Showing 15001 words to 18000 words out of 108136 words
Chapter 6 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt
kwanta,
Abinda ya burge Innaji da yanda, Umma take karatun alkur'ani, murmushi tayi cikin farin ciki da annushuwa,
.....Washi gari tun asuba, Innaji da Yaya Ishaq suka, shiga aikin kunnun gyaɗa da kosae irin na baba me kosae, tafiya masalaci yayi inda itama innaji tashiga sallah, tana idarwa tafito bakin aikinta tana cikin dama kunnun ishaq ya shigo da kulun kosai ɗin, shi ya buga mata bayan ta gama kunun ta fara sakun kosai, tana gamawa umma tana fitowa, har gurin cikin barkwace tace.
"Hajiya shine kikayi aikin baki tashe ni ba, ai bahaka ake ba."
Cikin jin kunyar Umma tace.
"Ayya Maman malam, ai bawani aiki bane, kuma yayansu mukayi kuma mun gama."
Ruwan wanka Innaji takai mata banɗakinsu ramla dake cikin ɗakin dake anan ta kwana,
Innaji tace mata.
"Maman Malam ga ruwan wankanki a bandakin,"
Duk da saura baki a gidan haka bai innaji yin kome ba, kusan ma mutane duk sun watse, sabida faruwa al'amarin.
Suna gama haɗa abin karyawa aka ɗibi na mutane gidan sannan aka kira almajirai suka kai na gidan rasuwar,
Koda Umma tafito tsaf ta shirya sannan Innaji ta gabatar mata da abin karyawa bayan ta gama suka fita tare inda tabar sauran aikn ga mutane daura,......
****
Bayan abokai sun rako Asad, suka biya kuɗin sayan baki, da kuɗin kawance,
Sannan sukayi sallama dasu,
Sabida rawan kai dakyar suka rufe gidan, sannan suka ci abinci sama sama, daga gurin cin abinci aka buge da hidima ba'a cewa kome kawai......
Share........plsss
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }
🌹🌹
*MATAR MALAM*
🌺🌺
_Wannan shafin nakune Sister Jamila safyanu tare da Nafi Dotan Sahibata,_
*:~12*
Hmm a gurin Asad yabarje amarcinsa, sabida yanda suka ɗaukantu da juna sai muce Allah ya basu zaman lafiya toh me zance bayan haka.
****
Cikin kwana uku da akayi rasuwar babu wanda bai ji ɓacin rai da Jameesha ba, dan ido da ido tafaɗa musu ita bazata basu key ɗin store su kwashe musu abinci ba, abinda ya fusata Malam kenan yafito ya fasa kofar store ɗin yace.
"ku shiga ku ɗiba abinci, ke kuma Allah yayi wadaran halinki, amma kicigaba lokacinkine sai dai kisa aranki nima Allah zai me yaye min gurbin Zahira, hmmm ba damuwa."
Kowa yaji ɓacin rai da abinda tayi sunsan halinshi ba ma'abocin magana bane ba wai dan bayayi bane a'a shi mutum ne me baiwa kowa yancinsa, a daddafe sukayi addu'ar bakwai wanda ita kam Umma tun ranar uku ta koma, yobe, cike da kewar Innaji,.
Bayan addu'ar bakwai iyayen zahira suka nemi kwashe kayanta dakyar ya amince aka ɗibi wasu sauran yace a bar masa, gaskiya sukansu sunsan yana cikin damuwa da kaɗaici aka suka tafi suka bar gidan, abinda ke ɗebe masa kewa yaranshi da kuma karatun da yakewa mutane a waje amma zaman gidanshi babu daɗi, ji yake kaman yana cikin wuta dalilin da yasa kenan ya shiga niman gurbin karo ilimi a kasar birtaniya ba tare da sanin kowa ba.
