Showing 12001 words to 15000 words out of 108136 words

Chapter 5 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt

08 Nov 2024

17198

nonon da kabani nasha ba, banza ɗan iska irinka kai wani irin.Abune bakayiwa Raliya ba har mata ka kawo mata gadon aurenta sai ni da nace na fasa auren Yar gwal shine har da tsine min albarka banza zan fita a motar dan Ub.. shege matsiyaci banza sai me Abba nazata iya tsine min zaka toh sai me."


"Toh kaji nazata kun daina wannan rashin hankali ashe har yanzun baku girma ba Irfan har da kai haka mi kika ɗauki rayuwane da baku ɗauki kanku da mutunci ba,.."


"Toh babban Malami Jalal kace yau wa'azinka akanmu zai tashi malam zaka mana shirune karka kuskura kasaka baki a wnn maganar ina ce nan Daddy Ya aura maka Ameerah amma sabida mugun gidadancinka sai da yar mutane ta kamu da hawan jini shine zaka buɗe baki kace zaka mana faɗa, Irfan ji min wannan garan." inji Asad.


"Banza munafiki zaka sauke hular fuskarkane ko sai na lailayo gundumemiyar Ashariya ns banks maka ɗan iska gwara da bakayi magana ba ince nan Papa ya aura maka Sayida karinga cutar yar mutane kana ɗirka mata ciki sai ya fito kace azubar baka shirya haihuwa yanzun ba kowannenku ina da tabonku sai kun tara yara ma zanzo nabasu labarin irin wainar da kuka toya banzaye jakuna."


Aikuwa take Asawad ya fusta sukayita abin kunya karshe sai da aka kirasu dan lokaci natafiya, gida suka koma Asad ya sauya kaya, shi da Irfan kunsan wannan ɗabi'arsu ce ta faɗa lokci ɗaya kuma acikin su Huɗun nan duk wanda yayi yunkurin bada hakuri sai ahucce akanshi tun daga sankandiri suka haɗu har zuwa jami'a, basu rabu ba sai ma dasuka gama aiki ya rabasu amma duk shekara suna kokarin haɗuwa a gidanjen junansu, kuma suke awarware masalahar data taso cikin junarsu kuma sai adace dake sunsha fama da rayuwa a cikinsu Jalal ne yw tashi da iyayenshi duk biyu, Asad ya tashi a hannun matan uba hsr biu kuma sun bashi wahala kafin Abbanshi ya auro Fatima hannuntq yaji daɗin matar uba,


Haka ma Irfan ya karamin wahala yasha ba da Iyabo bayerabiya babanshi ya auro inda tayi sanadin barin Ummanshi gidan tayita gana masa azaba har ya kawo kai nan kuma yace bai iya ji ba, dan dagske ya kwaci kanshi dan babanshi har koranshi yayi a gidanshi.


Sai Asawad labarinshi ɗauke yake da ban tausayi dan shi mahaifiyarshi har haukatata kishiya tayi shima sai da wan babanshi ya karɓashi sannan yaji sanyin dan kowannensu ya tashi da ciwo aranshi.


Bayan antashi daga liyafa sai dinne, kayan da *Naiha* zata sakashi aka bawa Ramla tasaka, sai ya zamana komi ramla zatayi sai da umarnin Baby, take ranta ya fara ɓaci...


Tukun nan inji me mugun labari👌






[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }





🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳







*Na:Real MaiDambu*


*:~10*
Shiryawa tayi cikin sauri dan har lokaci ya fara tafiya, inda baby takirata ta waya take faɗa mata abinda zatayi kashe wayar tayi ta shirya abunta koda aka fito da ita daga abba har Innaji babu wanda yayi mata faɗa haka, aka ɗauketa zuwa gidan Asad, a dai dai lokacin na gama cire Asad a rayuwata, asalima ko tunaninshi banayi.


Tunanin gobe nake, baxance bani da damuwa amma nasan nisa da gida danayi zai rage min damuwa, sosai.


