Showing 3001 words to 6000 words out of 108136 words
Chapter 2 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt
🌺🌺👳
*Na:Real MaiDambu Ce*
*:~3*
Mamakine ya kamashi ganin yanda nake maida masa magana cikin rashin kunya. Wani daga cikin ɗalibanshine ya mike tsaye zai isa inda nake, ya dakatar shi da cewa.
" Kyaleta yarinya ce, bata gama sanin kanta ba."
Murguɗa bakina nayi cikin ko ohho nace.
"Kanku ake ji."
Tafiyata nayi nabarsu da mamakin abinda nayiwa malaminsu ko ajikina fatana na isa gida lafiya.
Koda na isa gida ciwon marana ya ta'zara, amai nayi tayi, ga mugun ciwon mara da baya, har cinyoyina ciwo suke musaman bayana kaman zanyi hauka, ga jinin da yake fita da mugun gudu, daman haka yake min bani taɓa samun saukin abun sai mun dangana da asibiti toh yau ma haka, asibitin akai kaini, dake sunsan matsalata ba,a ɓata lokaci ba aka karɓe ruwa aka karamin,tare da allura wanda zai rage min zafin ciwon da kuma wanda zai rage min karfin zuban jinin....
Kwanana ɗaya da wuni aka sallame ni, inda akayi min kashedi narabu da kayan zaki idan ina son lafiyata.
Dawowana daga asibiti na jiyo mugun labaru masu ɗaga hankali ɗaya Mutuwar Ashow da kuma labarin da ya karaɗe unguwarmu wai ciki nayi aka kaini aka cire min, abinda yajanyo mugun rikici a unguwamu inda Abbanmu ya kusan kaɗuwa dan baya gari aka kaini asibiti, ranar da yadawo daga tafiya aka tareshi akq faɗa masa, duk abinda nake aikatawa.
Yana shigowa gida ya kamani yayi min mugun duka, sannan ya rantse na daina zuwa makaranta daga ranar, sannan zai badani sadaka duk wanda yayi masa.
Kuka nake ina rokon yan uwana, akan su shawo min kan Abba amma fur yaki, karshe wayar Innaji naɗauka na faɗawa Annah ita tazo da Kawu Ubale suka bawa, Abba hakuri ganin gimarmansu yasa ya kyale ni amma da sharaɗi bai amince min na riƙe waya ba, sannan babu ni babu yawo, gidansu Annah kuwa sau ɗayane asati nidai na amince, dan har lokacin mutuwar Ashow yana dake ni,sosai.
^^•••°°ΔΔΔ°°•••^^
Sati biyun da nayi cikin gida ba karamin kewar waje nayi ba da farin ciki nashirya zuwa makaranta koda gama ramla har ta tafi abinta, haushine ya kamani cikin sauri na shirya riga da wandone a jikina, sai karamin hijab, tunda nafito na lura ana nunani da yatsa, duk inda na wucce sai nunani suke abin yayi min zafi amma nayi fuska ban damu ba, Ta kofar gidansu Baby nabi ina son amsar wani text book ɗina da tazo ta amsa, bata dawo min da shi ba,.
Ina tura kaina cikin gidan naji muryan Baby tana cewa.
" Allah Mamanmu, bata da kome sharri nayi mata, kuma nice na haɗata da Babanta asalima nice da kaina nayi masa maganar abinda take aikatawa Mamanmu Naiha tana da farin jini kuma wallahi abinda boka ya faɗa min gaskiya ce, duk wanda zai nimeta babu karamin mutum, nice na rabata da Ashow nacw mata ya mutu, shima nayi sanadin da ya bar kasan baki ɗaya dan kurciya nayi masa Mamanmu na tsani Naiha, nice nayi mata sharrin zubda ciki aka mata kuma wallahi Mamanmu ina kishin samun farin cikin Naiha idan ina raye sai na hanata sukuni."
Jikina narawa nashiga gidan ina shiga nakifeta da mugun mari nace.
"Kasheni Baby nace ki kashe ni, tunda na hanaki rawan gaban hatsin me natare mikine, me kika nima a guna da banbaki ba, Baby Allah ya isa tsakanina dake, Kije Duniya tafi gabaruwa jimawa."
Ina faɗin haka nafito ina kuka hannuna ɗaya akaina, haka nazo na wucce majalisin Imam Usman, da yan majalisin suna ganin halin da nake ciki, basu wani damu ba, saima tsabgarsu da suke, shine kaɗai ya gaza hakuri har yace.
"Amma kun ban..."
