Showing 1 words to 3000 words out of 84595 words
https://www.facebook.com/profile.php?id=61567646455725
🌹RAYUWATA🌹
Story and writing
*Bilkeesu Sa'eed Aliyu Ikara*
💞*Billy pinky*💞
☀ NAZARI WRITER'S ASSOCIATION ☀
▪GARGAD'I !!! 📢
Ban yarda wani ko wata su sauyamin labari na Dan wannan littafin Mallakar marubuciya Ne dan haka be careful.
Wannan littafin nawa k'agyaggen labarine banyishi dan cin zarafin ki/ka inkinga yayi daidai da rayuwar ki/ka to alk'alamine🖊yazo da salonsa idan kuma kunci Karo da kuskure aciki kumin afuwa dan wannan shine littafina na farko dana fara wallafawa dan haka ba za'a rasa samun wasu kurakuren ba .
▪GUNDARIN LABARIN : ya kushin abubuwa da dama kamar :
*Fadakarwa* 📢
*Nishadi* 💓
*Ilimantarwa*👌
*Tausayi* 😘
*Soyayya* 💘
Ku kasance tare dani a cikin tafiyar Billy pinky💞 duk a wannan k'ayataccen littafin me taken *RAYUWATA*
Yah Allah inarokon ka da sunayen ka kyawawa masu tsarki, kabani ikon rubata abinda zai amfaneni nida al'umma. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar dani da al'ummar MANZO ALLAH (s.a.w) .Yanda muka fara lafiya Allah yasa mu kammala cikin farin ciki
🌹 SADAUKARWA ga 🌹
_Oum Maryam
_Aunty safiyya.
_Hajara
_Habibah
BOOK 1
EPISODE 🌷 { 1 } 🌷
Sanye take cikin hijabi, light blue fuskarta sanye da nik'ab, idanunta dara_dara ga gashin idanunta zara_zara, ta cikin nik'ab dinta na hango dogon hancinta hannun ta rungume da alQur'ani kafarta sanye da safa da alama daga islamiya tadawo cikin natsuwa take tafiya bata wani yi tafiya me nisa ba ta karaso kofar gidan mai black gate ta tura kanta ciki tare dayin sallama cikin zazzakar muryarta. Tsakar gidan bakowa tsitt yake haka takara sallama akaro nabiyu amah shiru parlour tashiga bakinta dauke da sallama amma bakowa a parlour bata damu ba kasancewar tasan yazun haka sunacan suna bacci suna jiranta tadawo ta daura girkin. Cikin natsuwarta ta karasa bedroom din nanma bakinta dauke da sallama amma matashiyar buduwar dake kwance tana danna waya bata dago ta kalle taba balle ta amsa mata sallamar . Saida ta karasa tsakiyar bedroom din sannan tacire nik'ab dinta tare dazame Hijabin nata ta ninke tasaka a wardrobe Masha ALLAH shine abinda na furta gaskiya Allah yayi baiwa anan . Saidai ace Masha Allah Dan gaskiya kyakyawace ajin farko saidai kuma black bauty ce baza a kirata doguwaba bakuma za'a kirata gajera ba tsaka_tsaki ga pinkish lips dinta gaskiya idan nacemaku zan lissafomuku kyanta za aja lokaci dan haka nabaku dama kowa ya kiyastota dakansa.
Cikin zakin muryarta tace '' anty Walida barka da hutawa '' .
'' Barka '' abin datace kenan tacigaba da chat dinta itama batare datace komaiba tafita adakin madafa tashiga ilaikuwa ga wanke_wanke nan tun na safe amma ba aiba saboda suna jiran baiwarsu tadawo tayi ahaka cikin natsuwa tayi tagama tafara kokarin dora tukunya komai tatuna oho nagadai tafita daga ciki tanifi bedroom din Mom dattijuwar ce dabazata wuce shekara 47year zaune tana waya amma tana shigowa kuwq ta yanke wayar annurin dake fuskarta gabadaya yabace ko gaishe ta dayake bata amsaba tafara fadin '' lafiya kizo kitsayamin aka ? " tana mai kafeta da ido
'' Dqma Mom zan tambayi me za'a dafane ? ''
Saida ta kalleta sama da kasa kana tace '' wai sai yanzu kika dawo daga wannan kaddararriyar makarantar ? ''
Tadaga kanta alamun amawa.
'' Tindazu muna jin yunwa sai yanzu kikaga damar dawowa kenan? ''
'' Ae yau Moma asabarne ba'atashi dawurine shiyasa ''.
'' Karki damu zancire ki a makarantar ne dan bazamu iya zama da yunwaba sai Walida cema ta jika mana garin kwaki musha dan haka dolle ki hakura da ita '' .
'' Dan Allah mom kiyi hakuri wallahi inason maranta ta ''.