.....Ankai Amarya gidanta dake g.r.a daga can suka ɗinguma zuwa dinner,


A gidan Imam kuwa matarsa Zahira ce ba lafiya cikin tashin hankali suka kwasheta zuwa asibiti, inda aka ɗaura mata ruwa, shine ya zauna a gurinta da Janeesha ba zama zatayi ba,


****
A gurin dinne baby tayi kokarin shigewa jikin Ramla take ta muna mata ita bata santa ba ba asalima kar abarta takaraso gurinsu, ta faɗawa Asad shi kuwa ya faɗawa Asawad tuni aka faɗawa jami'an tsaron gurin aka fitar da baby kaman kayan wanki.



Koda aka fita da ita hannun ta ɗaura akai ta fasa ihu tare da kurari ni zaki ciwa amana na ɗaukoki inuwa ki azani rana, baki isa ba,


Haka tayi ta sumbatu har lokacin tashi yayi aka fito bata samu ganin Ramla ba,


Daga dinne gida ya wucce da ita, ya kaita har ciki, falonshi da yake cikin gidan ya kaita suka zuɓe a jikin kujeran falon cire mata ɗankalin yayi sannan ya janyota jikinshi yayi cikin wani irin yanayi ya shiga isar da sakonshi da yatanada min yau gashi yana sauke a kan wata bani ba, ajiyar zuciya ya sauke kafin yacigaba da abinda yake a hankali suka hautsina juna cikin wani irin yanayi, bugun kofar falon ya dawo dasu duniyar da suke, dakyar ya mike ya gyara babbar rigarshi.Yafita buɗe kofar yayi yaga mamani hararashi tayi cikin ɓacinrai tace.
"Toh mara kunya kajira ayi buɗan kai sai kucinye juna" raɓashi tayi tashige ciki, ganin yanda Ramla tayi tsamo-tsamo yasa Mamani sake tsuke fuska tace.
"Zoki wucce maza mara kunya ko kunya baki ji kinzo kin sake ji zaki mika masa kanki c'ommon muje."


Simi-simi tafito, daga ɗakin kanta asunkuye,har inda kawayenta suke Mamani takaita ba karamin haushin mamani taji ba a ranta take aiyana abinda zatawa Mamani,


A bangaren Baby kuwa sai da tayi kuka san ranta kafin tafito daga wajen taron da kafa har gidansu, kowa na bacci cikin salama amma banda Baby tuna irin abinda zataiwa Ramla.


****
A gidan Malam kuwa Matarsa Zahira ce ba lafiya sosai a cikin dare suka ɗauketa zuwa asibiti, inda akaita kaiwa da komowa, kafin Asuba Allah ya amshi rayuwarta, cikin tashin hankali malam ya shiga ɗakin yana kallon fuskarta, wanda ya kasance zufa na tsatsafu mata, isa kan gawanta yayi cikin zubda kwalla yake shafa fuskarta, addu'a yake son mata amma bakinshi yayi nauyi, kwalla sosai yake zuba daga idanunshi dakyar ya haɗiye kuka yayi mata addu'a sannan yayi magana da nurse ɗin suka bashi takardu ya cika sannan ya fita da gawar, aka saka a motar ɗaukar gawa, yaja motarshi suka biyoshi har gida a falonshi aka sakata,


Suna fita ya shiga ɗakin Janeesha ya buga mata dakyar ta fito, fuskarta a yatsine tace.
"Ya jikinta dai?"


Ta wurga masa tambaya cikin ko inkula, murmushi yayi sannan yace.
"Ta warke ga tacan a falo kizo ki ganta."


Atakaice tace masa.
"Toh kaje tunda tana falonta ko zuwa gobe zan fito ni gaskiya bacci nake ji, kayi mata sannu da jiki."


