Showing 24001 words to 27000 words out of 108136 words

Chapter 9 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt

08 Nov 2024

17193

baki ɗaya, wani razananne ihu tayi wanda yasa mutane gidan suka fito kanta, Yayunta maza komawa ciki sukayi, sakamakon yanda ta wangale sawayenra. Matansune da Mahaifiyarta suka rufeta akayi asibiti da ita.


Cikin tashin hankali aka karɓesu, yayinda drs suka rufa mata cikin tashin hankali sun rasa ta yanda zasu fara mata,


Suna tsaye sun dallara mata haske a gabanta sai ta fara. Nishi can tayi wani mugun nishi sai ga Hawainiyar tazama katuwa jajjur, tasha jini ta koshi, sai kallonsu take, suma baya sukayi ganin sun mata kuri da idanun ai kawai ta juya zata koma ciki take wani, Likita yayi shahadar kuɗa ya raka mata wani karfe wnda ya hudata,


Fasu tayi fari fat, sai kiran mamanta take kiran mamanta sukayi dan sun lura bazata kai labari ba,


Ƙoda uwar tazo, yafitota tayi har dai dai bakinta nan ta labarta mata abinda tayi, a tsorace uwar ta janye jikinta cikin kallon Allah, ya wadaranki fuskarta cike da tashin hankali ta kalle yar wanda zuwa yanzun babu birbishin tausayinta a ranta tace.
"Wallahi kinji na rantse miki da Allah baxan yafe miki ba kuma hakkin raba ɗa da uwa baki ga kome ba anan duniya kenan kika ga wannan ki jira zuwanki gaban Mahaliccinki, Allah ya isa min ɗaukae cikinki da haihuwarki da nayi."


Tana gama fadin haka tajuya tabar ɗakin cikin tashin hankali, har bata san inda take jefa sahunta ba wannan masifar da me yayi.


Tana isowa gurin sauran Yaranta tace.
"Mu koma gida,kawai."


Zaro idanun sukayi cikin kaɗuwa babban yace.
"Baba fa'izan fa."


Zuwa musu idanun tayi sannan tayi magan cikin ɓacin rai tace.
"Duk wanda ya ɗauki koda gawartane ban yafe masa ba."
Juya tayi ta bar asibitin cikin zafin rai.


****
Wani irin hali Ramla tashiga dan abun sun shige jikinta da gudu tafita tana ihu, tana cire kayan jikinta, tana birgima kamar mahaukaci, yayinda Yara suka rufa mata a baya,






****
Asibiti kuwa nurse da likitane suka rufu akan Asad, Yayinda Abbanshi ya kira Mamani, tana tsaka da azkar, ta ɗauki wayar jin halin da Tilon ɗanta yake ciki yasa ta maza takira drvta tace.
"Maza katsina zamu nufa."


......
A ɓangarena kuwa Alhamdulillah, dan numfashina ya dawo normal sai godiyar ubangiji amma har wannan lokacin ban farka ba


A ɗakinshi kuwa ba'a jima ba ya farka, koda ya tashi cire drip ɗin hannunshi yayi ya fito ana rike shi, yans fizgewa,


Kai Ramla da Baby sun shiga rayuwarmu sai dai muyi faɗan Allah ya yafe mana sannan ya bamu ikon cinye jarabawarmu,
Kiran sunana yake tsakaninshi da Allah dan ya zauce nafita hankali, kiran da yake min, har ya iso bakin kofar ɗakina duk tareshi dake bai hana shi banke kofar sa nake ba ya taho da gudu ya hau gadon tare da rungume ni,


Yana me fashewa da kuka, yana k'ank'ameni, fincike shi Imamu yayi cikin ɓacin rai da wani wutar kishi tana azalzalarshi cikin muryan ɓacin rai yace.
"Kafara wace iyarka, karka shiga iyakar ubangiji mana, ai mahaifinta ya faɗa maka da aurena akanta ya kamata kashiga hankalinka inba haka ba za'a jimu, Naiha mat..."


Zuciya ce taciyo asad yakaiwa Imamu duka cikin zafin nama ya kauce masa, sannan ya rike hannunsu ya kifeshi da mari,


Take kokuwa tasake sarkafewa tsakaninsu, duk idanuna biyu mikewa nayi jiri na ɗibana, ga iyayenmu da likitoti sun kasa shiga tsakaninsu sai nice na mike, hankali na isa gurinsu na rike hannun imamu na girgiza masa kai dan ya dunkule z
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }


🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Real Me Dambu ce*








*Wattpad Mai_Dambu*


_Toh me zance wanda ya wucce kuyi hakuri da samun tsaikon da nake muku kuma ina kara baku hakuri akwai wani uzirin da yasha gabana na ajiye ɗayan buk ɗina sai nagama wannan da fatan xakuyi hakuri da haka_ Nagode...





