Showing 84001 words to 87000 words out of 108136 words

Chapter 29 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt

08 Nov 2024

18256

ya isa ya sashi dukana balle akai da ys shakeni, wallahi da ina ganinka a matsayinda yafi na mijin da nake aure amma a yau ganinka nake mutum mara kima da daraja, bazan taɓa niman saki ba, amma na haramta maka kaina har abada kaje inda sukafini su shayar da kai farin ciki me ɗorewa, Ubangiji yana madakata kuma shi zai bi min hakkina cikin ruwan sanyi.",


Gume ne yashiga karyo masa cikintashin hankali yasake ni yafita yabar min ɗakin, zama nayi tare da fashewa da kuka, karkuce asirine fa a'a logona ta gane, tare da amfani da rauninshi nason yara, kuma duk abinda muke akan kunnenta, tana jin yasakeni tayi maza ta sauko, ɗakinta baibi takanta ba yabar gidan baki ɗaya, kiran Uwarta tayi ta fesa mata, can suka sake kintsa wani, yanda zan bar gidan baki ɗaya,


Koda yafita ummanshiya kira ya faɗa mata kome jin maganar tayi wani banbarakwai, aikuwa ta buɗe masa wuta da masifa da koda wasa yasake dukana Bata yafe masa ba, dan bata ga abinda nayi da,za'a dake ni ba ai gaskiya na faɗa, banda rashin adalci akan gaskiyata zai dake ni, kashe wayar tayi sannan ta kirani duk yanda taso taji abinda zance kawai ce mata nayi babu kome, ranta yayi mugun ɓaci hakuri ta shiga bani, nace mata ba kome ya wucce.




A hankali abubuwa suke faruwa tare da wuccewa amma tsakanina da Imamu da matarsa ido sannu wannan bans musu kuma ba karamin damuwa ya shiga ba dan bin mutane yake waisu bani hakuri ni abin dariya yake bani,.......


Da yaga naki saukowa sai ya rabawa kowa kwanta, tare da zuwa kowacce kayan abincinta a store ɗinta, dake kitchen ɗin, dukda taso ɗago bori shima ya haukace mata dole ta hakura bayan ta faɗawa mahaifiyarta, daga kaina ya fara, kwanaki biyu duk yanda yake rawan jiki na nuna masa bansan wannan batun ba, asalima kuka nasaka masa tare da tuna masa abinda ya faɗa min *Har ina yarinya karama nasan daɗin namiji* shiru yayi ya ɗauke wuta, da wannan maganar muka gama kwanaki biyun mu yana gado ina kasa, dan nasan halina da son jiki idan nasan muna tare toh shige masa zanyi, ni kuma shawaran Umma nake aiki da shi,.


Itama yaje yayi mata kwanta, babu abinda yayi mata karshe sai naji da safe tana kuka da ihu, tare da kiran Uwarta ta faɗa mata, ina jinsu,ashe jiya ba harkane shine ya masa magana ya bige mata baki......🙊


*Hmmm vote yayi kasa ba karya zan huta nima nagaji, body nobe firewood*
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Mai_Dambu*
*Wattpad:Mai_Dambu*




Dominku my Wattpad fans😍 ina muku fatan alkhairi








*:~•44*


Dake Allah ba azalumin sarki bane sai gashi yau sun kaure nidai nawa ido, haka ya gama kwanaki biyu ya dawo ɗakina, tuwo nayi miyar kuka ina zaune ina ci hankalina kwance sai gashi ya hauro sama duk sai ya diririce ko nasan da mutum a gurin na cigaba da cin abincina,motsuwa yayi har inda nake yazo ya zauna, cikin inda inda, ya kai hannunshi cikin filet ɗinda nake cin tuwo ɗagowa nayi cikin tsantsar ɓacin rai, ina yake, nace.
"Har akwai abinda zaka ci daga yarinyar da tasan daɗin namiji? Ina ga me zai hana kaje gurin wacce batasan daɗin namiji ba, zai fi sauki, kuma matukar kacigaba da shige min zan kira Umma na faɗa mata, kome kaje bana son ganinka a rayuwata, dan baka san darajar Y'a mace ba."


