Showing 54001 words to 57000 words out of 108136 words

Chapter 19 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt

08 Nov 2024

17203

Tunda muka shiga jirgi nake zuba masa surutu, ina bashi labarin har na ɓengire da bacci.


Bansan iya adadin da muka ɗauka a tafiyar ba, sai dai jin yana shafa min fuskana haɗi da hura min iskar bakinshi, buɗe idanuna nayi naga ashe mutane sun sauka sai yan tsiraru, addu'ar tashi daga bacci mika nayi sannan nacire belt ɗin jikin kujeran ina kallonshi mika min hannunshi yayi na tashi muka fita daga jirgin,ina karewa garin kallo, ganin kaman ba london bane na juya gareshi da sinki sinkin tambayoyina kaman kuwa yasan da haka yace.
"Toh dubai ce, anan zamu fara yada zango kafin mu wucce london nasan sune tambayarki."


Gyaɗa kai nayi dan ya riga yagama bani amsar da nake nima miye amfanin bididigi, daga nan na tsuke bakina har muka isa masaukinmu muna shiga ni na shige banɗaki naje nayi wanka na gyara jikina sannan nafito, shima banɗakin ya shiga ya watsa ruwa sannan yafito lokacin ina kokarin shafa mai ajikina rike hannuna yayi yace..
"Wannan ba aikinki bane bani na shafa miki,"


"Au kamanta da zakayi sallane da zaka shiga wani aiki na daban jeka na gode. Nace maasa,


Bai kara ce min kome ba yayi wuccewarshi, jallabiya ya zare a jakarshi yasaka, hannu da kafa nashafa man sabida jin yanayin garin nasan akwai zafi kasance dubai suna cikin kasashen masu sahara da kuma, ruwa dan ba kasafai suke samun ruwan sama ba,
Amma kusan itace cibiyar kasuwancin duniya, buɗe akwatina nayi na shiga duba, kayan da zan saka can na hango wani yar doguwar riga, me siririn hannun irin hannun vest, sai dai yana da santsi kuma kuma ga tsagun da yake da shi har cinya shara shara, dan ko shafin da suka saka ba me kauri bane kana iya hango kome na jikin mutum, kalar brown, kallon rigar nake wato Fahima danace ta tayani ɗiban kayan da zan saka shine, tayi min wannan mugun aikin a hankali na shiga duba kayan, cikin haushi na ɗaura hannuwana akai Atamfufina kala bakwai tazuba min sai lashi biyu da shaddar fitan bikinmu, sauran kayan kuwa idan kacire kayan bacci duk Englishi wearna ta zuba min, tsakin danayi yafi a kirga dakyar na maida kayan, na ɗauki wnnan nasaka, sannan na karasa gyara fuskana, inda nayi kwalliya
Jan baki red nashafa irin dark ɗin nan, koda nagama na janyo hula cream colour nasaka, naje na,zauna a gefenshi har ya idar da sallah, mikewa nasakeyi dan na tuna wani turaren da Umma tabani yar ɗuri, naje buɗe shi garin na ajiye shi ya faɗi kasa ya zuɓe, kaman zanyi kuka na saka hannuna na kwashe na maidashi cikin kwalbar, sauran nashafe a jikina sabida kamshin turaren na min daɗi, *Allah sarki Umma Hankaka meda ɗan wani naka* Umma uwace da ta amsa sunar uwa dan ita ta ɗauki ɗan wani fiye da nata, umma mutum ce guda ba ɓari ba, domin farin cikin ɗan wani zata iya sadaukar da ɗarin cikin ɗanta tabaka kai matukar za' a zauna lafiya, kusan Yayun Imamu da kanenshi a ɗakinta suke fara karyawa ko cin abincin rana ko dare, umma ta iya tattalin mutum, shi yasa kafinsu Imamu su mata abu su Abba lawan sun mata, kuma duk kwanar duniya sai sun ajiye mata naira dubu uku uku, kusan maza biyar da suke gidan haɗi da turaruka masu kyau. Ajiyar zuciya nayi sannan na koma inda yake addu'a na kwanta a kan gwiwarshi shafa addu'ar yayi babu shiri, na riko hannunshi nakai kancikina, sannan na kalleshi a sakalce nace.
"Yunwa...."
A hankali yake murza fatar cikina lumshe idanuna nayi ina jin daɗin haka, shi kuwa kamshin turarena kawai yake shaka tare da jin kasala, hannunshi ya shiga turawa samar rigana nayi maza narike hannunshi nace.
"Nifa Yunwa nake ji,"


A kasalance ya gyara min kwanciyar ta hanyar mikar da kafarshi yace.
"Toh a cici, "
Wayar sadarwan cikin ɗakin zuwa kicin ya ɗauka yayi mana odar abinci, suka ce ajirasj nan da minti biyar,


Ni kuwa tura masa baki nayi tare da cire hannunshi daga jikina ina kunkuni, da cewa.
"Niba A cici bane."


