Showing 6001 words to 9000 words out of 108136 words

Chapter 3 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt

08 Nov 2024

17187

kawai yanke hukuncin tusawa Ramla banxan tunani akan asad kasa da murya tace.
"Wallahi nayi imani kishin Asad kike kuma alamu ya nuna sonshi kike, karkiyi wasa da damarki ni nan zan miki hanyar da zaki mallaki Asad amma sai da amincewarki idan kika bari aka saka auren Naiha da Asad toh har abda zaki zauna a gida babu miji karshe ma bazaki samu irin Asad ba, matsalar gidanku, ki barshi a hannuna Insha Allah kin mallaki kowa har Asad ɗin........"


*Shin me kuke tunani game da Baby,*




Pls nd Pls Share.........






OFFICIAL MAI DAMBU CE👌



[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }





🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Writtern*
By
Mrs Fulani🐄



_Ina kike Ummul khairi ga shafin nan dake kawai da kuma jin daɗinki_👌💋❤


*:~4*


Kafin asallame ni kuwa kowa yasan irin Son da Asad yake min, basan yanda zan kwatanta ba, dan Mahaifiyarshi sau uku tana zuwa dubani tare da alkhairori na ban mamaki, take wani jin kai da wani ɗagawa ya karu min, makarantar da nake, Asad ya cireni ya maidani makaranta mafi tsada, a garin katsina, waya kuwa Iphone+8 ne a hannuna, Ga Mamy ɗinshi musaman take haɗamin mayukan shafawa,da kaywn cosmetic, dalilina suka fara abota da Imam Usman, wanda ya tayashi murna da jin an bashi aurena,.


Yau juma'a tare muke dashi a gidan Annah sai shagwaɓa naketa lafta masa yayinda shi kuma ya ɗaukw duk abinda nake masa dan bai damu ba sai ma karin farin cikin da yake ciki idan yana tare dani yakan manta da kome da kowa shi burinshi ya mallakeni shi ɗayanshi, ganin haka yasani nima naki bawa kowa damar da zai takura min sai shi, kuma nake cin karena ba bu babbaka a cikin zuciyarshi dan nasan nice kadai babu wata domin ya gina cikinta da kaunata, cikin sakalci nace.
"Mine ina son ice cream, da cake me chocolat, sai shawarma" na tanɗe bakina cike da jin kwaɗayin abinda na lissafo masa.


Girgiza kai yayi cikin rashin amincewa da abinda nake so sannan yace.
"Second love, kiyi hakuri ba zaki samu kayan zaki da sanyi ba, asalima sai da Abba yayi min gargaɗi da bai yarda nasaya miki koda chewgun ba dan hak...."


Bai kai karshe ba na miqe cikin jin haushi da hasala na ɗauki wayata na fita ko sallamar Annah banyi ba, sabida jin haushin abinda Asad yace min.


A hanzarce ya biyoni yana bani hakuri amma fir naki kulashi ran yan mata ya ɓaci, bai fasa bina nima kuma naki sauraranshi, a haka har muka iso, layinmu, ganin zamu ratsa mutane yasa na juya nace.
"Ya isa kawai kaje gida sai ankwana biyo dan zamu fara exam kaga dole na maida hankalina akan karatu,"


Gyaɗa kai yayi cikin rashin kuzari yace.
"Toh amma muje na rakaki har gida kinji ko baby doll" ya karshe maganar cikin zolaya dan yasan na tsani kace min baby doll, kusan haka yan makaraɓtarmu suke ce min, baby doll, wai ina musu yanayi da biebis,


Tura baki nayi kaman na fasa ihu ina tafiya ina kunkuni shima bai fasa biyoni ba, haks muka ratsa mutane suna ganimu sai nunamu suke da yatsa, sabida yanda muka dace, Imam Usman kanshi a sunkuye yana gyara Yaronshi Khalif takalminsa, yaji Nura da Sayyed suna cewa ai hakane sai kaga yarinya tagama watsewa karshe ka ganta ta buge da auren mutumin kirki, kaga yanda ya mutu akanta wallahi da zatace yabata zuciyarsa da zai ciro yabata, sabida son da yake mata,,"


"Manzon Allah s,a,w yace idan baza kufaɗi alkhairi ba kuyi shiru." Abinda Imam Usman yace musu kenan take suka kame bakinsu.