Tana faɗin haka ta juya ta rufe kofarta cikin jin haushi akan me zai tadda ita tunda matarshi ta warke daman ciwon karyane anyi haka ne dan a hanata baccine kuma bazata fita ba sai gari ya waye,


Komawa falo yayi cike da takaici yana nazarin halayen matanshi dama Zahira tafi sauki al'amura toh taya zai haɗasu ma matar da yaranta ma basu dameta ba, balle wasu.Miqewa yayi ya faɗa banɗaki ya haɗa duk abinda ake bukata na wankar gawa yazo yayiwa matarshi dama shi yafi dacewa yayi mata, shi ya haɗa tsaf sannan ya koma banɗaki yayi wanka da alola ya sake kayanshi fitowa yayi da abin sallah ya tadda nafilla, bashi ya tsaya ba sai da aka kira asalatu, sai lokacin ya kira mutane yobe ya faɗa musu ai Zahira ta rasu,


Gidansu Zahira yakira mahaifinta ya faɗa masa, nan suka rokeshi da a dakatar da sallar gawarta zuwa goma nasafe,


Daga gidan Iyayenshi har gidansu Zahira suna idar da sallar asuba suka ɗauko hanya.


Bai samu bin sallar asuba a jam'i ba, masu zuwa karatune suka fara taruwa nan ya fito ya faɗa musu ai matarshi ta rasu, ta'aziya suka masa sannan suka tambayeshi yaushe za'a jana'izarta. Cikin karfin hali yace musu.
"Ƴan uwana da Mahaifinta suna hanya shi yasa suka nimi a ɗaga jana'izar zuwa goma."


Jinjina al'amarin sukayi sannan masu zuwa aiki suka tafi, wasu kuma suka zauna zuwa goma suma masu zuwa aikin goma nayi zasu dawo a sallaceta dasu.


****
Karfe goma saura kwata Abba lawan ya isa shida iyalanshi baki ɗaya, goma dai dai mutane yobe suka iso, ba'a ɓata lokaci ba wajen gudanar da salla ba aka sallaceta inda aka mikata gidanta na gaskiya.


Duk wannan bidirin da ake Janeesha tana kwance, khalil ya tashi amma sabida tsoron jibgan uwarsa yasa yaki fitowa, gashi duk yaɓata jikinshi da fitsari, sai Ummi yar karamar yarta itama duk tadama jikinta da kashi, amma dake uwarsu ballagaza ce tana kwance tana baccin asara,


Matar Abba lawance ta buga kofar ɗakin da karfi a firgice ta farko domin tana cikin mafarkine ga Zahira ana sakata a cikin rami, kuma tana jin muryanta tana mata gargaɗi, akan takula da rayuwarta da mijinta, kartayi wasa da damarta ta rasa shi, tana ji tana gani. Har aka rufe zahira da kasa, bata daina jin amon muryanta ba duk ta haɗa zufa,


Jin karan buga kofar yasa tayi karamin tsaki tace.
"Wai nikan banace zanzo na dubata ba ai aikin lada ba'awa mutum dole dan kana mallam kuma sai kowa ya koma mallamin."


Mamakine ya rufe kaltuma cikin ɓacin rai tace.
"Toh uwar marasa mutunci buɗe min kofa, wai yaushe zakiyi hankalinkanki hmm."


Jikinta narawa ta sauko ta buɗe kofar,danna kanta da kaltuma zatayi zarnin fitsari da warin kashi yasa ta dakata tayi mata kallon raini sannan tace.
"Maza ki kintsa ɗakinki kafinsu Umma su iso mara mutunci ake har zahira ta rasu amma kike kwance sabida mutane su tafi dake kina farin ciki kishiyarki ta mutu ko? Wallahi kin zubda mutuncinki a idanun Imamu bazai taɓa ganinki da kima ba, kinrasa shi kenan, tunda wannan halin kika tsiro masa."


Tass ta wanketa sannan ta juya tabarta cikin kuka dake bata da kunya cewa tayi.
"Miye laifina tunda kwanantane ya kare, koda ina tare da ita ai babu abinda zan iya mata, yanzun anzo ana ganin laifina, dan kawai banje na zauna ta mutu a gabana ba,"


Cike da jin haushin kowa har da ita mamaciyar Janeesha take aikin gyara ɗakinta, inda take sauke rabin haushinta akan Khalil da ummi.