Ina gama faɗa masa haka ns mike zuwa kitchen, raina nazafi, kwallace take son zubo min amma na hanata sauka so nake na koyawa kaina juriya,




A kitchen nakarasa cin abinci, ina wanke filet ɗin naji kamshin turarenshi mai suna Chancer, zuwa yayi ya haɗe bayana da kirjinshi, ina jin yanda zuciyarsa ke bugawa,kanshi ya sauko da shi dai dai kunnena yace.
"Kiyi hakuri mana Noor"?
Juyawa nayi a fusace na tureshi nace masa.
"Stop call me noor, Ni Aisha ce, bani bace na dace da haskenka tana kasa ɗauke da juna biyunka donAllah get out" na nuna masa hanya saukar da fuskashi yayi yana kokarin kallon idanuna, matukar nabarshi ya kalle cikin idanuna zai sauya min manufata, akanshi. Ni kuma bana jin haka ynx.


D'ago haɓana yayi cikin wani irin murya yace.
"Noor kalle cikin idanuna, ki faɗa min duk abinda yake bakinki zan jureshi nayau da har abada."


"Eh mana zaka iya jurewa sabida ka ɗibo jarabarka zaka juye min akaina ba, ka maidani injin saduwarka da,zaran ka matsu ga baiwarka nan, wai na tambayeka, tunda kake mu'amala dani, na taɓa nuna maka ina jin daɗinka da har kake da bakin da zaka faɗa min nasan daɗin namiji wow haka yayi ma jeka gurin wacce bata san daɗin ba," na faɗa masa haka nayi wuccewata.


Mamaki nabashi yanda nake iya faɗa masa magana son raina....


Fincikoni yayi na kwace kaina na shige ɗaki ina tafiya ina juya masa mazauni yanda zai cigaba da jin ba daɗi har na shiga na cire kayana sabida zufar da nayi na ɗauro towel, nafito na rufe kitchen ɗina, dan hauwa tana shigo min tana ɗiban abinci, yana zaune a falo nazo na wucce na rufe sannan na koma ɗaki da keyna ai kuwa ganina a haka yasa ya mike zubur yabi bayana, ina kokarin tattara kayana naji anjanyo ni da karfi mun faɗa gado,, cike da ɓacin rai na ɗago na dalla masa harara, sannan na mike na faɗa banɗakina, ina cikin wanka ya shigo yayita nimar maganata ban kulashi ba, har na fito na,zauna na sauya kayana a gabanshi nayi komena kai tsaye, mamaki yanda na fita harkanshi yake.......






«»
A cikin yan watanin nan da bana shiga damuwar kowa, na fahimci har shi kunyata da shakkana yake, balle kuma matarshi, wacce ta rasa yanda zata kuntata min,


Ina zaune a ɗaki dake dankalin turawa nayi da safe madafa da mai da yaji, yazo yasamu ina ci shine yasa hannu ni kuwa na mike nabar masa, dan dama naci nafarko da ban koshi bane na karo, abinka da manja, ya taɓa masa whiter shirt ɗinshi shine dake maiyace yana sauka ta gani shine ta tasoshi a gaba wai su zo abata nata, ban kulasu ba dan ina ɗaki kuma na rufe kitchen ɗin,




Fitowa nayi sanye da wani gajeran wandon iyakarshi cinya da dake jeans dark blue, sai pink body hook, na ɗaure kaina da wani siririn pink ɗin ɗan kwali, babu kwalliya a fuskana, harɗe hannuna nayi a kirjina ina kallonsu, dana ga sun tsaya kallona daga shi har matarshi sai najuya na koma, bayan rigar netne me sharp ɗin hrt, haka ma gaban rigar dan kana iya hango brz da nasaka, fari,


Dukkansu an rasa wanda zai min magana, shi kam gabaki ɗaya ya ɗauke wuta, yana lissafin rabunshi dani ina yace a ranshi, nike aurenki bake kike aurena ba..
.


Ita kam mahaukaciya kamar zatayi hauka sauka tayi taje ɗakinta tashiga niman kayan wanka,...


Tunda na fahimci babu abinda yake tafiya da hankalinshi kaman ya ganni cikin kananun kaya ba karamin tafiya da ruhinshi yake ba, da wannan nake masa gashin ƙuma,






Tun da yafita bai dawo ba sai dare, nafito kenan daga kitchen dake umma ta haɗani da tsumi na sai nasaka a frig duk dare nake, sha, wani lokacin da madara nake sha, wucce ni yayi ya shige kitchen can sai gashi rike da kofi ya mika min share shi nayu na cigaba da shan zumana, zama yayi a kusadani ya kamoni ya matseni sai da ya tabbatar na shanye ɗanye kwai da lipton....