*Page:19*


A gigice na ɗago kaina ina kallonta, ina sonyin magana bakina ya gaza furta kome asalima ita nake kallon cikin tashin hankali, na marasa mi zance tunda natashi ban taɓa fuskantar haka daga gareta ba,ita dai burinta ta kyautata min ko ya-yane, sunkuyar da kaina nayi ahankali na saki kuka mi cin rai, wanda yasakasu duk jikinsu yayi masifar sanyi. Imamu kuwa tsayawa yana kallon
yanda kwalla ke bin fuskana cikin, sanyi murya yace.


"A'a kuyi hakuri kubarta itama ayi mata yanda akewa ko wacce y'a mace itama tayi alfahari da haka, idan aka mata dole ya kamata ta wani gurin a kyautata mata, sannan akwai yarinta zirriyan a tare da ita kuyi hakuri sam ban ɗauki maganarta da wata fa'ida ba asalima shakuwace sila yasa tayi haka." Jikinmu ne yayi sanyi sabida maganar da yayi Babane ya juya ya bashi hakuri, murmushi yayi sannan yayi mana sallama ya fita, wani mugun kallon Innaji tayi min tare da buga min tsawa tace.
"Maza tashi ki rakashi mara kirki kawai." Jikina na rawa nabi bayanshi, da murmushi ta rakani, cikin sanyi murya tace.
"Insha Allah sai kinyi alfahari da auran nan da aka miki, kuruciya ya cika rayuwarki fam, sai yayi hakuri dake sosai."


Juyawa tayi ta kalle Aunty hajra tace.
"Ya kamata ki tafi fa, lokaci na tafiya kuma idan zaki tafi ki tafi da ita gidanki, Ni zan zauna a nan Ishaq da babanku zasu koma gida." gyaɗa kai Aunty tayi cikin share qwallar dake bibiyar fuskarta.


Koda nafita na same shi jingine da jikin motarsa, irin kallon da yake bina dashi yasa naji kafafuwana sun harɗe da junansu kaman zan kifa, ɗago kaina nayi, muka haɗa ido sai naga ya cika min ido ga wani uban kwarjinin da yayi min, komawa yayi ya buɗe motar ya shiga mazaunin, cikinane ya murɗa cikin tashin hankali na shiga rarraba idanun *mi yake nufi da nashiga motar, ba shi yace abarni ba toh mi yake nufi da haka.* Katse min zance zucina yayi inda ya sauke gilashin inda nake yace.
"Ranki shi daɗe, gobe zan koma ki shigo muyi abinyi."
Cikin inda inda na buɗe motar nashiga amma ban rufe murfin ba, wani kallo yayi min cikin murmushi sannan yace.
"Amma da kika bar kofar abuɗe kina gudun kar na miki wani abune, toh kuma ai naga ba wani abu bane a gurinki,tunda ba yau kika fara keɓewa da wasu maz."
Birki yayiwa maganarshi sabida ɗago kan da nayi ina kallonshi, amadadin yaji kunyar abinda ya faɗa sai ya basar, kuma yayi shiru nima sunkuyar da kaina nayi, cikin tashin hankali kokari nake na buɗe kukan da yaci karfina, amma ina na gaza, haka ashe daman duk abinda kayi koda shekara nawane xai sake dawo maka. Takar alkhairine kayi ta wata fuska Allah ya daeo maka dashi ta wani fuska, haka ma sharri, cusa kaina nayi cikin cinyoyina na sake kuka mara sauti, shiru yayi yana sauraron kukan nawa, kuma shi bai hana ba kuma bai masan ta inda zai dakatar dani ba, yasan abinda ya faɗa min ne yasani kuka dan haka sai ya shiga kokarin tada motar ɗago kaina nayi cikin sauri ina kallon inda zai kaini, cikin ko in kula yace.
"Sarkin kuka kenan, gaskiya kika da baiwa ta musaman ace mutum kuka baya damunshi,hmm ga wayar nan na cire layina nasaka miki layin Mtn, akwai kuɗi a ciki,!" shiru yayi cikin son isar da wani sako yace.
"Ban amince ki buɗe wata kafar sadarwa ba,,,,," kasa yayi da murya ya matso kusa dani, yace.
"Idan naga haka raina zai ɓaci matukar haka ya faru."
Komawa yayi mazauninshi ya zauna, sannan ya kalleni, har zuwa lokacin ban daina kuka ba girgiza kai yayi sannan yace.
"Nifa sauri nake ina da abinyi."
Buɗe kofar nayi na sako kafana waje, yayinda ya zubawA bayana ido, har zanfita sai na juya nace.
"Allah ya kara buɗe." sannan nafita daga motar bai tsamaci haka daga gareni ba, dan yaga yanda nake kuka ba lallai bane nayi magana ba, amma sai gashi nace masa Allah ya kara buɗe, a kasar makoshinsa yace.
"Amin."