Bai karasa ba, wata bakar mota tayi sama dani sakamakon tsallaka titin danayi hankalina baya jikina, karan birkin da me motar ya taka shi yadawo da hankalinsi kafin wani a cikinsu ya miqe har shi yarigasu zuwa gurina, shi ya ɗagoni, dan ni banma san me yafaru dani ba, motar mutumin yasakani, sannan ya shiga gaban motar suka kaini wani kuɗi cikin gaggawa aka karɓe ni, nan aka shiga bani taimakon gaggawa, bayan wani lokaci likitan ya fito ya kallesu, sannan yace.
"Kune kuka kawo yarinya nan ko."
Lokaci guda sukace "Eh mune"
"Toh babu wani damuwa buguwace kawai a cinyarta amma shima ba matsala zai warke." likitan ya faɗa musu.
Godiya sukayi likitan nabarin gurin sai ga Innaji da Ya ishaq suka iso, godiya sukawa Imam Usman, sannan suka shiga ganina, shima Mutumin da ya bigeni, hakuri ya basu.
Bayan yaga halin da nake ciki yayiwasu Innaji sallama ya dawo gida,
Mutumin da Ya bugeni kuwa, ya zauna har na farka yana ganin farka gurina yazo sannan yace.
"Preety sannun ko ya jikinki Allah yabaki lafiya."
Sun innaji sannu sukayita min sallama yayi musu akan sai dare zai dawo, kafin ya tafine ya kalle ni yace.
,"Toh bazaki faɗa min sunanki ba nidai sunana Asad,"
dake mutum ne me bakwarce tuni ya samu shiga cikin zuciyan yan gidamu, ni kuwa ko kaɗai bai burgeni ba dan akalla shekarunsa zaikai talatin da bakwai, kusan Imam Usman zai bashi irin shekaru hudu, dan shima bazai wucce, 45 ba, kin kallonshi nayi na kauda kaina, sabida irin kallon da yake min haushi yake bani,
Ina jin lokacin da Ya Ishaq yace masa.
"Sunanta Aisha amma muna kiranta da Naiha,"
murmushi yayi cikin nutsuwa yace.
"Nice name, sunan Mammyna sunan Yar autanmu suna me daɗi da daraja."
kara jin haushinshi nayi na rufe idanuna, inajin yayi musu sallama ban buɗe idanun ba, balle yasan inajin shi.
Asad Aminu Shema, ɗane ga mataimakin gwanar katsina, yana da kanne, maza da mata, kafin mahaifinshi ya zama maitaimakin gwana tsohun jami'in difulomasiyane, sannan ya zama jakadar naija a Zurich da Canada.
Sannan ya ajiye aikin ya dawo mahaifiyarshi kuwa,lauyace mai zamankanta, kuma malamace a jami'an ɗan fodio,, Amma sun rabu da mahaifinsa. Kusan rayuwarsa a kasan turai yayisu amma mutune mai mutunci dakamun kai, Gashi tuzurune🙊
......Da dare kuwa sai gashi sunzo shida mahaifinshi da kannenshi sun zomin da kayan dubaya, na ban mamaki sosai suke jana a jikina tare da bani wani irin girma na musaman, shi kuwa gogan sai wani lagwaɓar da kai yake, yana kallona, cikin wani irin yanayi sunkuyar da kaina nayi kaman zanyi kuka, dan ban taɓa ganin ana haka ba, sai ma kunya da ya kamani, shigowan Abbanmu da kawu Ubale, yasa na ɗago kaina sannun suka min, sannan suka shiga gaisawa hiran suka koma irin nasu na yan boko da kuma cigaban taɓangaren sha'anin mulkin, sun jima sannan Mataimakin gwana ya mike alamun zasu tafi, fita sukayi aka barni dashi, zuba hannunshi yayi cikin aljuhun rigarshi yana kare min kallo, can yakira sunana kaman me ciwon baki yace.
"Nai,,,,,ha, kin sace min zuciyata.."
Yana faɗin ya tsuguna a gabana yace.
"Kallo ɗaya danayi ya haifar min da soyayyarki don Allah karki k'i amsar soyayyata zan iya shiga gararin rayuwa, Pls kisoni ko ɗan kaɗan ne, inyaso zanyi maneji da wanda nake miki,."
Miqewa yayi sannan ya sumbaci goshina yace min.
" Akwana lafiya kiyi mafarkina."
....
Fita yayi cikin kasaita murmushi nayi a raina nace.
"_Nasamu miji irin wanda nake mafarkin samu."
Lokacin da iyayenmu suka fita Mahaifin Asad Alh Aminu Shema baiyi kasa a gwiwa ba gurin nimawa ɗansa nima ba cikin mutuntaka Abbana da Kawuna suka bada aurena amma an bari sai na gama karatuna.....
*Matar Usman*
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO 🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }
~Na~
*Real Mai Dambu Ce*
🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳
*:~5*
Murmushi na sake masa mai narkar da zuciya girgiza kai yayi cikin farin ciki ya lakuci hancina yace.