****
Hmmm rayuwata a kasar nijar ba laifi ina cikin kwanciyar hankali amma idan na tuna kome sai naji na tsani kaina har kuka nake, idan natuna irin burin da muka ɗauka nida Asad sai naji ko ina yayi min zafi, dana ga zaman gida ya ishani kawai sai na shiga niman inda zan fara karatu koda irin na computer nan ne, cikin ikon Allah nasamu, amma matsalar da yaren frence ne, amma haka na hakura nafara, inda kawu Uballe shi ya ɗauki nauyin kome Baban Neenah kuwa yabada mota kullum ana kaini ana ɗaukoni, a nan nasami raguwan damuwata sai dai nakoma shiru shiru wacce kome kashin abu sani kuka yake,
Sam abinda bani dashi da ya zomin cikin rayuwata wato miskilanci, sam banji kome idan zan zauna na awa hudu ban tankawa kowa ba, haka yafi min kome a rayuwata ga tulin kawaye da nayi, amma haka bai ɗaga ni yananani da kasa ba, dan bana son shiga damuwar kowa, kawata ɗaya ce yar uwata, da ita nake kome haka yafi min daɗi.
Wani sabon malami da aka kawo mana ne ya fara sani a gaba, tunda ya lura ban iya fransanci ba take yasaka min ido, inda ya shiga muzantani a gaban mutane, ban taɓa jin kome ba dan yanzun bana jin akwai abinda wani zai min ya ɓata min rai abu ɗaya kawai nasani shine idan yazo yana min haka kuka nakeyi, har ya fita,
Neenah nafaɗawa halin da nake ciki, tabani hakuri bata ce min zata faɗawa Babanta ba sai washi gari muna cikin class sai babanta yazo har ofishin shugaban makaranta yayiwa shugaban makaranta barazana da zaisa arufe makarantar tunda malaminsu yana tozartani, sanin kowaye shi tasa duk suka shiga bashi hakuri, bayan tafiyarshi shugaban mkrnt yasa aka kira masa malamin yayi masa faɗa,
Toh tun daga ranar nasami yancina, toh daman ba rigima nake da kowa ba balle ace ga dalili kuma ina maida hankalina sosai akaratun da nake.
****
Kusan watanin shida da ya tura sakonsa na niman gurbin karatu a Livepool, sai jiya da dare suka turo masa sakon sun bashi daman doctorin yake nima afanin law, kuma suka ɗaukeshi, cikin farin ciki ya tafi yobe ya, bayan isha ya sauka a gidansu, inda ya zube a falon Ummansa cikin gajiya ya gaisheta, amsawa tayi cikin farin ciki da jin daɗi, inda ta tura masa kayan abinci, sosai yaci bayan ya gama yake labarta mata, gurbin karatun ɗa yasamu addu'a ta masa, sannan tace.
"Amma da jameesha zaka tafi ai."
Eh ya ansa ba dan yaso ba, sai dan yanda tashiga maganar, hira sukayi sannan ya shige part ɗinshi.
***
Duniya tayiwa Ramla ɓarin gyaɗa sai morewa take, inda suka cigaba da zabgawa Asad sihiri, duk ya sussuce baya cikin hankalinshi, ta koma tankar hand bag gashi ya manta da kowa da kome, ramla ce kawai a gabanshi,
Hankalin Mamani inyayi dubu ya tashi, sakamakon haka har jininta sai da ya hau, sabida tashin hankali.
Akwai lokacin dataxo gidan Ramla tahana Asad fitowa, yana gaida mamani, duk yanda taso taganshi amma fir taki, cikin kuka tabar gidan tarasa inda zata tsuma ranta kawai sai tayo giɗanmu, gurin Innaji, tafaɗa mata halin da take ciki, ba karamkin kaɗuwa innaji tayi ba, bata bar maganar ba suka koma gidan koda suka zo shiga fir aka hanasu shiga, Innaji tace.
"Kacewa matar gidan Innaju ce tazo."
Kiran Ramla yayi a waya ya faɗa mata, amma tace.
"Kace koma waye yayi hakuri"
Wannan abu taɗaga hankalin.Innaji ba kaɗan ba jikinsu a sanyayye suka bar gidan tun daga ranar Innaji ta yafe Ramla, kuma bata gushe ba kullum sai tayi mata addu'ar Allah ya lalata auren, sabida ta shiga tsakanin ɗa da uwa.
