Showing 99001 words to 102000 words out of 108136 words

Chapter 34 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt

08 Nov 2024

17185

sarkin rigima ta fara addabar mutane, dake Amatullah tana da ciwon idanu,toh an bata medical glass, wani lokaci idan tasaka sai ta juya min Imamu, gabaki ɗaya ta ɗauke uban baki ɗaya wani lokacin har mamaki take bani, dake na raba musu sunayensu, Amatullah ina kiranta da Amatul, itakuma Amatuljalal, Ina kiranta da Amah sun raba ɗabi'a da kome nasu dabam ne, ita Amah tana da mugun niman faɗa rigima ga mugun ɓarna, duk inda taga barna jikinta har rawa yake sabida tsabar ɓarna kome na gidan a killace yake muna ganinta zamu fara ɗaga komi kai kofar kicinɗinmu a rufe yake nakan sakata a gaba inta kallonta cikin damuwa yau badan Wan Ubanta bane inda wasune sai sun koreni, dan akwai lokacim da ta buga musu laptop da kasa ina zuwa na ɗauketa da mugun mari, ranar naga ɓacin rai akan me zan duketa faɗa yayi tayi, ta fasa ma sai me ai yana inda ake sarrafa laptop ɗine.. Shine nayita tunanin yanda zamu da ita




Tadamemu a gida karshe sakasu mukayi a Day care,😹 ita kuma Amah tana da matukar hakuri ga tsoron masifa idan ka cire tsotson yatsarta bata da wani damuwa, amma haka bai hana Yar uwar sata kuka ba, dan rarumarta take da dame da cizo, idan ni dasune sai na zare mata ido take nutsuwa, idanunta kuwa yaga kayan kwalliya toh sunansa sorry(Ko akwai me bugar Amah tazo masa kwana biyu, dan har na hango yanda kamanin gidanku ya koma.)


Kamota nayi na,zaunar da ita tare da zare mata ido, amma haka bai isheta ba sai da ta zare madubin.idon Amatul, ta kama gudu, faɗawa jikina tayi cikin gwaramcinta tace.
"Mo agudu a me dudina" juyawa nayi na hangota tana gudu tana kutsa mutane sai dariya take, raina ya ɓaci narasa yanda zanyi da Amah, mikewa nayi nabita dake kaina a sunkuye yake ban ɗago ba, nadai ganta tana shigewa jikin wani mutum tana cewa.
"Oyeni Moh butata" yanda take maganar ya burgeshi murmushi yayi yasake rungumeta yana lumshe idanu, ina isa gurin kamshin turaren Dior ya bugi hancina take brain ɗina ya shiga hargitsi waye nasani da wannan turaren da naji kamshinsa take xuciyata ta amsa min da *Asad* a gaggauce na ɗago mukayi ido biyu dashi, matar gefenshi na kalla muka gaisa, sannan nayi kamar bansanshi ba nace.
"Yan mata fito daga jikinshi bana hanaki shigewa jikin mutane ba"


Karfin hali nake dan nariga da na aijye shi namanta da tunaninshi tunda nasamisu Amah na rage nauyin dake zuciyata na riko Yarinyar muka bar guri zuciyata na min rawa, tsabar tsoro da fargaba, jin muryanshi nayi na kirana...."Aishaaaa"


Cak natsaya cike da kaɗuwa na rasa banyi cigaba da tafiya ba, zuwa yayi gabana, ya ɗauki yarinyar yana kallona cikin murmushi yace min.
"Ina Malam yake, wannan cutie baby taki ce, masha Allah tayi min kyau muje mu gaida me gidan"


Shiru nayi har muka karaso wajensu, Abba lawan suka gaisa sannan yace min.
"Matar da kuka gaisa a inda take matata ce, har da yarinya me sunarki, itama Naiha nake kiranta, don Allah idan mun koma kizo Mamani kullum sai tayi maganarki."


Gyaɗa masa kainayi sannan ya mana sallama, yana barin gurin Abba lawan ya zabga min harara, cikin masifa yace min.
"Waye shi? Amma kinsan da auren ɗan uwana akanki kike kula wasu mazan?" shiru nayi na sunkuyar da kaina nayi cikin bakin ciki, abinda Yayan imamu yake min wato yana taya kaninshi kishi, murmushi nayi sannan nace.
"Kayi hakuri, Abokin Yayana ne unguwarmu ɗaya rabona dashi tun kafin aure shi yasa na kulashi."


Shiru yayi can kuma yaji kunya yace min kiyi hakuri.
"Kiyi hakuri,"


Murmushi nayi kawai dan na hango kihin ɗan uwanshi yake, Aunty kaltuma sai juya masa barbanci tayi cikin masifa ranta ya ɓaci da abinda yayi min.......


