Showing 87001 words to 90000 words out of 108136 words

Chapter 30 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt

08 Nov 2024

18262

lfy
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Mai_Dambu*
*Wattpad:Mai_Dambu*


*45*


Cikin tashin hankali ya fito da gudu, gani na nasauka da gudu nima nayi kanta yasa ya zuba mana idanu yana kallonmu abinda ya fara zuwa kanshi.........
*Mi yakawo Hauwa sama dan ga takalminta*


Sakowa yayi tana ihu, cikin ɓacin rai yace.
"Kiyi min shiru mi ya kawoki sama, a wannan lkcn ko bazan sauko bane"


Ciwon ciki ya hanata magana kaman zai rufeta da duka, idanunshi sunyi jajjur, kallon yayi cikin ɓacin rai wanda yasa naja da baya ina girgiza masa kai, cike mugun tsoron ina yarfe hannuna kwalla na bin fuskana, biyoni yayi har nadangana da bango, kai hannunshi yayi ya ciro min wani kwaro da ya makale min, sannan ya koma sama ya ɗauko wayarshi, kiran motar asibiti yayi, can sai gasu nan muka kintsata aka ɗauketa, zuwa asibiti tun tana yarfe hannunta da cewa na zubar mata da ciki har bakin ya mutu, nima abaya nasaka muka, bi bayanta har zuwa wannan lkcn yaki min magana sai share kwalla nake ina kallonshi, cikin damuwa kuma yaki bani damar da zan faɗa gaskiya.


Koda muka isa har an shiga da ita É—akin wanke ciki, sabida gabaki É—aya cikin yafita, a ciki kuwa scanner suka mata, inda suka fahimci, cikin ya lalace tun kusan mako biyu sakamakon wasu abubuwan da tasha na karin, ni'ima wato dai a takaice maganin mata, kuma har jinin ya fara sauka kafin wannan faÉ—uwar, babban abinda ya damesu matsalar da suke hangowa tattare da mahaifar, dan ba lallai bane ya sake rike É—a koda na awa arba'in da takwas......
Sun kirashi suka masa bayani sanadin lalacewar cikin, godiya yayi musu sannan ya fito ina zaune ne amma sabida tsoro ina ganinshi na mike jikina na rawa, tare da sunkuyar da kaina. Ina shasshekar kuka kasa kasa, yana isowa yasa hannunshi duk biyu ya rungumeni, kaina nakife a kirjinshi a hankali na É—ago ido ina kallonshi tare da girgiza kaina nace.
"Wallahi ban taɓ...."
"Shhhhh ya isa haka muje gida nan ba'a zama a jikin majinyace su suke kome, muje gida kibani abinci yunwa nake ji" ya faÉ—i haka ne dan ganin yanda hankalina ya tashi, kuma baya son ya sake rasa damarsa da yasamu, jiya shi yasa bai tanka maganar da Hauwa take ba.


Dakyar nake tafiya sabida wani baccin da ya cika min ido, hamma nake akai akai, har muka isa gida, kunun tsamiya nayi tare da dankali da kwai, ni kunun nasha nazuba na hauwa idan zai kai mata, ina shan kunun ina gyangyaÉ—i yana zuwa ya kalleni, cikin sigar tsokana yace.
"Zo nan, yar kwailar amaryata wacce batasan daÉ—in miji ba amma jiya naga harda kuka aka min...Don Allah karka bari don Allah kaci gaba wayyo zaka kashe ni da daÉ—...."


Toshe masa baki nayi da hannuna ina zare ido, cikin jin kunya cizon hannun yayi yana dariya, yace.
"Allah bakarya nayi miki ba abinda kika faÉ—ane jiya, toh nidai abinda bansani ba dama ina da sweet ne haka"




Ajiye kofin nayi cikin jin haushi tare da zubda kwalla nace.
"Nikam karabu dani ban sani ba, karka dameni. Ai kaima kayi ta surutu dan ban rike abinda kafa bane amma ai har da ihu kayi"




Zaro ido yayi tare da dafe kirji kaman wani karamin yaro, yace.
"Na shiga uku, don Allah karki faÉ—a kowa yaji nasan baki manta ba"


"Ai wallahi na tuna," nace tare rufe fuskana ina dariya, dariya yayi da son jin abinda ya faÉ—a, "hmm sharri ko Humairah, inba tsoron ba ki faÉ—a mana." yace tare da tsareni.