Shi kuwa Asad ko office idan yaje matukar aka masa wani abu toh sai yazo ya faɗa mata, Mamani bata hakura ba tabiyo shi har gurin aiki, abin takaici kiran Ramla yayi a qata ya gaya mata ga mamani nan tazo.
Afusace tazo har ofishin tana isowa ta kama hannunshi zasu bar office din ran mamani ya ɓace cikin kuka tace.
"Sai kinyi mutuwar wulakanci, kare sai yafiki daraja a cikin alumma, hawayen da nazubda sai sun zame miki bala'i da masifa kije nabarki da hakkin shiga tsakani ma."
Tana gama faɗin haka ta juya tabar garin baki ɗaya,
Inda takira Irfan ta faɗa masa, cikin tashin hankali ya faɗawa sauran abokansa,
Suka tsayisa shawaran a haduwa a zaria.
*****
Kwanar malam ɗaya ya dawo inda yashiga niman visa, matarshi da yaranshi.......
Kuyi hakuri Insha Allah goɓe akai more......
Pls Share.....😂
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }
🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳
*Na:Real Mai Dambu Ce*
*:•~13*
Karfin hali kawai yake amma sam a zuciyarshi baya kaunar tafiyarshi da Jameesha, itakanta bata san da, tafiyar ba har sai da Yayarta takirata, take tayata murna sai anan tasan da batun , farin cikin da tashiga bana wasa ba, yayinda tashiga hango kanta a kasan london,
Acikin abinda bai kai sati uku ba ya kammala musu visa. Sannan ya shiga gidanmu ya faɗawa babanmu tafiyarsa, sun jima suna tattaunawa kafin yayi masa sallama.
Ranar alhamis suka bar garin katsina zuwa abuja kwanansu ɗaya suka bar kasan baki ɗaya.
****
A garin zaria kuwa dukkansu uku sun haɗu cikin jimami da jajantawa mamani, Jalal yace.
"Mamani ki kwantar da hankalinki insha Allah kome zai dai-daita babu abinda yafi karfin Allah,qoqarin kwantar mata da sukayi sannan sukayi mata sallama.
Gaskiya faɗan halin da mamani take ciki kaman wasting time ne, kuyi tunani akan tsakanin ɗa da uwa, amma haka ramla ta rabasu takai har kowa nashi ya manta,
Ganin halin dasu jalal suka bar mamani yasa suka yanke shawaran zuwa katsina,
Sai dare suka isa a wani gidan masaukin baki suka yada zango washi gari suka dira a ofishin asad. Zuwa aka ce musu ai rabonshi da yazo aiki kusan wata biyu kenan, abin ba karamin kaɗasu yayi ba dan haka basuyi kasa agwiwa ba suka tawo gidanshi dake gateman ɗin ya musu farin sani bai kira ramla ys faɗa mata ba, kai tsayi suka shiga gidan,
Basu damu da niman iso ba suka danna kansu falon da sallama, babu wanda ya amsa musu, sai hangoshi sukayi a rakuɓe kaman maraya, duk ya takure a gefen kujeran da take zaune, ɗago kanshi yayi ya kalleta kaman me shirin fashewa da kuka, ya marairaice fuska, yana kallonta, tsaki tayi sannan ta juya ta kallesu Irfan cikin tsiwa tace.
"Da izin wakuka danno min gida waya kiraku, ko anzo asaka mana ido ko,,,"
Juyawa tayi ta kalle Asad tace.
"Kace sufita bana son ganinsu indai baso kake cikin jikina ya zuɓe ba."
Yanda tayi maganar ko rufe bakinta batayi ba ya mike yace.
"Pls kufita bata son ganinku, don Allah"
Niman ɗaya daga cikn kujeran falon Irfan yayi ya zauna cikin isa da gadara yace.
"Inga ubanda ya isa fidani a gidan nan sai na fasa kanshi da harshashin gun ɗina,kuma kowa na kashe ba wani abu bane a gurina dan ina da lasisin taɓin hankali."
Zaro idanun waje ramla tayi miqewa tayi tabar falon, cike da tsoron Irfan.
Juyawa yayi kan Asad wanda yake da niyyar bin bayanta, harara ya galla masa cikin bala'i yace.