Koda muka shiga jirgi bata fasa masifarta ba har sai da na riketa nace mata.
"Nidai nagaji da wannan ashariyar da kike min,in ba tsoron ba, ki juya hausa mana."


Na faɗa mata haka cike da zolaya dole tayi shiru dan haushi kam ta gama jinshi,


.......
Alhamdulillah mun iso lafiya a lagos muka yada zango kafin muka bi jirgin maiduguri, muna isa motar Imamu na gidan aka zo ɗaukarmu a ciki, dan gulma sai danaji kewar shi a raina, na rasa yanda zancireshi a raina,




Mun isa yobe lafiya muna shiga gidan akarambana ta shedawa mutanen gidan gata tazo, bikin fahima saura sati biyu amma sabida wasu abubuwa muka shiga zirgazirga, Ina barinsu a gurin Umma, nida Aunty Kaltuma da Aunty Falmata sai, ni da Aunty Kausar kawan Ummulkhair, Mamar Fahima sai da muka kwashe kwana goma muna zarya, zubewa nayi a gaban na gaji, dake ranar za'a fara wankar amarya nace.
"Wash Umma, kuguna kamar an ɓalla minshi jiya dakyar nayi bacci."


Murmushi tayi tana haɗawa Amatul Tea, ashe Amah tana kallon yanda ta buɗe Ovaltea da madara, da sugar yar baɗo Umma na ajiyewa ta shige bayan kujera ta durkusa ta buɗe madara da ovalte ɗin tajuye a kasa, ta ya mutsasi sannan tayi wanka dashi, tcigaba da sha ni kuma muka cigaba da hiranmu, shirun da naji nan na fara raba ido nace yar uwan taduba min ita har tafita waje bata ganta ba jin karan gwangwani yasa muka, leka nida umma "Keeee" nace mata da sauri ta rarrafa tafito tayi waje, wanda ya kaure da ihu, nima bin bayanta nayi na riko kunnenta ina make kanta, sam bansan abinda sukewa ihu ba sai jin muryan Khalil yayi, yana cewa.
"Mummy!!!"
Da sauri na juya ashe na murɗe mata kunnen kara ta calla sabida ɗan kunne ya matse kunnen aikuwa tasake a jiyar,zuciya ta zuɓe, tsorone ya kamani na rasa yanda zai mata, tun juyawa ta ya zuba min ido cike da mamaki, yaushe aka ganni tambayoyi da yawa suka diro masa, cikin zafin nama ya sunkuce yar yayi nayi maza nasha gabanshi na saka hannu na amshi Y'a wani firgigitacciyar harara na masa.........💋


Ojoromi ojoromi, I wan to to love joromi💃💃💃💃💃 inayin Simi💃💃💃💃
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Mai_Dambu*

*Wattpad:Mai_Dambu*




*52*
Mun isa garin katsina da karfe goma cif, Ya ishaq ne yazo ya ɗauke mu, lumshe idanuna nayi cikin wani irin farin ciki, yau gani a katsina shakar iskar garina nayi cike da zakuwar ganin Innaji, koda muka iska gida, da sauri nafita "Keeeeee!" Aunty Maryam tace min sannan ta rufeni da faɗa.
"Kina da hankalin kuwa da danye jikinki zaki lafta a guje, Anndi min bonni ni maryam"
Harara ta maka min sannan tayi cikin gida cike da takaici nima cikin nayi gidan a cike da jama'a ina zuwa nazuɓe jikin Innaji na sake kuka mai cin rai, ina dadda kankameta, itama kamkameni tayi, cikin karfin hali dan ta mikar dani mukayi ɗakin Babanmu, tun jiya yayuna suka faɗa mata abinda suka gani, akaina......


Zaunar dani tayi a kan kujera sannan ta zauna a kusadani.........
Shafa kaina tashiga yi, a hankali kafin tace.
"A lokacin da zuciya takekkashe daga abinda take ji, ambaton Allah ake sai tayi laushi, shi rayuwar duniya kanshi ɗan hakurine, sannan ita kanta auren ibadace mai zaman kanta, zan baki shawara guda ki rike sirrinki ko Yan uwanki bana son su sani, nima ban da Mahaifiyarshi da ta faɗa min bazanso ki faɗa min kome ba,kiyi hakuri Allah zai bi miki hakkinki."


Sosai nake kuka ina rungume da ita, sannan na mike nace.
"Bari na gaida mutanen cikin gidan."


Haka nafita jikina a sanyayye, nabisu ina gaishesu sai barka suke min, ni kuwa aka bari ni da yake......