Mikewa nayi sai da na isa, bakin kofa nace.
"Hmm Nana Aishana sarauniyar daÉ—i, zumata, haka kike dama wayyo nayi kewar wannn....."




Da gudu na kule É—aki, dariya yayi cike da farin ciki, yanda yaga nasake shima ya sami nutsuwa karyawa yayi sannan ya leko ya samu ina bacci, sumabarta goshi yayi sannan yafito, zuwa asibiti yana shiga ya ajiye basket É—in sannan ya zuba mata abincin taci, dakyar ta amsa tayi tana kuka, shi kuwa ko tausayinta bai ji ba, mikewa yayi zuwa jin window É—akin yana leken waje, ya juya mata baya hannunwanshi duk ya zuba a aljuhun wandonshi......




"Wato ke kin É—auka zan saki Aishane dan ta turoki daga sama ko, sabida kun maidani sauna kuka zauna kuna sani ina zaluntar Yar mutane, idan kece tayiwa haka zaki ji daÉ—i, toh ai badamuwa abinda kashuka shi zaka girba," isa inda take yayi ya damka mata sakamakon binciketa, yace.
"Ai nasan kina da ilimi ku duba abinda suka rubuta," a hankali ta warware, kin dubawa tayi cikin kuka tace.




"Wallahi karyane turoni tayi, daga sama dan nazo dubaka shine yanxun zaka kareta."


"Abubuwa da dama kinyi min ban ce miki kala ba, kuma nayi shiru ban É—auki mataki ba ba wai dan bana son É—aukar wani mataki a'a sai dan maganar da Hajja ta faÉ—awa Ummana, yanxun kam kina shirin wucce gona da iri, daga yau kar nasake ganinki a sama, kuma idan wani fitina ya kunno kai tsakanina da matata, abakin aurenki, koda wasa kika cewa hajja wani abu akan matata da Uwata shima a bakin aurenki, sannan ki faÉ—a mata abinda yajanyo zubar cikinki kika kuskura sunan Noor Ya fito, abakin aurenki ke koda kallon banxa kika mata," murmusa mata yayi sannan ya juya yabar É—akin da asibitin kuka ta fashe da shi,




Shi kam da ya dawo gida yasamu ina bacci , gefena ya kwanta muka cigaba da baccin tare, agogon falona ne ya buga wanda yayi dalilin farkawana naji mutum a bayana juyawa nayi na sake shigewa jikinshi, ina sauke numfashi, zuba masa ido nayi ina kallon fuskarshi, bakinshi na ke kallo,ina dariya nace.
"Mutum ba mace ba amma Allah yayi masa baiwar gashi haka, dubi yanda gashi ya saka É—an bakin a tsakiya, bakin da yake cinye na mutane"


"Wato gulmana kike ko?"


"Ni? Yaushe? Dawa kuma? Nifa banyi gulmarka ba" na tura masa baki, daman abinda yake nima kenan tuni ya shiga aikin lada, nikam nagaji da halinshi musaman yanxun da nake yawan baccin nan.......




Da dare aka sallamo hauwa naga tashiga hankalinta dana tambayeta ya jiki ta amsa min cikin sakin fuska,




***
Alhmdulillah mun sami nutsuwa a,cikin watanmu na hudu da zuwa london, Imamu na kokarin kamanta adalci a tsakaninmu idan kacire hanya É—aya da yake hora hauwa nice dai nake fama da bacci da cin abinci musaman tuwo, kaman zan cinye da kwanon nake ji, gashi nayi wani munafikin kiba, daga sama zuwa kasa, nayi fam har bana saka brz dan ciwo kirjin yake min......


Zubawa kayana ido nayi kaman zanyi kuka, kowani riga da skirt na É—auka zan saka sai zip É—in rigar yaki rufewa, daga dogayen riguna É—auko guda zan saka da murna na yana zuwa kirjina ya tsaya kuka na fashe da shi, na É—auki wayata nakira Umma ina kuka nace.
"Umma kinga kayana fa sunki shigata"


Dariya tayi tace.
"Da alamu yata tayi kiba kenan kai abin yayi min daÉ—i,Allah ya buÉ—i Idanu lafiya."


Ina na fahimci maganarta nanna shiga rabtaɓo mata bayani, abinda ke damuna ita kam sai masha Allah take faɗi tana dariya sannan nace mata.
"Umma ina kewar kununki fa"




"Toh ya knn Nana" aikuwa nasakata a gaba da rigima da kuriniya, shigowanshi yasa nayi mata sallama na koma kanshi ina bubuga kafa na fara ina shirin ɓare masa baki yayi maza ya rufe min da hannunshi ihu na kwalla masa tare da bori haɗi da kuka, ruɗewa yayi ganin yanda na baza kaya a kan gadon yace.
"Zuma faÉ—a min mi ke faruwa."