*Usman Shehu Usman shine cikaken sunan Imam Usman, Yafito daga jahar Yobe, ɗan babban gidane domin gidansu malamaine, ciki da wajensu, shine ɗa na Takwas a cikin gidansu baya ga kane da suke binshi maxa da mata,Zan iyacewa gidansu ilimin addini da zamani ya same mazauni. Acikin gidan, mahaifinsu ya jima da rasuwa, amma kafin nan yana da mata huɗu yara goma sha takwas, maza da mata, Babba yayansu Muh'd suna kiranshi da Yaya Abba lawan, yana aiki a babban asibitin abuja, sai Mai Abubakar, yana aiki a N.N.P.C, suna kiranshi Yaya Sadeeq, sai Aunty Aisha, tans aure a maiduguri,Sai Aliyu malamine a state poly damaturu, sai Xubair, yana kasuwanci a fataskum, Sai Hafsa, tana aure a Benin,sai Khadija ta rasu, sai Masur,sai Imam Usman sai Umma hani, Fatima Hauwa'u, sai Yan biyu Hassan da Usaina, sai karamarsu Balkisu,


Mata biyune a gidan ɗakinsu Imam su tarane, ɗakinsu Abba lawan kuma su biyarne, gidan akwai kyakyawan fahimta a tsakanin matan, sai suka ɗaura yaransu akan tausayi da jin kan juna, haɗi da girmama juna, babu raini a tsakanin junansu.


Imam Usman aiki ya kawoshi garin katsina, Inda shima alkaline, sabida ɗan kimanin Shakaru 46 zuwa da bakwai, ya karanci harkan shari'a a france, inda yayi degree ɗinshi a can, sannan ya koma jami'a madina yayi degree nabiyu an fanni shara'ar muslunci, bayan ya hada sai ya dawo gidan anan Abba lawan ya nima masa auren Zahira, tunda mahaifinsu ya rasu shi ya ɗauki duk wata ɗawainiyar Yan uwanshi, bayan shekara guda Yar kanwar Umminshi Janeesha tatada rigima ita idan bashi ba zata shiga duniya,


Faɗawa Abba lawan akayi take, ya nime masa aurenta akayi bikin. Yanzun haka yaranshi biyu, Zahira har yanxun Allah bai bata ba, sai Janeesha ita kuma bata kula da yaran sai Zahira ubansu.


_Wannan kenan_



Har gida ya rakone sannan ya zuba min ido kafin yace.
"Naiha Am so sorry kinji ba zan sake ba,"
Murmushi nayi sannan na rausayar da kaina nace.
" Ya wucce."








Pls Share.....


*Matar Usman*
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }





🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳







*Na:Real MaiDambu*


'''Shafin nakine Aunty Aisha kina magamtuwa ainun kana idanuna cike suke da kunyarki ga wannan shafin dominke'''


*:~6*


Zuciyar Ramlane ya shiga kisima mata wasu abubuwa, amma tunawa da tayi da kashedin Innaji tayi maxa tacewa Baby.
"Kaiii bana bukatarshi nafi son farin cikin innaji akan nawa, don Allah ki fita daga sha'anina, haka zai sama min nutsuwa," kashe wayar tayi baki ɗaya tafashe da kuka, domin tafara hango buhun damu atare da banzan tunanin da baby ta cusa mata,


Hmmm ina makaranta amma zuciyata cike take da zulumi, gami da damuwa haka muka gama exam nafito daman shine final ɗinmu,


.....A gidansu baby ajiye wayar tayi haɗi da shu'umin murmushi, kana ta rufe idanunta, tana hango balbalin bala'in da zai tunkaroni,


*Wacece Baby*


Sadaka yalla ce, kaman yandasu Annah suke bakin hawure haka suma suke amma su baby daga chad suke, tana da yayu maza guda biyu, sai ita maxan suna da mutunci, domin suna kokarin inganta musu rayuwa amma baby ta fanɗare, sakamakon ɗaurin mazaunin daga Mamansu, shi yasa yayun sukayi watsi da ita suka kame kansu, baby tagirmeni domin sa'ar Hajra ce, kenan har Ramla tagirma balleni, dake tana da karamin sanwa yasa ake mata kallo kamar sa'armuce,hmm kaɗan daga cikin halayarta kuwa bata damu da kasota ba idan kai mata ko kanka da k'awo sai tayi da kai, dan sam bata da girman kai asalima har faɗa muke da ita idan tana k'ask'antar da kanta haushi take bani a duniya na tsani wulakantakai, toh haka baby take sai abu biyu da ban faɗa muku ba,wato harka da maza ina mamakinta yanda tamaida rayuwarta, nabin maza, dukda saura kiriss tadulmeyar dani,Allah bai bata nasara ba toh a wannan bigirin ita karshece, dan ko kak'i Allah idan kayi mata, toh babu ruwanta dakanka zakazo har gurinta, idan tafagen surar jikine, akwai kome kyau diri balaifi ta haɗasu kan sai Hamdala,dan takace ni jikina shine jarina bana bara amma ina karuwa...! Wannan shine halayarta.