"Don Allah Naiha karki juya min baya dan mutuwa zanyi idan haka ya faru dani,"
Juya idanuna nayi cikin son burgeshi , sake gyara tsayuwta nayi sannan nace.
"Mine bazaka taɓa mutuwa ba sai mun tarawa Mamani, jikoki masu kyau da ban sha'awa ko my mine." Fari nayi masa da idanuna, wanda yasake susutashi, kaman ys goyani haka yake ji kaman ya cinye ni sabida son da yake min, ina alfahari da haka domin samun irin Asad babban sa'a ce fa duk ya mace wacce tasan ciwonta gashi cikin sa'a Ubangiji ya bani shi ba wayona ba balle dabara, murmushi nayi sannan nace.
"Ya kamata ka koma gida kaga yamma tayi kat a nimeka."
Na fad'i haka ne cikin sigar tsokana, hararata yayi shima cikin tsigar tsokana yace.
"Ai bawa abu bane k'insan ni d'in d'an farine kinga kenan ba wani abune dan an nimeni " d'aga min gira d'aya yayi shima. G
Tura masa baki nayi cikin shagwab'a ina bubuga kafata, tallafar kanshi yayi cikin wani irin shauki, wanda baisan yana da ita ba, sai da ya kasance dani,
Babu abinda ya shagalatar dashi kaman yanda jikina ke girgixa, jinjina kanshi yayi sannan ya tako har gabana, dai-daita kanshi yayi sannan ya ɗan sunkuyo, da fuskarshi dai-dainawa har ina jiyo fitar numfashinsa, ja da baya nayi, sakamakon hango Imam Usman, wanda duk abinda mukeyi akan idanunshine, kauda kanshi yayi daga garemu dan makarnace ya ganmu, wuccewa yayi, yayinda na hango tsanata akwance cikin idanunshi ɗaga kafaɗa nayi sannan nayi maza nacewa.
"Malam sai anjima, ka gaida Daddy, da Mamani idan kunyi waya zan shga daga ciki."
"Toh princess muje kirakani tunda kinga masu kula dani sun iso tun ɗazun." yace min,
Murmushi nayi cikin jin daɗi na wucce gaba yana bin bayana har na buɗe masa motar nace.
"Ka gaishe da gida maxa antaya ciki kusanbaɗi hanya,"
Shiga yayi tare da banka min harara, yace.
"Ba sai kimin koran kare ba, nima nasan hanya malama maza fecce."
"Oho dai kai kauce." Nace masa, dakyar yabar kofar gidanmu, yana tafiya, nima na juya da niyyar komawa cikin gida, nayi karo da Baby tanaɗe hannunta a kirji tana bina da yaudararren murmushi, cikin rangaji da takun kasaita nazo ns raɓa gefenta, zanshiga gida riko hannuna tayi cikin raunaniyar murya irinta mayaudara, tace.
"Naiha don Allah kiyi hakuri bazan sake ba, sharrin shaiɗane,"
Rike haɓana nayi nace.
"Haba dai? dagaske sharrin shaiɗane yasaki kulla min sharri well anyway, tunda hakane kije dan yanxun ma bansan da wani nufi kika dawo gareni ba, kije bana son ganinki yanda kika buɗe baki kika kulla min sharri, Allah natuba me zaki faɗa min na yarda dake, kije bana kaunar ganinki dan kina fama min abubuwa da dama arayuwata nagodewa Ubangiji da yakareni da ban taɓa ɗaukar shawararki ba balle ya kaini dayin danasani mara amfani."
Ina faɗin haka na wucce nabarta cike da mamaki, kwafa tayi sannan tace.
"Indai ina raye sai nasaki zubda kwalla muje zuwa shege kafasa,"
Tun daga ranar ban sake ganin kafar baby ba,ni kuwa na tattara kashinta na zuba a kwandon shara.
*••••••°°••••••*
Rayuwa ta mike min sosai nake tsula tsiyata babu wanda yake taka min burge har na shiga ss3 Ramla ita kuma ta gama, koda akazo sake jarabawa Asad ya biya min kuɗin Neco d waec, koda Iyayenshi suka sami labarin zan zana jarabawa sunyi farin ciki da haka, sai ma zuwan da sukayi nima masa aurena inda akayi kome cikin girmamawa da mutuntawa,
Wata biyu tsakani muka fara exam, cikin nasara muka fara waec, wanda ya ɗauke mu tsawon mako biyar (wato sati biyar kenan,) muka gama sati biyu tsakani muka fara Neco, bani da lokacin kaina, a cikin wannan yanayin har aka kawo kayan aurena, hmmm kusan abun mamaki, Yayuna mata da akayi aurensu kwanaki kosu basu sami irin kayan da nasamu ba, domin abin ya baws kowa mamaki, ga Ramla wacce ido da ido ta nuna min.Yan ubanci taya zan sami irin wannan kayan, abinda yaja har Innaji tayi mata mugun duka, tare da Yaya ishaq, bana gida suka mata duka amma da safe yar magana ce wacce baifi ayi dariya ba, take ta juya min maganar zuwa wani fassara nada ban ce mata nayi.
