban ɗaki ta murje min lalle sannan ta kwara min ɗanye madaran shanuwa ajikina, ta wankeni tass dashi, tana gamawa tazuba min rankwashi haɗi da cewa.
" Dan ubanki da kudinki xaki zo niman wannan abinda nai miki babu mijin da za taɓaki ya hakura dan ɗumin jikinki ma ya isheshi balle kuma ni'ima munafukar banza, irinkune masu maƙelewa miji yar banza ina nan ina jiranki zanci kaniyarki duk ranar da kika ɗibu bulogarin kafarki zuwa gidana da sunan niman wani abu zaki gane baki da wayo."




Rike kaina nayi ina sosawa, bakina a turo nidai na shiga uku daga fara bikin nan zuwa yanzun naga kokarin kwakwalwata da bata tashi aiki ba, sabida tsabar rankwashin da nasha, wani lokacin har shafawa nake ko yayi kulu(😂) sabida kwaɗeshi da ake,.


Wanka nayi da ruwan da tabar min sannan nafito nasami kayan da zan saka nan shafa mai, a jikina sannan na ɗauki kayan nasaka tsaf, goran da aunty maryam tabani na ɗauka ina lasa, cikin jin daɗi wayo zak'i har wani mingira kaina nake sabida daɗinsa kawai Auntƴ Zubaida ce tashigo tasamu inata lasar zumar na tafin hanuna nakarewa zan zuba wani. Talle keyata tayi sannan tace.
"Allah ya kawo miki sauki cikin rayuwarki ke kam sai gyaran Allah wucce muje Baba na kiranki sakarya zaki faɗa musu idan maranki ya fara ciwo wucce muje"


Rufe goran nayi na wucce ina tura baki, atamfar super wax ne a jikina a min ɗinki riga da zani sai lafayya da aka ɗauko wanda yayi kalar kayan ,amma hijab na ɗauka muka fita zuwa ɗakinshi. Dawo dani tayi ta ɗaura min lafayyar sannan muka fita tare, takaini ɗakin ita kuma tazo ta kwashe kayana tass ta mikasu waje aka zubasu a mota.






:::: Tunda na shiga ɗakin kaina a sunkuye, da addu'a ya buɗe bakinshi sannan ya ɗaura da nasiha, sosai suka min faɗa dan yana gamawa innaji takarɓa itama. Sai da tasambaɗe min kunnuwana dan har gyangyaɗi na fara, sannan aka fitar dani sukace nayi alola muyi sallarmu tunda hudu da ashirin da biyar muna idarwa sai ga motarmu yazo ɗaukarmu ɗakin innaji na shiga dan taki fitowa, zuwa nayi na zuɓe a jikinta cikin rawan jiki nace.
"Innaji karki bari sutafi dani, ni bana son zuwa ba zankara muku shirme ba da sha-sha-shan ba, na tuba don Allah ki barni na,zauna."
D'aurewa tayi cikin sakin fuska tace.
" Kin manta nima gidanmu na bari nazo gidan babanku ko kin manta cewa Mahaifiyarki itama aure ya rabata da danginta baki ga su, Zubaida a gidan wasu suke ba, muje na raka yarinyata ko." kuka na fashe da shi sabida itama naga idanunta cike da kwalla amma take boye min kuka nake ina bata hakuri ba xan tafi ba tabarni na zauna dasu. Amma ina sharewa tayi takaini har cikin mota, sannan ta juya da sauri nafita zanbi bayanta Aunty hajra tashiga motar ihu nake ina mike musu nikan bazanje ba, aikuwa mutane da zasu tafi suka shiga aka tada motar ina ji ina gani aka rabani da gidanmu, kuka kuwa da nayi babu iyaka dan dama suma sunyi sallarsu tafiya ake ba kama hannun yaro, ba mutsaya ba ko wani abu sai karfe shabiyun rana muka tsaya lokacin har baccin wahala nayi koda muka tsaya a gidan mai dakyar nafito naje nayi fitsari sannan akace tunda sha biyu da rabi tayi ayi sallar azhar, aikuwa haka mukayi, aka ɗan taɓa abinci sannan muka sake mikewa.


Aikuwa karfe uku da arba'in muka isa garin Yobe,munsami karɓa cikin mutuntaka da karamanci sai son aga fuskana ake, shashin Abba lawan aka saukemu inda daman da matarsa muka dawo ina jin wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login