"Me yake damunka Asad wani irin rayuwa kajefa kanka sabida kai Mahaifiyarka tana cikin wani irin hali sabida kai, anya zaka ga haske a alamarinka kuwa, wallahi kasake lale, wallahi kana cikin masifa bayyana nanniya, ina jiye maka tsoron fushin Allah."
Yanda ya sunkuyar da kanshi zaka ɗauka abinda suke faɗane yashiga jikinshi amma ina yana shiga takunnen dama yana fita takunne hagu,
......A ɗakin ramla kasa zaune tayi sai sintiri take, dataga babu mafita sai takira Fasu tafaɗa mata abinda takeso sannan tatura mata kuɗi wato mobil bank,
Koda fasu ta isa gidan bokan ta fada masa abinda yake faru take ya turawa Asad aljani, sannan ya ɗauki wani tulu ya mika mata yace.
"Wannan hawainiyar tsafice tasaka a inda baza'a gani ba, idan wani daga cikin yan uwanshi suka zo tabuɗe bakin tulun hawainiyar zata fita, taje ta shige jikinshi zata sakashi aikata kome, cikin dakika sittin."
Shima makarinsa karta kuskura tabari ya haɗu da wancan yarinyar inba haka ba, kome zai dawo kanta."
"Toh" tace, sannan tafita daga bukkan cikin rawan jiki.
....Koda Irfan yayi gama masa faɗa ya ɗago kanshi ya fara magana da cewa.
"Ina ganin haka na zabawa kaina tunda haka ne, kuwa bana bukatar ganin kowanneku, kufita min a gida kafin na durza muku wulakanci kufitan min a gida nace."
Ya daka musu tsawa cike da mamaki suke kallonshi, tabbas wannan ba Asad ɗinsu bane, wanda suka sani baya haka, jikinsu a sanyayye ransu a ɓace suka fita a gidan.
Tare da alkawarin zasu shiga au fita su ceto abokinsu.
Bayan fitarsu kadan fasu tashigo gidan inda tabawa Ramla sakonta ita kuma ta dinbulo kuɗi tabata,sannan ta sallameta.
_(Idan wasu suka samu duniya mantawa suke da lahiransu.)_
****
A tsatsaye Innaji tafara rashin lafiya wanda sai da ya kwantar da ita, duk yanda taso ɓoye damuwarta haka bai hana ciwon kada ita ba, abu kaman wasa, da asuba ta tashi sallah tayanki jiki ta faɗi, a cikin banɗaki babu wanda yasani, sai da suka dawo daga sallah Abba ya shiga ɗakin yajita shiru shine ya kutsa banɗaki anan yasameta a yashe, da sauri ya kira ya Ishaq suka ɗauketa sai Asibiti, cikin gaggawa aka amsheta,, inda suka shiga bata taimakon gaggawa.
Ishaq ne yakira kannenshi ya faɗa musu halin da mahaifiyarsu take ciki, amma bai samu layin ramla ba, Har sai da yaje gidan dakyar aka barshi ya shiga suna bacci basu tashi ba, bugun da yake yasa ta tashi, tafito ranta a ɓace, tana buɗe kofar taga Ishaq, daga bakin kofar yace.
"Idan kin gadama Innaji tana asibiti ba lafiya."
Yana faɗin haka ya juya yabar gidan yana tur da halinta, ko ɗar bata ji ba, asalima ita mamakin yanda Y'an uwanta suke mata hassada take, kwafa tayi cikin jin haushinsu. A hankali tace.
"Idan ana zuwa dole basai akaini ba."
Komawa tayi ciki takwanta abunta tacigaba da baccinta har zuwa sha ɗaya saura, sai a lokacin wani ɓangare na zuciyarta ya gargaɗeta da ta tashi taje kafin asamu abin faɗa akanta, shine dalilin shiryawanta.
***
*Baby* duniyar tayi mata atishawan tsaki domin kome ya lalace ma, takai zaman gidansu nason fin karfinta, haka ma fita waje domin wani irin bakin jini tayi,idan ta zauna surutu take ita kaɗai tana tona kanta da abinda tayiwa mutane musaman ma ni, dalilin da yasa mutane suka fara tsanarta kenan.