Dakin Innaji na yada zango nan nake jin wai waleema zasuyi jakunan nagani da hoton yaran abin ya bani mamaki, a tsakar gida kuwa, namar da muka zo da shi aka shiga hidimarsa.....




Alhamdulillah anyi kome cikin nasara har an watse wanka Innaji tayi min sannan ta kama jikokinta tayi musu, ina gama saka kaya nabi lafiyar gado, Yaran ma bacci sukayi, can Amatuljalal ta tsalla ihu, tana niman nono, ɗaukar ta Innaji ɗauketa tana girgizata sannan ta ɗan tasheni na zauna samin Yarinyar tayi a cinya. Sannan tajera min pillow a baya nagaji matuka gaya, amma haka na mike na zauna nasaka mata nono, tana koshi ta turo min kayana nima ajiyeta nayi na kwanta abuna, ban sake tashi ba sai asuba nashiga na gyara jikina
Na dawo na kwanta, bamu sake farkawa ba sai bakwai saura, abin karyawa aka kawo min kuɗin tsamiya da soyayye dankalin turawa, sai farfesun kan saniya... Brush nayi na wanko idanuna na zauna na cinye abincin tass na cinye abinci, ina gamawa muka shiga wanka can muka fito na zauna na caɓa kwalliya kamar me shirin zuwa gasar kyau. Abin takaici ina kallon kaina sai nake jin ina da Imamu nan yaga yanda nafito, wasu zafaffan hawaye naji, tare da jin tsanarshi. Zama nayi ina kallon Yarana wanda suka sha wanka, Amatullah na ɗauka na fara bata abincinsu sai da takoshi sannan na ajiyeta na ɗauki Amatuljalal, itakam kin sake nonon tayi sai da bacci ya ɗauketa sannan na kwantar da ita,




Kwanciya nayi nima ina nazarin abubuwa da dama, wanda suka shafi rayuwana dana Imamu...... Kwalla naji nabin fuskana......




............
Duniya tayiwa Imamu atishawar tsaki duk ya sukurkuce dakyar yake tafiyar da rayuwarsa duk yarasa ta inda zai fara....


«»‹›
Maiduguri........


Hankali hajja idan yayi dubu ya tashi kusan sati guda knn rabonta da waya da yarta sai mafarkinta take cikin mawuyacin hali, ta rasa gane kome cikin tashin hankali ta shirya sai yobe. In taje ta saka musu, kuka yarta hankalin kowa ya tashi dole suka shiga niman nomber Imamu basu same shi, kuka take wiwi...




«»‹›
WAIWAYE.......
Kwance take kamar mataciyya jini kefita ta kasarta ga bakinta da yake zubda jini, cikin tashin hankali Sara ke ɗagata amma sai ta sake komawa ta kwanta sabida yanda cikinta yake azabar ciwo, da gudu wani magidancin Bature ya shigo ya ɗagata yayi waje da ita cikin tashin hankali ya fita da ita yana murza hannunta tare da fadin...
"Meesha buɗe idanunki karki bari musake rasa wannan cikin a karo na huɗu ina sonki ina son abinda ke cikinki, sabida ke narabu da kowa nawa na musulunta sabida ke, pls ki taimaka ki buɗe idanunki..."


A kiɗime suka isa cikin asibitin aka wucce da ita ɗakin kulwa da masu irin matsalarta.....
Ko kun manta da itane......
Lokacin da jameesha tabar gidan Imamu, garin tabari baki ɗaya,ta nufi USA....
Inda ta sauka a calfonia, nan ta shiga niman yan naija mazauna can kuma tasamu, dan sun haɗu da Sara, sun haɗu a gurin cin abinci a nan take nuna mata tana niman abinyi itama sarah bata da wani abinyi sai rawa a club ana biyanta dan haka ta ɗauketa zuwa club ɗin da take, ba tare da wani jinkiri ba suka ɗauketa aiki dake son abin duniya tasa a gaba sai ta faɗa hulɗa da mazan turawa a cikin haka ta haɗu da Nicolas, shahararren mai kuɗi wanda yayi kaurin suna gurin kera motoccin yana da branch a cikin jahohin irinsu Mexico city, Machengahm, Indian, New york da Miame, kuma yana samun kuɗi ainu, tun sau ɗaya da ya kwanta da ita shi knn ya haukace ya hanatq hulɗa da kowa kuma ya hanata, rawa kuɗi yake sakar mata na na fitan hankali..