Kallon kirjina nayi sannan na kalle gadon ina nuna kayan da na fito dasu nace.
"Duba fa, duk kayan sunki shigata wai mi nake ci da nayi kiba haka, kaga fa ban isa saka brz ba haka nake yawo ko ina gandan gandan kamar budurwan kauye,"


Rike haɓanshi yayi yana nazari dan kwana biyu gudunshi nake duk lokacin da ya kashe arna toh zan wuni ba lafiya nayita amai da ciwon kai dana gane haka shine na fara gudun shi,


"Hmm magana nagaskiya zan dubaki amma sai munyi karatunmu a gado idan kuma bai miki ba kije abinki ki cigaba da zama super mamah." ya faÉ—a yana tsareni da ido.




Share fuskana nayi na gyaÉ—a masa kai, tura masa baki nayi, nace.
"Wallahi minti biyar zakayi idan ka wucce tureka,zanyi abuna."




Dake yaga bati sidan amincewa yayi da sharaÉ—ina mutumin kan ya shiga hidimarshi baji ba gani, sai dayafi mintuna biyar, dake nima karamar magulmaciya ce bance uffan ba har ya gama yashiga wanka yafito kayana ya maida min cikin wardrob É—in ina kwance bacci yayi gaba dani...........




Tsaf ya fahimci ina É—auke da cikinshine amma kiriniya irin tawa ya hanani fahimtar haka sai yayi shiru dan yana guÉ—un kar wani abu yasami cikin.




Yamma likis na farka naje nayi wanka tare da amai, sannan nafito, ganinshi nayi ya mika min kaya a jakar kwali yace.
"Kisa wannan, zasu miki."


Dogayen rigunane guda biyar da riga da skirt biyar kowanne high skirt, sai takalmar fata marasa nauyi, sakawa nayi ina godiya cass kayan suka min,






Haka ma hauwa yabata nata, dai dai yake mana kome, amma maganar gaskiya duk ranar da,zaiyi rayuwar aure dani sai nasami kyauta na musaman, idan nayi masa magana sai yace.
"Aisha zuciyatace bazan iya cireta nabaki ba amma da kome nawa zan mallaka miki"


Murmusawa nake kawai...


Lokaci natafiya sosai abubuwan da suka faru har sun wucce, sai dai muyi fatan Allah ya yafema kurakuranmu,




Muna da wata shida wanda yayi dai dai da cikin da bansan da shi ba wata huÉ—u caf, abin duniya ya,addabeni sakamakon fahimtar da nayi na haÉ—iye É—an tsaka ban sani ba, eh mana tayuwu ina bacci ya shige min bakina toh inba haka ba taya zan rinka jin mutsin kamar É—an tsaka na yawo a cikina da zaran naji yunwa toh haka zai addabeni da zillo da kutufo, ina cin abinci shi knn,gashi nasha kallon cikin ta madubi bana ganin karcewar danake, kuka nake ina magana ni É—aya nace.
"Yanxun don Allah miye laifina da zaka shige cikina kana yawo, ko so kake ka kasheni, ni wallahi fita zakayi"




Ban É—aki naje nayita kakari da Amai, ko zai fita amma shiru sannan na haura wajen pupu na gwada yaki dole nafito ina yarfe hannuna bansan yana É—akin ba sai da nasaka hannu akai na fasa ihu, ya mike zubur da cewa "lafiya
Kike ihu haka."


Zubewa nayi a kasa ina cewa.
"Wayyo na mutu na lalace na shiga uku na haÉ—iye tsaka yana yawo a cikina zai cinye min kayan cikina."




A ruÉ—e ya tambayeni yanda nake ji amma ina nabashi amsa sai kuka da ihu, himar yasami muka fita zuwa asibiti, gwajin farko aka gano ina É—auke da cikin wata huÉ—u da kwana goma caf, kuma muna lafiya, daga ni har abin cikin shawarwari aka bashi yanda zai kula damu........