Janyoni yayi yana kallon bakina, haka kawai yake ji kamanya cinye bakin nawa, sake tura masa nayi nace..
"Wato ga mahaukaciyana magan..."


Jin ɗumin bakinshi a cikin nawa yasa na makale sauran maganar, hmm bakina kan yaga takanshi dan cinye min shine ba ayi ba, amma jan bakin kuwa lolx😹 ai shanyewa yayi tass, masu kirari sunawa Imamu kirari da Imamu gatan gawa, amma nawa Imamun gatan sone, sabida ya iya ririta abinda yake so kaman kwai,
Jin ana buga kofarmu yasa ya sakeni zuwa kofar karɓan abincin yayi, inda ya shigo har inda nake ya ajiye min abinci, har lokacin ina kwance, rigana a sabule zama yayi a kusadani yace.
"Tashi ga abincin nan."
Dakyar na zauna na buɗe abincin cokali na ɗauka na fara cin chips ɗin da sauce ɗin namar kazar da aka yanyankata, sosai naci na koshi shima cin abinci yayi kaɗan.


Ruwan da nasha shi ya ɗauka ya karasa, mikewa nayi na koma bakin gado na zauna, abincin ya faɗa shima kusadani yazo yazauna, da na gaji da zama na kwanta tare da kallonshi nace.
"Yaushe zamj bar garin nan."


"Zuwa dare dan jirgin 8:30 muke da shi," yace min.


Kallon agogon ɗakin nayi nace.
"Karfe biyu saura kwata, toh nikam kwanciya xanyi." Juya masa baya nayi na kwanta. Aikuwa da karfi yajuyar dani,yace.
"Karki sake juya min baya"


Gyaɗa kai nayi na kwanta, abuna dawowa yayi kusadani ya raɓu dani yana sauke ajiyar zuciya, nikan bacci yaci karfina ashe har,zare rigarsa yayi, nima ya zare min nawa, amagagi na buɗe idanu nace.
"Nikan kai baka da wani aikine da yafi wannan."


Bai kulani ba yacigaba da jagwalgwalani son ran tun baccina yana tafiya dai dai har ya dawo ya gutsire, irinsu Imamu idan baka faɗa musu zakayi azumi ba, ka ɗauka toh wallahi sai sun karya maka shi, dan fitinarshi na dabance, duk da nasan ina hutun sallah, amma haka bai hanani taimaka masa har yasami nutsuwa ba wani abin ma sai daga baya kunya tasa ni na kifa kaina a kirjinshi ina wasa da gashin jikinshi, janyoni yayi yasa bakinshi dai dai kunnena, yayi min magana sake rungume shi nayi haɗi da rufe idanuna, ina dariya kasa kasa, ganin naki bashi amsa kawai sai naji harshenshi cikin kunnena, yana min tafiyar tsutsa, kamkame shi nayi nace.
"Allah nima wani buk aunty Kaltume tabani, rayuwar aure a muslunci, anan naga yanda zan baka kulawa idan bani da tsarki, don Allah kadaina min."


Zare harshen yayi yana shafa gadon bayana, yana hura min iskar bakinshi, yace.
"Tunda hakane xan duba miki wasu nima ina dasu sai ki karanta yanda zaki cigaba da bani kulawa kaman ɗan jaririnki ko *Haskena*"


D'ago kai nayi ina kallonshi kafin nace.
"Toh nagode Ruhina"
Dariya na bashi yace.
"Ruhinki kuma ai yana jikinki."


"Eh nasan da haka, a ynzun haka rayuwata bazata taɓa cika in babu kai ba, koda bana tare da kai, bazan taɓa samun nutsuwa ba, har sai mun kasance a inuwa guda, koda misali kaddara tashigo mana tabbas rayuwarmu zata zame abar tausayine tunda xuciyarmu ɗaya, ruhinmu ɗaya idan baka tare dani gangan jikina ba zaitaɓa moruwa ba,sai kana tare dani,,,, tashi mu zaga garin Dubai."


Na katse maganar nesabida irin kallon da yake min, cike da mamaki har yafito wanka nima na gyara jikina bansaka jan baki ba sai nasaka lips balm, muka fito har wannan lokacin kallona yake yana mamakin yanda nake zaro magana haka, hmm ji shifa ya ma yardani wata yar karamar yarinya.