Rufe kofar naƴi na juya ina tafiya a hankali cikin nutsuwa, har na kule ina bina da ido, dayaga na ɓacewa ganinsa, a hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanunshi cikin nutsuwa sam ya gaza fahimtar yanayin da yake ciki, duk da Zahira sun ɗan taɓa love da ita kafin aure, amma baiji kome akanta ba kaman yanda yake ji akaina ba, asalima yana nishaɗantuwa idan yaga ina kuka, tun farko bai taɓa jin tsanata ba, shi rawan kaina ma burgeshi yake, kuma ya nime aurena ne, dan kar mutanen unguwanmu su lalata min suna, sai dai yasan zai fama dani ne, dan ya lura ni zuma ce, sai an bini da wuta........ Da wannan tunanin yabar asibitin,


Tunda nashiga ciki sai kunyan Innaji ya hanani sakewa, sai raɓe raɓe nake kamar mara gaskiya, kaina a sunkuye Aunty hajra ce ta mike tayiwa Innaji sai da safe, sannan tafike hannuna muka fita, cikin xolaya tace.
"Kanwata irin wannan jimawar haka kuyi hakuri a tare mana, keda malam, karku ajiye mana ɗan tariya."kunya ce tasa na sunkuyar da kaina, har muka fita napep na muka hau zuwa unguwarta, ina son magana amma kunya ya hanani, a falonta muka baje kolinmu mukayi dake mijinta ba mazauni bane, haka yayi min daɗi, kwanciya nayi a falonta ina tuna abinda malam ya faɗa min, a hankali bacci yayi gaba dani.


Koda Aunty ta kawo abinci tuni baccina yayi nisa.


.......
Koda ya koma masaukinshi wanka yayi ya sake kayanshi sannan ya ɗauko wayarshi ya shiga niman Ummanshi kiran na shiga Khalil ya ɗauka tare da sallama yace.
"Abbi yaushe zaka mu tafi."


Murmushi yayi mai sauti sannan yace.
"Yaron Abbi zan dawo but ba daku xan koma ba, kaji good boy."


Cikin muryan kuka yaron yace.
"Abbi ina Mamanmu take har yanzun bata dawo ba."


Tausayin yarone ya hanashi cewa wani abu, sabida kewar mahaifiyarsu da suke dafe goshinsa yayi cikin tashin hankali idanunshi sun kaɗa jajur ga jijiyar goshinsa sun tashi a hankali yakashe wayar, Yana tunanin ina jameesha tashiga tabarsu shida Yaranshi,


Duk wani fari cikin da yake ciki ji yayi ya kaurace masa,


.....
Acan yobe kuwa duk abinda khalil yake faɗa Umma tana jinshi sai da yaga uban ya kashe wayar sai ya koma jikin Umma ya fashe da kuka, tausayin yaron ya cika zuciyarta shafa kan yaron tayi a hankali tace.
"Da sannun Allah zai muku sakayya abinda tai muku, Ubangiji dai ya nuna mata iyakarta, Yanda duniya ya rufe mata sai ta shayar da ita mamaki, sai ta juya mata baya inda duniya ce."


Rarrashin yaron tacigaba dayi har ya ɓingire da bacci.


......
Washi gari tare da Aunty mukayi abin karyawa, sannan muka tafi asibiti, Innaji tana zaune a kan kugera Abba na tsaye abakin kofa sai rama da take kwance, idanunta biyu, jin motsin shigowanmu yasa ta juya cikin nutsuwa ta kura min idanun qwalla ke wasan tsere akan fuskarta, cikin sassarfa na isa gareta, abin mamaki juya min baya tayi tare da runtsa idanunta alamun bata son ganina, komawa ɗaya gefen nayi ina kallonta, cikin rawan murya nace.
"Shin nayi deserve abinda kike min ne miye laifina na baki hakuri wallahi bazan tab'a farin ciki ba inda ina ganinki a haka don Allah Karki juya min baya, ban cancanci haka daga gareki ba, don Allah yar uwata."