A makabarta kuwa, ana saka gawar Zahira malam ya zube kasa sumanme,




*Tim up* karku manta da ɗaga darajar nan wajen dannan ɗan karamin tauraro nan.....vote..
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }




🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳








*Na:Real MaiDambu*


_Aunty Aisha, Mom Ahmad, Mom Sayeed da Hafsat shehu, tare da maɓalin zuciyata My Zahra ga sadaukarwarku nan_👌👌👌


*Page 11*


Fita da shi akayi daga cikin makabarta, bai masan inda kanshi yake ba, ana gama sakata a gidanta na gaskiya, mutane suka tsaya aka mata addu'a sannan suka fito zuwa gurin da aka ajiye motoccinsu, ba laifi ya dawo hayacinsa amma idanunshi bai daina zubda kwalla ba, har suka dawo gida, ɗakinshi aka shige dashi inda yayi ta kuka kaman yaro karami, har sai da Ummanshi ta shiga ɗakin yana cikin bargo yana rawan ɗari.


Zama tayi a bedside ta ɗan ja bargon cikin sanyi murya tace.
"Imamu gatan gawa, yau kaine kake wannan irin kukan bayan kai kake hana wasu yin haka, haba zunnuraini, hm haske biyu yau kaine kake zubda hawayenka tabbas mutuwar mace irin Zahira da zafi amma bata cancanci kuka daga gareka ba, addu'a takw bukata kaji Baba malam ɗina, tashi maxa kasha magani, kaji Allah zai maida maka da wacce tafita, ka zamanto mai juriya da hakuri, Allah yana sane dakai."


Cikin hikima da nasiha irinrta uwa, ai kuma tsakanin ɗa da uwa, sai Allah da haka ta samu kanshi.


Har yasha tea da magani yafito falo, lokacin Abbanmu yazo masa gaisuwa tare da yaya ishak,


A bangaren Jameesha fushi take tsakaninta da Allah akan me za'a takura mata, da faɗa gani take ai koda Zahira ta mutu ai ba ita takasheta ba, shi yasa taketa ta cika tana batsewa.


A cikin ranta kuwa cewa take humm Ya imamu zai zo yasame ni dani yake zance ai yafi kowa marairaicewa idan dare yayi nima zanyi maganinshi.


****
A ɓangarensu gidan biki kuwa yau za'ayi buɗan kai dan haka kan Ramla yafi nakowa rawa, dan ji take ta kusan kama Asad a hannun, ita kuwa mamani wani irin bakin cikine yake rufeta idan tayi arba da Ramla bawai dan ramla bata da kyau ko wni abu bane sai dan ƴanda lokaci guda ta birkita mata yaronta shine abinda yake bawa Mamani haushi, gurin guda aka shirya buɗar kai, kafin su fitane mamani takawo wasu daga cikin yan uwanta, da suka zo bikin har inda ramla take ta nunata,


Cikin ladabi ta gaidasu suma suka karɓeta, dan kar su gane Mamani tayita wasata a gabansu har suka fita bayan fitarsune, wata kawar ramla ta kalle sannan tace.
"Ramluv kinyi dace fa, domin mother-inlaw ɗinki tana masifar ji dake,"


Karamin tsaki tayi sannan tace.
"Wallahi bata kaunata, babu yanda ta iya danine, amma bataki ɗanta yace ya sake ni ba, ni bansa mi natsare mata ba,"


Gyara zama kawar tayi sannan tace.
"Zan baki shawara shine ki mike tsaye domin waje zatayi dake, irinsu haka suke kishi da matar ɗansu."


Kasa da murya Ramla tayi sannan tace.
" Hmm kedai bari bani da hanys ne amma ko ynx nasamu ba zanki ba."