Haka muka gaza garin dubai da siyayya,karfe huɗu saura muka dawo gida, na gama gaji, watsa ruwa nayi na fito shima ya shiga yayi alola yazo ya gabatar da sallah, nima kwanciya nayi sabida baccin danake ji,




Cikin ikon Allah bacci nayi sosai kaman me sai karfe bakwai da rabi natashi naga yana zaune rike da alkur'anin yana karatu yana kai aya ya ɗago kai yace.
"Ki tashi kici abinci,"


Wanke bakina nayi nazo naci na koshi....




Karfe takwas da wani abu muna airport, lokaci na cikawa muka shiga jirgi




~~~
Ranar monday da misalin sha ɗaya na safe muka isa garin london, bansan haka garin yake da sanyi da sauri na koma jikinshi. Makeleshi nayi shi kuna dariya yayi min muka fito. Juyawa nayi da niyyar komawa ya rike ni tam fuskarsi ɗauke da dariya, yace.
"Da nace kisaka rigar sanyi mi kika ce min, muje kawai ai nan da minti biyar mun isa gida."


Haka muka fito ina rawan sanyi har muka shiga taxi zuwa railway station, daga nan aka kawo min busstop, daga nan da kafa muka isa gida kusan layin uku muka shige, sannan kofar da zai shiga unguwarsu.
Nan motar tasaukemu ya biya kuɗin motar ya ɗauki akwatina, mi kuma naga jakarshi, yana buɗe gidan nashige da mugun sauri, ina niman maboya, dariya na kawai sabida yaga lokaci guda na rikice sabida sanyi, gaba ɗaya na gigice sai rawan sanyi nake hakorana na dukar juna,


Lokaci guda tausayina ya saukar masa, rufe gidan yazo ya zauna kusadani amma ina lokacin nagama birkicewa cire min kaya yayi yasaɓani a kafaɗa dan ina mamakin yanda yake kin kimana ba tare da jin wani nauyina ba, muna shiga ya yaye kyallen da ya lulluɓe gadon dashi, ya kwantar dani shima shiga yayi ciki tare da cire kayanshi body contacing cikin abinda baikai mintuna talatin ba sai gashi ina zufa, zare jikinshi yayi yashiga wanka da alola yaxo ya gabarta da sallar asuba, ni kuwa baccine yayi gaba dani........


*Kuyi hakuri da wannan sabida ina busy yau ɗin nan kusan rabin typing ɗin a unguwa nayi shi..*
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Mai_Dambu*
*Wattpad:Mai_Dambu*


*_Bazan gaji da nuna godiyata a gareku ba Musaman Watpad da Whatsp naga Comments ɗinki mai tafiya da zuciyar mutum dan haka kacokan Buk ɗin Matar Malam sadaukarwane gareku kuma Insha Allah in ba lalura ba zaku cigaba da samun kullum nagode gaku ga ImNai ko Imha💋💋💋_* Inayinku irin na karshen nan👌






*:~30*


A firgice na sauko daga ɗaukar da yayi har towel ɗina na shirin zamewa, bayanshi na koma still ban daina murza gashin kirjinshi ba lekowa nayi na kashe mata ido ɗaya, tare da ɗaga gira ɗaya, nace.
"Friend wacece wannan? Dan ban taɓa ganinta ba hala bata da lafiyane ta shigo ɗakin mutane babu sallama."


Hmm yana tsaye ya gaza furta koda harafi ɗaya daga bakinshi, asalima lumshe idanunshi yayi sabida abinda nake masa ba karamin kunna masa wutar fitina nake ba, jin za'a shiga sallah yasa na janye jikna daga gareshi sokuwar tana nan tsaye, ashe nan idanunta yayi kace kace da kwallar bamu sani ba, shashekar kukarta ya dawo dashi daga duniyar tunanin yanda zai min idan na shiga hannunshi, tsuke fuskarsa yayi cikin ɓacin rai yace.
"Baki yi kuka ba,tukun nan ma tunda baki da tunanin da zaki nemi izni kafin kishigo ɗakin mutane, ki godewa Allah da ba mugun gani kikayi ba, kyakyawan gani kikayi da kinyi da nasaniɓ dannowa mutane kai a rayuwarki gaki da kaman mae hankali amma sai baki da shi get out kafin na ballaki."


Ko ɗar babu a fuskarta sai ma share hawayenta da take ta karaso har gabanshi cikin tsanamin ɓacin rai tace.
"Karya ni, gani nan a gabanka hmm dani kuke zance kaman yanda nayi kuka kuma sai rayuwarku tayi kuka,farin cikin da kuke shirin ginawa sai ta ruguje, Na rantse da Allah sai kazo da kafarka kana rokona, ni kuma...." murmusawa tayi sannanta juya gareni, dariyan takaici tayi sannan tace.