Mttsss taja tsaki kana tace da ita a cikin isah da gadara '' keni jeki jollop zaki girka mana dan yunwa nakeji bansan surutun tsiya ''.
Haka ta juya ta tafi tana zuwa ta daura girkin ta kafin tagama ta gyara gurin yayi fes kamar ba wanda tashigo ta ganshi a haukace ba, wai daga jik'a garin kwaki shine akama guri haka Allah yashirya shine abinda kawai ta fada tana mai cigaba da aikinta .Bata dauki wani lokaci maiyawa takammala ta juye a kula sannan ta je tacema Mom takarasa tana wucewa daki bathroom tanshiga tayi wanka tare da daura alwala mafrib dan ta gabato .Koda ta fito bata ga Waleeda ba dan haka tasa rida doguwa mai dogon hannu mai taushi koda ta fito parlour Mom ce kawai ke cin abicin Walida kuwa ta cika tayi fam . Ta karaso domin itama ta zauna taci abincin dan yunwa takeji yau koh breakfast bataiba .
'' ke '' naji an furta cikin isah da gadara. Ban zata koh
Waye dani ake ba shi yasa ban dago ba. Amma a zayirin gaskiya ina sane cewar dani take shiyasa ban dago ba saida Mom tace '' wai safiyya ba dake ake magana bane? ''
'' Na'am Mom '' na furta yayinda nake dago da kaina.
'' Muna fuka kitashi k idafamin shinkafa dan na gaji da cin taliyarnan '', a cewar Walida ina niyar nayi magana Mom ta watsamin wani kallo ban ce komaiba natashi nafita nafara dafa mata ga yunwa na cina saida nagama dafa mata sannan naci tawa lokacin ma ta huce. Bayan nagama aka Kira mafrib na tashi domin na gabatar da sallah, koda na idar nayi azkhar. Walida Bata shigoba bale ince tayi sallah karatun alQur'ani nafara cikin natsuwa kowanne harafi ina bashi hakkinshi har akakira isha'i sannan natashi na gabatar da ita na dade ban tashi ba har Walidah ta dawo da alama waya take sanan nafita na yiwa Mom saida safe duk da bata kulaniba nadawona nayi kwaciya ta bayan da na karanto addu'o'in kwaciya barci........
My fans Dan Allah kuyi hakuri muhadu a page 2 karkumanta Kuna tare Dani Billy pinky💞
https://www.facebook.com/profile.php?id=61567646455725
💗 RAYUWATA 💗
©️ Bilkeesu .S. Aliyu
☀NAZARI WRITERS ASSOCIATION☀
Kyawawan Nazari kafin rubutu na damfare da bin 'ka'idojin rubutu. Nazari kafin rubutu kan kayata duniyar Adabin hausa.
🖊️🖊️ Alkalami yafi takobi ⚔️⚔️
EPISODE : 🌷 { 2&3 } 🌷
▪ Washe gari, 5:00 am
Ta tashi tare da shiga bathroom, bata wani dau dogon lokaciba ta fito fuskar ta, ta jike da ruwa, da alama alwala tayi. Sallaya ta d'ako ta kabbara sallah ta dau dogon lokaci kafin ta fara rera karatun alQur'ani cikin zazzakar muryarta mai dadin sauraro tadau tsahon lokaci kafin ta aje alQur'ani tafara Azkhar kana tamike tare da ninke sallayar kana ta karasa bakin gado .
'' Anty Waleeda kitashi ki sallah '', amma ko motsi batai ba . Takara Kai hannun ta da nifi Kara tashinta ta bige mata hannun tareda fad'in '' ke dan Allah tashi ki bani guri mutum na bacci kin ishi mututane in tashi in sallah to bazan ba '' . Mtss taja tsaki tare da jan bargo ta rife har kanta batare da tace komai ba ta tashi ta fita ta fara aikin gidan. Parlour ta fara gyarawa tareda share wa, sannan tayi mopping ta share tsakar gidan, wanki bayi tayi sanan ta dauraye kwanikan jiya kana ta daura breakfast kafin lokacin gari yayi haske bata dau lokaci ba ta gama breakfast ta shirya komai a parlour tana shirin shiga daki ta ji an kira sunan ta "Safiyya" Mom ce dake fitowa daga part d'in nata .
"Na'am mom" ta amsa mata tana mai tsuguna wa ta gaishe ta.
'' Lafiya kin gama aikin neh? ''
"Eh mom na gama '' Ta fad'a cikeda natsuwa .
'' Tom yau ba zaki barmu da yunwa ba mita jira har sai kin dawo dan haka ki soya mana miya idan yaso koni ce na dafa taliya tunda Waleeda ba girki ta iya ba '' a cewar Mom Kenan.
'' Amma Mom lokaci zai cika kurewa kuma zayi lati ''.