Tunda muka ɗauko hanya nake kuka dan basu min shi kuwa dariya yake tare da godewa Allah har muka shigo gida hauwa nafalo na wucceta fuuu tambayarshi tayi dalilin kukana nan ya faɗa mata kai tsaye, a kiɗime ta dafe kirjinta wani irin kallo yabita da shi, nan tashiga nuna murnanta a fili, yana,zuwa gurina ta shige tayi dialing nomber Hajja..............🤒 Yar gidan Bossiya








Wayyo Indo rigima........
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Mai_Dambu*

*Wattpad:Mai_Dambu*




*:47*


Wani irin murÉ—a cikin yayi min wanda ya haÉ—a da zubar jini guda guda, salati nayi haÉ—i da dafe cikin, wani irin duhune ya mamaye min idanuna, garin na yunkura na tashi, sai nasake kifawa akan cikin samadin haka na sake wani irin kara........




Shi kuma ya hauro dubani kenan yaji karan, da sauri ya shigo É—akin ganin halin da nake ciki yasa yayi turus yayi cikin tashin hankali, kamar wanda aka zarewa laka,haka yakoma dakyar da kyar ya iso inda nake, cak ya É—agani zuciyarshi kaman zata buga sabida tsabar tashin hankali da damuwa, mantawa yayi da akwai wata a gidan ya fita dani gurin motarshi,




Sakani yayi shida drv suka figi motar da gudu, suka isa asibitin da ni, koda suka isa ganin halin da nake ciki, dr's kusan biyar da nurse hudu suka rufa min akai, ana bani taimakon gaggawa duk da yawansu sai da suka sake kiran wata likita bakar fata, wacce tafita break, da gudu tashigo abin mamaki tayi kiciɓis da Imamu sama sama suka gaisa, sannan tashigo tana leka fuskanata zaro musu ido tace.
"Wannan ai kanwata ce, don Allah ku taimaka min.a cice rayuwarta,"


Jin Abinda Dr Halima ta faɗa yasa suka sake bada himma akaina, cike da saran samun Uwa da abin cikinta, abinda yafi ɗaga musu hankali subar jinin, dole suka kira dr Na'im, wani kwararrene a fannin mata masu ciki da kuma matsalar ɓari, da zubar jini, ba urdene ɗan kasan Iraq, zuwanshi yasa aka kawo masa wani kwayar magani yasa aka tura min, ko mintuna ashirin ba'ayi ba sai ga jinin ya tsaya cak kamar anyi ruwa an ɗauke, maida hankalinshi kan abin cikin yayi, sabida muhawaran da wasu daga drs ɗin suke wasu nacewa a min wankin ciki dr Halima ita kuma ta kafe akan babyn yana raye, dan taga alamun haka tun zuwanta, abisa bincikensu sun gano maganin zubda ciki nasha har dozen, shi yasa jinin ya zuba haka,


Karɓan abin scanner dr Na'im yayi yana dubawa a hankali cikin nutsuwa sai da ya gwada har sau uku kafin ya ɗago ya kalle dr Halima yace.
"Cikin kanwarki na wata biyar ne amma kuma ya lalace dole zamu mata allura a abin cikin ya fita, kiyi hkr nasan yanda kuke son yara amma sabida rayuwar Uwar dole a cire É—an tayin."




A hankali ta isa kaina tana shafawa, cikin damuwa ta juya tace.
"Don Allah kafin ku mata allura kubani dama É—aya ina jin akwai cikin a jikina a sake dubawa."




Zuba mata idanu suka kafin wani daga cikinsu ya je jikin na'uran ya shafa min gel, sannan ya shiga dubawa, Cike da Al'ajabi ya hango bugawar zuciyar babyn can kasa da .0½ juyawa yayi ya kallesu sannan yasake dubawa tabbas abinda ya gani ba karya harbawan czuciyar Babyn ya hango,
" Congrts Dr Halima Omar babynku na raye"


Ya faÉ—a fuskarshi É—auke da murmushi, kumowa gefe tayi sannan tace.
"Alhamdulillah, kafin hawaye suka samu damar saukowa daga idanunta,"


Jini aka nima tafita ta faɗa masa ana niman jini, ba ɓata lokacin aka ɗibi nashi, aka saka min, bai samu ganin kowa a cikin drs ɗin ba sai bayan awa biyu da rabi, sannan suka zo ɗakin da yake hutawa suka faɗa masa abunda ya faru,


Boye ɓacin ranshi yayi cikin dauriya har suka fita lumshe idanunshi yayi yana ɓacin rai har bakinsa na ɗaci, a ranshi yake faɗin *Wato Aisha sai da tayi yunkurin zubda cikin nan ko hmmm karshen zamanmu yazo knn taje gidansu ta haifa zan zo na amshi kayana*


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login