Jefa min wani alawa yayi me tsame tsame na shiga yawo dashi a bakina, shine naji dama dama, tun daga ranar yasani a gaba da bani ɗanyen kwai da lipton, a ɓangare guda gashin da nake masa ya takurashi kiran Umma yayi ya faɗa mata gsky abinda ya faru, faɗa tayi masa sannan ta masa hannunka mai sanda. Inda ta nuna masa toh idan bayi a hankali ba matarshi da uwarta kashe masa aure zasuyi yayi nazarin wasu abubuwan mana, take ya shiga nazari bayan sunyi sallama da Umma, lokaci guda ya faɗa kogin tunani, wato idan ya fahimta gadar zare aka saka masa, ni nasan da haka shine bai sani ba, koda ya shigo dake ranar asabarne kai tsaye sama ya hauro,






Ina kwance a falo yazo ya kwanta kusadani yana tura hannunshi cikin rigana, idanuna a rufe, ina jinshi nayi banza dashi, juyoni yayi muka haɗa ido yace.
"Don girman Ubangiji kiyi hakuri baya ga Ummana sai Zahira sune kawai nake iya basu hakuri Noor kiyi hakuri mana, bazan sake ba, kinji ina cikin begenki da kewarki."


"Hmmm kace jarabar ta motsa kenan sabi sabi, kaga tashi min bana jin daɗin jikina, bakona Yazo min,"


"Eh naji ni jarabbabe ne amma idan a gurinki nake haka a ko ina ni normal mutum ne don Allah kiyi hakuri da kuskurena kinji."




"Bazan iya ba tashi bana son ganinka, a rayuwata."


"Amma Aisha mi yasa baki manta bya ki fuskanci gabanki, ina ganin mu manta kome ma gyara gabanmu"


"Akan me zan manta baya tunda banji daɗinshi ba ai baxan taɓa mantawa dashi ba, kaga malam kafita min daga falo."




"Kiyi hakuri kinsan Allah nason masu hakuri, kuma yana tare dasu, saikiga a dalilin haka Allah ya yafe miki wasu kurakuranki....."
Kaɗa idanuna nayi kafin na amsa masa da cewa.
"Ai Allah da yace yana tare da masu hakuri bai ce acutar dasu ta kowani fuska ba, dan haka kafita bana son kara ganinka"




"Haba Noor kimaida abinda ya faru matsayin kaddara, wacce ta riga fata, babu wanda yake wuccewa kadɗaransa matukar yana raye."


" Datakar Akaramalla ita kaddaran dake bata da dangi iya balle baba shine za'a sakota akan abinda aka aikata da son zuciya, ita kaddaran wato maraininyar wayon mutane ko, dan bata anga bata,da wanda,zai tsaya mata ko yayi kyau"






Shiru yayi sabida ya fuskanci magana nake faɗa masa a fakaice, sunkuyar da kanshi yayi a kan wuyana yana sauke numfashinsa, dai dai kunnena yasa bakinshi yace.
"Ki saurareni mana"


Mikewa nayi sabida jikina yana ɓaciwa, maidani yayi na faɗa kanshi muku zubawa juna ido yace.
"Ki saurareni nace"


"Ɓaxan saurareka ba sabida nima baka saurara min ba, ai ynx bani da wani amfani a gare sabida abinda nake tutiya dashi karabani da shi, toh akan mi zanyi daraja a gurinka"




"Amma Aisha" nayi maza nadakatar dashi da cewa.
"Amma me mi zaka faɗa min mi zaka ce min dukana kayi fa, har da gori mi zaka faɗa min dan kare kanka, sabida ni bani da uwar da zata tsaya min, bani da wanda zai kwatar min yancina, ko ce maka akayi zan kira Ummanka na faɗa mata halin da nake ciki, tarbiyar da aka ɗaurani akai ba'a koya min kai kara ko suka."


"Toh ynx akwai abinda ake miki kenan bayan wanda ya faru."


Murmusawa nayi na mike cikin zafin nama nabar falon tare sai da na isa bakin kofana nace.
"Wannan kuma kuta dama, dan bani da lokacin kai kara ko faɗar korafi,"


"Don Allah ki tsaya mu fahimci matsalarmu tare mana," ya faɗa kaman zai rusa ihu .
Daga masa kafaɗa nayi da cewa. " matsalarka ce ba tawa ba"