.....•
Bayan na dawo, daga makaranta tsame jikina nayi da kowa dan tsoronsu nake gani nake kaman suma sun sauya, da naga hutawa na tafi gidan Annah, ban dawo ba, sai dare dan yamzun nadaina zuwa islamiya, zaman gida nake,



Sati guda dagama exam ɗina aka saka aurena nanda wata biyu, sune mafiya daraja a gareni sune watanin da bazan manta dasu ba,


Takanas Annah ta ɗauken zuwa nijar, inda akaita min gyaran jiki, kafin afara naje nagaida Dangin Mamata, anan naga abin mamaki, inda muka haɗu da Yayata da muke uwa ɗaya, Neenah jin nazo yasa itama tazo daga gidan Babanta nan Annah take faɗa min ai neenah yayata ce, kallonta nayi idanuna daf da kwalla nace.
"Annah mi kike qoqarin ɓoye mana Annah ki faɗa min miye ke farune?"


Murmushi Annah tayi sannan tace.
"Kwantar da hankalinki, Hafsatu itace mahaifiyarku, mun yan damagarane, muna can cikin wani kauye ne, Uballe shine ɗana na fari sai Hafsatu, tun suna kanana Mahaifinsu ya rasu, fari da rashin ruwa yasa Ubale ya dawo Niamy inda yazo yake niman kuɗi dukkarshe mako yana zuwa mana, dake akwai y'anuwana acan, cikin ikon Allah samu ya buɗe masa, har ya kamana haya, acan lokacin Hafsatu tana makarantar gaba da firamari, muka koma can, nima mata makarantar gwanati yayi inda tacigaba da karatunta, tana aji uku, aka kori yayanta a gurin aikinsa sakamakon Satar da aka musu a ma'aikatar munshiga ta gayara, kafin wani me kuɗi yaga hafsatu yana so, yana da mata ɗaya bata taɓa haihuwa ba, idan yayi aure ita ke kore masa mata, shi kuma ya haukace akan mahaifiyarku muku ma tsoron kar a sake mana ita yasa mukak'i ganin haka ya nimawa Ubale aiki, a kamfaninsa nan dai muka hakura aka bashi haftsatu,


Hmm bayan bikinsu kaman uwargida bazata ɗaga hankalinta ba, sai daga baya da taga Hafsatu da ciki, daman duk matanshi babu wacce take kaiwa sati uku agidan takoreta, sai Mahaifiyarku itace takai har wata huɗu, tunda takyala ido taga cikin fara shige shige har Alhaji Marwa ya saki Hafsatu, ta dawo gida inda tav cigaba da rainon cikinta har ta haihu, dukda ba a gidanshi take ba yayi mata bajinta sosai na haihuwa,


Bayan suna yazo ya maida ita har an shirya zata koma daga baya yace ya fasa dole haka muka hakura har Aka yaye Khadija sunan Mahaifiyarshi suna kiranta da Neenah, lokacin da aka yayeta bata kara sati biyu a gidanmu ba yazo ya ɗauki yarshi ya kaiwa Yahanasu, dake Allah yayiwa khadija kyau sai Ubangiji ya ɗaura mata sonta abinda ya kwantar da hankalinmu kenan dan ita da kanta take kawo mana ita, ana cikin haka kawunku ya dawo Najeriya da sana'ar shayi, shekaranshi biyu ya bar shayi ya buɗe shagon saida kayan shayin daga nan yazo ya ɗaukemu baya ya auri yar kanina, jibirilla, Mubarakatu kenan, toh dawowarmu katsina nan yasaka hafsatu a makaranta har tagama tashiga makarantar horan Malamai na N.c.e, yau da gobe har Allah ya haɗasu Mahaifinki cikin kankani lokaci, akayi bikinsu, ashe rabonkine ya kaita gidanku inda Allah ya haɗata da kishiya tagari inda suka zauna zama na amana,har tahaifeki ko saninki batayi ba Allah ya amshi rayuwarta, kunji labarin mahaifiyarku....."