Buɗe idanunta tayi cikin kuka tace..
"Wani irin zuciya kike dashine haka, mai ɓoye laifin da aka miki, taya halayarmu ya samu banbancine haka mi yasa kika yafe min abinda nayi miki, shin ban cancanci hukunci bane daga zuciyarki, da har kika manta da abinda nayi miki." Murmushin karfin hali nayi ina rike hannunta zan buɗi baki nayi magana sai ga Imamu sanye da sky coloure shadda, wanda akayi aikinshi da farin zare,sai hularshi fari haka ma takalminshi farine,tunda ya shigo kamshin turarenshi ya cika min hanci, gaisawa sukayi da mutanen ɗakin, ni kuwa na ɗauke wuta baki ɗaya kaman bana ɗakin.


Kallon ramla yayi cikin sakim fuska yace.
"Ramla ya jikinki? kema zata koya miki cutar kuka ko." Murmushi tayi cikin karfin hali tace.
"Da sauki sosai,A'a, ai ba wani abu bane idan nayi dubi da takaitaciyar lokacin da nake dashi, zan koyi wani abu daga gareta ko nima zan rabauta."
Yanda tayi maganar sai jikin kawo yayi sanyi ban dani dan ban fahimci yarenta ba, karkuyi mamaki aifa ba kome nake fahimta ba gani bahaushiya amma ban gane kome ooo.


Nasiha ya shiga mata cikin nutsuwa da kuma nuna mata muni laifin da tayi, da kuma yanda aka tanadi, hukuncinsa anan duniya, idan aka maka hukunci Allah zai sassauta maka nashi hukunci, cikin kuka tace.
"Nayi kuskure kuma na amince a sauke hadin zina akaina, dan ba zan iya fuskarta ubangiji da datin dake jikina ba."


A tsorace na rufe mata baknta jikina na rawa girgiza mata kai nayi ina,zare mata idanu, zare hannuna tayi daga bakinta cikin murmushi tace..
"Son zuciya kike nufin zan sakeyi bayan wanda na aikata a baya, haba ai an wucce wannan level ɗin, Matakin tuba nake karki lalata min zuciyan, amma kuma nasan zaku manta dani ko, ina rokonku don Allah duk wansa ya haifi y'a mace ya maida mata suna na,"


Hannuwana biyu na ɗaura a kaina na fashe da mugun kuka cikin tashin hankali yaushe ramla tasan da wannan batun.


Riko hannuna Innaji tayi, cikin rarrashi tace min.
"Jiya bayan tafiyarku ta farka nan ta shiga nimanki keda Asad, toh munce mata ke,zaki zo da safe nan saidai Asad Babanku ya kira mahaifinshi ya nime izin ganinshi da take sonyi shine Babanshi ya bawa Babanku hakuri ajiyan aka wucce da shi abuja za'a fita da shi, waje ganin likita, wai suna isa gida ya yanki jiki ya faɗi.................






1,708 words ba sauki fa.




_Fatan Alkhairi gareku Yan grp ɗin Aisha Sada Michika_


*Godiya tamusaman ga Ahalin Zauren Mai Dambu*


*Har Abada kuna raina*
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }


🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Real Me Dambu ce*


_Aunty A'i bani da bakin ce miki kome, dan kina biya to kowani fuska nagode sosai_😍


Kuyi hakuri ina busy ne😘
*Wattpad:Realmedambuce*
*:~•18*
Sunkuyar da kaina nayi inda nacigaba da share kwallata, muryanshi na tsinkayo kaman yana magana cikin ladabi, ina son ɗaga kaina amma ina jin a jikina ni yake kallo, har zuwa wannan lokacin bai daina zubda kwalla ba, musaman idan natuna irin abinda Ramla tayi min.


Ban ankara ba kawai sai naji kaman zan zauna very closing dani kamshin turaren, boss ya sannar dani, haka wato turarenshi a hanzarce na ɗago kaina,miqa min wayar yayi cikin kasa da murya yace.
"Ummata tana son magana dake, sannan ki daina wannan kukan dan bazai kareki da kome ba sai ciwon kai,"


Yana gama faɗin haka yabar falon baki ɗaya sabida lokacin sallah da yayi, kara wayar nayi a kunnena tare da sallama. Sautin murmushinta naji kawai tsigar jikina ya tashi, cikin ina ina na gaisheta.
Kafin ta amsa min tace min.
"Jekiyi sallah, lokaci yayi inyaso sai na amsa miki gaisuwarki."
"Toh." kawai nace mata cike da jin kunyarta,


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login