Da sabida ya huta da ita ya kebiyanta daga baya sai suka koma soyayya, ya bata kome na rayuwa kuma suna tsula tsiyarsu dashi, Jameesha ta zama babbar mata son ranta take murza nairori, ta manta kowa sai kanta suna cikin wannan zaman ta wayi gari da son da ya musulunta ita ta gaji da harkan sabida wani wa'azi da taji a wani gidan raidiyo, shine tq nuna masa zata rabu da shi, haka kawai karshe da yanima ba'asi sai ta fashe da kuka tace ita ko ya musulunta ya aureta ko kuma su rabu, dake yana masifar sonta bai damu ya amince koda ya faɗawa Iyayenshi suka ce basu yarda shi kuwa yace yanzun yaga rayuwa,


Gurin Limamin unguwarsu suka je masa da bukatarsu nan ya msuluntar da shi ita kuma yace sai tayi istibira'i, nan suka amince suka bar gurinshi koda suka tafi amadadin takame kanta tunda tana da iliminta a,a sai take biye mishi suyita shafe shafe dakyar dai sukayi wata huɗun nan ranar da ta gama aka ɗaura musu aure,




Tun daga ranar suka buɗe shafin rayuwa, shekaranta guda ta fara samun matsalae yawan mugayen mafarka da Yaranta musaman Ummi da zaran ta ganta a mafarkin shi knn cikin jikinta ya zube knn, gashi Allah ya ɗaura musu jarabar son baby, sau uku ana ɗaure mahaifar, amma abin mamaki tana ganin ummi a mafarki ta tashi a razane shi knn cikin ya tashi aiki, tayi kuka tayi addu'a har aikin hajj taje, amma Cikin ikon Allah tasmi cikin jikinta, a hanyarsu ta dawowa ne suka haɗu da wata mata, kallonta matar tayi cikin ko in kula tace mata.
"Bazaki taɓa samun biyan bukatarki ba sai kin koma kin nemi wanda kika zalumta.."


Dake a airportne shiru tayi kanta a sunkuye ta ɗago da niyyarwa matar magana, sai ta nemata ta rasa, abinda ya mugun tsoratata knn, ta riko mijinta cikin tsoro haka suka koma Usa cike da tashin hankali......
Ko sati bayi da dawowa ba suka nufi Liverpool, domin niman Imamu da Yaranta, bata sameshi ba amma sun gaisa da Mmn Husna ita ta bata nombeta....


«»‹›
Wayyo jego da daɗi yasin ga daɗi ga cima mai dadi, kusan satin mu huɗu munyi kyau man gyagije yaran tabarkalla kowa ya gansu sai yayi magana.........
A hankali muka cinye sauran kwanakin inda muka shiga bin Yan uwa muna musu bakwana dan tafiya Japan....






............
Allah sarki hauwa ta koma abin tausayi kamar mahaukaciya ga duka ga zagi haɗi da horon yunwa, kuma a haka mutane ke zuwa mata Anita tana amsar kuɗi, ba maza ba, ba mata ba..
Tayi kuka tayi danasani mara amfani
........
_Nifa Allah bacci nake ji, da zaran naci na koshi toh na zama lazy😂_
[5/4, 06:21] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Mai_Dambu*

*Wattpad:Mai_Dambu*



*54* No editing
Barin gurin nayi na shige falon Ummah kowa abin ya basu mamaki ɗai ɗaikune basu damu ba, asalima suna tunanin muna tare, ni kuwa ina shiga na,zuɓe a gaban Umma kamar zan fashe da kuka na mika mata Yarinya kaina a sunkuye, karɓa tayi ta umarce ni da nabata ruwan sanyi a frig da sauri na ɗauko na mika mata buɗe bakik goran tayi wanda yayi dai dai da shigowarshi tare da sallama,


Umma khadi da tafito daga ɗakin Umma itace ta amsa sallamar, cike da mamaki.....


Daga nk har Umma bamu damu dashi ba, ruwa ta gumtsa ta fessa mata aikuwa tasake ajiyar zuciya, Amatul na ganin haka taje ta rike hannunta suna dariya, mikewa nayi Umma tace.
"D'auketa kiyi musu wanka dan itama wancar sha zumaminyar taje kan madarah tayi nata shagalin, Allah yayi musu albarka ya shiryesu shiriyar Addinin musulunci, Amma Abba lawan ko Hassan ko mansur sai sun biyani madarata da ovelte na, in haka ba toh Allah sai dai kutattara kuje gurin Hajiya Saratu itama taji yanda suke min, yara da kiriniya sai kace ana jona musu chaji,"


Dariya nayi cike da kunya nace.
"Kayya Umma zan tafi da Amatul zan bar miki Amah."


Zaro ido tayi tace.
"Ni ban isa ba wata rana ni za'a samu a birkice sai dai Ko Khadi tana niman yar taya hira."


"Ni Khadijatu zan ɗauki wannan yarinya da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login