Juyawa nayi narungume Aunty Neenah ina kuka, itama kuka take sosai sabida kaunar mahaifiyarmu, nan muka ɗinke kaman mun jima da sanin juna har muka gama kwanakinmu, muna waya da Asad kullum shi ke tuna min da yau saura kwana kaza.....
Yanzun Labarina zai fara daga kwanakin da suka rage min na farin cikin da zan riski mijina abin alfaharina, kunshe yake da farin ciki da bakin ciki sanan kuka da kaɗaici Allah sarki idan na tuna nakanji kaman zuciyata zata buga a wannan kwanakin nayi maraicin uwa dan da tana nan da nasamu nutsuwa fiye da kima, bayan dawowarmu inda biki ya rage saura kwanaki, Kayan events ya kawo min Ranar litinin dan lahadi da dadare muka shigo, koda yazo kaman ya cinyeni, badan nayi masa jan ido ba da babu abinda zai hana faruwan wani abu, duk da amota muke, a kofar gidanmu janyoni jikinshi yayi yana sunsunar gashin kaina, a hankali ya tusa hannunshi cikin rigana buge hannun nayi na buɗe motar da niyyar futa daga cikin motar rike hannuna yayi yana murzawa yace.
"Kiyi hakuri wallahi bansan meke jan hankalina ba ba amma bazan sake ba."


Shikenan nace masa inda nacigaba da hiran bikin har ys tafi.


.... Talata aka fara da brideshow wanda ya samu hallarta kawayena na schl kota kan ramla ban biba balle nasamu matsala nida Neenah nimeta hidimarmu sai Naja'atu yar Kawu ubale, gaskiya abin yayi kyau.


Ranar Laraba abokanshi suka shirya mana eng'ment wannan ba aikin kowa bane sai na Irfan me Dalla, inda yazo mana da zubuna guda biyu, Na Asad azurfa nawa whiter gold me dutse lu'ulu'u, shigan ranar kawaye sanye suke da kaya golder da Pink, ni kuma da asalin peach colour me ratsin silver, doguwar riga, me wani mayafi a baya, takalmin ma, haka yake har pose ɗina, shi kuma ango da abokanshi, sanye suke da Suit baki, yayinda akayi gyaran gurin bukin da kome pinky golder,and black, bayan munzo aka gabatar min da abokanshi dashi wanda ya haɗa shagalin, sannan aka bamu damar fita muyi musayan zubuna, a garin tashi saura kadan na faɗi tareni yayi sannan ya durkusa ya gyara min, rigana da na taka sannan ya rike hannuna muka fita filin, anan aka miko mana zubunan nice na fara saka sannan ya saka min a madadin munyi aladar bature na sumbata sai aka miko mana, juice a glass cup, muka shayar da junanmu, sannan aka saka mana cool blue music muka shiga rawa ahankali kaman yanda sautin ke tashi,


Kankace me an ɗauki hotunanmu da vidio an ɗaura a social media, bamu tashia gurin ba sai karfe goma saura muka koma gida.


Ranar Alhamis kamu mugun Rana wanda ya ruguza min kome na farin cikina ya sani zubda kwalla babu adadi......Ku canks me zai faru💋👌😂


.....Inji india suka ce Khabi khushi khabi gham♥


Plss nd Plss share nd view your comments👌
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }





🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳







*Na:Real MaiDambu*



Suhaimah M Bello tare da Aunty Aisha da Shatu kune yan Team ɗin Malam Usee ko😹 ni dai ina team ɗin Asad...Ai comments ɗinku na daban ne,....


*:~7*


Tun safen ranar na tashi jikina a sanyayye ji nake kaman zan rasa kome na rayuwata, san hankalina baya jikina, ɗan abunda bai kai nakuka ba, toh ni a gurina nakukane, haka da Innaji ta gani, ba karamin tashin hankali tashiga ba, da ita da sauran yayuna, dukda kamun ankama mana wani hallne me masifar kyau, inda aka shirya kayan gurin da kome, dark green nd golde, nice me kaya dark green me ratsin golder, sai ya zamana kawayena kayanasun lemon green da head ɗinsu golder, tunda safe me makeup tazo daga Abuja Mamani, ta gayyatota inda tazo ta shirya ni, koda ake min kwalliya sai da yakirani muka zauna munata hira, tare da alkawari zamu zauna tare har abada, karfe huɗu aka shiga fita, inda nake danne faɗuwar gaban danake ji haɗi da tsoro, har motarshi ya iso, baby da ramla basu idarda shiryawa ba dan haka, wasu daga cikin kawayen suka fito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login