"Yarinya tare dake zamu zauna a gidan Asad kinga babu wanda zai damu idan kina tare dani, kafin kema Allah ya kawo miki mr Rigth ɗinki wanda yafi mine haɗewa da jin gayu, amma ba zance wanda yafishi kyau ba."😝 na zaro mata harshe ina gwalo, shiru tayi can nasake takalota nace.
"Aunty Ramluv me yasa baki ga kayan da aka kawo ba, muje ki ɗauki wanda yayi miki kinji."
Wai ni, dole sai nasata tasake dani, ga wani abun mamaki shine kawanceta da Baby can you imagine ace kawata kuma abokiyar gabana itace best frnd biological sisterna, mikewa tayi cikin azama ta ɗauke ni da wani irin mari wanda yayi sanadin kosan dake hannuna ya faɗi, dafe fuskana nayi cikin yake, nace.
"Tabbas kin sauya halinki daga Ramlatu zuwa ta fasashiya, meye laifina me kikeso na baki wallahi zan bar miki kome nawa indai bazakiyi fushi dani ba don Allah yar uwa karki juya min baya," abinda ta faɗa yayi matukar girgizani ashe bani ɗaya bace abin ya bawa tsoro zuwa mata ido nayi hawaye na sauka A idanuna, tace.
"Ni na tsaneki Aisha bana kaunarki ke jinki wata dan kinsami D'an mataimakin gwana shine kike jinkanki you pass everybody ko, bana kaunarki nafi kaunar mutuwata akanki kuma ki zuba ido kiga abinda zai faru ina faɗa miki dani kike zance."
Daman makaranta zan tafi ɗaukar jakata nayi nafita daga gidan hawaye na zuba daga idanuna, tafiya nake kawai, har na iso kofar gidan Imam, kallona yayi sannan ya buɗe motarshi ya shiga, ganin hawayen dake zuba daga idanuna yasa tafasa tada motar yafito,kirana yayi da cewa.
"Aessh!!!" tsayawa nayi cak sabida yanda ya kira sunan ya taɓa min zuciyata ainun, ji nayi duk wani kafan sadarwan jikina ya tsaya a lokacin domin sunan da yakira ya girgizani, takowa yayi har inda nake, ya ciro hankin daga alhujun rigarshi ya mika min,kaina a sunkuye na amsa, sannan na wucce ko godiya ban masa ba.
........A gida kuwa bayan fitata Ya ishaq ya fito daga ɗakinshi yana kallon Innaji cikin ɓacin rai yace.
"Kinji abinda tace kuwa, haka zamu zuba mata ido hassada muraran fa kenan yau da Naiha ce bata sami miji ba wallahi nayi imani da Allah bazata tsangwami Ramla dan tasamu miji ba Amma ita qarara ta nuna batayinta."
Kwallar da suka taru a idanun Innaji ta goge sannan tace.
"Idan baka karya min Ramla ba tabbas baka haifu a cikina ba ka gyara min zamanta sosai."
Komawa ɗaki yayi ya ɗauko dorina, yafito ya shiga ɗakinmu lokacin suna tsara, yanda zasu cutar da farin cikina, batare da tasan da zuwanshi ba ya rufeta da bugu tako ina tana ihu tana kome sai da ya fasa mata jiki sosai sannan yafita daga ɗakin Innaji itama ta shigo da muciya ta rufeta da bugu ta ko ina sai da suka mata liliss sannan innaji tace.
"Kika kuskura naji labarin kin cutar da Aisha toh na yafeki duniya da lahira nacireki a cikin yarana, Yarinyar nan tayi miki kome me kike so da ita kuma, toh koda wasa." Tana gama faɗin haka tafita,
duk abinda ake akunne Baby kashe wayar tayi sannan tasake kiran Ramla cikin kuka ramla ta ɗauka zata faɗa mata abunda ya faru da kadatar da ita tayi sannan tace.
"Listing to me carefully, kina son Asad?"
Jim tayi sannan tace.
"Nop, nidai kawai ina jin ba daɗine idan naga abinda aka kawo mata."
Ran babyne ya ɓaci toh ya zatayi ta cusa min ɓacin rai tunda ramla ba son asad take ba sai