'' Iyye ina magana kina fadin lokaci zaicika kure wa, to wallahi in kiyi wasa makarantar ma sae kin barta inga ta tsiya '' . Mttsss ta ja wani uaban tsaki kana ta dora da fad'in '' dan Allah bace min da gani ''.
Batace komai ba ta koma ta daura miya saida ta idar kana cikin sauri ta wanke kayan da tasan ta bata . Wucewa tayi bedroom shaf_shaf tashiga bathroom tai wanka ta fito daure da towel tana goge gashin kanta "Masha Allah" na furta ganin gashin ta har gadan bayan ta gaskiya tanada gashi mai cika da tsawo sae dai ace tabarakallah .Kaya ta saka ta shafa wani lotion mai kamshi amma na karamin kud'i ne, fauda ta saha iatama sama_sama sai kwalli da lips gloos kana ta fito parlour domin yin breakfas har a lokacin ba kowa a parlour. Tana kamallawa ta sake nufar bedroom , hijabin islamiyar ta ta dauko ta daura nik'ab a sama bayan da ta saka hijabe d'in tare da sa safa ta fiche daga gidan bayan da tayiwa Mom sallama . Batare da ko kallon arziki ta samu daga Mom balle tayi tsamanin zata amsa mata tayi tafiyan ta zuwa islamiya.
Du da faruwar wannan abun, sam ban damu ba ina fitowa naci karo da baby '' anty Safiyya ina zaki ? ''.
Da murmushi kwance a fuska ta nace '' zan tafi makaranta ne kinji my baby ? ''.
'' Tom anty sae kin dawo '' yarinyar ta fad'a tana mai daga min hannu . Daga mata nayi ina mai karisa fita daga gidan . Kai tsaye makaranta na nufa dan sanda naje ma har anfara amsar hadda, zama nayi a kujera ta na tarar da Rumaisa kawata kusa da kujerar da nake zaune . Gaisawa mukayi tana mai cewar ''kai sopsy yau fa gaskiya kin makara da yawa ''.
'' Uuhmm kedai bari kawai sis koh jiya dana fito da wuri koh breakfast banyiba ''.
'' Tab kina kokari wallahi sis ''.
Murmushi kawai nayi '' To yazan yi ?, ae sai haku na fad'a ina mai mekewa Naje nabada haddah muka cigaba da bita kasan cewar munyi sauka mai_maci ne mukeyi a yanzun . Koda aka tashi gida na nufa kaitsaye. Ba kamar jiyaba yau parlour da mutane, Mom ce sae 'ya'yanta suna fira cikin nishadi. Da sallama nashiga suka amsa ciki_ciki . Baby ce tazo da gudu ta rungume ni '' anty sannu da zuwa dama ina so zaki min home work anty Waleeda taki min ''.
Nashafa kanta nace '' tom my baby bari naje ciki nayi wanka sai na fito koh ''.
'' Yes antynah sai kin fito ''.
Mumushi namata ina mai shigewa bedroom, wanka nayi nafito parlour dan in sami abin da zan sawa cikina .Kitchen nashiga amma ba komai da alama sun cinye taliyar da tace zatay daga dan haka taliyar yara na dafa shaf_shaf naci a kitchen din na wanke kwanikan dan wallahi yau ba wacce. zan ma girki ehe sae dai abin duk abinda zai faru ya faru ba ruwana . Ina fitowa baby tace '' anty gashi ''. Karba nayi na tayata yin home work d'in kana na wuce dakinmu. Wayyata na dauko na bude dan harna manta inada waya ma. Call ne ya shigo wayar Yaya Ansar sunan dake yawo a screen din wayar kenan . Cikin zumudi ta dauka murmushi kwance a fuskarta .
'' Wa alaikas salm yayanah '' na amsa sallamar dayayimun.
"Na'am my little sis yakike? ''.
'' Lafiya lau yayanah yasu mom din? duk suna lafiya, Yaya yaushe zaka dawo'' ta fad'a a shagwabe .
'' Kai little har kin kosa nadawo ne? ''.
'' Yaya gaba daya na kosa ka dawo gidan duk ba dadi ''.
'' Ummh yanzu kina inane? ''.
'' Ina a daki ne ''.
'' Har kin kamalla aikin ki ne halla ? Kici gaba da hakuri little kisan dai Mom tamkar uwa take agurin mu, dan haka kikara hakuri my little sis ''.
''.Tom yayah ae inayi ''.
'' Nasani amma so nake ki kara akan wandda kikeyi komai a "RAYUWA" mai wucewa ne kinji ''.
'' Tom yayanah insha Allah ''.
'' Kinje islamiya ne a yau ? ''
'' Naje Mom tace ma saita cireni a makarantar bayan kuma ba ita ta sakani a islamiyar ba ''. Ta karashe zancen ta kamar zatayi kuka.
'' Kirabu