Duk ta inda ya ɓulo min toshewa nake, sabida naki bashi damar wanke kanshi, sai bibiyata yake, haka kawai zai shirya mana fita shan iska, ko nida shi ko dukkanmu, dukda haka naki kula al'amarinsu abu ɗaya nayi masa, shine ɓoye tsamarmu a gaban hauwa amma a bayan idanunta toyashi nake son raina, yau ina takfin wanka dake cikin gidan nazo hutawa, toh ya dawo bai ganin ba shine yabiyo sahuna gurin, ashe taga wuccewarsa ni kuma ina cikin ruwan, ina wanka a ciki, na hangoshi sai nayi fuska na cigaba da wanka, kaman ance ɗaga kai sai naga tana biyoshi da sauri na isa bakin inda ya duka yana min magana mika masa hannu nayi nace.
"Taimaka kafito dani,"


Kallon kayan jikina yayi, can kuguna na ɗaura wani kyalle kaman ɗan kwalli, sauke numfashi yayi ya mika min hannu aikuwa nayi baya na fincikoshi muka nutsa cikin ruwan, dai dai ta iso kenan,




Mikewa mukayi muna dariya ni badashi nake ba da ita nake da tabiyoshi, kafin yace zai min wani mgn tuni na sunkuyo da kanshi, na haɗa da bakina, rungume ni yayi cikin mugun kewana ya tallafi fuskana,..........Tsundum mukaji am faɗo cikin ruwan, aikuwa sai da ya famtsama ko ina tana huci ta shiga tsakaninmu, dama aɓinda nake so kenan. Ganin bai ɗauki wani mataki ba nafita nabarsu a gurin bin bayana yayi da ido, cikin kaɗuwa, dan salon yanda nake tafiyar ma abin kallone, fita yayi yabarta a ciki, ya biyo bayana ina cikin ban ɗaki ya shigo, duk yanda yaso yakai hannunshi taɓani naki, fir dan dole ya hakuri har muka fito birkice min ya nime yi aikuwa nima nabirkice masa ina kuka tare da haɗa kayana nace.
"Tsakaninka da Allah na taɓa shiga kanku idan kana wani abu da ita, mi yasa ni take min haka baka taɓa ɗaukar mataki ba ji bi fa, ranar da muka zo gidan nan abinda tayi mana mi kace mata sai nice ka maidani sauna ki kaje Zunnur bana son ganinka."




Janyani yayi muka faɗa gado, cikin idanuna ya zuba nashi muryanshi na rawa yace.
"Humaira sake nanata sunana kinji? Sake faɗar sunan, don Allah karki juya min baya kiyi hakuri dani wallahi zan tsaya miki daga yau bazan sake barin wani ya cutar min dake ba."


Abin tausayi kwalla naga yana bin fuskarshi,bansan lokacin da na mika masa duk wata yardata da amincewata ba, na bashi duk wata kulawa a wannan ranar, tabbas munyi kewar juna, dan kamar bazamu hakura da juna ba, haka muka kasance, sai dai kafin ya shiga ban ɗaki yafito bacci yayi gaba dani, yaso mushiga tare amma naki bayana ya dawo ya kwanta yana kwantar min da gashina da suka hautsine......




Da yaga baccin yaki karewa ne ya ɗaukenk cak sai jina nayi cikin ruwan ɗumi, nan ma wata muguwar kasala ta sauko min, shi yayi min wanka ni kuma nayi saura koda na gama kin fita nayi a cikin abin wanka na gyara kwanciyana, sai bacci gajiya yayi da shiruna ya shigo dariya yayi ya ɗaukeni cak,






Sau gadona anan muka tare, har dare yafita yayo mana abinci, ya kaiwa hauwa kasa nima ya kawo min tawa, dakyar naci, sabida baccin da ya tun karoni, sallar magibri da isha suma dakyar nayi nashafa addu'a na kwanta na,zata mutumin nan zai kyalleni ne amma ina a daren sai da ya hanani sakat, na wani lkc nikam bacci ya dame ni bana fahimtar kome har yayi min wanka yadawo dani sai da asuba yake faɗa min murmushi nayi masa kawai.




Koda muka kwanta danaga take takenshi wani abu yake bukata tuni na ware ɗaya ɗakin, ina fitowa naganta a bakin window ɗayar ɗakin dake kofar yana kusada matakalane, bata tsaya da kyau ba nace mata.
"Malama lafiya"


Sabida tsabar rashin gaskiya ta tafi da baya aikuwa ta daku da maxaunanta sannan ta cigaba da dunkurawa, ihu da salati muka sake nida ita sakamakon jinin da ya ɓalle, tana isa kasa ta fasa ihu da "wayyo Allah na ta kasheni ta turoni daga sama, ta,zubar min da cikina."




Ana kukan targaɗe ga karaya tasamu, Nace ku huta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login