"Ke kam gashi nan kicinye shi ma in zaki iya, zan saki kuka sai nasadaki da kunci, zaki san ni malanta gadon gidanmune nasha a nono, mu zuba Yanxun aka fara shege kafasa."


D'aga mata kafaɗa nayi da ita tasani ni ko a jikina, fuuuu tabar ɗakin ke kyace guguwa,


Cikin gaggawa ya shirya yafita daga ɗakin har yakai bakin kofa na biyoshi nace.
"Kayi kokarin ka rarrashi wancar matar dan ta ɗauka da ɗumi,." murmushi yayi tare da shafa fuskana, sannan yace.
"Kark damu zanji da kome."


Dasauri yafita dan har an fara sallah, nima kayana nasaka na tada sallah dan dama munyi alola a banɗakin.


......
Wato fitan Hauwa daga ɗakin da gudu tafita har tana ture mutane akan hanyarta na shiga ɓangarenmu, ɗakinta tashiga ta faɗa gado sannan ta fashe da kuka, me cikin rai zubur ta mike ta cire wayarta nomber Hajja Yakolo ta shiga nima tana ɗauka ta cigaba da kuka dakay tayi mata bayanin abinda ke faru,


Daga can uwar tace.
"Ba akwai abinda na baki ba kiyi amfani da shi mana," kaman tana ganinta ta girgiza kai tace.
"Ba'a bukatar haka hajja itace kawai nake son na illata bashi ba, ina sonshi sama da kome, hajja bana son su zauna lfy nidai ayi kome kawai, akanta yawwa eh hajja shima ya isa abarta da wannan ma, suje london ɗin, na basu nan da wata biyar suci amarci lafiya."


Katse kiran tayi tana share hawayenta,...


Ina zaune na idar da sallah sai gasu khalil sun dawo mikewa nayi na cire musu kayan makaranta nayi musu wanka bayan na umarcesu da suyi sallah abinci na kawo musu, munata hira dasu dan naki yarda infita mu haɗu da umma sabida kunyarta da nake ji. Mun jima dasu a ɗakin kafin suka shirya zuwa islamiyyan dake cikin masalacin gidan,


Shima ban sake ganinshi ba har dare naji muryanshi, suna sallama da wani ɗan uwanshi, a falon umma, nikam kayana akazo aka kaimin cikin gidanmu sannan matan Yayunshi suka rakani bayan umma taimin nasiha da muzauna lfy da abokiyar zamana, sannan aka fita dani daga ɗakin zuwa wajenmu, koda muka shigo yar shugaban kasa tana tsaye a bakin barandarta, tsaki tayi sannan tace.
"Muna bara muna karuwa gayyan banza arna a idi, dani kike wasa."


Shareta mukayi muka shige abinmu, inda muka tasa raharmu, kitchen na shiga domin su Aunty sun min bayanin gidan, manyan randunar kulikului da dubulan tawaita tsatsafa, gireba, nakiya da alkaki. Haka na ciko musu Ƙaton bowl da shi, na ajiye musu a gaba ina sosa keyana, cikin jin kunya nace..
"Kuyi hakuri da wannan."


Dariya suka sannan suka ce, "Ai an raba mana,wanda aka kawo na gara Allah mungode karki ji kome."


Girgixa kai nayi sannan nace.
"Don Allah ku karɓa indai ba kun raina ba, wancan daban wannan daban,"


Babu yanda suka iya dole suka amsa, suna godiya sannan suka fita, nima jan kofar nayi na shiga ciki ina rage kayan jikina, sannan na faɗa wanka sabida yanayin zafin da ake a garin, ina fitowa naji motsin kaman an shigo, karan fashewar kayayyakina yasa nafito da sauri, Hauwa ce rike da muciya sai fasa min kayan kallona na babban falo, ina ganinta nayi murmushi na juya abuna, ashe shima ya shigo gidan ina part ɗinshi daga, ɗakinshi wanda window ke cikin falon ya hangota da sauri, ya shigo daidai tana rutse plasma na, babbane, tv yana zuwa ya rike muciyar, idanunta ya rufe, burinta ta lalata min kaya tunda nafita, yana rikewa ya tsinka mata mari,


Jin saukar marin ya fito dani, da sauri na isa gurin zai sake marinta na rike hannunshi ina girgiza kaina, cikin sanyi murya nace.
"Kaifa Ubane kuma Wane kai, zaka so ayiwa Yarka ko Kanwarka haka, a matsayinka na Uba da Wa ba girmanka bane taje ai bakome kanta tayiwa bani ba, kaji, kawai kyaleta inyaso sai ka sayo min sabo, tunda matarka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login