****
*United Kingdom*
A jahar Livepool, duk da lokacin sanyine bashi ya hana mazauna garin fita hada-hadarsu na yau da kullum daga cikinsu kuwa har da Imamu, sanye yake da wata katuwar jacket me hula, da gashin zaki, rike hannunshi yake da Khalil, da kuma Ummi zai kaisu makaranta sannan ya wucce nashi makarantar, amma kafin ya wucce sai ya biya dasu gidan abinci, suci yayi musu pack ɗin wani a lunch box, abin tausayi yara da uwarsu tunda suka diro london ta fita sha'anin Uba da yaran, idan yana gida kulewa take a ɗaki taki kome, sai shine zai mata shi kuma baya son yawan magana shi yasa yake zuba mata idanun tunda hakkinshi ma kin bashi take, sai ya maida kanshi kullum yana azumi, ya cigaba da zuba masa idanun.
Wani gidan cin abinci ya tsaya yasaya musu noodle da chips sannan ya zauna suka ci, ya ɗaukesu sai zuwa makaranta, yana ajiyesu ya wucce nashi.
Tun zuwanshi makarantar akwai mata yar lebanon da take shige masa, amma haka yake mata fuskarsa ya wucceta, yau sun gama karatu da wuri, sai ga hukumar shara'a takasar ta turo wasu daga cikin mutanenta suzo su nima musu, wanda yake da kwarewa afanin shara'a yazo yataya alkali aiki, abin mamaki a cikin yan kwanakin da yayi har mutane sunyi bincike akanshi, kowa yana niman irin wannan alfarman sai gashi ya faɗa kanshi, abin yazo masa bazata, dan haka suka tafi tare, inda aka fara shari'a alkali ya nime shawaranshi aikuwa ya bada abinda ya dace take hukuncin yayiwa kowa daɗi, kuma suka gamsu da hukuncin, har suka nime yayi aiki dasu zasu biyashi albashi me kyau.
Koda ya dawo gida, ya samu yaranshi abakin kofa alamun uwarsu tafita, kenan buɗe musu kofar yayi ya shige ciki ya fara nima musu abinda zasu ci sannan yashiga ɗakinshi. Ranshi a ɓace, ya rasa yanda zaiyi da Jameesha,
Har ya gama abinda zaiyi bata dawo ba sai can gata sanye da riga da wando, sai jacket tayi roll kanta da yar mayafi, kallo ɗaya yayi mata ya kauda kanshi dafa gareta, wuccewa ɗaki tayi abinta suma yaran sun saba da halinta,
Can bayan wani lokaci ya tashi ya bita ɗakinta fitowa tayi ɗaure da towel, alamun wanka tafito hannunta rike da wani tana goge kanta, ganinshi da tayi sai da ta razana, shima kallon tuhuma yayi mata, juya kanta tayi ta kalle kusurwan gado(wato sider bed) shima gurin yakalla adugar mata,ya gani a hankali ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya kalleta cikin sanyi murya yace.
"Haka da kika zaɓa mana yayi miki, ko kin manta da hakkinmu nida yarana."
Cikin takaici ta kalleshi ganin irin shigan da yayi wato half janfane da wandonshi, sai takaici ya rufeta taki sake kallonshi, ciki ciki tace.
"Baxan iya wannan kauyanci ba, mutum an haifeshi a cikin city sai kace wanda aka haifeshi a cikin kauyen kayau."
Miqewa yayi yabar ɗakin tabi bayanshi da tsaki.
Wannan mugun halin da tatsiro tun shigowansu takewa Imamu kallon wanda bai san me ake kira da wayewa ba, gani take masa bai san rayuwa ba, kaman yanda mazan turawa da sauran mutanen garin suke tsukewa cikin riga da wando, caras shi yakw rura mata tsanarshi tunda har yaranshi ya hana tasa musu tsukekken kayan, kuma idan tayi shigar da bai masa ba, ya buɗe mata wuta ya hanata fitowa dan karta lalata masa yara, dalilin da yasa tabar masa yaran kenan,
***
Asibiti kuwa duk