Muskutawa kawar tayi cikin jin daɗi tasami abokiyar ɓata tace.
"Zan miki hanya amma naji dumus, kafin alkalami ayi masu faraku, shi da uwar ko a hanya ya ganta sai yasake hanya,"


Buɗe jakarta tayi ta ɗibo kuɗi, masu yawa ta mika mata har tasa hannun zata amsa taja kuɗin baya cikin munafikin murmushi tace.
"Zan iya baki yardata amma banda kimata kikayi min wasa da hankali mmmm.Basai nafa miki sauran ba."


Miqa mata kuɗin tayi sannan tacigaba da abinda take, dake yarinyar tana da tsoro take ta mike, tafita har jikinta na rawa tacewa ramla.
"Bari naje na dawo."


Fita tayi, daga gidan baki ɗaya.


......
Can wani kauye taje gurin wani bamaguje ta faɗa masa abinda Ramla take bukata, shi kuwa ba tare da ɓata lokaci ba ya buga kasa sai ga wasu kwayaye guda biyu yace.
"Gashi akai mata, tsakaninshi da Uwarshi har abada kaman yanda k'oyin nan ba zai iya fafe kanshi ba haka babu shi babu da uwarshi. Amma da sharaɗi."


Zama yarinyar tayi ta zuba masa idanun sannan tace.
"Wani sharaɗi kenan boka."


Dariya yayi sannan yace.
"Karta kuskura tabarshi yayi ido biyu da Yarinyar da yaso aura wato yar uwanta nan, matukar suka haɗu toh kallon da zasuwa junansu shi zai lalata wannan k'oyin tsafi har ya kyankyanshe kansa, jan kunne nakenan a gareku."


Gyaɗa kai tayi cikin sanyi jiki ta mike tafita da baya, har waje anan ta ajiye masa kuɗinshi, akan wani ɗan karamin gunki. Sannan tayi tafiyarta.


Koda ta isa tasamu ana buɗan kai da aka gama aka maida amarya apartmen ɗinta ta ɗauki kayan tabata sannan ta faɗa mata yanda zata ajiye abun wani irin ihu tayi sannan rungume yarinyar tayi tace.


"Fasu zan baki kyauta na musaman nagode kin gama min kome yanzun zan juya kowa son raina."


Buɗe jakarta tayi ta dunbolo kuɗi me yawa tabawa fasu tace.


"Kin zama abokiyar tafiya kiyi min dai dai, kema zaki ga dai dai dani, karki saka ha'incin ni kuma zan baki mamaki a rayuwa."


Godiya sosai yarinyar tayi sannan suka ci gaba da hiran ynd zasu kuntatawa mamani, sannan zatayi kokarin yanda zatayi kar abarni na dawo katsina.


Taɓɗijam.....


****
Gidan malam kuwa karfin hali yake, kawai amma daga zuciyarshi har gangan jikinshi baya jin daɗi, sam baya ganewa kowa, kewar zahira da rashinta suke damunshi. Gashi baya kaunar ganin jameesha dan baya jin daɗin ganinta, sam badan kar akaga baikeshi ba da turata gida,


Amma yasan yayi haka kaman yasayawa kanshi kaɗaicine, shi ƴasa ya shareta,


Wajen karfe ɗaya na rana akakawo abinci daga gidanmu, manya manya kuloli, haɗi da katun na drinka,


Abin ya basu mamaki yanda aka karmasu cikin mutuntaka, take Abbanmu yasamu mazauni a cikin zuciyarsu,


Sai addu'a suke masa na jin daɗi,abin da ya kara musu haushi yanda jameesha taki buɗe musu store suyi girki sai ga abinci daga gidanmu,


Na ranar da aka kawo bai kare sai ga abincin dare wajen karfe biyar da rabi,, Kaiii yan uwan Malam sun gaza ɓoye jin daɗinsu, har sai da suka faɗa masa irin karamcin da aka musu,




Da dare yayi gidan ya cika, dan har babu gurin kwanciya, karshe dake Innaji tazo tare da Umman malam suka tawo gidanmu. Nan innaji tashinga hidima dasu har suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login